Showing 144001 words to 147000 words out of 260999 words

Chapter 49 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

mata ido Waya Natasha tayi Boss Man, ko kina nufin har kin manta da shi? ta faWa tana duban hanya.

Yamutsa fuska Ummin america tayi Allah ya raba ni da ala?a?ai, bana fata wani abu ya ?ara hada ni dashi, jarababbe kawai

Natasha na dariya tace haba ummi, mutumin fa ya mutu akan ?aunarki, nayi ?o?arin ganin na maye gurbinki acikin zuciyarshi sai dai Ya nuna mun cewa ke kaWai ce za ki Iya sarrafa shi yadda ki ke so, kuma yana nan akan bakansa na cewa ba zai ta6a barinki ba har abada ke tashi ce

Mood din fuskarta ne ya canza zuwa 6acin rai.
 Natasha, I don t even want to hear his name, bawai don bana son shi ba, kawai ni bana son mutumin da zai nuna ?arfin iko akaina, kamar wani ubana, yaushe rabona da shi tun lokacin dana Wauki cikinsa na zubar ba tare da saninshi ba, muka samu sa6ani dashi ban ?ara ganin ?eyarsa ba, Kin san fa mutumin akwai zuciya ga girman kai, nasan zai neme ni ne tun da baya gajiya dani

Natasha tace kina wasa da damarki ummi, da Ace nice na samu matsayin da kika samu acikin zuciyarshi, bana tunanin zan iya bijire mashi, biyayya zanyi mashi sau da ?afa 

Ta6e baki ummi tayi nima ba gudunshi nake yi ba, Ciki ke bana so, saboda zai 6ata min shape din jikina, kuma ni tun kafin mu ?ulla ala?a dashi sai da na faWa mashi sharuWWana, nace mashi bana ra ayin yin aure kuma bana son ciki, ban damuwa ba idan zamu shekara munayin sharholiyarmu da shi in dai zaiyi min biyayya

Murmushin gefe fuska Natasha tasaki Ummi kenan, Yanzu mu ajiye zacenshi a gefe, ni dai shawarar da zan baki shine idan kika koma ?asarku, kada ki kuskura ki kula ?as?antattun mutanan da su ka yi silar barin ki Nigeria, bana so ki nuna kin san su, inaso ki nuna masu cewa kwandon shara yafi su mahimmanci a awurin ki

Maganar Natasha ta ta6a zuciyarta ummi, tuni ta Waure fuskarta, tunawa da wani abu da ya faru a rayuwarta.

 Please, stop talking about them, i don t wanna hear it rai a6ace ta furta hakan, jinjina kai Natasha tayi shikenan nadaina mutuniyar saboda bana son 6acin ranki mood din fuskar Ummi Ya canza sosai, abubuwan da suka faru arayuwarta take tariyowa, masu daWi da marasa daWi.

 Mutum biyu masu mahimmanci arayuwata, ina fata na sake haWuwa da su, Yarinyar dana bari inason na ganta duk da bani da tabbacin tana araye ko ta mutu, ba dan bana son ta ba, na tafi na barta, tun tana jaririya, shi kaWai ne danasanin da zanyi arayuwata

A cikin zuciyarta ta furta hakan ba tare da sautin muryarta ya fita ba, tuni idanuwanta suka cicciko tab da ?walla. Afakaice ta zaro hanky daga hand bag dinta ta share ?wallar idonta.

Sun jima suna tattaunawa da ?awarta Natasha, A lokaci Waya motar su, da motocin jami an da suka Wauko su Angel suka ?araso katafaren Airport din, slowly Ummi ta zuge glass din motar don ta samu damar ?are ma Yaran kallo ita da Natasha, kafin fitowarsu daga mota, suka soma Jin jiniyar motar sojoji, kusan guda uku suka nufi wurin da sukayi parking din nasu motocin, bayan sunyi parking din motocinsu, Commender ya fito daga motarshi, tare da Major da captain da sauran sojojin da su ka zo da su. kowan nan su yana sanye cikin kakinsa, ga dukkan alamu sunzo Yi masu bankwana ne.

Jami in dake tu?a motarsu Angel ne ya fito da sauri Ya zagaya Ya buWe masu kofa, Angel ce ta fito hannunta ru?e dana Danish, duk da face mask din dake akan fuskokinsu hakan bai 6oye tsantsar kyawun idanuwansu ba, Hankalin Natasha ba ?aramin tashi yai ba lokacin da idanuwanta su ka yi tozli da kyakkyawar surar Danish, tun kan ummi ta faWa mata wanene shi tayi saurin cewa kamar Yaron da kika faWa min ko ? Ummi na murmushin sha?iyanci tace may be shine, ai ni fuskar shi na gani a hoto, naga wannan ya sanya face mask, amma dai ina da tabbacin shi Win ne, masha Allah ?aramin mutum da babbar harka, Ni ma ban ta6a ganin shi ido da ido ba sai yau, Nayi tsammanin jin shi yafi ganinshi, ashe ganin shi yafi jinshi, lashe baki Natasha tayi da harshenta kamar wata mayya tace Ya tafi da imanina, Ya za ai ummi? Anya bazan biyo ku Nigeria ba? Kinga ke sai ki dinga rainon su ni kuma Ina biyan bu?atata da su

Ummi tace bismillah zaki Iya bin mu amma ki sani komai ya faru dake kada ki nemi ni, Chief owais sai yayi jajjagen namanki, idan kika ta6a mashi ?a ?anshi

Har ta ?arasa maganar, Natasha batasan me take cewa ba, idonta akan Danish, Bayan fitowarshi da Angel, Batul ta fito, Sauran Jami an suka fito tare da bubbuWe masu motocin. Gabriel ya fito tare da Haris da hannah, Naufal ya fito da parveen da javeed, dr laura ta fito daga motarta, ta bude masu Azeeza, suka fito suma, Nurses din dake atare da su da dr mark da brown kowan nan su Ya fito waje. Prisoners sun baza ido suna kallon inda suke, tun kafin su shiga cikin Airport din.

Ummi America da natasha sun tsaresu da ido
 Yaran Fa akwai kyau, Yanzu ummi har kina Iya zama wuri Waya dasu ba tare da kin rage zafi ba ? Shiru ummi tayi mata ba tare data tanka mata ba, hankalinta na akan prisoners, ta ?ura masu ido, hakanan ta dinga jin bugun zuciyarta na ?aruwa, ba tare da sanin dalilin daya haifar mata da hakan ba, jikinta yai wani irin sanyi, Waya bayan Waya take bin su da kallo, yayin da suke gaisawa da sojojin cikin raha suke amsa masu.

Sai daga bisani Ummin America ta buWe murfin motarsu, atare suka fito ita da Natasha, Hankalin su Angel Ya dawo kansu, Kallo Waya tayi mata sai da gabanta ya faWi, kuma nan take ta gane wacece ita, tun da taga uban hips dinta da boobs dinta da suka cika ?irjinta, ranta ya bata cewar tabbas itace matar da aka dam?a ma amanarsu, tun da ta fito hankalin kowa ya dawo kanta, taku Waya girgiza goma, wankan suit din jikinta ya tafi da imanin kowa dake awurin.

Kallon kallo suka soma bin juna da shi, tsakanin prisoners da ummin america, da kuma dr. Laura, da jami an isod, da sojojin da suka halarta, sama sama suka soma gaisawa da ita, Dr laura ta haWe rai kamar yadda itama ummin american ta Waure mata fuska, bayan sun gama gaisawa da juna, jami an suka buWe boot na motocin da suka zo da su suka Wauko suitcases dinsu tare da jakunkunan kayansu, gaba Wayansu suka Wunguma zuwa cikin departure gate din Airport, ta inda suka samu sau?i, Jirgin da zai Wauke su privet jet ne mallakin Jami an isod, babu bu?atar jira ko wasu shaidu, An riga An shirya masu komai su kawai ake jira domin tafiya, duk inda suka bi darewa akeyi abasu hanya saboda sojojin dake atare da su, prisoners sai ?an kalle kalle suke Yi, sunga wuri mai kyan gaske ga mutane launi daban daban suna ta yin zarya acikin wurin, Yankin da jirginsu zai tashi fili ne na musamman aka ware shi domin tashi da safkar jirage masu zaman kansu.

Tan?amemen Privet jet ne Aka tanadar masu, Mallakin Chief of isod, Aljannar duniyace ?ar ubansu a wurin haWuwa, tun daga wajen jirgin zaka fara cin karo da sunan ISOD da aka rubuta da manyan haruffa ajikinsa.

Idan ka shiga cikin jirgin kamar ka shiga haWaWWen villa ne saboda haWuwar kayan alatun dake acikin sa, akwai Falour wanda yaji hadaddun leather seats masu numfashi, tare da ?ayatattun tables, ga fine carpet shimfiWe saman floor na jirgin, bayan shi akwai large flat-screen TV, ga Conference table domin yin meeting, a kewaye yake da kujeru, ga kitchen da bathroom, and privet bedroom da kuma dining area, Komai fa akwai shi acikin jirgin babu ce kaWai ke babu, ta ko ina sanyin A.c ka ratsa cikinsa.

Bayan sun sauka abakin jirgin, Hankalin su Batul Ya?i kwanciya tun da su ka yi arba da jibgegen jirgin dake agabansu, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da abu kamar wannan ba, duk sun bi sun rude, sai faman zazzare idanuwa suke yi, badan Angel na atare da su ba, da tuni wasu daga cikinsu sun zauce saboda tsabar kiWima, bankwana suka somayi da sojojin da suka rako su, Dr laura hada hawayenta na rabuwa da su, Waya bayan Waya saida ta rungume su, tana yi masu fatan alkhairi, Jemimah da Azeeza sunji Wacin rabuwa da ita, sun sha kuka hawaye duk Ya 6ata fuskokinsu, lallashinsu ta dinga yi tana kwantar masu da hankali, tace kada su damu zata iya zuwa har Nigeria tagan su, babu wanda bai ji kewar rabuwa da su ba, Dr mark da brown suma sun matse ?wallarsu, hatta nurse jessica da Rebecce sai da su kayi kukan rabuwa da su, musamman masoyiya Angel kowa ya saba da ita, suna sonta sosai, ummin america tuni tayi sallama da ?awarta Natasha, bayan sun gama ?an rungume rungume, sojojin da ke atare dasu sunyi masu fatan sauka lafiya, lokacin da zasu hau matakalar jirgin da?yar suke taka staircases din, har dai suka samu damar shiga ciki, al ajabi ya kama su ganin haWuwar jirgin, kowan nan su Ya samu wuri saman tausasan leather seats din suka zazzauna, tun da suka shiga jirgin ummin america bata tanka masu ba, sai dai kallon kallon da suke Yi a tsakanin su, ita dai Angel damuwarta Danish Winta, Ya ?an?ameta, babu alamun lafiya atattare da shi, jikin shi yai zafi rau.??

Lokacin da jirgin Ya soma tafiya Yana bin hanya kafin Ya Waga sama, Hankalinsu Azeeza ba ?aramin tashi yai ba, jami an Sunyi ?o?arin kwantar masu da hankali, ganin yadda su ka ruWe jikin su ya hau yin kerma, sun fahimci mugun tsoro ne da su, Angel ce ta tunasar dasu akan suyi addu a, aiko atare suka hada baki suna karanta addu o in data koya masu.

Cikin ?an?anin lokacin jirgin Ya Waga sama Ya keta hazo can cikin sararin samaniya, Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke kamar an yaye masu tsoron da suke Ji, hankalin kowan nan su ya kwanta tun da aka kunna masu kallo a tv, ban da na Angel, Yanayin fuskarta ya canza, sakamakon maganganun da taji Danish yana furta mata acikin kunnanta, muryarshi arauna ce yake fadin baya son mutane, haushin su yake ji, yana ji kamar ya kashe su, jinin su yake sha ?an hanjin cikin ta ba ?aramin kaWawa su ka yi ba, sai faman zazzare ido take yi, babu wanda ya lura da halin da take a ciki, sau?in ma acikin kunne yake yi mata raWa, sautin muryar baya fita, kuma akwai tazara tsakanin seats dinsu dana sauran ?an uwansu, Waya daga cikin jami an isod ne Ya Wauko mashi eye mask ya mi?a ma Angel don ta sanya mashi a tunanin shi hasken jirgin ke bayaso shiyasa ya cusa kanshi saman kafadar Angel may be ko yana son ya runtsa ne.

Tun da ta sanya mashi eye mask taji yayi shiru ya daina magana alamar bacci ya dauke shi, a ?alla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ?irga, addu o i taci gaba da karanto mashi tana tottofa mashi saman sumar kanshi, fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane zai faru da shi, gashi ta manta bata nemi takardar dake Wauke da address din gidansu salsabeel, duk da bata tunanin ma ko sunje zasu samu abunda suke so.


A KishingiWe yake saman shimfiWeWan full-sized bed dinsa dake acikin privet room na jirgin, ya Waura kansa saman tattausan pillow, Shin wanene wannan kyakkyawan matashin saurayin? A jin farko afagen kyau da ?asaita, Namijin duniya, A halitta madai-dai ci ne, mai wani irin faffaWan ?irji a buWe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, Vest din jikinsa tayi tighting dinsa, kana iya ganin zanen ?irjinsa, Ko Wan wrestling bazai nuna mashi ?irar ?arfi ba, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, mutun ne mai ji da ?arfi, Allah yabasa kyawawan idanuwa farare tass ga su so sexy, masu Wauke da launin ?wayar ido reddish brown, har shining suke yi, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows Winsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haWe da juna saboda Yana da yalwatacciyar suma, lallausar sumar kanshi tasha gyara anyi mashi Military haircut yayi bala en yi mashi kyau, abun da yafi komai jan hankali a jikin shi tsadaddiyar launin fatar shi, chocolate colour, har wani glowing take yi, hutu ya zauna mashi, jikinshi ya wanku da dollar, duk inda namiji yakai to ya zarce nan, komai nashi na kece raini ne ba wasa a tattare dashi, kuma burin kowace ?a mace ne shi, a 6angaren wadatar arziki kuwa basai an faWa maka ba, su kan su kuWin raina kansu suke yi agabanshi, duk da tarin dukiyarsa baida girman girka, mutum ne shi da bai Wauki duniya da zafi ba, Allah ya bashi kaifin basira, Yana da ilmin addini dana zamani, ta ko ina Allah ya hore mashi, yana matu?ar jin ?an talaka, Yana da tausayi ga son taimako, shi sam abun hannunshi bai rufe mashi ido ba, kyawawan halayansa da Wabi unsa abun burgewa ne, shiyasa ya fita daban ko acikin jikokin family Winsu, ya shahara aduniya sosai, babu inda ba a sanshi ba, mutane basa gajiya da yabon shi, burin kowane ya yi tozali da shi, babban abunda ya tsana a duniyar nan shi ne yaga mugun mutun mara imani acikin mutane Yana zalunci, In kuwa ya dam?i irin su, mai ?watar su sai Allah, shiyasa mutane masu irin halin suke mugun jin shakkar shi, dai dai da sunan shi aka fada sai gabansu ya fadi, don baya yi masu da kyau, ni nasan bazan Iya misalta ?asaitaccen Namijin nan ba, KaWan ne na Iya faWa maku sauran ku biyo ni acikin labarin, Yanzu ne wasan Ya fara.

Tun da ya Waura lumsassun idanuwanshi akan tsadaddar laptop din gabanshi ?irar Apple macbook pro bai ?yafta idon shi ba, Hannun shi na dama na sanye da wrist watch ?irar Rolex submariner haWaWWar gaske, ya tattara dukkan natsuwar shi akan abun da yake kallo, duk wani motsin prisoners dake acikin jirgin yana kallon su ta cikin laptop dinsa, ?ayataccen table din dake agaban gadon shi Wauke ya ke da Mug na cofee ga fresh fruit da aka ajiye mashi, daga gefen shi saman mattress, suit jacket dinsa ce daya cire launin Navy blue, trouser din ta ne a jikin shi, hankali a kwance bai da wata damuwa.

Awanni da suka Wauka acikin jirgin ba ?aramin daWi suka ji ba, saboda an gatanta su, sunci abinci har sau biyu, sun yi bacci sun tashi, komai suke so yi masu ake yi, Danish ne kaWai baici komai ba, tun da bacci ya Wauke shi bai farka ba.


*=؋?ABBAN SOJOJI=؋?*
*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*


*Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ?addara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature*

*
'? Mu haWu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*_


~Middle step~

3,F 'DB/1d'>?
?d'


_THE PRISONERS E26=?%?=ث?_



*Daga al?alamin Boss Bature*



Confusion of the heart=ث?



Tun da Aneelerh ta turawa numbar sa?o har yau ba a tuntu6eta ba, abun ya dame ta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daWi, kullum ne sai ta ?ara jaraba kiran layin ko za aci sa a mamallakin wayar ya Waga amma wani iko na Allah a kashe take samun layin duk ta damu da son jin wanene.


Fitowa ta yi daga cikin Wakinta hannunta ru?e da wayarta, Wakin zahra ta nufa da niyar ta faWa mata halin da take ciki wata kil ta bata shawara akan abun da ke damunta.

A bakin ?ofar Wakin ta fara yin sallama, shiru ba a amsa mata ba, kusan sau uku tana kwaWa sallama zahra bata amsa ba, tunani ta soma yi ko dai ta koma wurin aiki ne? Ko kuwa baccin lalacin da ta saba yi ne, wata ?il kuma wanka ta shiga.

Haura ?afa ta yi ta shiga Wakin zahra, tun abakin ?ofar room din ta fara cin karo da takalmanta da jakarta da mayafin ta gaba Waya ta watso su saman floor, nan take hankalin Aneelerh ya tashi da sauri ta Wago da ido tana kallon gadonta, duvet dinta da pillow dinta duk ta watso su ?asa, Komai na Wakin ta tarwatsa shi.

Aneelerh ta fahimci babu lafiya wani abu ya faru da ita, Zahra da ta sani Mai tsafta dagangan dai bazata ta6a barin Wakinta a hargitse ba.

Cikin tashin hankali ta soma ?wala mata kira Zahra! zahra!! shiru babu amsa, ranta ne Ya bata cewar ko dai bata agidan ne ko kuma ta shiga Wakin ummi, da sauri Aneelerh ta fuce daga Wakin, Har zata gifta ta falo ta wutsiyar ido ta hango Mami da ummi zaune suna fira, juyawa tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login