Showing 252001 words to 255000 words out of 260999 words

Chapter 85 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

da yake da turai bata ta6a gigin katse shi yana cikin yin magana ba sai yau, hakan ya ?ara tabbatar mashi da cewa ranta yakai ma?ura a wurin 6aci,
 Mommy, yaya zaki, Ibad dr jazz ne ya ambaci sunayensu, a hanzarce suka kai dubansu gare shi.

 Zanyi maku bayanin komai
 A a jazz shi nake so yayi min bayani, gaba daya a raunace kake, ka daina yin magana zaka fama ciwonka ta faWa tare da kallon sir mubarak wanda yayi shiru yana kallon fuskarta...
 Meyasa ka tsareni da ido? Ba zaka yi min bayani ba ?
Bai tanka mata ba har saida ya samu wuri saman sofa dake fuskantar su, Ya zauna, tukunna ya samu natsuwar yin masu bayanin komai daya faru.......
A ?arshe yace bana bu?atar wani yaji abun nan saboda aikin sirri ne sukeyi, basu bu?atar kowa ya sani, Na faWa maku ne don na wanke kaina daga zargin da zakuyi min na halin da na jefa jazz
Cikin sanyin murya turai tace am sorry dear, nayi maka tsawa bisa rashin sani, kayi hakuri dan Allah, hankalina ne ba akwance ba
 Na fahimce ki, atakaice ya furta hakan
Mayar da duban ta tayi akan jazz dan Allah nan gaba kada ka ?arayin wannan gangancin, duk wani abu da zakayi ka sanar da mahaifinka koda ace ni bazaka sanar min ba, amsa mata yayi da toh,
Kafin ta juyo da dubanta kan sir mubarak Babe, babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin yi maka godiya saboda irin kulawar da kake ba jazz..... kafin ta ?are maganar sir mubarak yai hanzarin katseta Kada na sake jin kinyi min godiya saboda nayiwa jazz abu, kinsan banaso cikin sanyin murya tace nadaina in sha Allah
 Daddy, sannu da dawowa, nayi missing dinka sosai, meyasa jiya baka faWamin halin da kake aciki ba ai da nazo asibitin na tayaka jinya zaki ne yayi maganar yayin da yake ?o?arin zama gefen jazz
Murmushi sir mubarak ya sakar mashi sanyin idaniyata, ina fata na same ku lafiya ?
Mayar mashi da martanin murmushin Zaki yayi lafiyalou, sai dai jiya dukkanmu bamu runtsa ba saboda rashin ganinku da bamuyi ba
Sir mubarak yace shiyasa naga idanuwanku sun kumbura, ashe bani kadai na kwana azaune ba
Tun da suka fara magana ibad ya haWe ranshi,
 Daddy ni baka ganni bane ? Ya faWa yana duban sir mubarak
Girgiza kai ya Wanyi kafin yace naganka ibad, amma nida kai wanene ya dace ya fara gaishe da wani? Yamutsa fuskarshi yayi ?asa ?asa da murya ya furta sannu da dawowa dad ta6e baki sir mubarak yayi saida na ro?a, bubbuga ?afa ibad yayi
Mom turai tace mu shiga ciki, in taimaka maka kayi wanka zaro ido Ibad yayi haWi da furta Mom wa zaki ma wanka? Jazz ko daddy ? Duk da halin da suke aciki na damuwa hakan bai hanasu yin dariya ba, shi kanshi jazz din saida ya murmusa,
 Daddynku nake magana akai, hannu biyu yasa ya toshe bakinshi, Idan ya kalli sir mubarak sai ya kalli mom turai
Ko kaWan batajin kunyar ?a ?anshi, saboda ita aganinta bawani abu bane donta furta hakan agabansu.
 My son, zamu shiga
Zaki yace okey, zan tafi da jazz Waki, zan taimaka mashi yayi wanka ya canza kayan jikinshi
 Hakan yayi, ta faWa tare da duban Ibad Har yanzu mamaki bai sake shi ba, sai kace baiyi rayuwa a turai ba.
 Akwai kayan abinci dana shirya mana a kitchen, ka shiga ka dauko su a dining zaka jera
Amsa mata yayi da toh, da sauri ya juya ya nufi hanyar kitchen
Mi?ewa zaki yayi tare da ru?o jazz ya mi?ar dashi,
 Allah ya baka lafiya my jazz, amsa mata yayi da ameen, kafin suka nufi Wakin shi
Bayan tafiyarsu ta dubi sir mubarak ina ?ara baka hakuri, kasan ba halina bane
Murmushi yasakar mata kada hakan ya dame ki, ni dama fargabana halin da zaki shiga, but Alhamdulillah tun da kin fahince ni, yanzu bani da sauran damuwa Ya faWa tare da ru?o hannunta suka nufi bedroom dinshi
 Jiya nayi kewarka, idanuwana sunyi maraicin ganinka, dole na ha?ura na rungume pillow amadadinka tayi maganar ayayin da take taimaka mashi wurin cire Rigar jikinshi
DaWaWan kalamanta ba ?aramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba, shiyasa akoda yaushe yake ?ara jin sonta, saboda ?aunar da take nuna mashi, tun farkon auransu bata ta6a barin ya shiga toilet yin wanka shi kadaiba sai idan wani uzirinne mai ?arfi ya hanasu shiga atare, sannan ta hana ya ajiye mata masu aiki agida ba yadda baiyi da ita ba akan baison tanayin aikin wahala amma ta?iya saboda kishinshi da take yi, batason wata ta ?wace mata mijinta,
Atare suka shiga toilet.

*ANEELERHd'
=?%?*

Tun bayan da ta shiga toilet tabar Zahra atsaye tana kallon hoton su, lokacin da ta fito daga wanka bata taras da zahra a dakinta ba, shaf shaf ta shirya kanta cikin shiga ta abaya maroon colour, ta yafa mayafi akanta, fitowa tayi daga dakin a dining room ta taras da su gaba Waya sun hallara kan dining chairs, tun daga kan abie dinta, uncle Wan iya, mami da ummi da kuma mahboob, sai zahra kaf dinsu ne, kowa ya kimtsa domin yin Wa amin, Ana ce take yin serving dinsu tana daga tsaye hannunta ru?e da serving spoon.
Sautin takun takalmantane Yaja hankulansu ga dubanta, fuskarta da fara ta ?arasa cikin girmamawa ta soma gaishe da iyayenta
 Barka da safiya, ina kwananku, kun tashi lafiya
Fuskokinsu asake suka amsa mata.
Mahboob Yace Gm Auntyna, bismillah zoki zauna gefena ya faWa yana nuna mata empty chair din dake gefenshi
Zahra dake kallonsu, murmushi tasaki ganin yadda mahboob Yake yima Aneelerh fadanci abunda bai saba Yi ba.
Bayan Aneelerh ta zauna, Ana ta gaishe da ita, a mutunce ta amsa mata two days bana ganin ki, kin 6oye min sai kace ba gida Waya muke a zaune ba, sai dai idan ni na matsu da son ganinki in shiga kitchen time da kike Yin girki ko ? Sunnar dakai ?asa Ana tayi yanayin fuskarta babu walwala,
Mami tace Ai ba tun yauba na lura halinta ne batasan sakewa cikin mutane, kullum kina ?umshe daga kitchen sai Waki, yakamata kina fitowa falo muna yin fira dake cikin kulawa mami tayi maganar.
Cikin sanyin murya ta furta ay min afwa zan dinga futowa daga yanzu
Mami tace haka nakeson ji, ki daina daukar kanki a matsayin ?ar aiki, damu dake duk abu Wayane awurin Allah, so please adaina kuntata kai adaki murmushi Ana tadan saki har cikin ranta taji dadin maganar mami, zahra tace idan ma bata fitoba ni dakaina zan dinga zuwa dakinta ina takura mata da surutu dariya Ana tasaki,
ummi tace dako ta shiga uku dake, har bacci sai kin hanata saboda zafin Wuminki tur6une fuska zahra tayi, jin abun da ummi tace, harara ummi ta jafa mata lafiya kike kallona, ko nayi maki ?aryane? Kafin zahra tayi magana mahboob yace wallahi ummi gaskiya kika faWi yai maganar yana kokarin tura chips abakin shi Zahra badai Wumiba, kamar aku, inta fara zuba kamar radio mai jini, ga tambayar tsiya kamar tsohuwar ?ar jarida gaba Wayansu suka sanya dariya, ran zahra ya 6aci a ?ule tace hmmm mahboob ai ?warani, wai talla zaiwa audi gori, idan ni surutu gare ni kai fa? Saboda shegen ma?onka ko kuWi zaka ?irga sai ka shiga toilet don kada wani ya gani dariya su ka yi, Abie Da uncle Wan Iya sun kasa kunne suna sauraran su, ganin surutun nasu bame ?arewa bane yasa uncle dan Iya yi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanshi surutun Ya isa haka, kun cika mana kunne, Yakamata ku maida hankalinku akan abun da ku ke ci, kun riga da kunsan babu kyau ana cin abinci ana surutu tunda ya ambaci hakan kowan nan su yaja baki yayi shiru, baka jin sautin komai saina cokulansu kwas kwas tamkar zasu fasa plates din abincinsu, gaba daya hankalin Mahboob dana Aneelerh yana akan Ana, ga dukkan alamu sun fahimci babu lafiya atattare da ita, tun daga kan yadda take faman zazzare idanuwanta.

Cup din lemu Aneelerh ta dauka takai baki tana kur6arshi, bayan ta kammala sha tace ki koma Waki ki zauna ki hutu ta fada tana duban Ana
 Inaso ne ku kammala cin abinci in kwashe kayan, akwai sauran aiki da zanyi wanke wanke da gyaran kitchen idan na kammala sai in huta

Aneelerh tace kada ki damu zanyi maki aikin, just ki tafi Waki ki huta

Harta buWe baki zata kuma yin magana mahboob ya tari numfashinta da cewa Sis Ana, kiyi abunda aunty Aneelerh ta fada maki, nima zan tayata yin aikin
GyaWa kai Ana tayi cikin sanyin murya ta furta nagode madam, Mahboob thank u ta fada tare da juyawa ta nufi bedroom dinta da sauri, hatta yanayin tafiyarta babu natsuwa.
Kallon juna Aneeelerh da mahboob sukayi, da ido tayi mashi nuni dayabi bayan Ana yaji masu meke damunta.
Jinjina mata kai yai alamar toh, mi?ewa yayi daga kan kujerarsa yakai hannu ya yago tissue Ya goge bakinsa.
 mahboob harka kammala cin abincin ? Uncle Wan Iya ne ya jefa mashi tambayar.
 Ban ?oshi ba daddy, ina son zan shiga toilet ne uziri gare ni uncle ya amsa mashi da okey.
Da sauri Ya juya yabar dining area din,
Kasancewar Bedroom dinsa dana ana a 6angare daya suke shiyasa yai ?aryar cewa toilet zai shiga.
Tunkafin mahboob Ya shiga Wakinta ya soma jiyo shesshe?ar kukanta, Hankalinshi yayi mugun tashi, koda ya ru?o handle din ?ofar room din nata adatse ya Ji ta, muryarshi ?asa ?asa Ya ambaci sunanta shiru bata amsa mashi ba, knocking kofar yayi sis ana ki buWe min ?ofa dan Allah, Inason yin magana dake, Aunty Aneelerh ce ta aiko ni
Jin ya ambaci sunan aunty aneelerh yasa tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, jiki na rawa tazo gaban ?ofar ta buWe mashi ita.
Ajiyar zuciya ya sauke yana bin fuskarta da kallo, idanuwanta sun kaWa jawur da su.
Ru?o hannunta yai acikin nashi kamar wani babban mutun Yajata zuwa cikin dakin, Ya kulle ?ofar.
Tare da goya hannayensa saman ?irjinsa Yana kallon fuskarta
Ganin ya tsareta da ido ya?i yin magana ne yasa tace mahboob lafiya kake kallona? Me aunty Aneelerh tace ka fada min
Numfashi yaja kafin ya soma yi mata magana
 Meke damunki? daga ni har aunty Aneelerh mun fahimci bakya jin daWi kamar akwai wani abu dake damunki
Adabarbarce ta furta babu komai mahboob lafiyata qalou....
 Bazai yiwu ba Ana, saboda kafin na shigo Wakin ki na jiyo sautin shesshe?ar kukanki, taya zakice min bakomai? Bayan ga alamu nan nagani akan fuskarki, dan Allah Ana kada ki 6oye mana abunda ke damunki, kinga mun damu dake ni da aunty aneelerh dama sauran mutanan gidan ? A marairaice mahboob yayi mata maganar
Baiwar Allah tayi zuru da ido, komai nata ya canza.
?o?arin danne damuwarta tayi hawayen da suka taru acikin idonta tayi saurin mayar da su.
Can ?asan makoshi sound din muryarta ke fita







 Dagaske nake yi maka mahboob, babu abun da ke damuna, idan ma saboda shesshe?ar kukan da kaji ina yi ne to ka kwantar da hankalinka, sister dina ce janet ta kirani awaya tana fadin halin da take aciki Na rashin kuWin da zatayi amfani dasu, gashi bata da koshin lafiya ko aikin da take zuwa yi a hotel yanzu komai ya ta6ar6are mata, idan ba zaka mantaba na ta6a baka labarin ?an uwana Janet da esther, har na fada maka cewa mu marayune bamu da kowa neman na kanmu muke Yi, A halin yanzu dai nice nake taimaka masu da kuWin da suke siyan abinci da suturar sanyawarsu, nima idan natara kudin albashina ne nake samun wanda nake tura masu.....

tunda tafara magana jikin mahboob yai sanyi, tausayinta duk ya kama shi, har cikin ranshi ya yarda da abunda ta faWa mashi.
 kinsan da abun da ke faruwa da ?an uwanki shine baki faWa mana ba? Meyasa? Meya amfanin zaman taren Ana ?
Fashe mashi tayi da kuka tana fadin bana so ne na takura maku, shiyasa ban fada maku ba
Dafe kai mahboob yayi dahannu Waya ranshi ya 6aci afadace yace kin ban mamaki yanzu ko aunty aneelerh baki Iya faWama damuwarki ita da ta dauke ki tamkar jininta, gaskiya ni baki kyauta min ba Ana, banyi zaton hakan daga gare ki ba, ashe baki daukemu kamar yadda muka dauke ki ba
Ru?o hannayenshi tayi acikin nata yayin da hawaye ke fita akan fuskarta tace mahboob am sorry, idan ranka ya 6aci
Ta6e mata baki yayi Ni zanje na fada ma aunty aneelerh halin da ?ar uwarki take aciki, nasan zata taimaka maki, Nima zanyi kokarin baki wani abu, ki cika, itama zahra zan mata magana, sai mu haWa maki kudin da zaki tura masu ......
Godiya ta soma yi mashi
 Nagode mahboob, naji dadin taimakon da zaka yi min
Sakin fuskarshi yadanyi dan Allah daga yau ki daina sanya damuwa aranki, ni nafiso in ganki cikin kwanciyar hankali, fuskarki da annuri, idan ma wani abu na damunki, please ki run?a sanar dani, zan taimaka maki da abun nake dashi, ga kuma aunty aneelerh itama ki dinga fada mata damuwarki
 Zanyi hakan mahboob nagode da kulawarku agareni
Sai da mahboob ya tabbatar ya sanyata farin ciki, kafin Ya fito daga dakin Ya nufi dining area Koda ya ?arasa bai taras da Aneeleerh da zahra ba, Har sun kammala yin breakfast dinsu, daga can falo Ya hango mami da ummi, zaune suna fira tare da Uncle Wan Iya da abie.
Hatta kayan abincin an kwashe su daga dinning, harya juya zai nufi dakin Aneelerh ta wutsiyar idonshi Ya hango gifcinta a kitchen, da sauri Ya nufi kitchen tun kafin Ya ?arasa ya jiyo muryar zahra ta za?e tana ba Aneelerh labarin shagalin birthday din obie da akayi, maimakon Ya shiga sai ya la6e gefe daya ya kasa kunne Yana sauraronsu.

Babu wanda ya lura dashi acikinsu saboda sun bashi baya.
Aneelerh tana gaban Sink Ta tattara kwanukan da suka 6ata tana wankesu, zahra tana agefenta
 Aunty Aneelerh ina baki labari, wallahi Anyi 6arin dollar a wurin nan, dangin obie sun gaji arzi?i gaba da baya, wai kinga manya manyan mutanan da suka halarta? Attajiran masu kuWi masu manyan mu?amai, kowa kika gani a filin taron da matsayinsa, daga governor sai president, ga sanatoci da ministoci......
Murmushi Aneelerh tasaki tana fadin Gaskiya naji takaici da ban biki munje taron nan ba, da nima na kashe kwarkwatar idanuwana
 Aunty Aneelerh duk yadda zan baki labari bazan iya fada maki kwatankwacin abun da idanuwana suka gane min ba, nifa lokacin da ?a ?an baba obie suka fito tsakiyar fili sunayi mashi li?i Yana taka rawa wallahi ji nayi kamar inyi wuff in shiga filin in tattara kuWin in sa?e a hammata
Tuntsirewa aneelerh tayi da dariya tana duban zahra, hada kwatanta mata yadda zata kwashe kudin ta sa?e ahammata.

Mahboob dake a la6e yana sauraron su dariya ce kumshe abakinshi.

 Ni abun da yafi burge ni, haWuwar ?a ?an baba obie da jikokinsa, da surukansa sun Wauki wanka na mutunci na kece raini kai komai ma sun haWa, waWanda suka fi burgeni kinga prime minister Hateem, da president dinmu Sharafudeen sun iya dattako, komai nasu da aji suke yin shi, matayensu sunfi kowa haduwa gimbiya mujeedat da Hajiya malikat sarauta, sai kuma mutuniyata Hajiya saratu inayin matarnan saboda tana ?aunata mutane suna fadin masifarta ni wallahi bata ta6a yi min koda tsawa ba kamar ?ar cikinta haka take yi min magana.... da farin ciki akan fuskarta tayi maganar.

Aneelerh tace Jinin ku Ya haWune dana juna, Allah yasa ta zama surukarki kinga shikenan kema zaki samu matsugunni a obie estate wani irin ihun farin ciki zahra tasaki hada jujjuya qugu tana fadin Amen Ya Allah, Aunty Aneelerh Allah ya kar6i addu arki

Dariya Aneelerh tasaki yayin da take Wauraye plates din da take wanke wa da ruwan dake fita a faucet.

 Zahra baki faWamin haduwarki da mutumin ba ?
Kwa6e fuska zahra tayi annurin fuskarta ya ragu.

 Bai zo taron ba, duk irin burin dana ci nason ganinshi bai halarta ba, banji dadi ba dama nasan zai yi wuya yaje saboda mutunne shi da baisan hayaniya

 Eyyah zahra najiye maki ba?in ciki, in sha Allah wata rana zaku haWu da shi

Ta6e baki tayi Ni yanzu ba wannan ba auntyna, Inataso in baki labarin Nazli da Yazrin ?a ?an Prime minister da ?anwar Chief Owais hindu, kinga waWannan dana lissafa maki ?arshene su afagen kyau da aji, cikin maza kuwa in ka cire chief owais sai wani Wan uwansu menene ma sunanshi..... ta faWa tana cizon yatsa takasa tuna sunan.

 Namanta, shima a canada yake zaune, mutumin ya iya Waukar wanka, ga kyau da aji bayan shi sai twins sun haWuwa sunyi kyau kamar dollars.

Dariya Aneelerh tayi, jin yadda zahra ta ha?i?ance tana bata labari ko gajiya batayi.
 Yanzu faWa min alherin da sukayi maki naji Wazu kince zaki fada min
Gyara tsayuwa zahra tayi kafin tace
 Kinga da farko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login