Showing 18001 words to 21000 words out of 260999 words

Chapter 7 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

kalle shi a tsoroce Ta furta wanene kai ! Ras Ya ji gaban shi ya faWi, Can kuma sai ya tuna da fuskarshi daya cire, shiyasa bata gane shi ba.

 Salsabeel ne kallon shi ta dinga yi kamar yau ta fara ganin shi, ita kanta ba haka ta yi tsammanin zata ga fuskarshi ba.

 Ga Wan uwan ki nan, Na yi ?o?arin Wiga mashi ruwan zamzam Win sau Waya abakin shi bansani ba ko zai farka acikin hayyacin shi ko kuwa akasin hakan, Ba zan Iya jiran farfaWowarshi ba, hankalina ba akwance yake ba, Ina tsoron wani abu ya sami mahaifiyata Don haka zan tafi wurin ?an uwanki nasan tana atare dasu Angel na ?o?arin buWe ba ki tace mashi ya tafi da ita kada yabarta anan gudun kada Danish ya farka a matsayin Giant ya kasheta sai dai kash kafin tayi maganar Salsabeel tuni ya 6ace ma ganin ta...


A 6angaren Su tsohuwa zafreen kuwa Dambe su ka yi bana wasa ba, Saboda tsabar zalunci sai da ta cire mata kunnuwanta duka biyun ta cinye su, Jini duk ya wanke jikin tsohuwa tamira, duk yadda taso ta ?waci kanta ta kasa saboda rashin ?warin Jikinta, har sai da zafreen ta kwantar da ita ?asa ta dinga buga kanta Ga ?asa tuntuna motsi har ta kai sumewa.

Mahaukaciyar dariya zafreen ta saki ganin ta yi nasara akanta, FaWa da aljani ba riba maganar da zafreen ta furta a yayin da take mi?ewa ta nufi wu?ar da batul ta yi amfani wurin yi mata Illah, Jinin da ke a jikin wu?ar ta lashe kafin ta juyo ta dawo kan tsohuwa Tamira, Ta zu?unna tana Shafa Jikinta da tsinin wu?ar Na jiye maki ba?in Ciki, domin kuwa ayanzu Win nan zar farke Cikin ki, In kwashe ?an hanjin dake a cikin ki In cinye su, idan kin isa Ki kwaci Kanki, ?azamar banza har ni za ki kalli idona Ki gaya mini magana kamar bakisan wacece ni ba..... ta ambaci hakan tana mai sakin murmushi

Yun?urin caka mata wu?ar ta yi ba zato ba tsammani taji an buge kanta da wani abu mai nauyin gaske tamkar dutse kafin ta yi yun?urin juyawa don taga wanene taji an ?ara buga mata shi akanta, nan ta ke kanta ya juye Ta kife ?asa,.

Batul ce a tsaye Tana haki, Hannunta ru?e da sandar Zafreen da ta jefar ?asa, ?arfin sihirin da ke a jikin sandar ne yasa har ta yi nasarar kwaWeta da ita, daddagewa tayi da ?arfi taci gaba da buga mata sandar, Jijiyoyin wuyan ta duk sun furfuto waje saboda tsabar 6acin rai, babu sassauci atattare da ita tun tsohuwa zafreen na motsi har ta kai ga idanuwanta sun Juye, Jefar da sandar Batul ta yi ?asa tare da Waukar wu?ar da zafreen Win ta jefar, Saman ruwan cikinta ta haye ta daddage ta dinga luma mata wu?ar Jini yadin ga ambaliya kamar an kunna fanfo harta saman fuskarta, Kacaca tayi mata sai da ta farketa, A ?arshe dai Baful ta yi nasarar kashe tsohuwa Zafreen ko shura wa ba ta yi ba nan ta ke rai yai halin shi, harta mutu batul bata daina farke jikinta da wu?ar ba, saboda bata acikin hayyacinta, kuka ta ke yi tamkar ana zare ranta.

FarfaWowa tsohuwa Tamira ta yi a hankali ta buWe idanuwanta da suka ru?ida su ka yi jawur dasu, ta wurga su kan Batul da ke a zaune saman Zafreen tana aikin fiWa.

Muryarta na rawa ta ambaci sunanta Ba..tul.. Sai lokacin ta jefar da wu?ar hannunta, jiki na rawa ta sauko daga saman jikin zafreen ta rarrafo Zuwa gaban tsohuwa Tamira.

Fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, taci gaba da yin kuka tana faWin Ta zalunce mu ba mu yi mata laifin komai ba, ta kashe mana ?an uwan mu ta gama da rayuwar mu.....

Hannun tsohuwa na kerma ta Waura shi saman sumar kan Batul da ke a tarwatse da?yar take iya yi mata magana Batul babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin baku ha?uri akan irin jarabtar rayuwar da kuka fuskanta, Ku yi ha?uri kuyi ha?uri Allah yana atare da ku....... Da numfashinta na ?arshe ta ?arasa maganar nan ta ke rai yai halin shi, A matu?ar kiWime Batul ke Fuskarta.........




*Boss Bature
'? Mu haWu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*KURKUKUN ?ADDARA*_



_The Prisoners E4=?%?=ث?_


*Daga al?alamin Hafsat Bature*


~Middle step~



_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty=ؔ?._


wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruWu ruWu kamar zasu fasa fatarta, hatta saman fore head Winta jijiyoyin ne....

A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin Waki, tun suna kuka har sun fidda rai da ?an uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shesshe?ar kukansu har ta kai ga yanzu basu Iya jin komai, A bakin ?ofar Wakin tsohuwa Tamira suka zuzzu?una, Zuciyoyin na tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun ?afe, Haka zalika Naufal da javed babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba ?oshin lafiya ce da shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi, Da?yar ne yai tsawaicin kwana.

A firgice su ka Wago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin Wakin su, jiki na kerma suka mi?e suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba ?aramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin murya ya soma yi masu magana.

 Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima Wan uwan ku ne nasan ba ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni Wa ne ga tsohuwa Tamira ! Duk da basa acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi.

Cikin shesshe?ar kuka Haris yace ?an..uwan mu suna a cikin Wakin tsohuwa Tamira, Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su saboda ta datse ?ofar..... tun kan ya kai ?arshen maganar, Salsabeel Ya wuce da wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ?ofar Nan ta ke ?ofar Ta buWe.

A fujajen Ya faWa Cikin ?akin Hankalin shi a matu?ar tashe Ya ke binsu da kallo Waya bayan Waya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira har izuwa kan su Parveen da ke a sume ?asa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform Win su yashe a kasa da ta Cire masu, Da ?arfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa inna ilaihirraji un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya dun?ule, Tsabar ?unar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa ?irjin shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya haWiyi zuciya ya mutu haka ya ke Ji.

 Ya Allah ka Wauki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne Muryar Batul ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar tsohuwa Zafreen A can gefe Waya, tangal tangal yai kamar zai kife ?asa Da sauri ya tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai Wumin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba wlh da Waya daga cikinsu ba?in ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel Win har su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka fuskanta a wannan ba?ar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta zama mahaukaciyar ?arfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya zu?unna cikin rauni na murya ya furta ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni kaWai a cikin wannan Duniyar mai cike da ruWani ? Da?yar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma magana Batul ta Wago da runannun idanuwanta waWanda suka kaWa jawur dasu ta ?ura su akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi.

 Hada kai Aka kashe min ?an uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine ! Wago wa yai tare da kallonta, Kafin yai yun?urin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman jikinshi tare da dun?ule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko ina tana faWin Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe mana ?an uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne....? bata ?arasa maganar ba kuka Yaci ?arfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka Waukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ?ai, Maganar su ta ?arshe ya soma tariyo acikin kanshi.

 Salsabeel ko bayan ba raina inason yaran nan su ku6uta daga KURKUKUN ?ADDARA! Ka yi min al?awarin nan, ka taimaka masu ko dan su isar da sa?on mu zuwa ga mutanan duniya, Bana so acigaba da aikata zalunci agidan kurkukun nan Ina mai jin takaici da ba?in Cikin ganin yadda ake tauye wa ?ananun yara ha??insu na rayuwa, basu ji ba basu gani ba, An hana su more rayuwar su ta duniya, Ana kashe masu rayuwa a lalatasu A ?as?antar dasu kamar dabbo bi, sannan a kashe su, kuma su mutu a wula?ance! Ka faWa min Laifin me suka aikata da su ka cancanci Yin irin wannan rayuwar? Idan har kana so In yi alfahari da kai a matsayin ka na Jini na to ka cika min burina, Bana so Ganin mutuwa ta yasa zuciyarka ta raunata nafi so a lokacin da ka yi tozali da gawata ka ?ara Jin ?warin gwiwar aiwatar da umarnin da na baka, idan mutuwa ta ris?e ni a gidan kurkukun nan bana so kabar gangar jikina a gidan kurkukun ?addara Ka yi nesa dani kafin ka binne ni......... lokacin da tsohuwa Tamira ta yi mashi maganar sosai ya fashe mata da kuka yana faWin zai yi duk abunda take so amma tadaina maganar zata mutu, ya ta ke so ya yi da rayuwar shi? Bashi da kowa a duniyar nan bayan ita, murmushi ta yi tare da ce mashi Kana da Allah sannan bayan shi ga ?an uwanka nan suma basu da gatan daya wuce Allah da kuma kai, Don haka ka daina tunanin cewa sai da ni zaka Iya aiwatar da komai. Ni dai fatana Ku tarwatsa tarihin kurkukun ?addara, Azzaluman shuwagabannin da suka ?ir?ire shi ku tabbatar tun agidan duniya sun WanWani kuWarsu kafin su koma ga mahaliccin su bana so kubar hukuma ta hukunta su saboda duniyar nan acike take da marasa gaskiya idan kunga ba zasu baku goyan baya ba ku yi amfani da ?arfin ikon da ku ke dashi wurin yi masu mummunan kisan da sai sun yi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan, Kafin su mutu ku Azabtar dasu ta yadda zasu manta da duk wani jin daWi da su ka yi a duniya, Idan har ku ka yi min hakan to zan jin daWi, zan yi kuma alfahari da ku, Bayan ta yi mashi wannan maganar salsabeel yana kuka ya ro?e ta alfarma Waya kafin faruwar duk waWannan abubuwan yace mata yana so ta kar6i musulunci akaro na biyu ta yi imani da Allah, Numfasawa tayi tare da ce mashi Ba zai yiwu ba saboda Allah ba zai ta6a kar6ar tubanta ba ko da ta musulunci saboda Wumbin zunubban da ta aikata sun yi muni sosai, Salsabeel ya yi ?o?arin fahimtar da ita ta hanyar Yi mata nasiha ya nuna mata cewa shi Allah gafurirrahim ne yana son bayinsa waWanda su ka aikata zunubi suka gane kuskuran su kuma su ka tuba zuwa gare shi, da?yar ya samu tsohuwa Tamira ta sake kar6ar shahada maganarsu ta ?arshe data furta mashi Zan je wurin Yaran can inaji araina wani abu yana faru a Wakin su, Kafin na isa wurin su inaso ka yi gaggawar zuwa ?akin Madubin sihiri Ka canza ganin su ta yadda ba zasu fahimci abunda ke faruwa ba......wannan itace magana ta ?arshe da tsohuwa tamira ta furta mashi kafin tabar wurin shi, akan hanyar shi ta zuwa Wakin madubin sihiri Ya ga duk wani abu da ya faru da Angel kun ji yadda akai har yaje gare ta.

Cakumar Batul ya yi da hannun shi tare da janyota ta dawo saman faffaWan ?irjin shi, Rungumeta yayi da hannayenshi tamkar zai mayar da ita cikinshi, Hakan da yayi mata ne yasa ta sassauta kukan nata......

Tsoro da fargaban abunda idanuwansu zasu nuna masu ya hana su shiga Cikin Wakin, Bayin Allah suna atsaitsaye Bakin ?ofar suna sauraron gunjin kukan da Batul ta ke yi.


Idan mu ka koma 6angaren Angel kuwa tun bayan tafiyar Salsabeel tana zaune cikin matsanancin tashin hankali, Da fargaban farfaWowar Danish, Ba zato ba tsammani ta ga yatsun ?afarshi na motsi, A gigice ta yunkura da niyar ta mi?e Sai dai kash ?afarta ta ?i bata haWin kai, Wani irin tsami ta yi mata, a tsananin tsoroce take ja da baya tana kallon shi jikinta nata 6ari

A hankali Ya ware kyawawan idanuwanshi Akan ceilling Win Wakin na tsawon da?i?a talatin kafin Ya yun?ura ya mi?e zaune.... Ta wutsiyar idon shi ya ke hango kamar mutun na motsi, hakan yasa shi yin saurin kai idon shi gare ta, unexpected idanuwan shi su ka sauka acikin nata, da wani irin kallo ya ke bin ta da shi, gani ta ke yi kamar bai dawo hayyacin shi ba.

Ya kasa tantance wacece ita? Saboda daskararren jinin da ke a jikinta, ta koma mashi kamar aljanna, ranta ne ya bata cewar ko dai ya dawo hayyacin shi? Wata ?il saboda munin da ta yi ne yasa bai gane ta ba, Cikin jin shakkar shi muryarta na kerma ta ambaci sunan shi Da..nish..its me ur Angel Ware fareren idanuwan shi yai sosai akan fuskarta, jin muryar da ya daWe yana mararinta, ba zai ta6a mantawa da muryarta ba, A ruWe ya motsa la66ansa tare da furta sunanta Angel? Is that you ? Ita kanta batasan ya akai ta iya mi?ewa ba, Tsabar farin Ciki da gudu ta nufe shi tana ?arasawa gaban shi slowly ta zube saman gwiwowinta tare da faWawa saman faffaWan ?irjinshi sosai ta rungume shi tana ku ka, Bai damu da ?arnin jinin da ke a jikinta ba, sai dai zuciyar shi ta rikice ya shiga ruWanin ganin canzawar da ta yi, Jikinta duk raunuka ta yi muni kamar ba Angel Winsa ba, Tunawa da ?an uwanta da kuma ?urarren lokacin da ke gare su yasa tace mashi Ka tashi mu tafi Danish ka kaini Waki, na bar su Azeeza suna jiran mu shiru bai motsawa ba saboda ya rasa tunanin shi.

Bugun bayan shi ta dinga yi da hannunta Cikin shesshe?ar ku ka ta ke faWa mashi Ya tashi ya Wauke ta suje Waki ?an uwan su na acikin haWari,  da?yar ta samu Danish Ya mi?e Wauke da ita saman faffaWar kafaWar shi, daga ina ya ke a tsaye Ya 6ace bai dura a ko ina ba sai A cikin Wakin su, Tunkan ya sauke ta ta riga zame jikinta, Su Haris da ke a tsaye bakin ?ofar Wakin tsohuwa, a ruWe su ke kallon shi Musamman Gabriel yasha ruwan mamakin ganin Danish da idon shi Garas.

Muryar Angel na rawa ta soma ambaton sunayen su Ha..ris..Mubeen..Naufal..Javed.. ! akace labarin zuciya a tambayi fuska, Tun kan ma su yi mata bayanin abunda ya faru da gudu ta faWa cikin Wakin tsohuwa Tamira da ke a buWe, Idanuwanta Azazzare take kallon ?an uwanta dake kwance ?asa ba numfashi, Wata irin gigitacciyar ?ara ta saki ta fitar hayyaci wadda tayi silar faWowar Danish dasu Haris cikin Wakin sai lokacin su ka ga mummunan abunda tsohuwa zafreen ta aikata ma ?an uwan su. Silar ?arar da Angel ta fasa ne yasa Batul raba jikinta daga na salsabeel fuskarta jaga jaga da hawaye ta Wago idanuwanta, tana yin tozali da Angel da gudu ta nufota tare da faWawa saman ?irjin ta suka ?an?ame juna suna yin kukun zuci, Cikin shesshe?ar kuka Batul ta labarta mata duk abunda ya faru bayan tafiyarta, Tasha kuka kamar ba gobe, ta yi fatan ace dukkan su ne suka mutu hada ita, gaba daya shirin su ya tarwatse taya zasu iya barin kurkuku Bayan ?an uwansu duk sun mutu, Al?awarin data Waukar masu bata samu cika shi ba, Ga danish Win ta ci nasarar dawo dashi sai da kash Ta faru ta ?are, ?addara ta riga fata, Cikin raunatacciyar murya ta wanda ya gama sarewa da rayuwar duniya ta furta Nashiga Uku na bani na lalace! Ya Allah zunubin me muka aikata mu ke fuskantar irin wannan mummunar jarabawar daga gare ka? Idan ba ka son mu, ka Wauki ran mu mu huta, Mun gaji mun gaji Wayyo Allah na Na rasa Azeeza na rasa jemimah na rasa Deeja


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login