Showing 219001 words to 222000 words out of 260999 words

Chapter 74 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ka rage min

Sakin baki yai galala yana dubanshi oh dole sai na baka ragowa na zaka sha Waga mashi gira yai alamar eh.

Babu musu Ya mi?a mashi, don ya san rigimar ibad idan har ba bashi ragowar yai ba to kuwa zasu kwana azaune

Yana sha yana kallon fuskar Zaki, aiku sarkin Wumi.

 Big bro, where s my sister pretty ? You told me she came back to Nigeria. When can we see her? Should we go to their house, or will she come to ours? (Babban yaya Ina sister pretty dina? Ba ka ce min ta dawo Nigeria ba, to yaushe zamu haWu da ita? mu zamuje gidansu ko ita zata zo gidanmu?)

Dafe kanshi yai da hannu Waya Ibad, I don t like making noise, Please go to your room, lie down on your bed, and sleep.

 Shikenan zanje na kwanta amma kafin nan inaso ka fadamin gaskiya, dagaske babu soyayya atsakaninku ?

Ji yake tamkar ya dauki laptop din gefenshi Ya kwalama ibad saman kanshi, Ya takura mashi.

 Ka yi shiru bakace min komai ba !

Mi?ewa zaki yai ya dauki laptop dinsa Ya nufi sashen bedroom dinsu, da sauri Ibad Yabi bayanshi, har yakusa shiga dakin ya Wan dakata da yin tafiyar, in a cool voice ya soma magana

 Ibad, she is married and even has a daughter, And she loves her husband. But there is no love between me and her. taimakon da nayi mata dan Allah nayi shi

Da mamaki Ibad yace babban yaya kana nufin duk tsawon shekarun data dauka a canada a gidanka, da auranta? To ya akai ta gudu tabar mijinta da ?arta? kuma take rayuwa agidanmu harma kuke rungume juna ai ina ganinku idan kuna shan soyayya.... kafin ya ?are maganar, afusace zaki ya waiwayo da niyar ya kwaWa mashi laptop din hannunshi da gudu Ibad Yabar wajen yana dariya.

Guntun tsoki Zaki Yaja, Ya faWa katafaren room dinsa, saman gadonshi ya kwanta, haWi da daura laptop dinshi on his broad chest, hoton fuskarta dake akan wallpaper din laptop nasa ya ?urawa ido yana kallonta, bazai Iya misalta ?aunarta da yake ji ba, yana sonta baya jin zai iya son wata ?a mace aduniyarnan kamar yadda yaso baiwar Allahn nan, sun rayu na tsawon shekaru tamkar ma aurata rana Waya Allah ya ?addara rabuwarsu, yana fatan sake haWuwa da ita, da tunaninta bacci yai awon gaba da shi.


*ANEELERHd'*



Kiran sallar asubar farko, ringing din wayarta ya daki kunnanta, firgigit ta farka daga bacci tana faman sauke ajiyar zuciya, yayin da la66anta ke ambaton sunan baby junaid, mafarkin da tayi da shi ya Waga mata hankali, a ruWe ta mike zaune, rigar baccin jikinta duk ta yamutse, haka zalika sumar kanta a hautsine take.

Daukar wayar tayi dake ajiye gefenta, ta duba me kiranta, missed calls ta gani sun kai biyar na hajiya adama, aranta ta ayyana Allah yasa ba mafarkin da tayi bane ya zama gaske.

Bin kiran tayi nan take kiran ya shiga, bugu uku kafin hajiya adama ta Waga.

 Assalamu alaikum, daughter in-law, fatan dai ban katse maki baccin ki ba da buWar bakin Aneelerh sai cewa tayi mommy ina junaid
Sautin dariyar hajiya adama ne ya fargar da ita, da sauri ta dafe baki tamkar tana agabanta tace au...namanta ban gaishe ki ba, ina kwana mommy

 Lafiya lou Aneelerh, lallai yau na shaida kin ?osa kiga Wanki, tun da gashi har kin fara ambaton sunan shi tunkafin ki gaishe ni

Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace ba haka bane mommy, daga bacci na tashi bansan Na ambaci sunanshi ba

Hajiya adama tace oh am sorry na tada ki daga bacci tun da asubahi, agafarce ni, jikana ne ya takura min akan in kira mashi ke awaya, yaban mamaki da sunanki Ya farka yanata kuka yana fadin wurin mommy zaije shine nace bari na kiraki kuyi magana wata ?il hankalinshi zai kwanta, kafin mu shigo gidan zuwa anjima in sha Allah

Hankalin Aneelerh yaWan tashi jin abun da mommy adama tace, aranta ta ayyana kodai shima yayi kalar mafarkin da tayi da shi ne?

 Aneelerh kinyi shiru, ga shi ku gaisawa muryarta adabarbace tace toh mommy

Sautin kukan baby junaid ne ya cika mata kunnanta, murmushi tasaki tana fadin My baby boy, ba hello ba hi sai kuka? So kake hankalina Ya tashi ko ?

Cikin shesshe?ar kuka yace mom..my wallahi kizo ki Woke ni, idan ba haka ba bazaki sake gani na ba, mutuwa ma zanyi rass taji gabanta ya fadi,

 Junaid kadaina ambaton mun mutuwa, banaso, idan wani abu ke damunka ka faWamin mana! aWan tsawace ta furta mashi maganar, tunawa da hajiya adama yasa ta sassauta muryarta,
 My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, Yau in sha Allah mommy adama zata dawo min da kai

Tsagaitawa yai da yin kukan, Muryarshi da shagwa6a yace Ai ni tsoro nake ji, bana son zama agidansu.... bai ?are maganar ba tayi sauri furta shiru! Agaban mommy adaman kake fadin haka ?

 A a mommy, ba agabanta bane, ai ta fita daga dakin

Ajiyar zuciya ta sauke yanzu fada min me ke baka tsoro? Ko wanine yake bugunka ?

 A a mommy, idan ina bacci, sai ina ganin wani mutun sanye da ba?a?en kaya hannun shi ru?e da Wan kwano, kalar wannan abun na Wakin mami, wanda ake zuba fura a cikin shi, hannun shi za?o za?o da akaifu kalar na Ana mai girka mana abinci, wai yake ce min inzo mu tafi zaro ido waje aneelerh tayi Junaid ka natsu kayi min bayani, a mafarki kake ganin shi ko kuwa a zarihi? Kai kaWai ka ke kwana aWaki idan dare yayi

 Ni ba mafarki nake yi ba, dagaske nake ganin shi, kuma a Wakinsu nake kwana aneelerh duk tabi ta ruWe.

 Junaid kaji tsoron Allah, ka faWamin gaskiya, nasanka da ?arya, Idan baka fada ba, to bazan baka zoben Angel ba

 Kin siyane ? ?umshe dariya tayi don tundaga kan yadda ya tambayeta ranta ya bata cewar ?arya ya shirga mata.

 Na siya mana, ai jiya naba mahboob kuWi Ya siya maka zoben mai kyan gaske

Tuntsirewa yayi da dariya yana fadin to mommy wasa nake yi maki, wallahi dama awani cartoon ne da muke kallo a tv, anan naga mutumin fashewa tayi da dariya sosai har fararen ha?oranta suka bayyana yanzu naji magana Wan rainin wayau, duk kabi ka tasar min da hankalina, Yau har mafarkin ka nayi saboda nayi kewarka babyn mommy, ina sonka Yarona

Yace nima inasonki mommyn baby dariya tasaki, idan yana yi mata magana kamar wani babban mutun daya mallaki hankalin shi, sai idan yayi wata kwa6ar ne zaka gane ?aramin yaro ne.

 Mommy ina mamina? da abie, da uncle mai ?aton hanci, da mahboob mai son kuWi, da zahrah mai dogon wuya

Tsabar yadda take yin dariya hada dafe ciki,
 Junaid baka da mutunci, Uncle dinne mai ?aton hanci !
Kaitsaye yace mata eh mana, baida kyau Allah, mummuna ne uncle dan Iya, ni naji dadi ma bashine daddynki ba, da wallahi bazanyi kyau ba

Mamaki ne ya kama Aneeleerh, jin yadda yake kushe mata kawunta.

 Junaid dan Allah ka yi shiru kada wani yaji ka, Ni zan ajiye wayar, ka koma bacci zuwa anjima Mommy adama zatayi maka wanka ta shiryaka sannan zata dawo mun dakai gida, fadamin me kake so in tanadar maka ?

Da shagwa6a yace fura nakesho, asanya kwakwa da yoghurt aciki bakomai ya tuna mata ba face Angel, tana son furar da aka sanya kwakwa da youghurt, kusan kullun idan tazo gidansu sai ta sanya Aneelerh ta haWa mata ita, musamman saboda Angel take ajiye damarmar fura cikin robabi ta sanya mata su a frigde don su yi sanyi.

Tuni idanuwanta suka cicciko tab da ?walla, Muryarta na rawa ta furta zan ajiye maka my baby boy, ka kwanta ka huta zuwa anjima zamuga juna da?yar ta samu baby junaid Ya ?yaleta, badan ta gaji dashi ba, ta ajiye wayar on pillow, ta sauko daga saman gadon, A hankali take bin bedroom dinta da kallo, har idonta ya sauka akan hotonsu da ta li?a shi a bango, wanda sukayi tare da aminnanta, su uku abunsu, kowacce ta ca6a uban adon lace, fuskokinsu Wauke da murmushi.

Ta natsu tana kallon hotunansu, sam ba ta ji takun tafiyar mutun ba, har ta ?araso gefenta ta tsaya, ?amshin turaren zahra ne yaja hankalinta ga dubanta, tayi mamakin ganinta a Wakinta, tun ranar da abunnan ya faru na hajiya falmata ko magana bata ?ara haWa su ba, amma yau sai gashi ta tako ta shigo room dinta, dogon hijabi ne a jikinta daga ?asa har sama launin maroon hannayenta biyu ta fiddo dasu ta cikin hannun abayar, hada cazbaha ta ru?e tana ja kamar wata matan limam.

 Aunty Aneelerh Ina kwana, kin tashi lafiya ?

Da?yar ta iya amsa mata da lafiyalou, ina fata kema haka
Daga mata kai tayi alamar eh, idanuwanta sam basa akan Aneelerh suna akan hoton da take kallo, wani irin kunyarta take ji, tunawa da rashin mutuncin da tayi mata akan ta bata shawarar ta ba Hajiya falmata haWin kai, tayi danasani tun jiya da Mahboob Ya fayyace mata komai.

 Nayi mamakin ganinki a Wakina zahra, ai nayi tunanin mun rabu kenan har abada

Girgiza kai zahra tayi Idan kinga mun rabu to mutuwace ta raba

Aneelerh sam batasan Mahboob ya fada ma zahra ba, bayan ta gargade shi akan karya gaya mata, shi kuma bayason suna gaba atsakaninsu, don ya fahimci zahra ta fusata sosai, Idan har bai fada mata gaskiya ba to kuwa zata cigaba da zabga ma Aneeleeh rashin mutunci abisa rashin sani shiyasa ya yanke shawarar ?wara ya faWa mata, don ta yi takatsantsan kada ta wuce gona da iri azo aji kunya.

 Kiyi ha?uri da abunda Ya faru atsakanin mu, nasan na 6ata maki rai, tuntuni nake taso in nemi yafiyarki, sai dai baki bani damar yin hakan ba Aneelerh ce tayi maganar tana duban zahra.

Cikin sanyin murya zahra tace ni yakamata nabaki hakuri auntyna bake ba, saboda ni ce mai laifi, ban kyauta maki ba, duk irin sha?uwarmu da kyautatamin da kike yi amma nagaza fahimtarki, har takai takawo ina zarginki, maimakon na kyautata maki zato, wallahi naji kunya, daren Jiya da?yar na runtsa tsabar takaici, ?an kwanakin da muka samu sa6ani atsakaninmu aunty Aneelerh naji jiki ba kaWanba, na ?untata, na gane mahimmancinki agareni, Ina da abubuwa dayawa da suka faru wadanda nakeso in samu abokin firar da zangayama wa ya tayani farin ciki sai dai kash babu, ke kaWai ce nake jin dadin tattaunawa dake akan duk wani abu daya shafi rayuwata saboda nasan zaki ?arfafa min gwiwa ki kuma bani shawarar da zata amfane ni.... zafafan hawayene suka wanke fuskar Zahra, tuni idanuwanta sun kaWa jawur da su.

 Meyasa banyi dogon nazari ba akan shawarar da kika bani ?

Zuciyar aneelerh ba ?aramar karaya tayi ba zarah! Mahboob Ya fada maki ne ?

Jinjina kai tayi ?warai kuwa ya fadamin komai, har gargaWi na yayi akan kada na nuna na sani, saboda kince mashi kada ya gaya min, shi kuma a ganinshi bai kamata ki zubda mutuncinki a idanuwana ba, saboda ku rufa ma hajiya falmata asiri awurina, don in cigaba da ganin darajarta, hakan kuma bazai ta6a yiwuwa ba, saboda shi mutunci madarane idan ya zube baya kwasuwa, sai dai naji dadi da ke kika yi silar shiriyarta, ke din ta dabance Auntyna

Rungume Aneelerh tayi, atare suka fashe da kukan farin ciki, yau sun shirya da juna, babu wanda baiji jiki ba acikinsu.

Bubbuga bayanta Aneelerh tayi da hannunta Cikin shesshe?ar kuka take fadin komai ya wuce zahra, abunda ya faru laifina ne dana baki shawarar banza duk da ko a lokacin bawai zan zuba maki ido bane don ina jarabaki ne nayi hakan, wallahi duk wani motsinki atafin hannuna, tun bayan dana baki shawarar, fargabana kada ki amince da shawarata ki kama hanya ki tafi kai mata kanki, shiyasa na sanya maki ido, akarshe na yanke shawarar zuwa gidanta don in gargadeta akan ta fita sabgarki, Cikin Ikon Allah sai gashi na 6uge da yi mata nasiha, ashe nice silar shiriyarta, naci ribar jarabawar da nayi maki zahra, Naji dadi kuma nayi farin cikin samun ?ar uwa mai tawakkali irinki, zan iya cewa duk namijin daya mallaki mace irinki yayi nasara sai dai fatan ya cika da imani

Dariyar farin ciki zahra tasaki, tare da dago dakanta daga jikin Aneelerh
 Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya saboda babu su auntyna, Ina fatan nima Allah yabani abunda zan kyautata maki da shi, sannan mahboob Ya faWamin cewa kin bashi kyautar kuWi duk da ya?i gayamin nawa ne kinsan halinshi May be Yana gudun kada Ince ya bani kasona, baisan cewa Nima na samu alheriba, abunda nake ta so in faWa maki kenan

Waro ido Aneelerh tayi da alamun farin ciki akan fuskarta tace masha Allah, kice kun samu abun arzi?i Jinjina kai Zahra tayi zakisha mamaki auntyna, naga yanzu kika farka daga bacci, da anjima idan muka kammala yin breakfast zan fada maki komai

Murmushi Aneelerh tasaki Yau zansha kanun labarai, Yanzu bari na shiga toilet in yi wanka

 Auntyna wai yaushe za a dawo mana da baby junaid dinmu, nifa nayi missing dinshi, Allah na kusa zuwa in dauko shi, Jiya har mami na tambaya game da zancen dawowarshi

Aneelerh tace kada ki damu, Babyn mu yau zai dawo gida, Hajiya adama zata kawo shi, Nima yau da shi na tashi araina

 Allah ya kawo su lafiya, shima na tanadar mashi kyautarshi ta musamman da zan bashi Aneelerh taji dadin maganar zahra.

 Kada na cika ki da surutu, nayi kewarki ne auntyna, bari nabarki kiyi wankan in kin fito mun tattauna, amma kafin nan niko inaso in tambayeki wani abu in ba takura dariya aneeleh tayi kafin tace okey ina jinki fadamin menene

Da ido tayi mata nuni da hoton dake amanne jikin bango.

 Wacece wancan black beauty din mai diri? Ita kadai ke bansani ba cikin ?awayenki, nadai san Benazir mahaifiyar kyakkyawar yarinyar nan Angel

Jim Aneelerh ta Wanyi kafin ta furta Aishatu bintu sheikh Iman Malik, shine sunanta, kamar yadda na fada maki aminnan juna ne mu

Cike da son jin ?arin bayani Zahra tace to amma ta rasu ne ita? Naga ko waya ba ku yi, Ita dai benazir nasan abunda ya faru da ita a kagare ta jefa mata tambayar.

Cikin sanyin murya Aneelerh tace ?addarace ta afka mata wadda tayi silar tarwatsewar farin cikin rayuwarta, baiwar Allah, nan da kike ganinta mahaddaciyar al?ur anice, tun tana ?ar shekara goma sha wani abu ta haddace shi, Tana da kaifin basira mace ce mai kamun kai, tana da aji, idan nace zan baki labarin rayuwar Aisha wallahi saikinyi sha awar yin koyi da ita, saboda kyawawan Wabi unta da halayanta, Ni kaina ban ta6a tsammanin zamu rabu da itaba..... tun da ta fara magana zahra ta kafe ta ido tana sauraronta, idanuwan Aneelerh sun kaWa jawur, sam bata son tuna baya, hakan zai fama mata ciwon dake acikin zuciyarta.

 Aunty Aneelerh kinyi shiru? tun da kika ambaci kyawawan halayanta naji na kwaWaitu da son jin tarihin rayuwarta

Girgiza kai Aneelerh tayi Am sorry zahra, bana son tunawa,  bubbuga ?afa zahra tayi tamkar zata fashe mata da kuka tace please Aunty Aneelerh, wallahi tana burgeni duk da ban ta6a ganinta ba

Murmushin ya?e Aneelerh tasaki tana duban hoton yayin da hawaye ke bin fuskarta Ni kaina bani da masaniyar tana araye kota mutu, tunkafin muyi aure tabar gidan iyayenta, Silar wani mummunan abu daya faru, wanda ni nayi imanin bata da laifi, tuggune da makirci aka shirya mata..... dakatawa Aneelerh tayi dayin maganar tana kallon zahra, tsabar son jin gulma har ta jefar da cazbar hannunta batare da saninta ba.

 Aunty Aneelerh kinyi shiru! Meya faru da ita? Wanda yaja har tabar gidan iyayenta? Wani irin tuggune aka kitsa mata ?

Tuntsurewa Aneeleeh tayi da dariya, juyawa tayi da sauri ta nufi toilet door tana fadin Zahra ?wara ki fidda rai da son jin labarin Aishatu Bintu sheikh imam malik, dan zan baki shi ba yanzu ba sai kin ?ara hankali ta kare maganar ta shige toilet taja kofa ta datse.

Ta tafi Tabar Zahra da cizon yatsa, idanuwanta akan hoton fuskar Aisha, aranta ta ayyana ai wallahi saina ji labarinki baiwar Allah, Ai ni dama tun da naga hotonki na shaida kinbar tarihi arayuwarki, Oh ni ?ar ubansu, gata kyakkyawa, mace har mace, ga diri kamar nicki minaj, ko tana ina ahalin yanzu ? Sambatu zahra tadingayi tana kallon hoton aisha, sai daga bisani ta du?a kasa ta dauko cazbaharta, ta futo daga Wakin ta nufi nata dakin don ta kimtsa kafin lokacin yin break fast.


*Daular Alhaji Musa

A zaune take kan darduma, bata jima da kammala sallar asubahi ba, hijab din data sanya launin milk, gaba Waya ta tattara natsuwarta akan addu ar da take Yi, ta Waga hannayenta sama cikin harshen larabci take karanto addu o i, yayin da hawaye suka cika idanuwanta, bakomai take ro?o ba face Allah ya dawo mata da mijinta lafiya da ?arta, bata da burin daya wuce tayi tozali da su, tayi matu?ar ?agara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login