Showing 108001 words to 111000 words out of 260999 words

Chapter 37 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

haWa baki wurin furta sunan baba

 Haba Mommy, Akan wani dalili zaki je ki faWa mashi? So kike ki tashi hankalin shi, Gaskiya a a ki koma ki zauna, zamuje mu nemo daddy duk In da ya shiga

Ru?o Hannunta Zayn yai, Suka koma Cikin Wakin, Gefen gado ya zaunar da ita,

 Zayn pls, Ku duba daddynku, Ni damuwata kada ace wani abunne ya same shi dama jiya ya faWamin baya jin daWin jikinshi muryarta tamkar zata fashe da kuka ta yi masu maganar.

Zaid Yace in sha Allah ba abunda ya same shi mommy, yanzu zamuje mu nemo shi ya ambaci hakan Tare da ru?o hannun Wan uwansa suka fuce daga Wakin.

Ransu ya 6aci matu?a, daga gaban ?ofar Wakin suka tsaya suna kallon juna
 Mutumin nan Wan rainin wayau ne, wlh Zaid zan tona mashi asiri awurin mommy, Ta ya ya zai bar mahaifiyarmu cikin damuwa, Yana can Yana sharholiyar shi, dama zuba mashi ido nakeyi ina tara shi.... duk yadda zaid yaso ya dakatar da Zayn Akan Yai shiru ya?i rufe baki saida Yakai ?arshen Aya

 Ka daina Waga murya bro, Ni bawai ina goyan bayan abunda yake yi ba ne, just ka yi tunani mana, muddin ka tona ma daddy asiri wlh mu zaka ja ma bala e, Kana ganin irin gorin da ake yi mana a family, akan mahaifinmu yana zama gidan surukansu Yanzu idan ka faWama Mommy cewa daddy Yana bin matan banza me kake tunanin zai Biyo baya ?

Sassauta fushin fuskarshi Yai Hakane Zaid amma abun Yana ?ona min rai, why ya ke son ja mana ba?in jini? Dame mommy ta rage shi da har yagaza kama mutuncin kansa, wai shi so yake dole saiya 6ata mana suna tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ?walla

Ya ci gaba da cewa Shine silar komai dake faruwa arayuwarmu, Zaid Ina kishin mahaifiyata sosai, Ina jin takaici da ?ululun ba?in Cikin mutumin nan, wlh duk ranar da mommy taji labarin abunda Yake aikatawa tabbas zuciyarta zata Iya bugawa saboda tana da kishi kuma Tana son daddy, ni har kokwanto nakeyi anya daddy yana son mommy kuwa? Ko dai Abunda mutane suke hasashe akanshi gaskiya ne? ya aureta saboda dukiyar family dinmu yana magana hawaye naci gaba da taruwa acikin idanuwanshi.

Dafa kafaWarshi Zaid Yai duk abunda ka ke ji zayn nima inajin shi, Amma Ya zamuyi? Mu tamu ?addarar ahaka tazo mana, Muyi ha?uri wata rana sai labari Sannan Yakamata muna tayashi da addu a akan Allah ya shirye shi, saboda shi mahaifinmu ne duk inda za aje adawo mu jininsa ne kuma ba zamu so mutuncinsa ya zube a idon jama a ba.

Lallashin junansu su ka yi, Hannunsu ru?e cikin na juna suka Nufi Babban falon gidan, masu aikine keta kai komo.

Suna dab da zasu fuce daga falon, Kwatsam Pravin Ya faWo Sai faman zumbula sauri Yake Yi, Jikinshi sanye da Suit dinsa light brown, ?iris Ya rage su ban gaji juna da shi, duk da faWin ?ofar kasancewar Kowan nan su Hankalinshi ba a kwance yake ba
Har zasu gifta shi, suka ci wani uban burki agabanshi, Tun daga Kan Yarda suke jefa mashi kallo yasa shi kame kanshi.

 Har kun dawo daga aikin ? Tambayar daya jefa masu kenan.

Zayn tamkar ya sha?e baban nasu haka Yake ji, takaici Ya hana su yi magana.

 Lafiya? Baku ji ina magana ba ?
Saida suka taushi zuciyoyinsu tukunna suka Iya yi mashi magana,

Zaid yace Sannu da dawowa daddy, Ya office din? Naga yau ka yi marece ko duk Aikin ne ya ru?e ka ?

Basarwa Yai tare da cewa Eh,  daga haka bai ?ara tanka masu ba, Sai bi da yai ta gefen su Ya wuce, kamar sakarkaru haka suka Bi bayanshi da kallo, Sam baisan cewa sun san abunda yake aikatawa ba.

Kusan atare suka girgiza kawunan su.

 Zayn tunda Ya dawo mu koma Waki, dama Ni agajiye nake wlh, inaso na Wan kwanta In huta
Juyawa sukayi Atare suka nufi part dinsu.

Hajiya saratu na zaune gefe gadonta, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta Hannu biyu ta zabga uban tagumi, gabanta sai faWuwa yake yi gani take yi kamar wani abunne Ya faru da mijinta, Kasa samun natsuwa tayi zumbur ta mi?e kamar an zungureta da sanda, safa da marwa taci gaba da yi acikin Wakin tana ?arewa agogon bango kallo.

Ba zato ba tsammani muryar Pravin ta ratsa kunnuwanta Assalamu alaikum tunkafin Ta juyo ta kalleshi ta soma sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tsabar farin ciki da sauri ta nufeshi, hannu biyu ya rungumeta a ?irjinsa.

Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, yayin da take ?ara sha?ar ?amashin turaren jikinsa.

 Am sorry My wife, nasan ban kyauta maki ba.... tunkan Ya ?arasa maganar, Hajiya saratu ta dago da fuskarta, babu annuri ko mis?ala zarratin tuni yasha jinin jikinshi.

Da kakkausar Murya ta furta PRAVIN DAGA INA KAKE !? Rass Yaji gabanshi Ya faWi
 Na kira p.A dinka Awaya ya sanar dani cewa tun ?arfe 12 kabar office, Inason Jin ya akai kabar office ina kuma kaje ? Rai a6ace take Yi mashi magana, Hannunta ru?e da qugunta.
Ya tsareta da Ido batare daya furta kalma ba, hakan ba ?aramin ?ona mata rai ba, Tsawa ta daka mashi kamar mahaukaciya Ta cakumi Gaban rigarshi.

 Nace ka faWamin Ina kaje pravin? Saboda ka maidani shashasha ban da amfani awurinka shine zaka kama Hanya kabar office tun ?arfe sha Biyu baka kirani awaya ka sanar dani ba, Kasa duk nabi na tashin hankalina akanka, ni na Waukama wani abunne ya same ka sai gashi ka dawomun lafiyarka qalou

?an hanjin cikinsa tuni sun soma kaWawa, Abunka ga shu umin namijin wanda yasan takan mace, runtse idonshi yai tare da kai hannu ya dafe gefen cikinsa.

Nan take Hankalinta yai matu?ar tashi la66anta na rawa take faWin pr...pravin? Lafiya? Meke damunka
Da wata irin kasalalliyar murya ya furta My stomach, bana jin daWi ai tun Jiya na faWa maki, ya ?arasa maganar yana faman cizon la66ansa, lokaci Waya fushin fuskarta ya sassauto, tsananin tausayin shine Ya kamata, ganin yana tangal tangal kamar zai faWi yasa tayi saurin talla6e waist Winsa, da taimakon ta suka ?arasa gaban Gado Ya hau Ya kanta Yana fuskantar ceilling, daga gefen gadon ta zauna daga gefenshi tana kallon shi


 Pravin am sorry nayi maka faWa bansan baka da lafiya ba, kaine ka?i Yi min magana, why pravin kasan baka da lafiya meyasa baka kira awaya ka sanar dani ba? Cikin kulawa take yi mashi magana, har ta manta da zancen tambayarshi Ina yaje.

Wahalallan Yawu ya haWiya, Cikin mawuyacin Hali Ya furta wayar bata a hannuna ne a mota nabarta, Ina Cikin Yin draving zan dawo gida, Ciwon ciki Ya takura min, draving dinma na gagara Yi, shine na wuce gidan abokina dake anan kusa, to acan bacci ya kwashe ni,

 Pravin why baka je asibitin Gida ba? ai da komai yazo maka da sauki, yanzu ka tashi ka shirya In kaika asibiti da kaina inyaso sai in dubaka acan

Tana ?o?arin mi?ewa yai saurin fusgo hannunta, gaba Waya ta faWa saman jikinsa, ?an?ame ta yai da hannayenshi biyu

Yana faman cizon le6e ya furta rashin lafiyata bata asibiti bace, My wife kece kike damuna saboda rashin bani ha??ina da bakya yi akai akai, shiyasa nake fama da ciwon cikin nan, ko da yaushe Aikinki ne agabanki, idan dare yai nayi maki magana kina danna laptop sai kice min In jira ki kammala daga nan har bacci ya Wauke ni baki gama ba......

Pravin Ya kashe mata Jiki da kalamansa, ta yarda da abunda ya faWa mata saboda tasan bata kyauta mashi ta 6angaren nan mafi yawan time idan Ya matsa mata tana Yin aiki bata kula shi saita kammala.

 Am sorry dear, indai nice zan gyara, kayi ha?uri nayi kuskure but bazan ?ara Ba, tun da abun Yana affecting dinka . Lumshe ido Yai, har cikin zuciyarshi ba ?aramin daWi Yaji ba, ganin yai nasara akanta.

 Yanzu ka faWamin me kakeso? Za ka yi wanka in taimaka? Ko zaka fara Cin abinci ne

Yana faman sakin nishi Ya furta nafi bu?atar wankan, amma idan kin amince muyi atare
Murmushi tasakar mashi is Okey, shine kaWai abunda kakeso ? ?aga mata Gira yai alamar eh, A hankali ta Waura yatsun hannayenta saman coat din jikinsa Ta cire mashi ita, kafin ta zame mashi belt din wandonsa, yun?ura yai tare da mi?ewa ya sauko daga saman gadon Ya ?arasa zame wandon ya rage daga shi sai short da singlet dinsa, Yaja hannunta suka nufi toilet, da gudu nabi bayansu sai dai kafin in ?arasa Pravin Ya kulle ?ofa.

*EX-PRISONERSd'*

Idan muka koma 6angaren Prisoners, sai dai muce Alhamdulillah, tun bayan da Dr laura davis ta tattauna da Sojoji bata ?ara Ji daga gare su ba, An dai samu damar Kammala Yi masu injections Winsu kuma kullum sai sunsha magani na safe daban na rana daban na dare daban, injection Win duk mutun Waya uku suke Yi mashi arana, Likitoci sun ci kwakwa Wurin ma Matan allura, Musamman Azeeza da Jamimah, mugun tsoron Allura su ke ji, idan za ayi masu sai an kira Angel ta ru?esu, tukunna ake samun sau?in yi masu allurar, Mazan dai da sauki basu tsoron Allura tamkar basu son ana tsira masu ita a jikinsu ba, cikin kwanaki huWu da su ka Yi a Texas Rayuwarsu ta fara canzawa, saboda kyakkyawar kulawar da suke samu tarairayarsu ake Yi kamar new born babies, abinci sau uku ake basu, Breakfast, lunch and dinner, Lafiyayyan abinci mai gina jiki, sau Waya ake sanyasu yin wanka, su canza Kayan Jikin su, Su Angel an dage da yin sallah da addu a, har tsakar dare tana tashi yin night prayers, yawanci addu o inta akan Danish ne, ta ro?i Allah da ya kare mata shi, idan farkawarshi Alkhairi ce Allah Yasa ya tashi cikin amince, idan kuma farkawarshi ba Alkhairi bace Allah yasa yaita sharar baccina har zuwa su koma Nigeria zaifi masu sau?in su Yi control dinshi, duk da yanzu ta fara fargaban kada su zo Nigeria A nemi Ruwan zam zam arasa tabbas ba ?aramar matsala za a samu ba, damuwarta yanzu akan Sojojin ce shiru basu dawo ba, Kuma bata Ji daga bakin dr laura Ya ake ciki ba, Shin za a maidasu ?asarsu ne ko kuwa a a, Ta dai zubawa sarautar Allah Ido =?@?

Sam ta kasa runtsawa, tun wuraren ?arfe tara na dare ta farka, saboda mugun bugun da ?irjinta ke yi mata, tabbas tana ji aranta wani abun ne ke shirin faruwa.
Mi?ewa Tayi zaune saman gadonta, ta jingina Bayanta Jikin pillow, idanuwanta suna a lumshe, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinta Yake yi wata irin kasala take Ji da matsanancin faWuwae gaba.
 Masoyiya Angel, Lafiya kika farka daga bacci? Na lura kamar wani abu ke damunki
Muryar Nurse Jessica ce ta fargar da ita, har saida ta Wan zabura don bata yi tsammanin jin Muryar mutun a kusa da ita ba.
Slowly ta wurga eye balls Winta akan fuskar nurse Win, tana daga zaune saman chair ta kusa da gadonta, hannunta ru?e da wayarta, fara ce sol, uniform Win jikinta light blue ne kalar nasu, ta Waure jar sumar kanta da ribbom.
Nauyayyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa sister, nagode da kulawarki agareni, nakasa runtsawane saboda inason ganin yan uwana ko zaki Iya taimaka min ?
Smiling gently nurse jessica tace Na lura kina son ?an uwan nan naki, cos tun ranar dana fara kula da ke, sau uku kike zuwa room Winsu Kina duba su, faWamin ko dai akwai damuwane? Ko tsoro kike ji kada mu sace maki su ? Da zolaya nurce jessica tayi mata maganar
Cikin jin kunya Angel takama ?an kame kame tana faWin am.... Ba haka bane just inason su sosai, mun sha?u da juna, shiyasa bana samun natsuwa idan ban gansu akai akai ba

Nurse jessice tace Kuna burgeni sosai, inaso Inga ?an uwan masu son junansu, masu haWin kai, ta hakanne ake cin ribar zaman duniya, idan har kana da Wan uwa mai share maka hawayenka, mai nuna maka ?auna wanda baya gajiya dakai tabbas ka gode ma Allah, zai yi wuya ka rasa madafa a duniyar nan, babu wanda zai yi gigin cutar dakai muddin kuna da haWin kai a tsakaninku, amma idan Ya kasance kuna ?an uwa baku da haWin kai, danasani zai biyo baya cos dayawa rashin kulawa keja har damuwa tayi ma Wan uwanka Illa, ya akaita abunda zakuyi danasani gaba dayanku

Angel ta natsu Tana sauraron Kalaman Nurse Jessica, Ha?ika kalamanta sun ta6a mata zuciya, sai taji ta ?ara ?aunar ?an uwanta, ta Wanyi mamakin yarda nurse Win take sakar mata fuska suke Yin fira, saboda ta ta6a Jin ana faWin turawa sun tsani ba?ar fata suna nuna masu wariyar launin fata, sai dai tayi tunanin ba duka aka taru aka zama Waya ba, sannan kuma su basu da banbanci dasu, hasken fata, launin ido da kuma sumar kai, shiyasa suka zama Waya.

 Ki tashi muje in raka Ki Wakunan ?an uwan naki, Nima Inason ganin su, musamman twins Win nan murmushine Ya bayyana akan fuskar Angel jin abunda nurse Win tace, tuntuni ta faWa mata, ba twins bane Jamimah da azeeza Waya ta girma Waya amma ta?i yarda, ba ita kaWai ba hatta sauran nurses Win da likitocin kallon twins suke Yi masu acewarsu Basu da banbanci, Komai nasu kala Waya.

da zumuWi Angel ta sauko daga saman gadon, light blue uniform Winta ne a jikinta, sai da ta fara zuwa gaban closet Win Wakin ta buWe ta Wauko Hijabin da aka bata Nayin sallah ta zura a jikinta.

Hannunsu ru?e cikin na juna ita da nurse Win suka fito daga Wakin, hasken electric bulbs Ya haskaka Asibitin tamar da rana, a tsanake suke Yin tafiya suna tattaunawa a tsakaninsu, Wakin Gabriel suka Fara shiga, tayi mamakin ganinshi idon shi biyu Shida nurse rebecca, ta kunna masu kallo sun natsu abunsu.

Jin motsin shigowar Mutun yasa suka kai eyes dinsu ga ?ofar, murmushi ne ya bayyana akan faces dinsu

Mayar masu da martanin murmushin nasu Angel tayi Wan uwana, Baka Yi bacci ba? Fadamin meya hana ka Yin bacci !
Kafin Ya bata amsa nurse rebecca tace Ni na hana shi, Ko bakisan mun fara soyayya bane, Gabriel baka faWa mata ba ? Gaba daya suka sanya dariya, jessica tace har kinyi kamu kenan Waga mata gira tayi yap, taya zan bari damar nan ta wuce ni ? Firarsu ba ?aramin nishaWi take sanyasu ba, Angel tuni ta haye saman gadon gabriel, Ru?o hannunshi tayi acikin nata,
 My sister, meya hana Ki yin bacci ? ?asa ?asa da murya ta furta Danish, Hankalina Ya?i kwanciya da rashin farkawarshi, Yaufa kusan One week kenan a lissafina, Gabriel bansan ya zanyi ba, Ni nafi so Mu koma nigeria.... katse mata maganar yai da cewa ai kin faWamin dr laura tace zata taimaka mana mu koma can ko?

?aga mashi kai Tayi eh, amma har yau shiru, banji daga gareta ba, Kuma kaga sojojin basu ?ara dawowa ba

Ganin kamar duk ta damu yasa shi kwantar mata da hankali Wani jinkirin alkhairi ne Angel, wata ?il ki ga gobe anzo mana da kyakkyawan labari, don haka Mu ?ara ha?uri kada mu damu kanmu komai zai tafi dai dai My lovely sister Yai magabar Tare da jan kumatunta da hannunshi, Hakan ba ?aramin dariya Ya bata ba.

 Masoyiya Angel, zamu Iya tafiya  ? Muryar nurse Jessica ce ta katse masu tattaunawar tasu.

Peck tayi mashi saman cheek dinsa ka kwanta ka huta, ta ambaci hakan tare da saukowa daga saman gadonshi ta nufi nurse jessice taja hannunta suke fuce bayan sunyi masu sallama.

Room Win Batul suka shiga, A kwance suka same ta saman gado, ta ?udundune da bargo, da alama tayi zurfi abaccinta, Basu shiga Wakin ba suka wuce Wakin Jemimah, Itama baccin take Yi, ta wawware ?afafuwanta ta saki baki da hanci, nurse din dake kula da ita, Tana acikin Wakin har gaisawa sukayi da ita kafin suka nufi Wakin Azeeza, Kamar yarda suka samu jemimah haka suka sameta a kwance bacci yai daWi, murmushi Angel tasaki kafin suka ?ara gaba zuwa Wakin Parveen, Hallau dai mai hali Baya ta6a canzawa, bata Yi mamakin ganinta a zaune gefen gado ta tasa abinci saici take Yi, An kunna mata tv tana kallon mbc channel Suna Yin cartoon tom and jerry, Sai ti?ar dariya take Yi kamar zata kifa kanta saman table din gaban gadon, babu alamun bacci a idonta, sam bata ji motsin shigowarsu ba, plate Waya ne agabanta sha?e da chicken wings, gefen plate Win kuma Apple juice ne, Duniya Ta yi mata daWi, Gyaran muryar da Angel Tayi mata ne yai silar Jawo Hankalinta ga dubansu, bakinta cunkushe da nama ta furta  Angel

Nurse Win da suka zo atare da ita sai murmushi take saki, Da alama parveen ta burgeta, ba tun Yau ba, duk in tazo dubata sai ta sameta tana Cin abinci, da wuya ka same ta bakinta babu abun taunawa.

Farin Cikine Ya bayyana akan fuskarta, Da sauri ta ?arasa suka rungume juna ita da Angel.

Shafa sumar kanta Tayi Parveen kowa Yai bacci banda ke, kina nan kinata cin abinci Ko gajiya bakya yi, so kike ki karya masu jari ko ? Da zolaya tayi maganar, bayan ta raba jikinta daga na Angel, Just


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login