Showing 249001 words to 252000 words out of 260999 words

Chapter 84 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

yace ka karanci Wan uwan nan naka sosai, naji dadin jin hakan, may be wankan da mu ka yi mashi ne yasa shi jin daWi har yayi bacci
Saldabeel yace ?warai kuwa yalla6ai, ay kayi ?o?ari, Allah yasaka maka da mafificin alkhairinsa kamar yadda ka faranta mashi rai ka gatanta shi kaima inayi maka fatan Allah ya faranta maka ya ?ara Waukaka ka Har cikin ranshi yaji daWin kalaman salsabeel,
 Yalla6ai kaima ban barka abayaba, domin kuwa kayi namijin ?o?ari wurin ganin Wan uwana ya samu lafiya, Allah ne kaWai zai Iya biyanka ya faWa yana duban chief owais.
Jinjina mashi kai yayi batare daya furta komai ba.
Kiraye kirayen sallar Azhar da aka farayi ne Yaja hankalinsu
da sauri chief ya zaro agogon azurfar hateem tare da Zobensa daga aljihu Ya mi?a mashi.
Bayan ya saka a hannun shi, Waya bayan Waya su kayo alwala, kafin fitarsu daga dakin saida prime minister yaje har gaban gadon danish ya Wan duka tare da kai small lips dinsa saman forehead din danish Ya manna mashi peck, ji yake kamar karya tafi yabar shi, ganin abun nashi bamai ?arewa bane ga time Win salla na tafiya ya kafe danish da ido babu ?yaftawa da sauri chief yaje ya ru?o hannun shi ya janyo shi a hankali suka nufi ?ofar fita Wakin.

Adai dai lokacin Unaisah dake la6e bakin ?ofar Wakin tana sauraron su, jin motsin tafiyarsune yasa tayi saurin watsawa da gudu ta la6e a wata ?ar corner.
Akan Idonta, Chief Owais Ya fito hannun shi ru?e dana prime minister, still bata samu damar ganin fuskokinsu ba, sai dai salsabeel daya biyo bayansu shi tagani da kyau, tunani ta somayi aranta ko wanene wannan babban mutumin, taso ace taga fuskarshi shida chief, Allah bai bata sa a ba, Har saida suka 6ace ma ganinta tukunna cikin sanWa take bin bango tana nifar Wakin danish cikin sa a ta buWe ?ofar ta shige, daddaWan ?amshin turarenshi ne ya daki hancinta har saida ta lumshe idanuwanta tana sha?ar shi ......

Cikin takun sanWa ta nufi gadon, yayin da idanuwanta suke hango mata Man dinta, hayewa saman gadon tayi daga gefenshi ta dakata tana bin body dinsa da kallo, from head to toe, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin shi cikin shiga ta farar jallabiya yayi mata kyau, aranta ta ayyana nasan waWannan mutanan ne suka taimaka mashi wurin gyara jikinshi saboda boss ya faWamin cewa ko yatsanshi bai iya Wagawa, idan kuwa hasashena gaskiya ne naji daWi ubangiji Allah ya saka masu da gidan Aljanna, ta ?are zancen zucin fuskarta Wauke da murmushin farin ciki.

Ta rasa gane bacci yake yi ko idonshi biyu, amma dai tayi missing dinshi na tsawon awannin daya Wauka tun jiya a halittar maciji, ashe dai da rabon zata sake ganinshi da ainihin suffarshi, yayin da take kallonshi karaf idanuwanta suka sauka akan jan tabonnin dake akan farar fatar dogon wuyansa, harzuwa saman fatar hannunsa.

Ras taji gabanta ya faWi, ta zazzaro idanuwanta waje tana fadin My man meke damunka? Jan tabon menene nake gani a jikinka ? Ta ?are maganar fuskarta Wauke da matsananciyar damuwa, hawaye tuni sun ji?e gashin idonta.

Ziraran yatsun hannunta ta Waura saman wuyanshi ta soma shafa tabonnin slowly ta zame fingers din daga neck dinsa zuwa kan broad chest dinsa, a hankali take 6alle links din gaban jallabiyar don ta samu damar ganin sauran tabonnin da ke akan fatarshi, da ta buWe faffadan kirjin nashi, hankalinta yayi matu?ar tashi da ganin tabonnin ta ko ina, ji tayi tamkar zuciyarshi bata bugawa da sauri ta kanga Kunnanta na dama saitin zuciyarshi, natsuwa tayi tana sauraran yadda take harbawa cikin kwanciyar hankali, tsawon mintuna bata Wago da kanta ba saboda dadin sauraran heart beat dinsa da take ji, A hankali ta Wago da kanta karaf idanuwanta suka sauka akan soft lips dinsa batasan ya akai ta tsinci kanta dayi masu kallon ?urulla ba sun Wan kumbura, zuciya ce ta soma tunzurata akansu, unaisah da kasada ta Waura yatsun hannunta na dama kan la66ansa tayi squeezing Win su, ba zato ba tsammani taji yaja dogon numfashi da ?arfin gaske, tsabar kiWima jiki na rawa ta rarrafa ta ta wulkita can ?asan gadon ta faWo ta labe zuciyarta na harbawa da ?arfi da ?arfi jikinta ya hauyin kerma duk tabi ta ruWe gani take yi kamar ta fama mashi ciwon shi...


Runtse idanuwanta tayi hadi da matse pink lips dinta wani irin yanayi take ji mara misaltuwa atattare da ita, Jin shiru ya daina jan numfashin ne yasa ta lalla6a ta Wago da kanta tana le?enshi, babu abun da ya canza yaci gaba da yin baccin nashi.
?asa ?asa da murya ta furta I m sorry to disturb you, I ve missed you so much. I can t take my eyes off you.


Lalla6awa tayi a hankali ta haura saman gadon da rarrafe ta nufe shi, rumfa tayi mashi da sumar kanta ta natsu tana sha?ar ?amshin turaren jikinsa, tabi ta addabi rayuwarshi da sunan tayi kewarshi tahana mashi sukuni abaccinsa, don taga babu kowa aWakin shiyasa take yi mashi iya shege....

Lokacin da Chief da prime minister tare da salsabeel suka sauko down, kaitsaye suka nufi babban falon, tunkafin su ?araso takun takalmansu Ya isar da sa?on zuwansu, A hanzarce Sheikh imam da su Boss man suka mimmi?e tsaye suna jiran ?arasowar su, su sajeed dake zazzaune kan carpet suna kallonsu, lokaci Waya suka shiga ruWanin ganin fuskar prime minister Hateem data chief Owais, duk da shi chief ya sanya face mask a fuskarshi, a matu?ar ruWe suke kallonshi bakunansu asake babu alamun zasu motsa.

 Sannu da fitowa Yalla6ai Boss man ne yayi maganar, Big guy yace barka da fitowa amsa masu yayi fuskarshi asake,
Sheikh Imam yace ya jikin yaron?
Prime minister yace Yayi bacci shiyasa muka ?yale shi zuwa time da zai farka
 Alhamdulillah, naji dadin jin hakan, baccin nan da yayi hutu ne agare shi

 Babana, muna ?ara yi maka godiya bisa ?o?arin da kayi mana, mun hana ka sakat mun kuma hana ka huta, Allah ne kadai zai iya biyanka..... fuskar sheikh imam dauke da murmushi ya furta bakomai Hateem, kada kaji komai, ai indai akan aikin lada ne bazani ta6a gajiyawaba, koda zan shekara inayi ne, ni dai fata na shine Allah ya dubi kyakkyawar niyarmu akan yaron nan ya bamu nasara akan ?udirin da muke dashi na ganin mun raba shi da miyagun dake bibiyar rayuwarshi jinjina kai kowan nan su yayi, shiekh imam ya daura da cewa idan na samu natsuwa kafin zuwa dare, Zan turama shi Awaisun addu o in daya kamata arun?a mashi akan komai da zaiyi amfani dashi, kada a kuskura abarshi ya yi gamon kan shi, tun da shi ba musulmi bane bai yi imani da Allah ba, shaidanun dake ajikinsa bazasu ta6a bari ya ambaci sunan Allah, ko ruwan addu a zaku bashi ku tabbatar yasha akan idonku idan bahaka ba shaidanun zasu iya zubar dashi ko su canza mashi ruwan batare da kun ankareba, tun da su ba ganinsu akeyi

 Insha Allah malam zamuyi ?okarin yin hakan acewar Boss man.

Ga dukkan alamu Prime minister Hateem bai lura dasu Batool ba, hatta shi kanshi chief owais din, wani iko na Allah salsabeel dake kallonsu har kallonshi sukayi babu alamun sun gane shi, nan take ya fahimci basu ru?e kamanninshi ba, saboda sau Waya suka ta6a ganinshi kuma a lokacin basu acikin hayyacinsu, jamimah da Azeeza da parveen su dama basu ta6a ganinshi ba, asume aka fitar dasu daga kurkukun.

 Lahh! Ji wani mai kama da Danish dinmu muryar Jemimah ce ta fargar dasu, kusan atare suka daura idanuwansu akan yaran
Zumbur jemimah ta mi?e taje gaban prime minister ta tsaya hada ru?e qugu tana ?are mashi kallon mamaki da al ajabi

?aya bayan Waya yake bin yaran da kallon, Ya fahimci kallon mamaki suke yi mashi, Boss man ne yai masu gyaran murya tare da cewa Sajeed, kuzo ku gaishe da Kawun Chief dinmu Owais sunanshi prime minister Hateem, wannan kuma shine chief dinmu Owais ya faWa yana nuna masu chief da hannun shi.
Atare suka mi?e tsaye suka nufi prime minister cikin girmamawa suka gaishe da shi, kafin suka gaishe da Chief Owais.
Murmushi prime minister yasakar masu har dimple dinshi ya lotsa, da mamaki suka kalli juna ganin yadda kamanninsa da danish suke ?ara bayyana.
 Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, My Son ina kuka samu kyawawan ?an mata da samari masu kama da jinin family dinmu? Ai ni nayi tsammanin Danish ne kadai yake kama damu amma sai nake ganin fuskokin ?an uwana akan faces dinsu kodai idanuwana ne suke nuna min badai ba ?
Sheikh imam na murmushi yace ba kai kadai ba Hateem, ni kaina tun da nayi tozali da yaran nan nake ta mamakin kamannin ku dasu

 Uncle, waWannan sune sauran yaran da muke kula dasu, ?an uwan danish ne chief owais Ne ya faWa yana nuna su da hannun shi.
 My son Allah Ya tayaku ru?o, Ina ?ara yaba maka da jinjina maka akan ?o?arinka calmly chief ya furta mashi thanks
 Sajeed, mu tafi masallaci, Batool kija sauran ?an uwan naki ku tafi Waki ku yi sallah, Boss man ne yayi masu maganar,
Cikin sanyin murya batool tace Idan muka kammala yin sallah zamu Iya zuwa Wakin Wan uwanmu Danish mu duba shi da ta furta maganar har chief owais saida ya kalleta kafin ya kau da idon shi.
Salsabeel ne yace ku ?ara hakuri yanzu bacci yake yi, sai dai zuwa anjima idan sun farka amsa mashi tayi da toh, tayi mamakin ganin yana sakar mata murmushi, yayi tsammanin idan sukaji muryarshi zasu gane shi amma still babu alamun zasu gane Win.
 Ina ?ar uwarku Unaisah ? Ya jefa mata tambaya, kafin ta bashi amsa boss man ya rigata cewa taje Wakin ummi ne
Prime minister yace In sha Allah zuwa anjima idan na dawo gidan zanyi magana daku ya faWa yana nuna su batool, amsa mashi sukayi da toh, hadi da yi masu godiya.

Bayan tafiyarsu Batool taja sauran ?an uwanta mata suka nufi Wakin su.





*SIR MUBARAK
'*



Tun wuraren ?arfe takwas na safe suka baro asibitin kafin tafiyarsu saida Sir mubarak yayima Dr fawan Alheri saboda yaji daWin Yadda ya taimaka mashi wurin ganin Jazz Ya samu lafiya, da matsakaicin gudu motarsu ta haura saman titi, Major ne yake yin driving dinsu, yayin da sir mubarak da jazz suke zaune a back seat na motar.

Ya ru?e hannun jazz acikin nashi, kamar ance za a ?wace mashi shi, Jazz sai faman lumshe idanuwanshi yake yi kamar mai jin bacci,
 Jazz me kake tunani naji kayi shiru tun da muka fito daga asibitin baka ce komai ba, cikin kulawa Sir mubarak yayi mashi magana yana dubanshi
In a cool voice ya furta Ina tunanin khadija, bata sha maganinta na safe ba bansani ba ko salsabeel Ya bata
Murmushin gefen fuska Sir mubarak yayi idan na fahimceka kana magana ne akan Yarinyar nan mai ta6in hankali ta gidan kajin da kuke kiwo ko ba haka ba ya fada da zolaya yana Waga mashi gira, tuntsirewa sukayi da dariya gaba Wayansu hatta major dake driving dariyar yake yi.
 Daddy dan Allah mu daina tuna abun da ya wuce sir mubarak ya ce okey na daina my son, tun da baka so
Gyaran murya Major yayi sir mubarak ya dago yana kallon fuskarshi ta cikin mirror.

 Sir, ina zamu nufa? gidanka ko can gidan da Yaran suke?

Shiru sir mubarak ya danyi kafin yace mu wuce gida, jazz yana son ganin mommynsa, nasan tayi kewarshi, in yaso daga baya sai muje can gidan Amsa mashi yayi da toh.

 Idan mun isa gida please ka kira tiger A waya ka tambaye shi awani hali yaran suke aciki, inason sani
Cikin girmamawa Major Ya ce in sha Allah Yalla6ai zan tuntu6e shi
Ajiyar zuciya sir mubarak Ya sauke tare dakai dubanshi ga Dr jazz,
 My son, ya zamuyi? Bansan ta yadda zanyima mommynka bayani ba, gashi ni ban iya ?aryaba, nasan dole ta shiga damuwa idan ta kalli fuskarka, fuskarshi a yamutse yayi maganar, har cikin ranshi baison 6acin ran turai duk da yasan zata fahimce shi amma dole taji ba daWi.
 Daddy kada ka damu, idan mukayi mata bayani zata fahimce mu in sha Allah
 Allah yasa my son daga haka babu wanda ya ?ara yin magana acikinsu, har suka shigo estate, Motarsu bata nufi ko ina ba sai katafaren gate din Gidansa
A harabar ajiye motocinsa sukayi parking, babu wanda yasan da zuwansu, da sauri Major ya fito ya zagaya ta baya ya buWe masu mota, sir mubarak ne ya fara fitowa kafin Ya taimaka ma Dr jazz shima Ya fito, hannunshi Waya dafe da waist din shi. saboda baya iya tafiya dai dai, tun lokacin da sir mubarak ya cakumi rigarshi ya buga shi da ?asa ?afarshi Waya ta lan?washe da?yar yake iya takata a yanzu.

A haka suka nufi cikin gidan, banda Major wanda tuni Ya nufi sauran ?an uwanshi sojoji dake kai komo a cikin gidan.
A zaune yake saman Sofa, ya Wauki wankan dark jeans and white V-neck shirt kayan sun bi shape din jikinsa, hankalinshi a kwance yake operating laptop din gabansa dake ajiye kan table,
Fitowa mom turai tayi daga cikin kitchen hannunta ru?e da mugs guda biyu na coffee, ta nufi cikin falon fuskarta asake taje gaban table din Zaki ta Waura cup Waya
 Ga wannan My son, Nasan zaka bu?ace shi Wagowa yayi fuskarshi Wauke da murmushi ya furta mom nagode da kulawarki agareni, kina ji da Wan nan naki
Kafin ta kuma cewa wani abu muryar ibad ta janyo hankulansu ga dubanshi, fitowarshi kenan daga cikin Waki Sai faman yin mi?a yake yi haWi da yin hamma, daga shi sai short a jikin shi
Muryarshi da shagwa6a ya furta mommy nifa ?
Zaki ne ya bashi amsa da cewa Na ?arfi ne zoka ?wata, Wan rainin wayau sai yanzu ka ga damar tashi daga baccin
Tur6une fuska yayi babban yaya jiya fa bamuyi wani isasshen bacci ba, shine nake yin ramuwar na jiyan
Dariya mom turai tayi shagwa6ar ibad har mamaki take bata, duk da shima jazz idan abun ya motsa yana yi mata shagwa6a
 Ranka zai 6aci ne idan ka ci gaba dayi min shagwa6a kamar wani ?aramin yaro,
Bubbuga ?afafuwanshi yayi hada ru?e qugunsa wato yayi sai dai ayanka shi
Mom turai tace sai fa kana ha?uri da shi, kasan autane kuma kai ka rainesa duk abun da yayi kai ne ka sangartar da shi
Ta6e baki Zaki yayi tare da kau da idonshi daga kan fuskar Ibad Ya mi?a hannu ya Wauki mug Ya soma kur6ar coffee..
 last born zoka kar6i wannan girgiza mata kai yayi no mommy, na hannun shi nakeso yasha ya rage min, wannan nakine ki sha a sukwane Zaki ya dakata da shan coffeen Ya waiwayo yana dubanshi, Ya rasa gane dalilin dayasa Ibad yake yi mashi haka, aduk lokacin da zai ci abu saiya sa rigima akan yaci ya rage mashi kamar wani tsaran wasan shi
 Kada ka damu zan shiga kitchen in haWa nawa, kai dai kar6i kasha mom turai ce tayi maganar
Ibad ya ma?e mata kafaWa mom ni ai nafison yasha ya rage min
Girgiza kai Zaki yayi tare da kallon mom turai yace zan rage mashi
 Amma ai baida yawa taya zai isheku ku biyu abunda baifi rabin cup ba
 Idan bai ishe mu ba, zan turo shi ya ?aro mana wani a kitchen
GyaWa kai tayi okey, Har ta nufi sofa zata zauna, sallamar sir mubarak ta katse mata hanzarinta,
Kusan atare suka kai idanuwansu ga duban ?ofar falon
Shigowa Sir mubarak yayi hannunshi dafe da dr jazz, tsabar firgice Yasa mom turai ta saki mug din hannunta gaba Waya ruwan coffeen Ya zube kan floor, Jikinta na 6ari ta nufe su, Hankalin kowan nan su ya tashi, zaki tuni ya dakata da shan coffeen a hanzarce ya mi?e ya nufi sir mubarak, Ibad kuwa hannayenshi biyu ya Waura saman kanshi yana ambaton mun shiga uku, Wan uwa Jazz meya same ka? Kayi hatsarin mota ne?

Muryar turai na rawa take fadin innalillahi wa inna ilaihirraji un, babe meya faru da jazz Wina? idanuwanta har sun fara fitar da ?walla,
Sir mubarak bai sauraresu ba, Ya nufi sofa da sauri zaki Ya taimaka mashi suka zaunar da jazz.
A Hankali Ya Wago Yana dubansu Waya bayan Waya kafin ya tsayar da idanuwanshi kan mom turai da tafara sharar ?walla, Jikinta asanyaye ta nufo su ta zauna gefen jazz ta ru?o hannun shi acikin nata,
 Kayi shiru bakace komai ba? Meya faru da jazz ?
 Daddy kai muke sauraro, acewar Ibad wanda tuni ya dawo gefen Wan uwanshi zaki ya tsaya hadi da ru?e qugunshi
A tsanake ya soma yi masu magana ku kwantar da hankalinku..... tunkafin ya ?arasa maganar, mom turai ta katse shi ta hanyar yi mashi tsawa tana fadin taya zakace mu kwantar da hankalin mu? Yaro ya fita gida lafiyarshi qalau yanzu kuma ka dawo dashi goshi Waure da bandage ga tabonni akan fuskarshi, sannan babu kayan da ya fita da su a jikin shi, ni dama tun jiya hankalina bai kwanta da fitar jazz ba, babe ka faWamin meya faru da yarona !! idanuwanta azazzare tayi mashi maganar.

Tun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login