Showing 141001 words to 144000 words out of 260999 words

Chapter 48 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

sunyi bala en yi mashi kyau, ya fito a garkuwarsa, Garzon namiji mai jini ajika, sannan kuma mai ji da kyau da ?arfi, haWaWdar sumar kanshi dark brown curly sun gyara mashi ita, sunyi cutting dinta sun Waure mashi ita, ta sauko saman dogon wuyan shi, takalman ?afarsa leather shoe ne launin black suit dinsa.

Fuskarshi tamkar anyi mashi make up tsabar haWuwa, ga wani irin zazzafan ?amshin turare dake kurWaWowa sa?o da lungu na jikinsa kamar wanda aka tsamo daga cikin kogon turare, Agogon hannunsa silver ce sai Waukar ido take Yi, wani abu da zai baka mamaki duk irin haWuwar da yai acikin kayan babu annuri akan fuskarshi ko mis?ala zarratin Ya haWe rai kamar wanda aka Waura ma aure da mutuwa, Yana tafiya a bubbuWe kamar wanda zai Yi dambe, Kyawun surar danish yayi matu?ar tafiya da Imanin Nurses din dake a kewaye da wurin da likitoci, all eyes on him ba matan ba mazan ba, kowa kallonshi yake yi kamar zasu haWiye shi, kai hatta Jami an isod sai da gabansu ya faWi sunyi matu?ar girgiza da ganin shi, har dai wani daga cikin su ya gaza jurewa muryarshi ?asa ?asa cikin harshen turanci Ya furta Nayi tsammanin daga Chief din mu angama halittar Namiji mai kyan fuska da sura, ashe ba haka bane nayi kuskure, a yau naci karo da namijin duniya kamar garzonmu OWAIS, wannan Yaron Bai da mararraba da shi, banbancinsu Launin fata


*=؋?ABBAN SOJOJI=؋?*
*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*

*Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da kuma kurkukun ?addara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala, ga wadda za a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message from Boss Bature*

*
'? Mu haWu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*_


~Middle step~

3,F 'DB/1d'>?
?d'


_THE PRISONERS E25=?%?=ث?_



*Daga al?alamin Boss Bature*



Confusion of the heart=ث?


Jami in dake gefen wanda yai maganar ne ya daura da cewa Ni kaina na girgiza da ganin matashin saurayin nan, Gaba Waya ma na rikice, na tabbata ko shi Boss Owais din Yai arba da wannan Yaron sai yayi mamakin shi.

Amenity Ward Ya ruWe da sambatun mutane akan kyawun Garkuwa, shi ko Dan tahalikin Duk yabi ya rikice A rayuwarshi ya tsani kallo saboda Yana affecting din natsuwarsa, Yana Haya?a shi, idanuwanshi sun makance neman Angel Yake yi, Gata akusa dashi amma ya kasa ganewa, sai ?an waige waige yake yi a ?o?arinsa naya gano ta, An rasa me Iya buWe baki yayi mashi magana acikin ?an uwan nashi, baisan cewa shine ya ruWe su ba, Ya canza masu sosai cikin sabuwar shigarshi.

Sai da Haris Ya Waga murya Ya furta Danish gamu anan tukunna ya wurga reddish eye balls dinsa akan fuskokinsu, cikin takun sauri Ya nufe su yana ?arasawa ba yi ?asa a gwiwa ba Ya rungume Angel a saman broad chest dinsa, Ya cusa fuskarshi saman kafaWarta Yana faman sauke ajiyar zuciya, lumshe idanuwanta tayi lokacin da ?amshin turarensa Ya daki hancinta, gaba Waya taji ta a wata duniya tacan sama jannati, in a throaty voice ya furta mata bana son kallo, Ki faWa masu su daina kallo na, suna cutar dani

Sam takasa yin magana, saboda yayi tighting dinta a kirjinshi, ya zagayo da arms dinsa saman bayanta, mutanan dake awurin sai faman sakin murmushi suke yi kamar zautattu, bakomai ne ya burgesu ba face hugging din da Danish yai ma Angel, sunyi tamkar ma aurata, kayan jikinsu sun yi fitting dinsu black and red, kamar furanni.

Gyaran Murya Waya daga cikin Jami an isod Yai masu, muryarshi a bubbuWe ya furta Zamu Iya tafiya, amma kafin nan Shi wannan Yaron Ina face mask dinsa Yake ? Ya yi tambayar Yana nuna Danish da indext finger.

Da sauri Dr Mark, ya tura hannu cikin front pocket din coat dinsa, Ya zaro face mask, Ya nufi Danish, yana fadin

 Handsome man, namanta ban sanya maka mask dinka ba, Kar6i ka sanya kamar yayi magana da gunki, Ko motsi Baiyi ba, tunda ya ?an?ame Angel dinsa yayi shiru kamar maiyin bacci.

Numfasawa dr laura tayi sai lokacin ta samu damar buWe baki tace Danish yana yi maka magana, kaga sauran ?an uwanka duk sun sanya nasu face mask din, Kaima ya kamata ka kar6a ka sanya, jami an isod suna jiran ku zasu Wauke ku zuwa Airport ne


Lamarin Ya Waure masu kai, Babu alamun zai motsa, Ga Angel tana so ta raba jikinta daga nashi don ta lallashe shi, ya?i bari tayi hakan saboda matsetan da yayi a chest dinsa, hatta numfashinta da?yar take Iya fitar dashi


Cikin ?agara Haris Yace dan Allah Danish ka sake ta, Ka kar6i abun fuskar kai ma ka sanya ko mun samu mu tafi

Magiya suka dinga yi mashi akan ya saki Angel Amma Ya?iya ko kallo basu ishe shi ba

?aya daga Cikin Jami an Isod Ne yai nazari akan Yaron, kasancewar suna da kaifin basira, nan take Ya fahimci wani abu dangane da shi, Waya bayan Waya ya kalli nurses din dake a ward din da likitocin da suka tsaya suna kallon su, Muryarshi a kausashe Ya furta Idan ba damuwa kowa Ya koma bakin aikinsa !

Jin hakan yasa kowan nan su Juyawa suna tafiya suna waiwayon prisoners, Mutun Biyar ne suka rage, dr laura da mark da brown sai nurse jessica da nurse rebecca.

Tun kafin Jami in Ya tambayi lafiya su basu tafi ba? Dr laura tace Muna so muyi masu rakiya har zuwa airport, nasan suma Yaran zasu so hakan

Jinjina kai yai tare da Waura eye balls dinsa kan Bayan Danish.

 Danish, likitocin da suka duba lafiyar ku ne su ka rage sai kuma mu jam an da muka zo domin tafiya da ku, babu kowa bayan mu, muna jiranka please kada ka 6ata mana lokaci ! Cikin kwantar da murya yai mashi magana.

Sai da Ya ambaci hakan tukunna da?yar Ya raba jikinshi daga na Angel, numfashinta da sauri sauri Yake fita, hada tarinta saboda mugun sha?ar da tayima turarensa ya sar?eta.

Dr mark ne Ya sanya mashi mask din saman fuskarshi, da zolaya jami in yace ka tabbatar ka rufe mashi hada idonshi, don wannan idan mutane suna kallon shi tsab zai haWa mana traffic jam a saman titi

Gaba Wayan su suka sanya dariya, ban da Danish, sam babu kwanciyar hankali atattare da shi, Hakanan Yake jin haushin mutane babu gaira babu dalili, ji yake kamar ya rufe su da bugu har sai sun mutu. Su Batul kuwa duk sun sha jinin jikin su, ganin Jami an Isod suke Yi tamkar mutanan prison, tun da suka shigo ko motsin kirki sun gaza yi, Sai faman binsu da ido suke yi, ko magana jami an su ka yi sai sun razana babu wanda Ya lura da hakan.


Bayan Dr. mark ya kammala sanya mashi mask din, ya juya ya ru?o hannun Angel acikin nashi, a jere suka nufi Hanyar fita daga ward din Yayin da dr laura da mark da brown suke Abayansu, su kuma jami in Isod suna a kewaye da su, domin basu tsaro, duk inda suka gifta a sibitin ido na akansu, ba marasa lafiyan ba, ba ?an zuwa dubiyan ba, ba Ma aikatan cikinsu ba, kowa hankalin shi na akan su, Danish sai ?ara matse mata hannunta yake yi a cikin nashi, hankalin ta ba akwance ya ke ba don ta fahimci akwai wani abu dake damun shi.


Kaitsaye suka nufi parking space na asibitin, wasu dan?ara dan?aran motoci ne masu numfashi jigunannun gaske, a killace a harabar, da su akazo Waukarsu, hankalin su Batul Ba ?aramin tashi yai ba, Basu ta6a ganin abu irin wannan ba, Motocin dake a killace aharabar suke ta faman bi da ido, Angel ce tayi amfani da harshen hausa wurin yi masu magana akan su natsu kada su tsorata, abun hawa ne da akeyin anfani dasu wurin tafiya mai tsayi wadda ?afa bazata Iya yinta ba, sai da tayi masu bayani cikin kwantar da murya tukunna suka fara sakin jikinsu.

Kafin su shiga motar sai da aka fara sanya kayan su a boot, akwatuna ne da duffle bags kusan guda biyar, Suturar da dr laura ta siya masu ce, tare da Takalmansu da magungunan da zasu dinga sha, da sauran care product da zasu yi amfani da su. Bayan an kammala shigar da kayan cikin motocin Waya bayan Waya jami an suka bude masu car doors din, motar farko Danish ne da Angel sai Batul suka zauna a mazaunin Baya, Mota ta biyu Gabriel ne tare da Haris da Hanna, Mota ta uku Naufal ne da parveen sai Javed.

Dr. laura ta nemi alfarmar jami an akan tana son su bata damar Waukar jemimah da Azeeza a motarta, Jami an suka ce mata zata Iya Waukarsu ba wani abu, A back seat na motarta, Azeeza da Jemimah suka shiga, Ita kuma ta zauna A driver seat domin Yin driving dinsu, Dr mark da dr bown suma hada su za a tafi kaisu airpot din, A cikin motocinsu zasu tafi tare da Nurse jessica da rebecca.

Tun da prisoners suka shiga cikin mota, suke ta ?an kalle kalle wa yaga ba?auye yazo birni, duk sun sha jinin jikinsu, Fargaba suke Yi kada a cutar dasu, badan Angel ta kwantar masu da hankalinsu ba, da kuwa Anga hauka, kusan A lokaci Waya masu tu?a motocin suka tada su, Jemimah ta rungume Azeeza jin sautin tashin motarsu, Jikin su ya hau yin kerma kamar waWanda sanyi ya kama, Dr laura dake kallonsu ta madubin motar, fuskarta Wauke da murmushi ganin yadda suka ?an?ame tace masu su kwantar da hankalin su, babu abunda zai same su.

A motar su Parveen Ta ?an?ame naufal saboda tsoron da taji, hada javed sun haWu sun mannewa juna kamar kifayen gwangwani.

A motar su Gabriel kuwa, Hannah da Haris sun ?an?ame shi, sai faman ti?ar dariya yake yi, shi dama wayayye ne bakomai ne Ya manta na memory dinsa ba, Hannayen shi biyu ya sanya saman bayansu Ya ?ara tighting dinsu ajikinshi yana kwantar masu da hankalinsu.

Danish kuwa tun da suka shiga motar, ya kwantar da kanshi saman kafaWar Angel, ko motsi baiyi, Yana zaunea left hand dinta, yayin da Batul take a zaune saman seat din dake a right hand dinta, Ganin yadda Batul ta ruWe jin tashin mota, Hannayenta biyu ta Waura saman kanta, kamar zata fasa ihu da sauri Angel ta dam?o hannunta tare kwantar mata da kanta saman laps dinta, ?an?ameta tayi sosai tana faman sauke ajiyar zuciya, abun ne yazo masu wani iri basu saba ba.

Slowly motocin suka nufi hanyar babban gate din asibitin, gaba da bayansu motocin Jami an isod ne, Sun sanya motocin da aka Wauko su dana su dr. laura a tsakiyar nasu motocin domin basu tsaro.


Da matsakaicin gudu motocin suka haura saman titi, prisoners sun ga abunda yafi ?arfin idanuwansu, Ta glass din window su ke Hangen dan?ara dan?ara gine ginen birnin san antoni, masu ?ayatarwa, ga wuraren sha?awata da kuma mutanan dake zarya ta ko ina, sun natsu suna kallon ikon Allah abun ya Waure masu kai.

 My man, bacci zaka yi ? angel ce tayi mashi magana tana duban fuskarshi, tayi mamakin ganin zufa na tsastsafo mashi saman forehead dinsa, duk da sanyayyan Sanyin A.c na motar, Batool tuni ta mi?e daga saman laps din Angel, ta koma bakin windown motar tana kallon Ikon Allah.
In a low voice ya furta mata Am not feeling well, ina jin wani iri a jikina kamar wani abu zai faru dani shafa sumar kanshi tayi da hannunta In sha Allah ba abunda zai faru da kai My Man, Ina atare dakai, so ka kwantar da hankalin ka, bari nayi maka addu a ta faWa haWi da manna la66anta saman lallausar sumar kanshi, addu o i ta soma karantowa tana tottafa mashi asaman kanshi.

Muryar Batul ce ta katse mata hanzarinta Angel wai su mutanan duniya dama haka suke da gudu kamar zasu tashi sama ?
Dariya ce ta kubcewa Angel, ta wurga idonta kan batul data mannewa glass din tagar motar, ta ?ura ido tana kallon al amurra.

 Batul ba mutane bane suke Yin gudu, Abun hawan da muka hau ne ya ke yin gudu damu

Ba tare da batul ta juyo ta kalle ta ba tace Oh, yanzu na fahimta daga haka bata ?ara cewa komai ba.


*UMMIN AMERICA=؋?*

A hankali motar su take tafiya saman shantalelen titi, tana a zaune saman front seat, ta Wauki wankan pant suit sunyi bala en yi mata kyau, dogon wandone fari da sexy vest fara ta matse ta kirjinta Ya fito sosai, don ma ta Waura Blue coat daga sama, ta canza launin sumar kanta zuwa blue, light make up ne asaman face dinta , fararen idanuwanta suna a manne da farin glass hakan ba ?aramin ?ara mata kyau ba, Matar dake driving dinta, ?awarta ce *NATASHA* baturiyar England, Aminnan junane, sai dai daga ganinta babu digon imani a zuciyarta, fitsararrace ta bugawa a jariga. Kayan dake a jikinta da su da babu duk Wayane, doguwar rigarta tamkar net take shara shara kana Iya hangen inners din ta, A yayin da take zaune saman driver s seat, Cigrette ce a hannunta na hagu, Wayan hannun kuma da shi take juya sitiyarin motar daga gani ta ?ware a iya driving, Tsabar Iya shan taba harta hanci ta baki take huro hayakinta.

fira suke Wan ta6awa a tsakaninsu cikin harshen turanci.

 Zanyi kewarki ummi, yanzu idan kika tafi yaushe zaki dawo? Natasha ce ta jefa mata tambayar.

Numfasawa tayi kafin calmy ta furta  bazan daWe ba, temporary guardianship ne ba permanent ba, da zarar na kammala yi masu aiki zan dawo America

Dariyar sha?iyanci Natasha ta saki, tana mai cigaba da hura hayakin tabarta.

 idan ki ka yi wata Waya baki dawo ba, zan biyoki Nigeria don bazan Iya jure rashin ki ba ta fada tana duban fuskar Ummi.

 Zaki tafi ki barni da mutananki, don nasan ba zasu ?yaleni ba, da zarar sunji ki shiru ni zasu tuntu6a, Ummi tace Zaifi ki canza layin wayar ki, kafin in dawo, don bana so kowa yasan da zancen barina ?asar nan ko kuma inda zanje, Yana daga cikin sharuWWan da sojoji suka gindaya mini.

 Ai nayi mamaki da kika amince zaki kar6i jagorancin kula da yara har goma sha Waya, idan nice bazan Iya ba, kema nasan ba hakanan kika kar6i aikin ba. akwai wata manufa a ?asa ta ?are maganar tana dariya.

Ummi tace kamar kin shiga zuciyata, tabbas inaso naje Nigeria ne don karan kaina bawai don aikin da sojoji suka bani ba, nima akwai abun da zai kai ni, da ba don haka babu abun da zai sa in bar America.

Natasha tace yayi kyau mutuniyata, ina fata zaki cigaba da she?e ayarki, bana so silar zuwan ki ?asarki ki shiryu nafison ki ?ara lalacewa ki 6ata masu mazajen auransu, dariya suka sanya gaba Wayansu.

Ummi tace Yaran fa da aka bani in jagoranta kyawawane fa akwai wani zazzafan Yaro acikinsu, yana da kyawun sura lumshe ido natasha tayi muryarta tamkar ta mashayin giya tace kice yaron babbar harka ne, tun kafin ma in ganshi na ?yasa

Ummi na dariya tace yadda kike shaiWaniyar nan nayi imanin idan kika ganshi da?yar zaki Iya runtsawa, kallon shi kaWai zai tada maki da maitarki, Natasha nayi mu amala da maza kala daban daban amma shi wannan Yaron na musamman ne, Kamar dai Chief Owais, kinsan shima Yana da zazzafar sura.

Natasha tace Har yau ban daina kallon hotonshi ba saboda bana gajiya, aduk lokacin dana rasa abokin harka hoton shi nake kallo in rage zafi, gayen ya haWu duniyace shi cikin jin shau?i Tayi maganar

Ta ?ara da cewa ?awata zan baki shawara, matasan Yaran da za a baki rainon su, kada ki raga masu, idan jarabarki ta motsa kibiya bu?atarki da su, ai ke wannan Aikin da sojoji suka baki gaba ta kai ki, in banda abunsu sun ta6a ganin inda aka ba kura ajiyar nama ? Da sha?iyanci ta faWa tana sakin shu umin murmushi na tantiran ?an duniya.

Ummi ta Wan zaro ido haWi da cewa ba zai yiwu ba natasha, ke kin san wanene Chief owais, yafi bomb bala i, akan shi na fara jin tsoron namiji a duniyar nan, Mutumin bai da fara a Yana da kamun kai, sannan bai da imani idan ya dam?i Mara gaskiya, idan har na kuskura na ?etare Iyakata akan Yaran wlh tsaf zai Iya kasheni har lahira, ni ko dai ban shirya mutuwa ba, akwai sauran bururrukan da nakeson cimmawa.

Fashewa Natasha tayi da dariya fararen ha?oranta a jere kamar gonar auduga, sam firar su bata Wauke mata hankali ga yin driving din da take Yi ba, har ta zu?e tabar hannun ta duka.

 Dole kiyi mini dariya ?ar rainin wayau ta fada tana hararar ta.

Tsagaitawa Natasha tayi da yin dariyar ta dubi fuskar Ummin america mutuniyata, Kina ta zumuWin zuwa Nigeria, banji kina maganar mutumin ki ba cikin rashin fahimtar kalamanta ta furta Wa? Kashe


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login