Showing 171001 words to 174000 words out of 260999 words

Chapter 58 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

 Bakomai yake iya ci ba, danish me kake son ci ? Ta jefa mashi tambayar, shiru bai bata amsa ba, kamar tayi magana da kurma.
Ummi tana yamutsa fuska tace ai na lura kamar mune muka takura mashi, ?warama ka saki jikin ka, saboda atare zamu cigaba da rayuwa acikin gidan nan

Boss man yace baya son ba?in fuska ne, amma tunda naga yafi sakewa da shi, Ki jaraba bashi wannan muga idan zaici yai maganar tare da ru?o plate din farfesu ya mi?a mata, bayan ta kar6a ta furta mashi thank u ta tura plate din agaban Danish.

Cikin muryar raWa tace pls ka saki jiki ka ci, tunda gani atare dakai, banason kana damuwa jinjina mata kai yai alamar toh, duk don ya saki jikin shi yasa ta sanya hannu a plate din ta soma ci shima ya sanya hannun shi suka cigaba da ci atare.
Sun dauki lokaci suna cin abincin, sunyi kulu wash rabu hani an kafin daga bisani Waya bayan Waya suka fara mi?ewa,

Masu aikin gidanne suka tattara kayan abinci, bayan sun kwashe komai suka gyara dining room din tamkar ba a ta6a 6ata shi ba.

Falo suka koma, kowannansu ya zamu wuri saman sofa ya zauna, kamar yadda Man Ya basu Umarni, yana daga zaune shida ummi suna fuskantar su, sanyin A.c sai ratsa fatar jikin su ya ke.

Sun natsu suna jiran jin me zaice da farko dai Ina yi maku barka da zuwa gidan nan, ina fata kunji daWin kasancewa acikin shi ya faWa yana dubansu.
Amsa mashi suka yi da eh, yace  good, ina fata zaku bamu haWin kai, mu zauna peacefully babu faWa babu cacar baki, Waga mashi kai sukayi alamar eh.

Ya ?ara da cewa na fahimci bakomai ne kuka sani ba, to duk abunda baku gane ba kada kuce zakuyi gamon kanku, hakan zai iya haifa maku matsalar da bama fata, idan kunga abu kunaso kuyi amfani dashi baku san yarda akeyi ba, Ga auntyn ku nan yai maganar yana nuna ummi dake zaune saman sofa ta Waura ?afa Waya bisa Waya.

 Ku tambayeta zata koya maku, kada kuji shakkar komai, ku Wauke mu tamkar iyayenku ko yayyanku, ina fata kuna jina ? Jinjina mashi kai su ka yi, Angel tayi shiru tana kallonshi, muryarshi ta tsaya mata aranta, ji take kamar tasan me irin muryar sai dai takasa gano komai.

 Zaku Iya tambayar ?ar uwarku Angel itama, don na fahimci kamar tafi ku sanin wasu abubuwan amsa mashi su ka yi da toh.

 Sannan duk abunda kuke bu?ata ta 6angaren aike ni zaku yi ma magana, in sha Allah zanyi maku shi, Idan time din sallah yayi zanzo in tafi da mazan dake acikin ku muyi sallah akwai wurin da muke yin ibada acikin gidan nan, ina fata gaba Wayan ku musulmai ne ya faWa yana dubansu
Parveen tai karaf tace banda Danish da Gabriel sun?i kar6ar shahada zaro ido ya Wanyi yana duban fuskar Danish daya haWe rai babu annuri.

Gabriel Yace nifa ?arya take yi min, Nima musulmin ne

Da zolaya boss man yace idan har dagaske kai musulmi ne to ya akai naji sunanka bana musulmai ba ?sunnar dakai ?asa Yai yana faman sakin murmushi.

Angel tace nice namanta ban biya mashi shahada ba, ya faWamin yana so ya musulunta shima jinjina kai boss man yai, ya dawo da dubanshi gareta shifa danish? Wani addini yake yi ?

 Bashi da addini dafe kai boss man yai Eyyah banji daWin jin hakan ba, kuma bashi da ra ayin ya musulunta kamar Gabriel ? Girgiza mashi kai Angel tayi bayasoma anayi mashi maganar ai, ranshi 6aci yake yi, shiyasa muka ?yale shi

 Okey, kada hakan ya dameku, in sha Allah asannu zamuja ra ayin shi ta6e baki Danish yai jin abunda boss man yace.

 Gabriel na dawo gareka, tunda kana so ka musulunta, babu bu?atar 6ata lokaci, Zan biya maka kalmar shahada saika maimaita da kyakkyawar niya murmushi gabriel yasaki bashi ba hatta sauran ?an uwanshi sunji daWi, ba tare da 6ata lokaci ba, Ya biya mashi kalamar shahada, wani irin daWine ya lullu6e su Angel, shima Gabriel din daWin yake ji sai faman washe baki yake yi.

 Ina taya ka murnar shiga addininmu, ko kana bu?atar na canza maka suna? tun kafin gabriel ya bashi amsa su Batul su ka yi saurin cewa Eh wallahi acanza mashi, sunan shi wahalar faWi yake yi mana, dariya boss man yasaki jin abunda suka ce.
 Okey, daga yau zamu dinga kiranshi da..... bai ?arasa sunan ba yai shiru yana kallon fuskar Gabriel duk sun ?agara da suji wani suna za a sanya mashi.

 SAJEED wani irin ihun farin ciki suka saki, Sunan yayi bala en yi masu daWi musamman Azeeza.

 Ina fata sunan yayi maka ? Jinjina mashi kai Gabriel yai eh, nagode sosai
Boss man yace okey, daga yanzu sunan da zaku dinga kiran shi da shi kenan wato Sajeed, Kefa Angel meye asalin sunanki farfari tayi mashi da ido kafin ta bashi amsa da cewa Unaisah
Tamkar baisan sunan ba yace wow suna mai daWi, mai zai hana kema mu dinga kiranki da asalin sunanki zumbura mashi baki tayi ba tare data furta komai ba, tana son asalin sunanta sai dai tafi son sunan Angel saboda daddynta ne ya za6a mata shi.

 Dan Allah Angel ki amince mu dinga kiranki da Unaisah Yafi daWi Allah Batul ce tayi maganar, Hannah tace nima nafison Unaisah din yana da daWi
Haris ma yace nima shine za6ina, Unaisah
Ta6e baki Angel tayi tare da kallon fuskar Danish don taji me zaice, batasan boss man na kallon ta ba, Ya fahimci tafi ?aunar Danish akan sauran ?an uwanta, saboda yadda take bashi muhimmanci.

Da ido tayi mashi alamar ta amince da sunan ko kuwa ? ?aga mata gira yai alamar eh.
Dawo da dubanta tayi akan fuskar Boss man shikenan na amince, adinga kirana da Unaisah
Murmushi ya saki ba tare da sun gani ba saboda mask din fuskarshi.
Javed ne yace  um sallah ma Angel ta koya mana amma bamu taba yi ba dama tace in muka zo zamu rinqa sallah da karatu

Jinjina kai yayi tare da fadin  karku damu zamu rin?a karatu tare in sha Allah komai zaku iya wanda ya shafi addinin muslunci Da alama sunji dadin maganar
Jemimahh tace wai kai ba zaka cire abun fuskarka ba ?
Girgiza mata kai yai a a tace  to meyasa baka son mu ganka? Ko dai mummuna ne kai baka da kyau ? Dariya ce ta kubce mashi.

Azeeza tace bakya jin magana jemimah ina ruwanki da shi? Ke komai sai kin nuna za?ewa harara jemimah ta watsa mata Ni ki ?yale ni, ta faWa tana duban shi dan Allah ka cire muga fuskarka
Javed yace nima inason naganka, tun da kace atare zamu rayu agidan nan, please ka cire mu ga fuskar ka.

Girga mashi kai yai Ku yi ha?uri ba yanzu ba, tunda muna atare wata rana zaku ganni
Angel tace babu komai, Allah ya nuna mana lokacin, Ni sai na ke jima kamar nasan muryarka don dai kace ba yanzu zaka buWe fuskarka ba ni kuma da saina gane wanene kai hakanan ta faWa bada wata manufa ba, tasan batasan shi ba.

Murmushi yai ba tare daya tanka mata ba, kallon Ummi yai, tun da ta zauna tana sauraron su bata ce komai ba
 Ba abunda zaki faWa masu ne ?
Yamutsa fuska tayi kamar bata son furta magana tace naso yau in taimaka masu su gyara kansu, amma nabari sai zuwa gobe ko jibi, idan na ?ara hutawa

Yace okey, ku tashi mu tafi inaso zan nuna maku ko ina na cikin part dinku, duk abunda kuka gani wanda kuke neman ?arin bayani akanshi Ni zaku tambaya suka amsa mashi da toh.
Mi?ewa sukayi Ummi ma ta mi?e don tana son itama ta ?arema ko ina na part din kallo, cikinsa da wajensa.
Yinin Ranar sunsha yawo, Sunga abubuwan ban mamaki dana Al ajabi, ido ya samu abinci, kamar karsu dawo cikin gidan, Boss man yasha tambayoyi kamar ?an jarida, duk abunda basu gane ba sai sun tambayeshi ba ?aramar wahala yasha ba, itama ummi tana taimaka mashi wurin amsa masu tambayarsu, duk yawon da suka sha basu le?a wajen gidan ba, kuma basu shiga sauran part din ba.

*JOS CITY*


Idan muka koma 6angaren Alhaji ubaid, tunda garin Allah Ya waye da sassafe Benazir ta farka tana sambatu akan mijinta da ?arta, Alhaji ubaid Ya jira kiran Dr.shureim sai dai shiru, har kiran layin wayarshi yai amma bai Waga ba, ya kira Alhaji musa akaci sa a kiran ya shiga kusan sau goma tana ringing ba ayi picking ba, gashi lokaci yana ta tafiya babu alamun zuwan Shureim, daga bisani suka kira likita domin duba lafiyar benazir, bayan ya duddubata ya faWa masu cewa lafiyarta ?alau, sai dai akwai abun da ta ?wallafa rai akanshi yaji tana fadin mijinta da ?arta yace to kada su kuskura suce zasu faWa mata zancen babu su, don a halin da take aciki yanzu bazata Iya jurewa ba, zata Iya samun ta6in hankali, zaifi suja baki suyi shiru, sannan suci gaba da kwantar mata da hankali har zuwa lokacin da zata samu natsuwa sosai, tukunna su faWa mata, sunji dadin shawarwarin da likitan ya basu, bayan tafiyarshi cikin ikon Allah, Benazir ta dawo hayyacinta a lokacin da basu yi tsammani ba, ganin Iyayenta a gefe da gefen gadon da take akwance yasa ta rushe da kukan farin ciki tana ambaton sunayensu haWi da ro?on yafiyarsu akan babban laifin da ta aikata na guduwar da tayi ba tare da sanin su ba, tayi mamakin jin suna kwantar mata da hankalinta, sukace su basu ru?eta aransu ba, sun yafe mata, ta daina kuka komai ya riga daya wuce, tuna baya baida amfani tun da ya riga da ya faru, ?addarace da babu wanda ya isa ya canza ta, ha?i?a taji daWin kyakkyawar tarbar da ta samu awurinsu tayi tsammanin zasu koreta ne idan sun ganta, saima suka koma suna lallashinta haWi da tarairayarta, abinci ma abaki hajiya layla ta bata shi, duk bayan ?an mintuna sai ta tambayesu ina mijinta da jinjirar data bari a cikin kwamin wanka? tana son tagansu, idan suna agida dan Allah su taimaka su kaita wurin su, hajiya layla ta bata ha?uri da cewa sunyi tafiya basa a ?asar amma tana da tabbacin sun kusa dawowa, sai lokacin tace toh ita yarinyar ta rayu? Waye ya rene ta harta girma? Kuma ya sunanta ?
Hajiya layla tace ta rayu mana, kyakkyawar budurwa ta Wauko hasken fatarki, kamannin fuskarta ne dai ta Wauko na daddynta, hankalinta ba ?aramin kwanciya yayi ba, tana ta faman sauke ajiyar zuciya tace baki faWa min sunanta ba? Kuma tasan ni? An faWa mata sunan mahaifiyarta? Kuma Kuna nuna mata hotona ? Shiru hajiya layla tayi don batasan amsar da zata bata ba, ita kanta ba zumunci take yi da tajuddeen ba, saboda bada son ranta ya auri Benazir ba, shiyasa ko zuwa gidan bata ta6a yi ba, tun lokacin da suka koma dubai da zama, a hotone ma ta ta6a ganin Angel din, taji nauyin amsar da zata ba benazir, da?yar ta Iya furta mata sunanta Angel, tana faman murmushin ya?e tace ai tasanki ya za ai mu ?i nuna mata hotonki, duk in tajudden ya kawota gidan nan sai mun nuna mata hotunanki, Yarinyar tana sonki sosai, kullum maganarta ina mamanta take? Yaushe zata dawo? Meyasa kika tafi baki waiwaye ta ba jin hakan yasa benazir ta fashe da kuka, Hajiya layla duk tasha jinin jikinta, fargabarta ranar da Allah zai haWa benazir da ?arta idan har tana araye tabbas zaiyi wuya yarinyar ta amince da ita, ga kuma ?aryar data faWa mata.

Cikin shesshe?ar kuka benazir tace amma dai baku fada mata a yanayin da na tafi nabarta ba ko ? Hajiya layla tace eh bamu faWa mata ba, mun dai ce mata kin 6ace ne ba asan inda kika tafi ba, to dayake yarinyar tana da tawakkali kuma tana samun kulawar tajo da kuma kulawar da muke bata hakan bai dameta sosai ba
baiwar Allah benazir jikinta duk yai sanyi, tace Ina aneelerh da mijinta ?
Hajiya layla tace ai mijin aneelerh baya nan shima tare suka yi tafiyar, ta matsa lamba akan tana son akaita gidansu Aneelerh don taganta, Alhaji ubaid ya sanar da ita cewa ai basa garin jos sun koma abuja da zama, badan taso ba ta ha?ura, damuwar hajiyar laila Waya kada tace su nuna mata hoton ?arta saboda babu maishi acikinsu, har ?wara Alhaji ubaid wata ?il asamu hutunanta na yarinyata saboda yana son yarinyar, cikin ikon Allah benazir bata tambayesu game da hoton Angel ba, saboda halin damuwar data shiga gani take kamar bazata ta6a ganin mijinta da ?arta ba, duk da mommynta ta kwantar mata da hankalinta.
Masu gadin gidan kusan sau uku suna shigowa cikin gidan domin duba lafiyar benazir, duk sun damu da ita, haka zalika zainab takasa samun sukuni duk bayan ?an mintuna saita le?o ta dubata, hakan ba ?aramin daWi yayi mata ba ganin yadda kowa ya damu da ita.
Tana akwance saman gadonta, hajiya layla tana a gefenta, a lokacin Alhaji ubaid Ya koma dakinshi, damuwar duniya ta ishe shi, tun da ya jaraba kiran layin shureim dana Alhaji ubaid basu Waga ba, ya rasa sukuni, sai faman yin zarya yake yi acikin Wakin shi, kaf family dinsu babu wanda yasan da dawowar benazir, saboda bai sanar da su ba, hatta mutanan da suke zumunci da su bai faWamawa ba, saboda mai gemu ya basu shawarar su dan jinkirta tunda ba asan wanene yai silar yi mata asirin ba, zasu Iya ?ara cutar da ita idan suka ji cewa tana araye kuma ta dawo gida, da ace Iyayensu na araye da kuwa sune mutun na farko da zai fara sanarmawa donsu taya shi murna sai dai babu su, mutum biyu ne yafi yarda dasu ?anin shi Alhaji musa sai ?anwarsu autar gidansu Hajiya Laurat, second wife din mai girma sharafuddeen obinna, itama ya jaraba kiran layin wayarta bata yi picking ba, abun duniya duk ya ishe shi.

tunda tayi wanka ta canza kayan jikinta zuwa rigar shan iska bata ?ara saukowa daga saman gado ba, ta tsare hajiya layla da tambayoyi
 Mommy shifa yaya shureim ko baya kasar ne ?
 Yana agidan uncle dinki
 Baku faWa mashi na dawo ba ne?
 Mun faWa masa tun jiya da daddare shima yayi farin ciki hada kukanshi, yace ma yau zaizo saboda ke murmushi tasaki naji dadi Allah ya kawo shi lafiya, nayi missing din yayana
Hajiya layla ta amsa mata da ameen.
Kafin benazir ta ?ara furta wani abu, Alhaji ubaid ya shigo da sallama abakinshi, atare suka Wago suna kallon shi, da sauri benazir ta mi?e zaune tana ambaton sunanshi
Murmushin yasakar mata kafin ya zauna daga gefen gadon yana dubansu yace Bansan meya faru ba, Ina ta kiran layin shureim dana musa babu wanda ya Waga acikinsu, Har laurat na jaraba kira itama bata Waga ba kafin wani ya furta magana acikin su ba zato ba tsammani, sautin ringing din wayarshi ya daki kunnuwansu, hajiya layla tace wata ?il wani daga cikin su ne yake kiranki da sauri ya ciro wayar daga aljihun shi ya duba sunan me kira, murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi
 Wanene ? Layla ce ta tambaya ganin yadda ya saki fuska
 Musa ne Ke kira ya faWa tare da picking call din Ya kara a kunnan shi
Saboda ji da kai na Alhaji musa sai da Ubaid Ya fara yi mashi sallama tukunna ya amsa mashi da cewa wa alaikum salam, ina kwana yayana fatan kun wayi gari lafiya
Alhaji ubaid na faman washe baki yace lafiyalou, ya iyalin naka ?
 Suna lafiya atakaice ya amsa mashi, tun da ubaid ya fara waya, layla da benazir suka zuba mashi ido suna kallon shi duk da basa Iya jin me alhaji musa yake fadi
 Shureim bai faWa maka zancen dawowar benazir ba ? Ya tambaya ne don yaji baya da niyar yi mashi maganar
Da gadara Ya furta ya faWa min, tun Wazu da safe, na tayamu murna, Ina fata tana lafiya
Alhaji ubaid yace ai gatanan ma zaune kusa dani, Ko in bata wayar kuyi magana ne ?
Da sauri yace No need, basai munyi magana da ita a waya ba, dama dalilin da yasa na kira naga missed call dinka ne, Wazu da safe shureim ya shirya zai taho nan jos, Ni na hana shi, nace mashi ya bari zanyi maka magana kuzo nan abujan gidana da mamaki Alhaji ubaid yace amma dai wasa kake yi min ko? Tayaya zakace min in kwaso iyalina inzo gidan ka? Ni dakai waye ya dace yazo gidan wani? ai nayi tunanin idan na fada maka dawowar benazir jiki na rawa zaka kwaso iyalinka kuzo nan domin tayani murna sai kuma naji akasin hakan
Alhaji musa yace bazan Iya zuwa jos din bane, saboda Ina da ayyuka dayawa da zanyi, shiyasa nace kuzo nan Win,
Mamaki da al ajabi ne akan fuskar hajiya layla, don taji martanin da alhaji ubaid Ya bashi.
 Baikamata kace min haka ba, yanzu ayyukanka har sunfi ganin ?ata da za ka yi muhimmanci?
Babu alamun damuwa a muryarshi yace yaya kasan banason jan magana, meye aciki don nace kazo gida na? Laifine? Alfarma nake nema bawani abuba, idan ba zaka yi min ba zan aje waya
GyaWa kai alhaji


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login