Showing 15001 words to 18000 words out of 260999 words

Chapter 6 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

magana sai dai ta kasa saboda sautin muryar ta ya?i fita ko da tana yin kukan babu sauti.

 Ban faWi hakan don na fama maki ciwon da ke acikin zuciyarki ba, Nasan kina yi ne duk don ki cece rayuwan ?an uwan ki, don kuma ki cika mana al?awarin da ki ka Waukar mana, sai dai kash gaggawar da ki ka yi ta yi silar jefa rayukan mu cikin haWari, Zai yi wuya mu tsira sai dai bazan bari Ki rasa ran ki ba, Zan yi maku ?o?ari Ayau Win nan ku fuce daga cikin kurkukun nan kafin Hankalin Matsafan ya dawo kanku, Mun ci sa a shuwagabannin kurkukun basu aciki, Sauran da suka rage Giant ne masu haWarin gaske, Ni kaina da na ke da sihiri a jikina bazan Iya ja dasu ba, A yanzu haka da nake Yin magana da ke nayi ?o?arin Sarrafa Wakin Da ke Wauke da madubin tsafin su shiyasa ba zasu Iya ganin mu ba, Nan da Awa Waya Zamu Aiwatar da komai Idan har lokacin nan ya cika kuna acikin kurkukun nan mu dukan mu zamu Mutu bayan azabtarwa da zasu Mana.

Baiwar Allah duk da raWaWin da bakinta ke yi mata ahaka ta daure ta cije ta soma Yi mashi magana muryarta araunace da?yar sautin ma yake fita

 Sun cire min uniform Wina, Ruwan zamzam din Yana a cikin aljihun wandona bansan Ya zanyi ba cikin ?unar rai ta ambaci hakan

 Zanje na Wauko maki Uniform Win ki, cikin minti Waya Yana ambaton hakan ya 6ace ma ganinta.

Yun?urawa ta yi da?yar ta mi?e zaune, ?arnin Jinin jikinta ya addabi hancinta, bargon da ke shimfiWe saman gadon ta janyo ta yafa ma jikinta, Zuciyarta acunkushe take da damuwar halin da ?an uwanta su ke a ciki, Ita ba ta damu da kanta ba, sune damuwarta. Fatanta Allah yasa tsohuwa zafreen bata cutar dasu ba kamar yarda ta faWa mata.

Durowa Cikin Wakin salsabeel Yayi hannu shi ru?e da uniform Winta, Jar vest Winta da wandon ta Ya mi?a mata su, yatsun hannayen ta na kerma ta kar6e su, Agaban shi ta zura kayan bayan ta kammala sanya su ta zaro ?ar ?aramar robar zamzam daga cikin aljihun wandonta, Idanuwanta acike tab da ?wala ta kalle shi tare da cewa Ta ya ya zan Iya ganin Danish har in bashi ruwan zam zam Win ?

 Bamu da isasshen lokaci, A saman bayana zan goya ki in kai ki inda Ya ke kuma zan taimaka maki mu bashi ruwan, ya kai ?arshen maganar tare da Juya mata baya ya zu?unna daga bakin gadon, matsowa ta yi tare da kama bayan shi ta haye, Ya yun?ura Ya mi?e, Daga inda ya ke goye da ita Ya 6ace 6att....


Ba su dura a ko ina ba sai A wani katafaren ?aki mai tsawo da faWi komai na cikin shi launin Ja ne, hatta dogayen labulayen da ke a kewaye dashi red colour ne. wani irin sanyi ne ke ratsa sassan Jiki acikin Waki kamar sanyin A.c, daga gani special room ne na kurkukun ?addara, Tsadaddun furniture Win da ke a cikin Wakin kaWai abun kallo ne.

Jin shiru bata motsa daga saman bayan shi ba yasa shi yi mata magana muryarshi cikin raWa ya furta Mun ?araso, Ki tashi ki ga Wan uwanki yanayin yadda ya yi mata maganar ne yasa taji gabanta FaWuwa shi kanshi Salsabeel Win A tsorace Ya ke da abunda zai Biyo baya balle ita kuma da ta ke ?ar ?waruwa wadda bata taka kara ta karya ba. Tsoro ya hana ta Wago ta kalli inda Danish Win Ya ke duk irin kewar shi da ta yi, Sosai ta runtse idanuwanta Hannayenta ?an?ame da Salsabeel.

 Na faWa maki bamu da isasshen lokaci ki sauka mana yai maganar tare da zu?unnawa don ta sauka, Kamar wadda ?wai ya fashe mawa akai jiki na kerma ta sauko daga saman bayanshi, sai lokacin ta samu damar Ware idanuwanta sosai Tana ?arewa Wakin kallo tun daga kan labulayen dake a cikin shi har zuwa kan shimfiWaWen Carpet Win dake a ?asa Ga wani ?ayataccen table mai Wauke da Dinner set, plate ta gani na tangaran mai Wauke da kayan marmari, ga wani apple da aka datsi saman shi, hada sawun ha?oran mutun, Ga wani glass cup mai Wauke da wani abu acikinsa ruwane amma launin shi yayi bright red kamar an surkashi da wani abu. Duk fa wannan kalle kalle da ta ke yi ba ta yi tozali da shi ba, saboda ta hana idonta kaiwa gare shi, Har sai da Sabsabeel yai mata gyaran murya tukunna ta soma Juyar da ?wayar idanuwanta a hankali ta Waura su kan katafaren king sized bed Win da ke kafe a cikin Wakin, Gado ne irin na sarakuna launin shi Golden Colour an shimfiWe shi da lallausan Bedsheet launin Ja, slowly ta sauke idonta akan dogayen ?afafuwanshi wa iya zubilla tsabar ruWu yasa ta dabarbarce saboda ta kasa yadda cewa shine, Halittar Jikin shi gaba Waya ta canza, Ya zama jibgegen ?ato, Samun Namiji mai irin ?irar ?arfin shi zaiyi wuya, ?ira ce mai matu?ar tsoratarwa, rikitarwa da kuma jan hankali, Ga dukkan alamu bacci ya ke yi a giant Win ma bai bar halin shi na yin bacci ba, Dogon wandone Ba?i A jikin shi, Sai Jar t shirt ta matse jikin shi, ta bayyana ainihin surar shi, musamman damtsen hannayen shi tamkar zasu fasa rigar saboda tsabar ?arfi.

Sun canza shi sosai Farar fatar wuyan shi hada zanen tattoo launin ba?i da Ja wanda ya kasance Tambarin kurkukun ?addara ne duk wani Giant yana da Zanan a wuyan shi, sun rage mashi tsayin sumar kanshi, Anyi mashi kitson zane guda shida, wutsiyar kitson ta sauka har saman Broad-shoulders Win shi, Ya koma kamar ?an iskan turawan nan, waWanda tun daga suffarsu zaka shaida cewa, ba bu ?igon Imani A zuciyar su.

Zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta a yayin da ta ke ?are mashi kallo, Ta gaza yarda da abunda idanuwanta su ke Nuna mata, Wai Danish Winta ne Ya koma haka? Hankalin shi kwance ya ke sharar bacci babu alamun damuwa atattare da shi, duk irin kewar shi da ta yi shi baisan ma da zaman ta ba balle sauran ?an uwan shi, saboda zalunci na mutanan nan sun rabasu da Wan uwansu.

Cikin shesshe?ar Kuka Ta furta Sunan shi Da..Nish.. walking nervously ta nufi bakin gadon ta zauna daga gefe tana ?are mashi kallo, Ya yi wani irin haske mai kyan gaske, tsabar kyan fuskarshi tamkar zai kashe mata ido, la66ansa sun yi jawur dasu kamar na Jinjiri, Dogon hancin shi ya tafi tsaye ba lan?wasa, kwarin idon shi ta zuba ma ido, dogayen eye lashes dinshi masu kyau da tsari.

 Don t waste Our time! Mintuna kaWan suka rage mana, Muryar Salsabeel ce ta fargar da ita, Ji ta ke kamar ta faWa mashi ta rungume shi a jikinta ko ta samu sassauci a cikin zuciyarta.

Matsawa kusa da ita sabsabeel yai  Ki buWe murfin robar, Ni zan hau saman gadon In ru?e shi gudun kada ya farka ya ham6are ki, naushin giant yana da haWari sosai Bugu Waya su ke Yiwa mutun ya mutu In ba wani iko na Allah ba Wannan maganar da ya yi ta Waga mata hankali, ta ?ara jin tsoron shi.

Yatsun hannunta na kerma ta soma ?o?arin buWe murfin, tana dab da zata ?arasa cire shi, Kamar An ce ta kalli fuskarshi taga ?wayar idon shi na motsi ta saman kwarin idon shi, da ?arfi ta furta Ya farka

Sautin miryarta ne ya daki dodon kunnanshi, Aiko kamar an zungure shi Ya ware manyan idanuwanshi launin russet brown akan fuskarta, wani irin ?war jini yai mata a furguce Ta mi?e daga gefen gadon Tana ja da baya, idanuwanta azazzare, Salsabeel da ke yun?urin ru?e kafaWun shi don Ya hana shi mi?ewa A zafafe Yai wurgi dashi tun daga saman gadon Ya ?undumo ?asa Ji ka ke tummm, Hankalin Angel fa ya ?ara tashi ganin yarda ya jefar da babban mutun kamar Salsabeel yadda kasan kallon tamola haka ya jefar dashi wanda a haife salsabeel zai Iya haifarshi, Durowa yai daga saman gadon Yana huci Kamar mayunwacin zaki, breast Win shi har motsi su Ke yi, Wani matsiyacin kallo da taga yana binta dashi yasa ta haWiyi yawu mai zafin gaske, kallon da Danish ke yi mata kamar ma baisan wace ce ita ba, Tunkararta Ya soma yi Yana gurnani har wani jijjiga jikin shi ya ke yi, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada Ya rikiWa Ya canza halitta don ta fahimci abinda ya ke shirin Yi kenan, Juyawa ta yi da gudu tana neman inda zata 6oye kanta don kada ya cimmata, saida ta gama shan wahalar kewaye Wakin Kwatsam taga Ya bayyana agabanta. ?agowa ta yi a tsananin tsorace ta ke kallon shi tana girgiza mashi kai haWi da marairaice mashi fuska don Yaji tausayin ta amma ina ai ko kallo arzi?i bata ishe shi ba, Muryar Salsabeel ce ta karaWe kunnuwanta a kausasace ya ke bata Umarnin ta gudu daga gabanshi kada ta bari ya Dam?e ta.

kafin ta yi yun?urin Canza hanya Cikin rashin sa a ta ji Ya dam?i qugunta Kamar Wiyar roba Ya Waga ta sama Muddin kuwa Ya bugata da kasa sai qugunta Ya 6alle saboda ?arfin dake gare shi bana Mutun bane na ba?in shaiWanin aljani ne, Yana ?o?ari makata Da ?asa Salsabeel ya cimma shi Gaba Waya yai wurgi da ita ?asa ta kife robar zamzam Win da ke a hannunta tuni ta gangara ?ar?ashin table Win da ke a Wakin gashi murfinta ya fara zamewa zai cire saboda buWeshin da ta fara Yi, ruwan da bai wuce Kur6a Waya ba Ya kare idan ya zube shikenan sun rasa damar da su ke da ita.

FaWane ya kaure a tsakanin Salsabeel tsohon ?ashi da Danish garkuwar kurkuku, Yadda Danish Ya Waga salsabeel Ya buga shi da kasa ba ?aramin gigita Angel yai ba, lamarin ya tsoratar da ita babban abunda take jima tsoro kada Ya kashe shi da bugu, da ko ta shiga uku, ?arfi ba Waya ba Danish ya zarce salsabeel Nesa ba kusa ba saboda shi matsayin babban giant ke gare shi masu haWarin gaske, Salsabeel Kuwa Ko star Waya bai da ita a mu?amin Giant, ta inda Allah ya taimake shi ?warewar da ya samu A fannin sarrafa tsafi, ba don haka ba da tuni Danish ya jima da karkarya ?asusuwan jikin shi, Bugun da ya ke yi mashi da ace Lafiyayyan mutun ya yi mashi wanda baida sihiri a jikin shi da tun a bugun farkon, ga6o6in jikin shi zasu daina aiki.

Ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji daWi faWansu ya yi matu?ar ta6a ?wa?walwarta, Ku ka ta dinga yi hannayenta daddafe da kanta, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya farmata, muryar Salsabeel taji a raunace ya ke faWa mata ta Wauko zam zam Win, da sauri ta rarrafa ta nufi table Win har ta kusa ?arasawa Taji an Janyo ?afarta da ?arfi Yai wurgi da ita gefe Waya har saida kanta ya bugu da bango tsabar raWadi Yasa nan ta ke ta sume. Sai faman huci ya ke yi yana gurnani, gaba Waya ya gama na?asa ?warin gwiwarsu , shi kanshi Salsabeel Yana dur?ushe ?asa kanshi Ya bugu sosai ga6o6in jikinsa sun rauna, akan idon shi Danish Ya jefar da table Win da ?afarshi, Kayan marmarin da ke asaman shi duk su ka tarwatse ?asa, Ashe yana sane da robar Zam Zam Win hannunta, Kafarshi Ya Waga da niyar ya ta ke ta don ta fashe, A kiWime Salsabeel Ya fasa ?ara tare da Mi?ewa Yana jan kafarshi Ya nufi Danish.

Shu umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar shi hada juyowa ya kalli Fuskar Salsabeel Ya Waga mashi gira muryarshi tamkar ta mashayin giya ya furta What?

 Kada ka fasa ta na ro?e ka ko dan saboda ?aunar da ke a tsakanina da kai danish, Nifa ne Ya yan ka, Yau da hannun ka ka ke buguna kamar zaka kashe ni? Sai ka ce baka sanni ba? Laifin me muka aikata maka? Kalli kaga yadda ka Bugi ?ar uwarki Angel kamanta irin ?aunar da ke atsakaninka da ita ? Ta6e la66ansa yai who is she ? Tambayar daya jefa mashi kenan

Muryar Salsabeel tamkar zai fashe da ku ka Ya ce  Ka kalle ta da kyau yar uwarka ce Angel, Ba ka yi kewarta ba? Idan bazan manta ba lokacin da ka ke rashin lafiya saboda matsalar da idon ka ya samu sunanta ka ke faWi acikin sambatun ka ko ka manta ne ? Kwa6e fuskarshi yai Alamar bai tuna komai ba.

Salsabeel sai Jan hankalin shi ya ke yi da surutu A yayin da ya ke tunkararshi duk don ya samu damar Wauke robar zamzam Win da ya ke Yun?urin fasawa.

 you re trying to deceive me Danish Na ambaton hakan Ya dire ?afarshi saman robar, kukan Kura Salsabeel Yai tare da cakumar Wuyan shi Da iya ?arfin shi na ?arshe Ya daddage Ya janye Danish gefe Waya, A gaban robar Sabsabeel Ya zu?unna Yana Kallon Yadda ruwan Cikin ta ya tsiyaye ?asa, Tsabar takai Ci yasa shi Fashewa da kuka kamar ?aramin Yaro, ?ululun ba?in ciki ne ya addabi zuciyar shi, Damar da su ke da Ita ta ?are, zaiyi wuya su tsira.

Jikin Salsabeel na tsuma Ya yun?ura tare da mi?ewa Ya Waura idanuwanshi akan Bayan Danish wanda ke ?o?arin Tunkarar Angel don Ya ?arasa kasheta, A hankali ya Waura yatsun hannun shi saman rigar jikin shi ta kakin Giant, For the fast time da yai nufin bayyana ainihin suffar shi, Cire Rigar jikin shi yai tare da jefar da ita ?asa, FaffaWan ?irjine dashi Irin na sadaukan Ya ?i, 6an6are mask Win da ke akan fuskarshi Yai tare da jefar dashi saman rigarshi.

Namijin Duniya Kyakkyawan gaske, fatar jikin shi Jawur ta ke, Ya fito a baturen shi, Idan ka kalli fuskar shi ba za ka ta6a yarda cewa shi jinin tsohuwa Tamira ne, saboda ita mummunace tsufa Ya 6oye kyanta.

 Na bika ta lalama ka ?i banin haWin kai yan zu zan yi maka ta tsiya, Danish ko ni ko kai A yau Win nan Jin miryarshi yasa Danish dakatawa da yin tafiyar, cikin Takun Qasaita Ya waiwayo yana kallon shi, ganin ya tu6e rigarshi yasa ya fahimci shirin faWa Ya yi, jijjiga jikin shi yai nan ta ke ya rikiWa ya koma Jibgegen zaki ?osasshen gaske sai gurnani ya ke yi yana wage bakin shi.

Hankalin Salsabeel Yai matu?ar tashi ganin ya rikiWa, saboda shi sihirin shi bai kai ?arfin da zai Iya rikiWa ya canza halitta ba, ganin yadda ya ke tunkaro shi a fusace Yasa shi ja da baya ya soma tunanin me yakamata yayi don Ya dakatar dashi, idan ba haka ba A kashe zai kashe shi har lahira.

Waige waige ya dinga yi yana bin Wakin da kallo har idon shi ya sauka akan Wu?ar yanka kayan marmarin da ke yashe saman floor, Ba zai iya Waukarta ba don bai son Ya cutar dashi, Lallashinshi ya soma yi yana faWin Am sorry Danish ni ba faWa zanyi da kai ba, Pls ka saurare ni Danish dan Allah ka canza halittarka zuwa ta mutane ina son yin magana da kai..... Magiya ya dinga yi mashi amma Wan tahalikin nan ya?i sauraron shi, Juyawa yai da gudu ya nufi saman gadon Wakin Ya daka Uban tsalle Ya haye saman shi tare da sanya hannu ya rarumo bargon dake nannaWe saman shi, dai dai lokacin da Danish Yai kukan kura Ya daka tsalle da suffar Zaki Zai kai mashi hari Yai saurin Rufe shi Da bargon Ya nannaWe shi a ciki, Allah ne ya taimake shi Ya bashi ?arfin da shi kanshi yasan bana shi bane, a saman floor suka faWo, Sosai Ya matse Danish Acikin bargon, ru?o bana wasa ba kamar zai kashe shi, tun yana jin sautin gurnanin shi har ta kai ga yai shiru babu motsi alamar ya suma.

Tsabar farin Ciki yasa shi sakin dariya yayin da hawaye ke bin fuskarshi, tunawa da lokacin su da ke shirin ?arewa saura Mintuna 30 ya rage masu kacal, A hanzarce Ya zame bargon da ya lullu6e shi a ciki, har ya koma suffar shi ta mutane a ?asa ya kwantar dashi, Mi?ewa Salsabeel yai da sauri ya nufi robar zam zam Win da ya tsiyaye, Ya Wauko ta a tsakiyar tafin hannun shi ya dawo ya zu?unna agaban Danish, a hankali ya buWe mashi ?aramin bakin shi ya dinga matsar robar ta ?arfi kamar zaiyi hauka da?yar ya samu Wigon Ruwan Ya faWa bakin shi, ?igo Waya kacal, Gani ya ke kamar ba zai isa ya dawo hayyacin shi ba, hakan yasa shi cigaba da matsa robar duk don ya samu ruwan ya ?ara Wigowa a ?arshe da ya gaji ya jefar da robar ?asa, ya dafe kanshi da hannu biyu zuciyar shi na harbawa da matsanancin sauri.

faWuwar da gaban shi ke yi ya tabbatar mashi da cewa wani mummunan abu na faru da wani nashi ko dai mahaifiyar shi, ko kuwa yaran da ya ke ?o?arin taimakon rayuwar su, Mi?ewa yai a zabure Jiki ba ?wari ya nufi Angel da ke yashe ?asa tun Wazu da Danish ya jefar da ita ta sume bata ?ara motsi ba, hannu biyu ya sanya tare da Waukar ta, Ya dawo ita gefen Danish Ya kwantar da ita, kafin ya ?ara mi?ewa Ya nufi Kayan saman table da Danish Ya watsar dasu ?asa, A cikinsu ya samu robar ruwa, ya Waukota tare da dawo wa gaban su Ya zu?unna yana faman fitar da huci Shi kanshi a raunace ya ke daurewa kawai ya ke yi duk don ya samu ya ?arasa taimakon su.

A Saman fuskar Angel Ya watsa ruwan a Firgice ta farka haWi da mi?ewa tsaye tana Faman zazzare idanuwanta fuskarnan jawur ta kumbura suntum.

 Unaisah Cikin sanyin murya Salsabeel ya ambaci sunanta ko da ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login