Showing 174001 words to 177000 words out of 260999 words

Chapter 59 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ubaid yai shikenan, zamu fidda lokaci mu shigo abujan
Ya amsa da yawwa, sannan bana bu?atar ku zo a mota, Ni zan shirya maku komai na tafiyarku amsa mashi yai da toh, daga haka Alhaji ubaid yayi rejecting call din, yana mai mamakin Halin Alhaji musa.
 Me ku ka tattauna ne ? Layla ce ta jefa mashi tambaya
Muryarshi a raunace ya furta yace bazai samu damar zuwa nan ba, shine ma ya hana shureim zuwa saboda yafi son muje can gidan shi
Ta6e baki hajiya layla tayi shine kai kuma sai ka ce mashi zamu samu lokaci muje can din ko?
Jinjina mata kai yai alamar eh, masifa ta soma zazzaga mashi kasan Allah babu inda zamuje sai dai kai daya gama asirce ka kama hanya ka tafi,Ni ban ta6a ganin mutun mara kunya irin shi ba, yarinyar ta 6ace tsawon shakaru sai jiya tsakar dare ?arfe shabiyu tadawo bata ahayyacinta shine zaice mu kwasa mu tafi gidansa saboda muke son yaganta? Kwata kwata bashi da tunani kuma baida hankali, kaida kakeyi mashi biyayya gayanan shi bai damu da ?arka ba,
... tun da tafara faWa, jikin benazir yai sanyi duk sai taji ba daWi, Cikin sanyin murya tace mommy dan Allah ki yi ha?uri, kada hakan ya dame ki, Ni banga laifin shi ba saboda ai ni na gudu da kaina ba korata akayi ba, wata kil Yana jin haushin abunda na aikata shiyasa yace muje can....
Katseta hajiya layla tayi benazir ba abunda kike tunani bane, mutumin nan baya ?aunarki, saboda bai damu dake ba, tun lokacin da kika 6ace bai ta6a magana akanki ba, Mune kaWai muka damu dake munyi nemanki har mungaji mun fidda rai da kina araye, amma musa bai ta6a sanya baki akan maganar 6atanki balle har ya taimaka wurin bada gudummuwar mu nemo ki..... Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mata maganarta kidaina faWa mata wannan maganar, bai dace ba, taya zakice kawunta ?anin mahaifinta bai sonta? Akan wani dalili? Shiya furta maki da bakin shi
Harara layla ta watsa mashi alama nagani shiyasa nace haka
Idanuwan benazir ne suka cicciko tab da ?walla, cikin sanyin murya tace Ni ban damu ba, koda ace baya sona, tun da Iyayena suna sona Alhamdulillah, soyayyarku kaWai ta ishe ni sai kuma ta mijina da ?ata, da kuma Yayana, sannan Ni na amince zanje abujan bawai don saboda shi ba, saboda inason ganin Aneelerh
Girgiza kai layla tayi bafa zan ta6a bari ki je gidan mutumin nan ba, Saboda Ni ban yarda da shi ba, Idan kuma kika takura akan kinason zuwan bazan hanaki ba sai dai ki sani bazan biku ba babu alamun wasa akan fuskarta tayi maganar.
Magiya benazir ta dinga yi mata akan ta amince suje da ita, don ita batason suyi nesa da juna, da?yar layla ta amince zata bisu abujan, da wata manufa a ?asan zuciyarta don taci alwashin idan sukaje gidan Alhaji musa saita fada mashi ba?a?en maganganun da zasu hana shi sukuni, yanzu dai sun tsaida magana zuwa jibi zasu yi tafiyar.
Aranar shureim ya samu damar kiran Alhaji ubaid ya fada mashi uzirin daya hana shi Waga kiran shi, bayan sun gama magana, har benazir yace abata waya su gaisa, sun jima suna waya da ita kusan awanni suka kwashe, kafin daga bisani yayi masu sallama.

Idan muka koma 6angaren zahra tun bayan da ta koma gida, babu mutunci a tsakaninta da Aneelerh ko gaisuwar arziki bata haWa su, ta canza mata bata sakar mata fuska ba kamar yarda suke ada ba, aranar mahboob yai mata maganar motar ta da wayarta yace dama jingina yabada su, idan tana so zata bada kuWin adawo mata dasu, farin ciki kamar zata zuba ruwa ?asa tasha dama bada Son ranta ta bada su ba, ta haWa mashi kudin ta bashi, a daren ranar ya dawo mata da su, tuni ta fara amfani da wayarta bayan ta mayar da sim dinta.
A washe garin ranar laraba suka fara shirye shiryen fara aiki a Obie estate tare da sauran Interior designers dake aiki a ?ar?ashin company dinsu, tuni kaya sun iso daga dubai, Hankalin zahra ya kwanta bata da sauran damuwa yanzu, ta ?agara gobe tayi don suje su fara gudanar da aikinsu saboda gagarumin taro ne zasuyi idan obie zai yi birthday kamar shagalin biki saboda dukiyar da suke kashewa wurin ?awata gidan, shiyasa zasu fara yi masu aiki tun alhamis kafin Juma a da za a gudanar da shagalin

d'>?
?d'>?
?d'>?
?d'>?
?d'>?
?d'>?
?d'


d'ANEELERHd'





A zaune take saman mirror chair, bata jima da fitowa daga wanka ba, ta zauna ne domin gyara jikinta, ?ar rigar wanka ce a jikinta, ta kasa ta6uka komai hannunta na a ru?e da wayarta layin hajiya adama take dannawa kira, phone din na fara ringing taji sanyi ya ratsa zuciyarta, bayan hajiya adama tai picking call din Aneelerh ta yi mata sallama, on the other hand muryar Hajiya adama ta bayyana da alamun kasalar bacci wa alaikum salam daugher in-low, ya ki ke ya gidan yasu mami da ummi

Da fara akan fuskar Aneelerh tace Lafiya lou mommy, yasu daddy fatan duk kuna lafiya
 Alhamdulillah Aneelerh, halan kin ji ni shiru yau ban neme ki ba shiyasa kika kira
Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace haka ne dama nakira ne don mu gaisa da zolaya Hajiya adama tace kodai kin kira ne don ki faWa min jibi zaki zo Waukar baby junaid tun da time ya cika

?umshe dariya Aneelerh tayi kamar tana agabanta sai faman no?e kai take yi, jin tayi shiru yasa Hajiya adama cewa dama nasan ba zaki faWamin ba, to ki kwantar da hankalinki, in sha Allah friday zanzo dashi gidan naku

Abeelerh taji dadin maganarta nagode mommy, Allah yakaimu lafiya.
 Nima ngde ki kulamin da kanki, ki kuma gaishe min da su mami, junaid din bacci yake yi zuwa anjima idan ya farka zan kira ki video call ku gaisa, dama yanata sambatu yana ambon shi wurin mommy zaije
Murmushi Aneelerh tadan saki kamar tana agabanta zasuji nima agaishe da daddy,  daga nan suka yi sallama da juna.

d'A washe garin ranar Alhamisd'

Wuraren sallar Asuba Unaisah tana zaune saman darduma ta zumbula hijabi, Batul tana akwance agefenta saman dardumar, tun jiya da suka fara sallah da zarar sun gama sai ta kwanta wahala take ji idan tana yin sallah hada ?arin rashin sabo har ?wara ita akan su azeeza masu yin kalle kalle in suna yin sallah, mazan cikinsu sunfi natsuwa shi kanshi Boss man yayi mamakin yadda suka Iya sallah da karatunta ya ?ara jinjinama Unaisah akan ?o?arinta, yanzu karatun addinine zasu ?ara koya masu dana boko kafin asanyasu makaranta bayan kammala bincike akansu.

Tafin hannayenta biyu ta Waga sama tanayin addu a muryarta abuWe take fadin

 Ya Allah ka ji?an ?an uwanmu da suka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah kakai rahama ?abarinsu, Ya Allah kabamu ikon cinye jarabawarka, Ya Allah ka bamu ha?uri da juriyar rungumar duk wata ?addara da zata riske mu mai kyau ko mara kyau, Ya Allah ka tsare min sauran ?an uwana da nake atare dasu da sauran al ummar musulmai, ya Allah ka bamu nasara akan burinmu da muke son cimmawa na ganin mun kawo ?arshen azzaluman mutanan da suka ?as?antar da rayuwarmu suka cutar damu Allah kada ka basu nasarar cigaba da aiwatar da zalunci.......... cikin shesshe?ar kuka ta ?are maganar, hawaye tuni sun wanke fuskarta tunawa da rayuwar sauran ?an uwansu ?ananun yara da ake cutarwa a cikin kurkukun ?addara, tasan ba zasu fasa cin zarafinsu ba suna lalata rayuwarsu kamar yadda su ka yi silar mutuwar ?ar uwar su Unaiza ?ar gidan daddy da Majnoon yaran da ba suji ba basu gani ba.

Sautin kukan Unaisah ya karaWe cikin Wakin, batul ko motsi batayi ba, tunda ta kifa kanta saman darduma bacci mai dadine yai awon gaba da ita ko addu a bata samu damar yi ba.

 Bazan ta6a mantawa da wasi?ar da kika bani ba, kuma bazan manta sunan mugun mahaifinki ba, In sha Allah zan Waukar maki fansa koda kuwa zan jefa rayuwata ne cikin haWarin da zaiyi silar mutuwata ne..... cikin karyayyar murya take furta kalaman masu ta6a zuciya, idanuwanta sun kaWa sunyi jawur, hawaye sun kwanta saman fatar fuskarta har zuwa gaban hijabin dake a jikinta.

 Ya Allah ka bayyana min daddyna idan yana araye, Inason nasake ganinshi shi kaWaine nake da burin haWuwa dashi a duniyar nan

Tunda ta fara karanta addu o i, yana la6e bakin ?ofar dakinsu Yana sauraronta, basu jima da dawowa daga sallar asuba ba, ya rakosu Sajeed ne tuni sun nufi bedroom dinsu.

Zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta, abubuwa dayawa sun so su rikitar dashi, kamar yarda take zubar hawaye haka shima yake zubar da su saman fuskarshi, farar jallabiyace a jikin shi ya sanya mask akan fuskarshi, Ji yake kamar ya faWa Wakin Ya rungumota a jikinshi, duk a tunaninshi Unaisah ta manta dashi ashe ba haka bane yana aranta har addu a tana yi mashi, ha?i?a yayi farin ciki mara misaltuwa, cikin sanWa Ya juya zaibar ?ofar Wakinsu kwatsam muryar Jemimah ta tona mashi asiri da ?arfi ta furta BOSS MAN!!! cak Ya dakata da tafiya, hatta Unaisah dake a Waki saida taji sautin sunanshi da jemaimah ta ambata, aiko da sauri ta mi?e ta nufi kofar fitowa daga Wakin.

A hankali Ya waiwaya baya yana duban jemimah, tasha dogon hijabi ajikinta kamar zatayi tuntube da gudu ta nufo shi, Azeeza ma ta fito tabiyo bayanta itama hijabin ne a jikinta.

Kallon da yake binsu dashi tamkar kallon da uba yake yiwa ?a ?anshi ne, saboda yana matu?ar ?aunar yaran ya dauke su kamar jininsa, musamman yadda suka fara nuna mashi yarda, Jiya izuwa yau sun saki jiki dashi, duk in zai gifta sai sun ambaci sunanshi kamar su suka raWa mashi.

Jemimah na ?arasowa ya sanya hannu biyu ya Wagata sama, ta kama ti?ar dariya tana fadin dan Allah kada ka sauke ni ?asa

Fuskarshi dauke da murmushi yace raini ya fara shiga tsakanina dake ko? Tun jiya badama kiga na gifta sai kin ?wala min kira kamar wani tsaran wasanki, bakisan ni baba ba ne ?

Tace to aini daWin sunan nake ji, Boss man shiyasa nake kira, tana magana yana kallon jajayen kumatunta bakomai yake tunawa ba face Angel Winsa, lokacin ?uruciyarta yaci wuyarta yakuma ji dadin shiriritarta.

 Jemimah Ina fata yau kinyi sallah ta hankali, don jiya Azeeza ta faWa min abun kunyar da kika yi ya faWa yana sauketa ?asa, duban Azeeza yai har ya mi?a hannu zai Wauke ta ganin ta tsare shi da ido yayi tunani ko itama so takeyi ya daga ta sama, da sauri ta ma?e mashi kafaWa tana fadin ai ni ba ?arama bace, Na girmeta da shekaru dariyace ta kubce ma Boss man.

 Oh saboda kin girmeta shine bakyaso in Wauke ki? To aini a wurina jinjira nake kallonki ya faWa tare da Waukarta ya ru?eta a hannunshi, Kunyar duniya ta cika Azeeza sai faman no?e mashi kai take Yi.

 Kasan Allah Boss man itama Azeeza bata Iya sallaba, ko karatun sallah ma bata iyaba, idan nayi ?arya kace ta maimaita maka Rabbighfir li tuntsirewa yai da dariya.

Ran Azeeza ya 6aci tace wallahi ?arya take yi min, ai acikin zuciya nake yin karatun sallah tayaya har tasan abunda nake faWi acikin zuciyata gwalo jemimah tayi mata oho dai, ni dai duk rashin Iya sallana nasan yadda ake karatun sallah

Idanuwan Azeeza tuni sun cicciko da ?walla, boss man yace badai kuka zakiyi min ba ? Cikin shesshe?ar kuka tace wallahi ?arya take yi min na iya karatun sallah, kaji na rantse maka, idan ma kanaso sai in faWa maka kaji, itace fa bata Iya komai ba, jiya muna sallar isha i tana buga min dundu abayana, kuma ban rama ba

Kwantar da kanta yai saman kafaWar shi haWi da daura hannun shi saman kanta Yana lallashinta.

Idanuwanshi akan jemimah dake ta dariya, dama tun jiya da yayi tozali da fuskarta ranshi ya bashi da?yar in bata iya rashin ji ba, kamar dai Angel dinsa da tana ?arama .

Lallashinta yai yi hakuri my daughter, kuruciya ke damunta dama kince min kin girmeta don haka inaso ki ru?e girmanki kada ki biye mata, idan tayi ba dai dai ba kiyi mata nasiha a matsayinki na babba mai hankali da tunani, in sha Allah wata rana zata daina ne tunda ya fara magana Azeeza take amsa mashi da toh, jemimah kuwa sai faman ta6e mashi baki take yi hada ru?e qugu, tana fadin tab ita Win zata min nasiha, Allah ya kiyaye, ai ni bana jin maganar kowa idan bata Unaisa ba

Mamaki jemimah take bashi gata ?ar ?arama idan tana magana sai kayi tsammanin ta Ware shekarunta.

Sauke Azeeza yai saman floor, yace da ita ki ruke hannun ?ar uwarki ku tafi Waki, da anjima idan nashigo zamuyi magana ta amsa mashi da toh nagode, kafin ta ru?o hannun jemimah tuni ta watsa da gudu ta nufi hanyar komawa Wakinsu duk don kada azeeza ta ru?e hannunta.

Murmushi ya saki yayin da yake bin bayansu da kallo, Har ya Waga ?afa zai nufi hanyar fita Wakin, Muryar Unaisah ta dakatar dashi Boss A hankali ya juya baya yana dubanta tun Wazu tana tsaye tana kallon su, sai da ta bari su Azeeza sun tafi tukunna ta yanke shawarar yi mashi magana.

Ta wanke hawayen fuskarta, tana tafiya hijabinta na ja da ?asa, har gabanshi ta ?arasa ta tsaya, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, ji yake kamar ya rungumeta koya rage radadin da yake ji acikin zuciyarshi, sai dai ba halin yin hakan yasan yadda take da masifa idan Ya kuskura yai hugging dinta tsaf zata mare shi tunda batasan wanene shi ba.

Ido cikin ido suke kallon juna, tsawon mintuna kafin ta numfasa tace ina kwana? Ka tashi lafiya? ya fama da mu
Cikin sanyin murya yace lafiyalou Unaisah, ya akai naga idanuwanki sun canza launi, ko baki da lafiya ne ?

Girgiza mashi kai tai, cikin disasshiyar murya ta furta lafiyata qalou, kasalar bacci ce,

Jinjina kanshi ya Wanyi, ji take kamar tace mashi ya cire face mask dinshi sai dai bata son ta takura mashi don ta fuskanci bayason su san wanene shi.

 Kin tsare ni da ido kina kallona ko akwai wani abu da kike son fada min ne ?

Murmushin gefen fuska ta saki, Har dimples dinta suka lotsa,

 Dan Allah taimako nakeso kayi min sai dai bani da ko sisi a hannuna
 Kada kiji komai ki faWi koma menene zanyi maki shi in sha Allah

Tana faman no?e kai tace um dama waya ce da Aunty laura ta bani kyauta Waya daga cikin likitocin da suka kula da lafiyarmu a america, to wayar babu sim aciki gashi inason in fara amfani da ita

ta faWa tana duban fuskarshi, ya natsu yana sauraronta idan tana magana kuruciyarta yake tunawa, yarinyar data sanya shi ciwon kai da zazza6i, cikin ikon Allah yanzu ta ?ara girma ta zama kamilar mace ta mallakin hankalinta.

 Sim kaWai kike bu?ata ? Girgiza mashi kai tayi a a, da Allah kada kace na takura maka,  aranshi ya ayyana takura kuma ta nawa My Angel, nida nayi jinya gadon asibiti saboda ke

 Cikin Kayan da aka tsunto mu da su a daji, akwai backpack Wina inason jakar, gadonmu ce bansani ba ko sojoji sun haWo mana da su ta tambaya tana dubanshi.

 Duk wani abu naku yana atare damu, saboda muna bu?atar abubuwan da zasu taimaka mana wurin yin bincike tamkar shaidune agare mu, amma kada ki damu zan Wauko maki backpack din, da anjima zan shigo maki da ita tare da sim din da zaki sama wayar wani irin farin cikine Ya lullu6e Unaisah, godiya tadinga yi mashi, yace mata yaji daWin ganin farin cikinta, juyawa tayi da niyar ta koma Waki, hijab din jikinta dake jan ?asa ta harWe ?asan takalmin ?afarta, gaba Waya ta tafi zata kife kasa da zafin nama Boss man Ya ru?o damtse hannunta Ya janyota ta faWa saman kirjinsa, har saida taji gabanta ya fadi, ?an?ameta yayi da hannayensa biyu daya zagayo dasu ta bayanta, Jikinta yai wani irin sanyi kamar wadda aka zare ma laka, bawan Allah tunda ya rungumeta yai tighting dinta kamar karya saketa, ita kanta takasa raba jikinta daga nashi, saima hannayenta data zagayo dasu saman bayanshi, ta ?ankameshi, Jini Waya ba wasa ba, sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi at same time, batasan ya akai ba ta tsinci kanta da jin hawaye sun cicciko idonta, shi kuwa tuni sun wanke face mask dinshi.A hankali yake Wan bubbuga bayanta kamar yana lallashinta, tsawon shekaru rabon daya ji Wumin jikinta anashi, bazai ta6a manta ?addarar data afka masu ba, wadda tayi silar rabuwarsu, bazai ta6a manta sautin shesshekar kukanta da muryarta a lokacin da yake gudu dasu cikin mota tana daddy hancina jini, haka zalika bazai ta6a manta lokacin da ya jefar da ita cikin ruwa ba duk don ya ceci rayuwarta Sai gashi cikin ikon Allah ta rayu Allah ya tsare mashi ita, Allah kaWai yasan irin wahalhalun rayuwan data fuskanta da ?ananun shekarunta.....

Kamar yadda yake tariyo rayuwarsu haka itama take tunano daddynta, ji take kamar shine ya rungumeta, shiyasa ta ?ara narke mashi tayi lamo saman wide chest dinshi......

Gaba Wayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba zato ba tsammani Boss Man yaji dirar wani abu saman bayanshi, da sauri ya Wago da kanshi idanuwan shi sun canza launi sun kada jawur kamar mai fama da ciwon ido, yayi mamakin ganin pillow da aka jefo mashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login