Showing 132001 words to 135000 words out of 260999 words

Chapter 45 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ta bani wayar, ta fita falo, ni kaWai ne a Wakin

A faWa ce tace ?arya ka ke yi mini junaid, ba ita bace ta baka wayar, kaine ka Wauka ka kira ni, maza ka aje mata wayarta tun kan na 6ata maka rai, ta yi maganar tamkar ranta ya 6aci sai dai azahiri ta yarda bashi wayar akayi, kawai tana son ta haya?a shi ne.

Sautin kukan shi ne ya cika mata kunnuwanta.

 Mommy ba ki yi missing dina ba, shiyasa kike yi mini faWa, Kin barni ni kaWai agidan su, ni wlh gida zan dawo, ko dai kizo ki Wauke ni ko kuma in gudu in 6ace kamar Angel maganarshi tayi matu?ar bata dariya, cikin sigar lallashi tace am sorry my baby boy, wlh nayi kewarka kamar zan zauce, yanzu dai ka yi ha?uri kadaina kuka, Mommyn ka bata son zubar hawayen ka

Cikin shesshe?ar kuka yace ni dai kizo ki Wauke ni mommy, ko in gudu hankalinta ya dan tashi, zuciya da sa?e sa?e saita dinga tunanin ko dai wani abu akayi mashi ne wanda ya 6ata mashi rai har yake neman dawowa gida.

 Junaid, faWamin meya faru? Basa baka abinci ne? Ko ba ayi maka wanka ne? Ko wani ya buge ka ne ! A jere ta furta hakan.

 Ni ba su yi min komai, ina cin abinci kuma mommy adama tana min wanka har sau biyu safe da dare, ni kawai ke nakeso kizo ki dauke ni, ko in gudu ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta har ya Wan kwanta.

 My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, zasu dawo mun da kai nan bada jimawa ba,

Rigima ya sanya mata Allah in baki zo ba saina gudu dariya ce ta kubce mata, jin sautin dariyarta ba ?aramin 6ata mashi rai ba.

 Mommy dariya kike mini ko! Shikenan zan kashe wayar da sauri tace sorry nadaina, pls kada ka kashe min waya, Ina jin daWin yin magana dakai, Yanzu faWa min a kwance kake ko a tsaye

 Saman gado ya bata amsa atakaice, har ta buWe baki zatayi magana ya katse ta da cewa Mommy, na tuna sunan mutumin nan da ya kira ki a waya, ran nan, amma ba zan fada maki ba, In kina son ji kizo nan

 Am sorry my baby boy, yakamata ka fahimce ni, babu yadda za ai inzo, Zasu yi tsammanin ban yarda Wazu bane shiyasa na biyo ka, dan Allah ka faWa min sunan shi, ka ji yaron kirki

cikin ?agara da sonji tayi mashi maganar.
 Toh mommy, zan faWa maki amma bana so kowa yaji har zahra muryarshi da shagwa6a yake magana.

 Junaid, Ni kaWaice a Wakin, Zahra bata nan taje wurin aiki, Mahboob ma baya acikin gida, Abie da Uncle basu dawo gida ba, mami da ummi ne kuma basa a Wakin, suna a can palour suna fira

 To zan faWa maki, amma kada ki faWa ma zahra da mahboob ta rasa ya za ta yi da shi, Ya?i faWa mata sai jan maganar yake yi kamar baya son fadi.

Kukan ?arya ta soma yi mashi tana fadin dan Allah baby junaid dina ka faWamin, zuciyata zata iya bugawa idan ban ji ba tuntsirewa yayi da dariya yana fadin mommy wasa kike ba wani kuka ai na ganoki gajiya tayi da tsayuwar, ta koma gefen gado ta zauna, tamkar tana agabanshi ta marairaice mashi fuska tana fadin pls my baby boy, ka faWa min, komi ka ke so zan yi maka

 Zoben Angel, da ki ka ce zaki siya mini in bata tun da na maida ba mahboob nashi

 Kada ka damu, kafin ka dawo gida zan siya maka zoben, Nayi maka al?awari, Yanzu faWa min toh

Sai da ya mula ya ishe iska tukunna Ya furta wai ma...waima daddyn Unaisah, haka yace min fa shiru tayi jimm tana tunanin sunan daya furta mata daddyn unaisa? Wanene daddyn unaisa? Ita kanta unaisan wacece ita!, sunan ya shige mata, jin tayi shiru yasa Baby junaid ambaton sunanta mommy kin yi shiru baki ce komai ba

 Junaid, na ruWe ne, na kasa gane wanene daddyn unaysa, amma shi mutumin Iya abun da ya faWa maka kenan ?

 Eh, bai faWa min komai ba, Mommy ki kira shi ki ji toh wanene shi, ko daddyn Angel dina ne?

lokaci Waya taji gabanta Ya faWi Jin Ya ambaci ?ila daddyn Angel ne, nan take ?wa?walwarta ta tunano mata sunan wacece Unaisa, a sukwane ta mike tsaye Tana faman zare idanuwanta, zurfi tunani ta shiga duk duniyar nan mutun Waya ta sani mai sunan daddyn unaisa, wato Tajuddeen, ta gaza yarda da abinda zuciyarta ke faWa mata.

La66anta na kerma ta furta ka tabbata haka sunan yake? Ko dai abakina ka ta6a jin na ambaci sunan daddyn Unaisa?

 Mommy wlh dagaske nike maki haka yace min wai in faWa maki daddyn unaisa ne, mommy zan kashe wayar, ga mommy adama nan zata shigo dakin kafin ta yi mashi magana yai rejecting kiran.

Hakanan tadinga jin bugun zuciyarta na ?aruwa, jiki asanyaye ta koma gefen gadon ta zauna, tsawon mintuna zuciyarta nayi mata kokwanton maganar da junaid Ya faWa mata, har dai a ?arshe ta yanke shawarar cire nombar daga black list, don ta kira ta ji wanene mutumin da junaid ya fada mata cewa daddyn Unaisa ne, fatanta Allah yasa Dagaske ne hasashenta.

Yatsun hannunta har kerma suke Yi wurin daddana wayar, bayan ta cire number daga black list, ta danna call cikin sa a Kiran Ya shiga, wayar ta fara ringing, tsabar zumuWi jikinta har kerma yake yi, Har kiran yayi rejecting ba a Waga ba, Mi?ewa tayi tsaye ta zame dogon hijabin jikinta ta jefar saman mattress, safa da marwa ta cigaba da yi a tsakar Wakin, ta ru?e wayarta a hannunta, a ?alla Ta Kira layin kusan sau biyar Yana ringing ba a Waga ba, Hankalinta ya?i kwanciya burinta taji wanene mutumin nan daya kira kanshi da sunan daddyn Unaisah.

Har ta fidda rai da za a Waga Kiran, Unexpected A kira Na shida data yi mashi sai gashi Anyi picking call din.

Cikin rashin natsuwa ta furta Assalamu alaikuma maimakon ta ji muryar Namiji sai taji muryar matashiyar mace tana yi mata magana da wani yare.

 Baiwar Allah, bana jin harshen da kike yi mini magana dashi, Idan kina jin hausa mu yi magana da shi

Ko da Aneelerh ta ambaci hakan, matashiyar sai ta canza harshenta zuwa Yaren hausa ta ?an koyo tace wanene ke magana ? A ?agare Aneelerh tace sunana Aneelerh, dalilin dayasa na kira Layin, kwanakin baya ana yawan kirana dashi, Ina tunanin ko wani ne ke nema, pls ina neman me wayar ta faWi hakan ne don junaid ya fada mata cewa Namiji ne Ya daga kiran lokacin da aka kira.

Matashiyar budurwar tace Ni ce me wayar, wato irin kune ku ke bibiyar mazajen mu don ku ?wace mana su ko ? Sakin baki Aneelerh tayi jin abun da matar tace.

 Kiyi ha?uri, Nima matar aure ce kamar ke, kawai inason nasan ainihin wanene me wayar, ki taimaka min a ?agare nake da son ji da alama matashiyar Yarinyar Akwai ?uruciya atattare da ita, tun daga kan kalamanta zaka shaida hakan.

 Nace maki ni ce me wayar, atsawace ta furta hakan, Aneelerh tace ba wayar ki bace, saboda ke da kanki ki ka ce irina ne masu bibiyar mazajan mutane don mu kwace masu miji, hakan na nufin ba wayarki bace wayar mijin ki ce sautin dariyar matashiyar ne ya cika mata kunnuwanta, lamarin ya Waure ma Aneelerh kai, gashi duk ta ?agara a matse take da son jin wanene.

 Ke dai zan faWa maki gaskiya, tun da kin gano ni, ba wayata bace, wayar mijina ce, kuma baya nan Ya fita ni ka Wai ce agidan

 Okey, pls Ko zan Iya sanin sunan mijin naki ?

 A a gaskiya, salon ki je ki kai ma boka sunan shi ayi maki asiri ki mallake shi duk yadda Aneelerh ta kai ga jurewa saida ta fashe da dariya jin abun da Yarinyar tace, da?yar ta sassauta da yin dariyar tace wlh ni bana bin boka, Ko hanyar zuwa wurin shi bansani ba, Yar uwata ba duka aka taru aka zama Waya ba, ni bana Waya daga cikin matan dake zuwa wurin boka, saboda na dogara da Allah shi kadaine zai Iya biyamun bu?atuna

matashiyar tace Ni ban yarda dake ba, mata dayawa suna son ?wace mini mijina saboda kyakkyawa ne kuma yana da ?arfi

Aneelerh tace baiwar Allah na faWa maki nima matar aurece, da mijina akan me zan nemi mijin ki !

 Oho nima bansani ba, idan kin gama magana zan kashe wayar amsar data ba aneelerh kenan Shiru aneelerh ta Wanyi tana tunanin hanyar da zata 6ullo mata, ta fahimci Yarinyar bata da cikakken Ilmi da wayau sai a hankali. Dabara ce ta faWo mata.

Dariya ta fara saki, Matashiyar tace me kike yi ma dariya Aneeleh tace Ai dole inyi dariya, ke yanzu baki gane muryata ba ne? Aneelerh fa ce matar abokin mijin ki Shu aibu

Da buWar bakin budurwar sai cewa tayi ?arya kike yi aini mijina basu nan shi shu aib ba, TAJ ne sunan shi, Kina son ki yi mini wayau ne

Jin ta ambaci sunan Taj Yasa Aneelerh Tsayawa cak ta dakata da yin tafiya, yayin da bugun zuciyarta ya ?aru, Muryarta na Wan rawa ta furta ?arya kike yi, ba sunan mijin ki tajuddeen ba, so kike in yadda don kada ki faWa min ainihin sunanshi, ai ni nasani Shu aibu ne sunan shi

Matashiyar budurwar tace To kada Allah yasa ki yadda ma, kuma wlh ma ?arya kike yi mini cewa wai ke matar abokinsa ne baki da gaskiya, da alama ranta ya 6aci ta fara harzu?a.

Sassauta murya Aneelerh tayi Ki yi ha?uri, ba yadda ki ke tsammani bane, Dan Allah ki faWamin ina mijin naki yake inason yin magana dashi

Dogon tsoki matashiyar Taja, kafin ta furta ba kin ce ke matar abokinsa bane? To ki ce ma shu aibun Ya kawo ki gidan mu, kafin Aneelerh ta furta wani abu, Matashiyar ta katse kiran!

Hankalin ta Ya?i kwanciya, Jiri ta soma gani acikin idanuwanta, a daddafe ta nufi gado, Ta haye ta kwanta, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta ta shiga ruWani, tun da Matashiyar ta ambaci sunan tajuddeen, natsuwarta tabar jikinta, taso ace tayi waya da shi don ta tabbatar da abun da take hasashe.

Har ?ara jaraba kiran layin tayi amma matar ta?i Wagawa.

Dubara ce ta faWo mata aranta, da sauri ta rubuta mashi sa?o cikin harshen turanci.

_Idan ka karanta sa?ona, dan Allah ka kira ni, Inason Yin magana da kai, sa?o daga Aneelerh muhammad falgore_

Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kammala rubuta mashi sakon, Ta Waura wayar saman side drawer, A gogon Wakin ta kalla ?arfe Uku na rana, kwanciya tayi saman gadon tana jiran tsammanin Kiran me wayar.


d'ZEENATUd'


A 6angaren zeenatu kuwa tun da ta fito da gudu daga Wakin Dr. Shureim ta koma Wakinta, ta fada saman gado taci gaba dayin kuka tamkar ranta zai fita, cikin muryar kuka take fadin yaya shureim ba sona yake yi ba, wata yake so daban, dama nasani babu namijin da zai yarda yaso ni saboda rashin natsuwata,

Idanuwanta sun kaWa jawur, mi?ewa tayi zaune ta soma cire lace jikinta a saman floor, ta watsar da kayan hada ribbon din da aka daure mata gashin kanta, iya undy ta bari a jikinta, ta jashi saman ?irjinta, tana huci yayin hawaye ke cigaba da wanke mata fuskarta, saukowa tayi daga saman gadon ta nufi gaban dressing mirror dinta, cikin 6acin rai ta sanya hannu ta watsar da jerin turarurrukanta komai sai da ta wurgo shi ?asa, bayan ta gama ta koma gaban wardrobe dinta, Waya bayan Waya sai da ta wurga da suturar saman floor, hankalinta bai kwanta ba har saida ta maida Wakin kamar na mahaukata, tukunna ta koma saman gadon ta haye tare da jan bargo ta lullu6e zuciyarta na ta farfasa.

Bayan Dr. Shureim ya fito daga wankan, kimtsa kanshi yai ciki shiga ta larabawa Ya feshe jikinsa da turare,
Ya ru?o wayar shi a hannun shi, tare da car key dinsa, walking quickly ya fito daga bedroom dinsa, Ya nufi Wakin zeenatu, duk inda Ya gifta a paloun masu aiki ne suke Yin aikace aikacen su cikin girmamawa suke gaishe da shi.

 Yalla6ai barka da fitowa muryar Tani ce ta katse mashi hanzarinsa, dakatawa yai da yin tafiyar ya juya ya dubeta

 Yawwa barkanki, Ya aiki fuskarta da fara a ta amsa mashi Lafiyalou Alhamdulillah,

Har zai wuce ta Ya kuma tsayawa ya kalle ta ?akin zeenatu nake nema Da rawar Jiki ta ce Yana a second floor, muje in nuna maka Wakin ta faWa tare da yin gaba Yabi bayanta, Yayi matu?ar ?agara da son ganinta, duk don Ya lallasheta akan laifin da yayi mata.

Bayan sun hau elevator ta sauke su a second floor, Tani ta nuna mashi ?ofar Wakinta.

 ki shiga ki faWa mata inason magana da ita
Tani ta amsa da toh, tana zura ?afarta Wakin zeenatu, gabanta Ya faWi ganin irin 6arnar da tayi, hankalin ta ba ?aramin tashi yai ba, jiki na rawa ta nufi gefen gadonta.

 Zeenatu! Lafiya meke damunki ne? Meyasa kika hargitsa suturar ki ?

Shiru zeenatu bata tanka mata ba, saima ?ara ?udundune kanta da take yi cikin bargo.

 Dan Allah zeenatu kiyi mini magana, nasan 6ata maki rai akayi ki fada mini wanene

Jin tayi shiru ba ta yi mata magana ba yasa tace ba zan takura maki ba, Yanzu ki tashi Yayan ki shureim Yana a ?ofar Wakin ki, shine yace in yi maki magana yana son ganinki

Kamar jira ta ke yi Tani ta ambaci sunan shureim, Cikin shesshe?ar kuka tace Tani, I don t want to see him. Please tell him I won t come. Yaya Shureim doesn t love me wata yake so daban, tun jiya yayi min al?awarin zamu fita yawo atare, yau kuma da kanshi yace min inje in shirya kafin in dawo zai yi wanka ya shirya, Tani da naje Wakin shi babu abunda yayi, yana akwance saman gado yana kallon hoton girl friend dinsa a laptop.... da?yar ta ?are maganar.

Jikin Tani yai sanyi, duk sai taji ba daWi, sai yanzu ta gane dalilin dayasa ta shiga halin da take aciki.

 Kiyi ha?uri zeenatu, ki tashi ki gyara jikinki, Yace yana son magana dake nasan yazo ne don ya baki ha?uri, kuma naga ya shirya hada key din mota a hannunshi.... Katse ta Zeenatu tayi Na fasa zuwa ki faWa mishi bazan je ba, tun da bayaso na

Cikin muryar raWa Tani tace yana fa jin ki, bai kamata kina Waga murya ba, sannan ke in banda abunki waya fada maki budurwashi ce yake kallo awayar?

 Ai naga hoton da yake kallo, Yana a kwance saman gado ya rungumeta a kirjinsa ta fada tana jan numfashi ta?i fitowa daga bargon.

 Zeenatu, kiyi mashi kyakkyawan zato, yaya shureim yana sonki fiye da yadda kike son shi, Ni shawarar da zan baki shine kada ki bari ya gane kina son shi, idan kika kwantar da hankalin ki da kan shi zai furta maki kalmar so

Sassauta muryarta tayi Tani, zan iya jure wannan amma bazan Iya jure kallon hoton budurwarshi da Yake Yi ba,

Dafe kai Tani tayi da hannu Waya zeenatu baki da tabbacin budurwashi ce, pls kibi komai a sannu zamu gano ainihin wacece Yake kallo awayarshi, Yanzu Ki tashi muje Yana awaje yana jiranki

 Tani ki daina wahalar da kanki, Nifa ba inda zanje, Ki fada mashi bana Jin daWi bacci Nike Yi

Duk yadda Tani taso ta lallashe ta akan ta tashi ta je gare shi ta?iya, a dole ta ?yaleta ta juya ta fuce daga Wakin.

A tsaye ta same shi Ya jingina bayanshi jikin bango.

Harya fara Gajiya da tsayuwa
 Ka yi ha?uri, Zeenatu tayi fushi bansan meya haWa ta dakai ba, nayi ?o?arin In lallasheta amma ta?i amincewa ta amsa kiran ka, ban ji daWi ba shureim, duk da bansan meya haWa ka da ita ba, amma bai kamata tun yanzu afara samun rashin jituwa a tsakaninka da ?anwarka, zeenatu tana da ha?uri sai dai tana da zuciya idan aka 6ata mata rai

Tun da ta fara magana Ya natsu yana sauraronta, sai da ta kai karshen maganar tukunna yace Inaso zan shiga ciki

bai jira amsar da Tani zata bashi ba yai saurin haura ?afarshi cikin Wakin zeenatu.

Dafe kai tayi da hannu Waya tunawa da 6arnar da zeenatu tayi a Wakin, gashi kuma Ya shiga hake zai je ya same shi kamar bola, can kuma ta ayyana aranta cewa Wan uwanta ne, daga haka ta ?ara gaba.

A tsanake Yake bin ko ina na Wakin da kallo, yayi mamakin ganin yadda ta hargitse komai, ta rikita mashi tunanin shi, Ya rasa gane fushin menene take yi da shi? Don shi a tunanin duk akan fitar da yace za su yi ne.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login