Showing 240001 words to 243000 words out of 260999 words

Chapter 81 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Duk da yana jin shakkar shi saida yai ?o?arin jaraba tambayarshi ya akai jazz yaji mummunan rauni saman goshinsa.
Kasancewar baya acikin natsuwarshi, da kanshi ya labarta ma dr fawan abunda ya faru.
Dafe kai fawan yai da hannu Waya tunawa da ranar da sukazo asibitin suka tirkeshi kan ya fada masu abunda jazz yake aikatawa shi kanshi yayi tsammanin wani mugun abun Jazz yake kullawa ashe ba haka bane sun yi mashi mummunan zato.
Ru?o hannun shi sir mubarak Yai fawan ka taimaka min, bansan ya zanyi ba, ina jin fargabar jazz ya farfado ya juya min baya saboda bugun da nayi mashi nasan da?yar zai fahimce ni, nayi kuskure fawan na yanke mashi hukuncin cikin fushi batare dana saurare shi ba cikin rauni na murya ya ?are maganar, tsananin tausayinshi ne Ya kama dr fawan, hatta major ya tausaya ma shi.

 Daddy, har abada bana tunanin jazz zai Iya juya maka baya, Saboda ni shaidane akan ?aunar da yake yi maka, balle kuma baka da laifi, laifin shine dabai sanar dakai ba a matsayinka na mahaifinsa, sannan duk abun da kayi mashi daddy kayi ne saboda ba ka son ya jefa rayuwarshi cikin hatsari, ni aganina kayi abunda ya dace kowani uba na gari yayi, shine ya tsaya tsayin daka don ganin yaronshi bai 6ace hanya ba..... tunda dr fawan ya fara magana sir mubarak ya natsu yana sauraronshi, major sai faman jinjina kanshi yake yi alamar gamsuwa da bayanin Dr fawan
Sai da ya kai aya a maganarshi kafin major ya daura da cewa yalla6ai gaskiya ne abun da dr fawan ya ke gaya maka, kuskuren da mukayi bisa rashin sani ne, tun da kake da jazz baka ta6a nuna mashi wariya ko acikin ?a ?anka ba sannan baka ta6a yi mashi koda tsawa bane don yayi maka badai dai ba, don haka bana tunanin jazz zai juya maka baya saboda abunda ya faru, zai fahimce ka kuma zai gane kuskuren shi

Nauyayyar ajiyar zuciya sir mubarak ya sauke, fatanshi Allah yasa maganar su dr fawan ya tabbata, don bayason jazz ya guje shi saboda ?aunar da yake yi mashi.

 Major ka kira layin Zaki ka faWa mashi muna atare da jazz sai zuwa gobe zamu dawo gida

 Okey Sir Major ya faWa tare da zaro wayarshi daga aljihu, Ya danna ma Zaki Kira, Bugu Uku kafin Yai picking, bayan sun gaisa Ya isar mashi da sakon Mahaifinsu kafin daga bisani su ka yi sallama.

 Daddy ku zauna mana, ko zamu shiga daga cikine ka kwanta a resting room dinmu

Girgiza kai Sir mubarak Yai alamar a a,

 Bazan Iya runtsawa ba, Nafi bu?atar farfaWowar Jazz hankalina sai yafi kwanciya

GyaWa kai Dr fawan yai bari na koma ciki daddy juyawa yai da sauri ya shiga medical room din, Sir mubarak Yana atsaye ya dan jingina bayanshi da bango, major yana daga gefenshi, idanuwansu sunyi masu nauyi, ga gajiyar hidimar shagalin da akayi ga bacci da damuwar halin da jazz yake aciki.
A ?alla sun kwashe awanni a tsaye, dare ya nutsa sosai, a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin muryar jazz ya karaWe kunnuwansu, da ?arfi yake fadin daddy zanyi maka bayani ka daina buguna, wayyo Allah kaina zai fashe zafi yake yi min

A gigice Sir mubarak Ya nufi dakin da aka kwantar da shi da sauri major Ya take mashi baya suna shiga suka tarar da Dr Jazz zaune tsakiyar gadon hannayenshi biyu tallabe da kanshi dake a nannaWe da bandage, gefen gadon dr fawan ne atsaye Yana lallashinshi, gaba Waya ya birkice sai sambatu yake yi masu.

A hanzarce Sir mubarak Ya zauna gefenshi, Muryarshi a raunace ya ambaci sunanshi Jazz My son

Har saida ya firgita jin muryar sir mubarak, adabarbarce yake dubanshi da rinannun idanuwanshi waWanda suka kaWa jawur, abunka ga farar fata fuskarshi tayi ja la66ansa sunyi suntum bawan Allah Ya bugu ba kaWan ba.
Ido cikin ido suke kallon juna,
 Am sorry jazz, na gane kuskurena na bugunka da nayi ba tare da nayi bincike ba, Dan Allah ka yafe min a hankali ya ru?o hannun jazz acikin nashi ya ru?e shi sosai.

Babu alamun zai furta mashi kalma, sai faman jan numfashi yake yi haWi da lumshe idanuwanshi har yanzu allurar da dr fawan yai mashi bata sake shi ba.

Da?yar ya iya buWe baki ya furta meyasa ka buge ni daddy? Dama kaine kake bibiyata daddy? Laifin me nayi maka? Kai da kanka ka faWamin ba zaka iya ta6a lafiyar jikina ba, kuma bazaka bari wani ya cutar dani na, Ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka yi min haka ba, sai gashi yau ka nemi ka raba ni da rayuwata..... a wahalce ya ?are maganar yana fitar da huci.

Girgiza kai sir mubarak yai hawaye tuni sun taru cikin idanuwanshi.
Muryarshi asanyaye ya ce Jazz ba laifina bane abun da ya faru, rashin sani ne, Jazz kaine tun farko baka sanar dani game da aikin sirrin da kake yi ba, a tunanina ka Wauke ni kamar mahaifinka wanda yai silar zuwanka duniya but why kake 6oye min abunda ya shafe ka? jazz kamanta al?awarin da muka Waukarwa junanmu ? Runtse ido jazz yai hawaye suka soma wanke fuskarshi.
Cikin shesshe?ar kuka ya furta ban manta ba daddy, kayi hakuri, yaya Owais ne Yahana in faWa maka, shiyasa ban gaya maka ba, nayi ?o?arin fahimtar dashi kuskuren yin hakan amma sai yace min kaima kasan da case din Yaran....... jin wannan maganar yasa hankalin sir mubarak ya ?ara tashi aruWe yake kallon fuskar jazz tamkar yana karanto wani abu, Major da dr fawan suka kalli juna, da alama sunyi mamakin jin abunda jazz ya furta, dafe kai sir mubarak yayi da hannu Waya tunawa da zancen case din yaran da sojojin ?asar ghana suka nemi hukumar sojin nigeria data kar6i case din daga hannun su, a lokacin basu kar6i case dinba sai suka nemi hukumar Isod da su shiga lamarin yaran, bai ta6a ganinsu ba ko a hoto yadaisan da zancen, sannan baida masaniya akan aikin da owais ya Wauki Jazz Na kula da lafiyar yaran shiyasa aka samu matsala.

Jinjina kai sir mubarak yayi, cike da danasanin hukuncin daya yanke mashi,

 Jazz ina ?ara baka ha?uri, dan Allah kada ka ru?eni a zuciyarka, da ace bana sonka wallahi bazan damu da rayuwarka ba, amma saboda ?aunar da nake yimaka ne yasa harna yi maka shisshigi...... a tsanake sir mubarak ya labarta mashi duk abunda ya faru tundaga rana ta farka daya fara jin shi yana waya a garden kan maganar kaji har zuwa ranar daya yi mashi la6e a toilet yajiyo shi yana fadin akasheta...
 Jazz kasan ba mummunan abu kake aikatawa ba, amma meyasa kake amfani da kalamai masu hatsarin gaske kamar kalmar kisa da naji kana faWi ?
Numfashi jazz yaja kafin ya bashi amsa da cewa saboda yaya Owais ya gargaWeni akan kada na kuskura wani ya san aikin da nake yi, koda kuwa mommyna ne shiyasa nake yin amfani da waWannan kalaman, lokacin da kaji nace bayasan hanyar da zai kashe ta ba, Ina nufin yasan hanyar da zai magance matsalarta, a lokacin Salsabeel ne ya kirani a waya, ya fada min haukan khadeeja ya motsa, shine nake fada mashi maganganun da kaji inayi
 Wanene salsabeel ?
 Shine babban cikinsu, atare da yaran yake, ba ?aramin mutun bane ya girmi yaya owais
Shiru Sir mubarak yayi, still bai kawar da idanuwanshi daga kan fuskar jazz ba.
 Ya jikin naka? Ina fata babu inda keyi maka ciwo ?
?aga mashi kai jazz yai alamar Eh.
 Yunwa fa ?
 Bana jin yunwa, ina son yin magana da mommyna
 Ba zamu iya kirantaba a yanzu, tayi bacci, sai zuwa gobe zamu tafi gida
Don dole jazz ya ha?ura da sonyin magana da mommynsa.
A daren ranar major a resting room din dr jazz Ya zauna, shi kuma sir mubarak ya kasa tafiya yabar jazz, kan kafaWarshi jazz ya Waura kanshi, anan bacci yai awon gaba da su manne da juna.

Ata?aice kenan abunda Ya faru daren Jiya dangane da sir mubarak.



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'?*



Idan muka koma 6angaren Sheikh Imam tun bayan da Chief Ya buWe ?ofar dakin Danish, Kowa fargaban Abunda idanuwanshi zasu gane mashi yake yi, ?arfin hali chief owais yayi wajen zura ?afarshi cikin Wakin, rass yaji gabanshi yai mugun faWuwa ganin hular sheikh imam da arab turban dinsa yashe kan floor kamar an wurgo dasu sun tarwatse, ga takalmansa ware Waya bakin gadon ware Waya kan carpet, a ruWe chief Ya wurga eye balls dinsa kan katafaren gadon Danish, lamarin yayi matu?ar Waure mashi kai, ganin bargo lullu6e da mutun, ?afafuwansa sun le?o waje, farare sol da su, Iya neck dinsa bargon Ya lullu6e hakan ya bayyana lallausar sumar kanshi data tarwatse saman wuyanshi hatta gefen fuskarshi ta lullu6e, Chief Ya fahimci yaron ya dawo suffarshi ta mutane sai dai abunda bai gane ba Ina sheikh imam yake? Saboda kwata kwata babu shi a Wakin babu alamar shi.

 Yalla6ai lafiya ? Salsabeel ne Ya ambaci haka yayin da yake shigowa Wakin daga bayanshi boss man ne da prime minister hateem suka shigo Wakin suna ?arema ko ina kallo.

Idanuwan mai girma prime minister basu sauka akan kowa ba sai akan matashin dake lullu6e da bargo, tun daga kan shantala shantalan ?afafuwanshi yasoma kallo har izuwa kan brown hair dinsa, aruWe ya furta dama yaron macace ba Namiji ba ? ya jefa tambayar yana dubansu.

 ba maca bace, Namijine Yana da sumar kai ne acewar Boss man

 Ni abunda bangane ba, Ina sheikh Imam ? Chief ne ya faWa yana bin ko ina na room din da kallo.

 Allah dai yasa ba wani abunne ya faru da shi ba acewar Boss man.

Sunyi tsaitsaye cirko cirko bakin gadon fuskokinsu da alamun ruWanin rashin ganin sheikh imam.

Prime minister ya kasa kau da idonshi daga kallon sumar kan Danish da yake yi, Ya ?agara da son ganin fuskarshi.

A lokacin da ba su yi tsammani ba, suka soma jiyo motsin buWe toilet door, kusan atare suka kai idanuwansu ga kallon ?ofar, bakowa bane yake fitowa face sheikh imam malik, hannun shi ru?e da cazbaharshi, hankalin shi kwance sai dai da alamun damuwa akan fuskarshi.

Nauyayyar ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, har suna haWa baki wurin ambaton sunan shi Sheikh Imam! Muna fata babu abunda ya same ka ?
Jinjina masu kai yayi batare da yace komai ba, har saida ya dawo gefen gadon ya zauna tare da Waura idanuwanshi kan bargon dake lullu6e da danish tukunna
A hankali Ya furta Alhamdulillah, cikin Ikon Allah nayi nasara, Yaron ya canza halittarshi........ ya faWa fuskarshi da matsakaicin annuri.

Har cikin ransu sunji daWin jin hakan, musamman prime minister, atare suka haWa baki suna ambaton Alhamdulillah sannu da ?o?ari malam.

Girgiza kai sheikh imam yai kafin ya Waura da cewa sai dai ina mai ba?in cikin sanar daku cewa Har yanzu ba?a?en shaidanun dake atare da shi suna nan daram da?am, babu alamun zamu yi nasarar raba shi da su..........

Kallon juna su ka yi kafin suka maida dubansu ga sheikh imam
Cigaba da yin magana yayi Ina bu?atar neman ?arin bayani dangane da abunda ke faruwa da yaron? Shin Menene Yajaza mashi faWawa tarkon miyagun matsafa? da har suka samu ?arfin ikon Juya shi son ransu ?

Kallon salsabeel Boss man yayi kai kaWaine kasan komai Ya kamata ka sanar da Sheikh Imam, kada ka 6oye mashi komai dangane da rayuwar yaran ta hakanne kaWai zai Iya shawo kan matsalar.

Jinjina kai salsabeel yayi alamar ya gamsu da bayaninshi.
 Labarine mai tsayi, zai Wauki tsawon lokaci, acewar salsabeel.

Sheikh Imam Yace tun da kace labarine mai tsayi, inaga mubarshi zuwa lokacin da yaron zai wartsake, Yanzu Yana bu?atar kulawarmu

Prime minister yace Ni kaina zanso naji tarihin kyakkyawan matashin saurayin nan, In sha Allah saboda shi zan nemi iznin ?ara kwanakin tafiyata, but abunda nake son sani, Yaron idonshi biyu? Ko bacci yake yi ? ya tambaya yana kallon sheikh imam.

 Ba bacci yake yi ba, idonshi biyu, sai dai bazai iya Waga ko yatsan hannunsa ba, shaiWanun sun sakar mashi da kasala Ya jigata sosai, Bayan haka akwai tabonni saman fatar bayanshi sheikh Ya faWa tare da mi?a hannu ya ru?o bargon tare da janshi Ya yaye shi gefe Waya, faffaWan bayan danish ne Ya bayyana, Fari sol sai dai ko ina da tabon ja.

 Wannan tabon na bayanshi, sahun harsashin bindigar da jami an isod suka harba mashi ne, dama ya faWa min sunyi mashi illah acewar salsabeel.

Tsananin tausayinshi ne ya kama prime minister, ji yake tamkar ya rungumoshi, baisan ya akai ya tsinci kanshi da son ganin fuskar yaron ba, shi dai ya kwanta mashi arai,
 Nayi mamakin ganin suffarshi, naji kace min yarone amma surar jikinshi bata yara bace prime minister ne yai magnar yana duban owais
Chief dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa ya furta wata kil halittarsace haka, Girman jiki da ?ananun shekaru
Jinjina kai prime minister yayi kafin ya kuma cewa baba Yanzu me yakamata muyi mashi don mu taimakashi ya dawo normal? Ko dai zamu kira likitane Ya duba shi ?
Sheikh Imam Yace kada ayi haka, saboda bakowa bane zai Iya tunkararshi a wannan yanayin ya zauna lafiya, kawai kubi shi da addu a in sha Allah zai warware
 Akwai ruwan zam zam na addu a da na ta6a jaraba bashi, inaga da za a same shi wata kil Ya taimaka mashi wajen samun lafiyarshi, Kafin rasuwar mahaifina Yana yin amfani da ruwan zam zam din wurin yin treatment din mutanan dake fama da irin lalurarshi.
Salsabeel ne ya kora masu jawabin, sheikh Imam Yace ?warai kuwa zam zam Yana da amfani, idan akwai inda za a same shi kuyi ?o?arin samun shi
Prime minister yace in sha Allah zamuyi ?o?arin samun zam zam din, baba mun gode da ?o?arin da kayi mana, Allah ne kaWai zai Iya biyanka
Boss man yace ya sheikh ya akai rawaninka da hular suka faWo ?asa? Allah yasa dai ba wani abun bane ya faru Ya furta maganar tare da juyawa ya nufi bakin ?ofar, Ya dauko mashi rawanin da hular.
Murmushi sheikh imam yasaki kafin yace kai dai bari, sha ani da ba?a?en shaidanu ba abune mai sau?i ba, ai dambe muka yi dasu, suna bugu ina bugu na haWasu da ayar Allah, Ni ban ma lura babu rawanin akaina ba sai da ka yi magana murmushi kowannansu yakeyi, maganarshi ta basu nishaWi.
 Yaron nan fa sai mun dage da yi masa addu a, Yana bu?atarta, domin kuwa shaiWanun dake atare dashi mugayen shu umaine suna da hatsarin gaske, ba a ta6a su a zauna lafiya, amma da yake mu da Allah muka dogara kuma munyi imanin cewa shi kadaine gatanmu in sha Allah babu wani mahalu?i daya isa Ya karya mu sai dai mu muga bayanshi, Na tausaya ma rayuwar yaron kuma ashirye nake da in bada gudummuwata don ganin mun raba shi da su da kakkausar murya sheikh imam yayi maganar, gaba Waya sun natsu suna sauraronshi, har ya kai ?arshen maganarshi kafin chief owais ya soma yin magana a tsanake sheikh zamu iya sanin me yaron yake bu?ata a yanzu ?
Numfasawa sheikh imam yai yayin da yake bin sumar kan danish da kallo ya furta Idan zaku Iya taimaka mashi yai wanka, tabbas zaiji daWin jikin shi, sannan ashirya mashi lafiyayyan abincin da zaici inyaso ko abakine sai abashi tunda bai iya ci da kanshi, Bayan haka daga rana irin ta yau duk wani abu da zai yi amfani dashi kada a kuskura abashi batare da an tofe shi da addu a ba, tun daga kan ruwan da zaisha, shimfidarshi, ruwan wankan shi da suturar sanyawarshi........ kafin malam ya ?are jawabin, Boss man yai hanzarin tarar numfashinshi da cewa Allah yaja da ran malam, yaron ba musulmi bane, hakan zai yiwu kuwa? Yar Uwarshi unaisah ta fada min cewa sunyi fama dashi akan ya musulunta amma ya?iya, ko kalmar bismillah bai ta6a furtawa ba

Har cikin zuciyar prime minister baiji dadin jin cewa Yaron ba musulmi bane, Sheikh Imam yace in ba wani iko na Allah ba zaiyi wuya ya musulunta idan har shaidanun jikinshi basu rabu da shi ba, sune suke hana shi ambaton sunan Allah saboda lagwon su ne, In sha Allah zamu magance matsalar nan badajimawa ba
Ajiyar zuciya prime minister ya sauke, haWi da numfasawa yace Ina son ganin fuskarshi ya furta hakan Yana duban chief owais, da sauri salsabeel Ya zagaya ta 6angaren daman gadon, Ya haye tare da ruko bargon da hannun shi ya tattare shi gefe Waya kan mattress, santala santalan cinyoyinsa farare sol sunyi sambal dasu, sai uban tabonni, kafin komawarshi maciji short ne ajikinshi haka zalika A yanzu haka da yake akwance gajeran wandonne.

Sanin nauyin jikin Danish yasa salsabeel nannaWe hannun jallabiyarsa ya daddage Ya ru?o kafaWunsa da hannayensa ya juyar dashi ya fuskanci ceilling, still fuskarshi bata bayyana ba saboda yalwatacciyar sumar kanshi data rufeta.
Cike da zumuWi prime minister yace da salsabeel please, ka jinginar dashi kan headbored, Ka nannaWe min sumar kanshi daga kan fuskarshi inason ganinshi da kyau
Cikin girmamawa Salsabeel Ya amsa mashi da toh, Kafin Ya daddage Ya Wago da Danish Ya jinginar dashi jikin headboard, A hankali Ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login