Showing 54001 words to 57000 words out of 260999 words

Chapter 19 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

surukan naki sunzo zamu ?ara yin wasu hotunan tare, Hakan Yana ?ara dan?on zumunci, fuskar Aneelerh Wauke da murmushi ta ke bin Bayan Zahra da kallo, gefen gadon ta zauna tana Jiran dawowarta.

*EVIL FOREST*

Tun da garin Allah Ya waye Masu a cikin ?urmin dajin, Kowan nan su Ya farka, Da wata irin matsiyaciyar yunwa, suna zazzaune abakin bishiya sun jingina bayan su, Sai hamma suke Yi, Jiya basu ci abinci da yawa ba kafin Kwanta, sauran Kayan marmarin da suka rage ne su ka sha, dan ma suna da jumurin yunwa, Hankalin su ba akwance Yake ba, Danish Ya?i farkawa daga bacci, tsawon awanni tun daren Jiya da Angel ta sanya shi yin bacci yake ta yi, Ko motsi Ba ya yi numfashinsa ne kaWai ke fita, tun suna sa ran zai farka har sun fara tunanin Anya kuwa Lafiya? Baccin ya wuce na hankali, domin kuwa tuni safiya ta jima da wuce wa sun shiga tsakar rana. Sun tsare shi da ido suna kallon shi, A saman shimfiWar da Angel ta yi mashi, ya ke a kwance sun ?udundune shi da bargo, tuntuni su ka so su tada shi daga bacci amma Angel ta hana su, ita aganinta bai kamata su takura mashi ba, tsawon wata Waya baya runtsawa kullum shine yin gadinsu, Na yau kawai Ya samu ya runtsa ai bai kamata su katse mashi hutun shi ba.

 Angel Yunwa mu ke Ji Parveen ce Ta yi maganar, Fuskarta A kumbure ga miyan bacci a gefe da gefen bakinta, sumar kanta A haukace take babu gyara kamar ?ar mahaukaciya, Angel da ke Fuskantar su tana zaune daga gefen shimfiWar Danish, fuskarta sam babu walwala, abun ya fara damunta ganin ya?i farkawa fatanta Allah yasa baccin lafiya ne ya ke yi.
 Genie we are feeling hungry, pls cikina kukan Yunwa yake mini Jemimah ce tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka, idon Angel akan fuskokinsu, Batul sai hamma take Yi, tana faman yamutsa fuskarta.

 Ki jaraba Tada shi mana, wata ?il Ya farka, Tun da kinga mu bamu san kan dajin nan ba, balle mu ce zamu shiga ciki mu nemo abinci Naufal ne yai maganar muryarshi da kasala.

 Ni zan Iya zuwa na nemo mana abincin sai mu ci Gabriel Ne yai maganar, hannunshi Waya asaman sumar kan Azeeza da ke kwance saman ?irjin shi.

Girgiza kai Angel ta yi A a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne kaWai zai Iya shiga dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba, bubbuga ?afa jemimah tayi cikin shesshe?ar kuka tace wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki tada shi ki tada shi Kin ?iya so kike mu mutu ko ?

Gaba Waya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel faWa, ita kanta Angel kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar fusata.
 Angel ku tada shi mana Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro kurkuku, baya magana daga Eh sai a a, su kaWai ne abunda Yake iya furtawa, amma yau sai gashi yayi masu magana, sun Wanyi mamaki kuma sunji daWi ga dukkan alamu sau?i ya samu
Saboda maganar Haris yasa ta kai hannu ta bubbugi kafadar Danish, Muryar ta ?asa ?asa take furta sunanshi Danish wake up! Ka tashi suna jin yunwa, shiru bai motsa ba, Kusan sau biyar tana yi mashi magana har acikin kunnanshi takai bakinta

Nan fa gabanta ya fara faWuwa, Parveen tace ki buge shi mana wata ?il ya farka Ba tare da ta kalli parveen ba tace bazan Iya ba ta ambaci hakan tare da cigaba da kwala mashi kira.

 Angel nauyin bacci ne da shi, Ba haka yakamata Ki tayar dashi ba, let me help u,  Gabriel ne ya ambaci Hakan, Sai da ya fara janye azeeza daga jikinshi, tukunna Ya matsa gaban shimfiWar Danish, bubbuga kafadarshi ya yi Da ?arfi haWi da ambaton Sunanshi Danish! Danish! yadda yake kware murya hatta su kansu sautin Ya cikasu, amma wani iko na Allah Danish ko girgiza Bai yi ba, Zuciyar Angel a jagule ta Waura Kunnanta saitin ?irjinshi Bayan ta yaye mashi bargon, jin heart beat Winsa yasa ta Wan sauke ajiyar zuciya sai dai ta yi mamakin dalilin rashin farkawarshi, Hankalin sauran ?an uwan Ya?i kwanciya, Gaba Waya suka dawo kewaye da shimfidarshi Kowa Ya zu?unna
Su Azeeza har sun fara shesshe?ar kuka suna faWin Wayyo Allah Danish Winmu meke damunka, dan Allah ka farka ka yi mana magana ko hankalin mu ya kwanta, Mu mun ha?ura ma da abinci kai kawai muke so ka tashi.

 Ko dai suma ya yi ne? Ku duba cikin gorar ruwan mu idan akwai sauran ruwa ku Wauko Mu yayyafa mashi Gabriel ne yai maganar cikin rashin kwanciyar hankali, Angel tace a a kada ku watsa mashi ruwa, Zuciyarshi fa tana bugawa, bacci ya ke yi, kunsan Danish da nauyin bacci, Balle kuma da ya Wauki tsawon kwanaki bai runtsa ba, Waya bayan Waya suke jogana kunnansu saman kirjinshi don su ji idan zuciyarshi na bugawa, Hankalinsu Ya Wan kwanta da jin sautin heart beat din nashi.
 Nasan nan bada jimawa ba zai farka, Mu Wan ?ara ha?uri Mi?ewa Jemimah tayi tare da bubbuga ?afarta, abunka ga yaro ba ha?uri, Yunwa ce ta addabeta, Juyawa tayi gaba Waya suka bi bayanta da kallo, agaban korayen ciyayen dake shimfiWe a wurin ta tsugunna, ta soma tsigowa tana turawa abaki tana ci, hakan da tayi ne ya tuna masu da Ganyen da ake basu a prison, aiko da sauri batul da Parveen da azeeza suka mimmi?e agaban jamimah su ka zu?unna kamar akuyoyi haka suke cizgar ciyawa suna ci, tsawa Angel da daka masu Meye haka dan Allah? Kunsan wani irin ganye ne ku ke ci? Ku daina a tsawace ta ?arasa maganar, ta mike ta bi su Waya bayan Waya tana kwace ciyawar da suka dam?a a hannun su, Fashe mata da kuka Parveen da jemimah su ka yi Nan take taji zuciyarta ta karya, cikin shesshe?ar kuka suke faWin ba za su iya jurewa ba, yunwa ce ta addabe su, ta taimaka tabar su su ci ganyen, suna jin daWin shi ahaka.
Idanuwanta acike tab da ?walla tace Is ok, Bari na shiga cikin dajin in nemo mana abincin da zamu ci, mi?ewa Gabriel yai Zan bi ki Angel girgiza mashi kai tai A a gabriel, Ka zauna ka kula da su Azeeza, Yanzu zan dawo ba don yaso ba ya amsa mata da toh, Kallon sauran ?an uwan nasu tayi Javed Naufal, Ku kula da su Azeeza, Yanzu zanje na dawo, Naufal yace meyasa zaki tafi ke kaWai, bayan kin faWa mana mu yi takatsantsan da dajin nan akwai mugayen halittun da zasu Iya cutar damu, why angel? Gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ke kaWai ba, sai dai mu tafi mu duka, Yai maganar tare da mi?ewa, Javed ma Ya mi?e, haris ne kaWai Ya rage a zaune yana sauraronsu.
Ita kanta gabanta faWuwa yake yi gani ta ke yi kamar wani mugun abun zai iya faruwa da ita
Murmushi ta ?a?alo akan fuskarta duk don ta kwantar masu da hankulan su yasa tace Bawani abu fa, da zarar nayi addu a Allah zai tsare ni har inje in dawo lafiya, ku kwantar da hankalinku girgiza kai Gabriel yai bazai yiwu ba Angel, bana so wani abu ya same ki ta silar mu, idan har ba zaki bari mu bi ki ba, To ki bari Danish Ya farka Ya je da kanshi ya samo mana abincin.... tunkan ya ?arasa maganar Angel tai saurin katse shi da cewa su Azeeza yunwa su ke Ji, Na yadda Gabriel Ka raka ni mu tafi, ku kuma ku zauna yanzu zamu dawo Hankalinsu ya Wan kwanta, Atare da Gabriel Suka nufi Cikin dajin, Hannunta ru?e da ?aramin kwandon su, komawa su azeeza su ka yi abakin bishiya suna zaman jiran dawowarsu.

Cikin dajin suka kutsa suna tafiya suna dan tattauna fira a tsakaninsu, ta ko ina bishiyoyine masu tsayi Da faWi, Rassansu sun lullu6e wurin da inuwar su.

 Hankalinka ya kwanta ka biyo ni, ni ban san ma ina zamu dosa ba, Ka ta6a shiga daji ? Ta jefa mashi tambaya, girgiza mata kai yai alamar a a bazan Iya tunawa ba Angel, na manta da komai na rayuwata, amma inaji araina koda ace ban ta6a shigowa daji ba, zai iya yiwuwa na ta6a kallon shi a waya, Ni yanzu burina mu fita daga Cikin Dajin nan, Ko mun samu mu tona asirin zaluncin da ake yi a cikin kurkukun ?addara, Angel na damu da rashin ?ar uwata, ina tsoron kafin mu yi nasara su kashe min ita yayin da yake yin maganar yanayin fuskarshi ne Ya canza, abun ba ?aramin ta6a zuciyarshi yake yi ba duk in ya tuna da ?ar uwarshi Gabriellah.
Cikin nuna jin tausayin shi angel tace ka kwantar da hankalin ka, Idan Allah yasa mai tsawaicin kwanace zamu ganta, in kuma ta riga mu gidan gaskiya, Allah Ya ji?anta, yana daga cikin ?addarar bawa, ba dole ya rayu da abunda ya ke so ba, wata rana ma kowa zai mutu ba wanda za a bari gadin duniyar....... fira ta yi daWi sai nutsawa suke Yi, cikin Dajin ba tare da sunsan inda zasu dosa ba, Ga wata iska mai daWi da ta ke kaWawa, wasa wasa ?arfin iskar sai ?aruwa ya ke Yi, ta cika masu idanuwansu da?yar suke buWe su.

Yayin da su Angel suka tafi nemo masu abinci, Sun yi zazzaune zaman jiran tsammani, Har sun fara lumshe idanuwan su saboda iskar dake kaWa masu ba ?aramin kasala take haifar masu ba, kwatsam! Ba zato ba tsammani kunnuwansu suka soma Jiyo masu wani irin sautin gurnani mai matu?ar rikitarwa da razanarwa, A firgice suka ware idanuwansu, Yayin da zuciyarsu ke buguwa da ?arfi da ?arfi tamkar zata 6allo ?irjin su, tsananin tsorone Ya kamasu sai faman wurwurga ?wayar idanuwansu suke Yi, a ?o?arinsu na su gano ta inda sautin gurnani ke fitowa, sai dai sun kasa sani kuma sun kasa ta6uka komai, Azeeza tuni ta shige ma Batul kamar zata koma Cikinta, Jikin su sai faman yin kakarwa yake yi saboda gurnanin ya cika kunnuwansu, Haris dake azaune gaban shimfiWar Danish muryar shi adabarbarce ya ke ambaton sunanshi da..da..nish ka tashi, pls ka tashi danish, Wani abu yana tunkaro mu Da rarrafe su batul suka ?arasa gaban shimfiWar Danish, Cikin fitar hayyaci suke bugun Jikinshi don ya farka ya ceci rayuwarsu, duk sun bi sun ruWe tsigar Jikinsu ta tashi hai?am, Har suna haWa baki wurin ambaton sunanshi Danish mun shiga uku, dan Allah ka farka, Wannan wani irin sauti ne haka babu daWin ji, ga Angel bata nan sun tafi tare da Gabriel, Ni dama nasan zai yi wuya mu bar dajin nan da ran mu cikin shesshe?ar ku ka suke magana hawaye na bin fuskokinsu, Jemimah da azeeza tuni sun rushe da kuka mai sautin gaske, tunkafin ma suga menene ke tunkarosu, sautin kukansu Jemimah shiya ?ara Janyo hankalin Abunda ke nufo su, basu san sune suke Janyo shi ba, babu wanda yai hankalin Ya tsawatar da su akan su daina Yin kukan suyi shiru, ba su yi tunanin yin hakan ba, lokacin da sautin gurnani ya ?arfafa hatta ganyayyakin dake a wurin Girgixa suke yi, nan take idanuwansu suka tsaya cak akan wurin da suke zargin zai 6ullo, Kamar An Jeho suka faWo ?asan wurin, wasu irin Mugayen Halittun namun dawa, masu gashi gashi a jikinsu babu kyan gani gwanin ban ?yama, Suffarsu tamkar ta majici sai dai sun gurmi maciji a halitta tsaf zasu Iya haWiye mutun su nannade shi a cikin bakunansu, Tashin hankalin da ba a sama shi Date, Wata irin gigitacciyar ?ara suka fasa, Ganin Yadda halittun suke KurWaWowa sa?o da lungu masu Yawan gaske gasu manya manya, Gadan gadan suke tunkarosu Harwani nannaWe Jikinsu suke yi suna harWewa, tsabar firgi da tsoro ne yasa suka Watsa da gudun gaske kamar zasu Tashi sama, Gudu su ke yi na fitar hayyaci, gudun ceton rai, su kan su basu son Inda zasu dosa ba, wani ?arin tashin hankalin Halittun da gudu suke binsu, Ga sauri da Allah yai masu, sun fuskanci matsanancin tashin hankali mara misaltuwa, musamman ?ananun cikinsu Azeeza da jemimah duk sun tarwatse kowa Da inda nufa, dan bala i, Halittun suna lura da kowace kusurwa suka faWa, Yadda suka raba kawunansu haka suma halittun su ka karkasa kawunansu wurin binsu, Haris da ba ?oshin lafiya gare shi ba, tuni Numfashin shi ya soma sar?ewa, bakinshi ya soma fitar da jini, Gashi kowa Ya watse sun barshi, Yana ji yana gani halittar nan Ta ta taWiye ?afarshi gaba Waya ya kife ?asa, tana gurnani ta wage bakinta masu ha?ora a jere babu kyan gani, ta Zurma ?afafuwanshi.....Innalillah

A 6angaren Azeeza da ke ru?e da jemimah suna ti?ar gudu, hada tuntu6e sun rasa ina zasu dosa, Jemimah sai kuka take yi tana ambaton sunan Genie, Cikin rashin sanya Wasu muggan ?ayoyi suka Sargaho ?afafuwansu kusan atare suka rubza ?asa kansu ya daku.

A 6angaren Batul da parveen da Hannah da suka nufi Hanya Waya, Halittun nan sai binsu suke yi, sun rasa ina zasu dosa, suna gudu Sumar kansu Na rufe Masu idanuwansu, ba zato ba tsammani ?afafuwansu suka zurma a cikin wani rami da ca6ali ya cika shi, gaba Waya su ka nutse cikin shi, Ko numfashi basu Iya fitarwa.

Idan muka Koma 6angaren Angel da Gabriel, lokacin da suka ?araso bakin wata bishiyar Mangaro sun tsaya suna tunanin hawa saman bishiyar don su tsigo su, atare suka haye suna aikin tsinkar magaro, sai da suka gama Wibarshi a cikin kwando, Gabriel na yun?urin zura ?afarshi Ya sauko ?asa kwatsam idanuwanshi suka sauka akan kurar dake ?asan bishiyar tana cin wani namun dawa data kamo, wahalallan yawu ya haWiya tare da kallon Angel, ita sam bata lura da abunda ya hango ba,
 Gabriel mu sauko mana, Suna jiran mu Muryarshi Na kakarwa yace Angel mun shiga uku, wlh kura ce a ?asa take cin nama, Sai lokacin ta wurga Idanuwanta ?asan bishiyar, Gabanta yai mugun bugu, muryarta da tashin hankali ta furta Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Kafin Gabriel ya furta wani abu daga can cikin Dajin ihun muryar Naufal Ta karaWe kunnuwan su, Kallon Juna su ka yi nan ta ke su ka fahimci babu lafiya a wurin ?an uwan su, zufa tuni ta wanke fuskarsu, ganin tana yun?urin sauka yasa gabriel dam?o hannunta, muryarshi a hargitse yace Kada ki sauka angel kashe ki za ta yi Girgiza mashi kai tayi idanuwanta sun rikiWa jawur dasu tace ?wara ta cinye ni, wlh sai naje wurin ?an uwana, Baka ji ihun naufal ba, Allah kaWai yasan meke faruwa dasu kokawa suka soma yi da Gabriel a saman bishiyar, ya hana ta saukowa sai kiciniyar kwace kanta ta ke yi, aiko Suna cikin Yin kokawar nan Gaba Wayansu suka ?undumo ?asa agaban kurar nan, Bakin ta ca6a ca6a da jini, Kafin ta Wago da ido ta kallesu, Da iya ?arfinsu na ?arshe suka yun?ura suka mi?e a guje suka watsa, da gudu itama kurar tabisu tana gurnani, babu wanda bai fita hayyacin shi ba, lokacin da suka faWo wurin da suka bar su azeeza hankalinsu ba ?aramin tashi yai ba, gabin babu kowa ga kuma Danish a kwance yana ta sharar baccin shi. Kafin Angel tayi yun?urin zuwa wuri shi kurar nan ta dako uban tsalle ta faWo masu, Da ?arfi gabriel Ya fusgi hannunta tana kuka tana ambaton sunan danish Tana mi?a hannu yaja ta da gudu, wani iko na Allah kurar ta tsalle Danish tabisu da gudu, su kawai ta ke hari, kurWaWawa suka yi cikin dajin suna gudun famfalaki Kura ta zamar masu masifa ta hanasu sakat.........

*Boss Bature
'?*

Tun bayan da dr shureim ya fito daga bedroom Winshi ya nufi Palour, A zazzaune ya samu Alhaji ubaid tare da Uncle musa zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Layla tana a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, Idon shi na akan Uncle Win nashi, Ya Wauki wankan tsadaddiyar shadda mai Waukar ido, ?amshin turaren shi Ya cika palourn, idanuwanshi suna a lumshe, hannun shi na dama haWaWWiyar agogon diamond ce wadda a ?alla price Winta ya kai 300m, mutunne mai ji da naira, hutu ya zauna mashi ko Alhaji ubaid ba zai nuna mashi tarin dukiya ba, ko a mu?ami bai kai shi matsayi ba, Alhaji musa ?anine ga Alhaji ubaid uwa Waya uba Waya, kuma shine former president, akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, A kyawun halitta Musa ya zarce Alhaji ubaid, Yana da hasken fata yayin da Alhaji ubaid yake da duhun fata, Sannan yana da Yalwatacciyar sumar kai tasha gyara ga sajen gefe da gefen fuskarshi ba?i wulik, Kamar matashin saurayi. Ya iya Waukar wanka ga aji ga kuma ji da kai.
Daga ?asan carpet dr Shureim ya zauna cikin girmamawa ya gaishe dasu, Alhaji ubaid ne kaWai ya amsa mashi, kawun nashi kuwa ko arzi?in kallo bai samu ba, har sai da hajiya layla tace mashi baka ji shureim yana gashe ka ba ? Ba tare daya buWe idon shi ba yace Naji, sanin halin shi yasa Shureim bai damu ba, Layla dai ce ranta ya 6aci dama ita bata iya 6oye fushin ta, Alhaji ubaid ko murmushi ne akan fuskarshi, Har yau mamakin Halin ?anin nashi Yake yi.

 Shureim, kasan shi fa mutumin turaine ba haka yake son ka gaishe shi ba, Ka matsa kusa dashi yaji Wumin Wanshi a jikin shi acewar Alhaji ubaid,

Yatsina fuska layla tayi, aranta kuma ji take kamar ta sha?e wuyan Alhaji musa, jin kanshi na matu?ar ?ona mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login