Showing 99001 words to 102000 words out of 260999 words

Chapter 34 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

baban nasu, maganar shi ta tuna mata ?uruciyarta, shi dai burinshi saratu taci abinci ta kwanta ta huta idan ta dawo daga makaranta, bayason tana aikin wahala.

 Nagode da kulawarka akaina baba, Allah yabar mana kai abun alfaharin mu

Amasa mata yai da amin, Juyawa tayi ta kalli Sir mubarak da turai

 Ni zan wuce yayana, a huta lafiya bata jira amsarsu ba, da sauri ta fuce daga Wakin.

Bayan fitarta, tattaunawa suka cigaba da yi game da yadda za a tsara komai na shagalin da za su yi.

Tun da ta shigo Wakin, komai na ciki agyare ta same shi, Safa ta kawo mata lunch Winta yana asaman table ta Waura mata shi.

Cire lapcoat din jikinta tayi a saman Hanger ta sagala ta, shaf shaf ta canza kayan jikinta zuwa, rigar shan iska, daga bisani ta koma gefen gadon ta, ta zauna domin cin abinci, farawa da bismilla ta kai hannu ta dam?i haWaWWan cup na cofee ta kur6e shi, bayan ta gama ta soma shan farfesun naman kaza da zafi zafinshi, cikin ?an?anin lokaci ta shanye shi ta kuma dam?ar Chips ta cinye ta cakumi cheese burger ta tura abaki hankalinta kwance take cin abincinta.

Ringing Win wayarta ne ya janyo hankalinta ga duban hand bag dinta dake ajiye saman pillow.

Ba ta yi niyar Waga kiran ba, don ita a ?a ida bata picking call idan tana cin abinci saita kammala, hakanan dai tayi ra ayin duba me kiranta, tissue ta yaga ta goge bakinta, kafin ta yunkura ta ruko handbag din, duba sunan me kiran nata tayi sunan ya fito 6aro 6aro asaman screen Win iphone Winta

*Princess Mujeedat* murmushi hajiya saratu ta saki da zumuWi ta Waga kiran cikin harshen turanci ta soma yi mata kirari

 Uwargidan shugaban ?asar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta HaWaWWiyar Daular Larabawa! Sarauniya Waya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ?ari mun kulle ?ofa sautin ?ayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya karaWe kunnuwan saratu, da alama taji daWin yabon da saratu ke yi mata.

bayan ta gama yi mata kirarin ta Waura da cewa Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem Win baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke (idan kaga hajiya saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba ?aramin mutun bane, babban gorone magogin ?arfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da kalar yadin>?#?)

Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice Winta zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arzi?i waWanda suka gaji abun, da izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata.

 Ba abun da ki ke tunani bane ?anwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma na kira don mu gaisa itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa.

 Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka ?asarmu fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana.

 Naji daWin kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ?ara godewa Allah daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, ha?ika ban ta6a danasanin auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ?ar?ashin inuwa Waya har Allah ya azurtamu da samun zuri a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna nuna min ?auna sosai nima Ina sonku

Hajiya saratu baki ya?i rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta ?arasa haWiye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya.

 Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu ?anwata baki daina ciye ciye ba ko ? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta sai ?ara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara neman izni ba to bata Waga kiran nashi.

*A GIDAN ?AN IYA*

Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su Wan ?ara kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu cewa Ai sun samu gidan da zasu zauna a abuja ya 6oye ne bai sanar dasu, harma ya samu aiki a companyn sharufuddeen, ba ?aramin farin Ciki su ka yi ba sun tayashi murna sosai, musamman da suka ji cewa bazasu raba Aneelerh da junaid ba ko da yakai shekarun da zasu Iya kar6ar shi ne, Zasu ha?ura ne har Allah ya bayyanar masu da su Uzair, dama rashin Wan nasu ne yaja har suke son kar6ar shi, Aneelerh hada kukan farin Ciki, Ta ?ara jin son surukan nata, ba ita kaWai ba hatta su mami sun ji dadin ziyarar da suka kawo masu sun kuma jinjina ma ?o?arinsu na barma Aneelerh Wanta, su kansu sun fahimci ba ?arami so suke yima yaron ba tun da gashi ta dalilinsa sun dawo abuja da zama, ba su kai ga barin gidan ba, abie ne ya dakatar da su yace su Wan jira akwai malaman da zai sanya su yi masu safkar al?ur ani a sabon gidan su, hakan ba ?aramin daWi yai masu ba, don su basuyi tunanin yin hakan ba.

Hankalin Mahboob ya?i kwanciya tun da yayi tozali da hoton Angel, a daren ranar da?yar Ya iya runtsawa, saboda fuskarta da ke yi mashi gizo, ya kwana da mamakin baiwar Kyan da Allah Yayi ma yarinyar, bai ta6a ganinta ido da ido ba sai dai ahoto yasanta tun tana ?ar ?aramarta, Aneelerh take Waukar ta hoto da video tana sanyawa a status dinta to anan yasanta, a ?arshe daya gaza ha?ara bayan sun dawo daga sallar asubahi, ya lalla6a yaje Wakin aneelerh, tsabar Iya fadanci hada Kiranta da aunty, bai ta6a kiranta hakan ba sai yau da Allah ya jarabe shi da son sanin komai dangane da Angel.

Tambayoyi ya tsare Aneelerh da su akan ta fada mashi dagaske yarinyar mutunce bata haWa jinsi da aljanu ba? Don shi gaskiya bai yarda da kyanta ba, Ya zarce na jinsin mutane, tun da yake kallon indian film, da korean drama bai ta6a ganin jarumar da ta kama ?afar Yarinyar a kyau ba.

Aneelerh taci dariyar wautar Mahboob, har tambayar shi ta yi ko dai sonta ka ke yi ne? Naji kanata zuzuta kyawunta,  da sauri ya dafe ?irjinshi da hannu Yana faWin Sai kace dai bani da hankali aunty Aneelerh? Ae rijiya ba wurin gaWar makaho bane, Nasan ciwon kaina ban shirya yin jinya a gadon asibiti ba, ni kawai kyanta ne ya ruWe ni ba wani abu ba, tsakani da Allah yarinyar ba matar yaku bayi bace, ko makaho ya shafa fuskarta zai shaida hakan tafi dacewa da Manyan ?a ?an masu kuWi waWanda suka ji?e da naira, ni yanzu idan nace zanso ta, ko zan aureta, Aunty Aneelerh ina zan samu kuWin Waukar Wawainiyarta? KuWin man shafawarta dana zuwa saloon kaWai sun isa su takaita jarin mutun balle ni da ba kuWi gare ni ba

tsabar dariya Aneelerh hada hawaye, shiko fuskarshi a daure yayi mata maganar bada wasa ba, ya ?ara da cewa ?wara na auri ?ar talaka wadda ba ta da tsayin gashi, sai yafi min sauki, in manna mata ?ar naira Wari biyar taje gidan kitso ayi mata, man shafawa a jiki kuma Ko vaseline na siya mata ya wadatar, Iya kuWin ka iya shagalin ka, Amma wannan Ifritun yarinyar wlh aunty Aneelerh duk talakan da ya aureta ya cuci rayuwarta, yasin ni har kotu zan Iya kai ?arar shi, ita kanta idan ta auri talaka batayiwa kanta adalci ba fisabilillahi.

Lamarin mahboob sai addu a, Haka ya dinga santin kyan Angel, Har faWi yake shi ya kosa A gano su, in sha Allah zai tayasu da addu a akan Allah ya bayyanar dasu, burinshi idan Allah yasa ta dawo gidansu da zama zai zama na hannun damanta saboda idan ta auri basarake ko wani mai ji da naira, ya dinga samun ?an canjin kashewa.

Saboda Angel Ya manta da zancen neman zoben shi, gaba Waya ya Waura burin duniya akan Angel, harya fara ?iyasta kuWin da zai tatsa wurin Mijin da zata aura.

Da?yar Aneeleerh ta samu mahboob Ya fita daga Wakinta, ya addabeta da zancan kyawun Angel.

Alhamdulillah, a yau labarin 6acewarsu Angel ya dawo tamkar sabo a shafukan sada zumunta, ta ko ina buga labaransu Akeyi tare da hotunansu, tun da Ont suka fara yaWa labarin nan take sauran gidajen jaridu suka bubbuga labaran da gidan radio. Ta ko ina zancen su akeyi kamar yau abun ya faru, labari ya dawo sabo, Yanzu shine Top story dake trending a social media, mafi yawan mutane Kyawun Angel ke ruWarsu har su kaiga Waukar labarin su karanta sannan suyi share Winshi don ataimaka a gano su.

Fuskar Aneelerh tun safe da annuri akanta, Mutane sai kiranta sukeyi awaya sunayi mata jaje haWi da tambayarta wasu bayanai da suka danganci Angel, a ?arshe sunayi mata fatan Alkhairi, Numbobinsu ne akan labaran da akayi share nasu shiyasa mutane ke ta kiransu suna yi masu jaje.

Ta natsu saman mirror chair, turkish gown ce a jikinta launin maroon tayi bala en yi mata kyau, babu mayafi akanta zallar sumar kantace
Hannunta na aruke da wayarta, tun Wazu take maimaita karanta labarin su Angel da akayi posting Winsa a shafin Ont na insta

 Mommy muryar junaid ce ta janyo hankalinta ga kallonshi, ta cikin mirror, Hajiya adama tayi mashi gayu don yau ma a Wakinta Ya wuni, ita tayi mashi wanka, tasa Aneelerh ta kawo mata kayan shi ta santa mashi jeans da shirt fara, sumar kanshi tasha gyara.

?arasawa yai gaban kujerar da take a zaune, ya daura kanshi saman laps Winta, ?amshin turaren jikinsa na Hajiya adama ne da ta shafa masa
 Wow my baby boy, kayi min kyau sosai, lallai granny Win nan taka tana matu?ar sonka irin wannan gayu haka da tayi maka

?aura wayar tayi gaban mirror, ta sanya hannu biyu ta Wago da junaid ta Waura shi saman laps Winta, langwa6ar da kanshi yai saman kirjinta

 Mommy namanta ban faWa maki ba, jiya wani mutun ya kira awaya har yace wai in faWa maki.... katse shi tayi yaushe aka kirani? Bana son ?arya fa
Muryarshi da shagwa6a ya ce  mai ?arya fa Wan wuta mommy, ni dai Allah ba ?arya nake maki ba mi?a hannu Aneelerh tayi ta Wauki wayar, tana shiga call logs tayi arba da New number da aka kira kuma an Waga kiran.
 Junaid bana hanaka Waga min kira ba ?
Zumbura mata maki yai to ai nayi tunanin Angel ce ke kira, kuma baki a Wakin shine na Waga, kuma yace in kai maki wayar ku yi magana ni kuma na?iya nace sai dai ya faWamin in gaya maki tun da ya fara magana ta ?ura mashi ido tana kallon shi, komai nashi burgeta yake yi, musamman in yasanya shagwa6a a maganar shi.

 Meyasa baka kawomin wayar ba ?
?ura mata ido yai ba tare daya furta kalma ba
Sam hankalinta bai kwanta da ba?uwar number da ake yawan kiranta da ita, tuntuni take ganin missed calls daga Number ta?i yarda ta Waga kiran don har yanzu bata daina fargabar mutanan nan da suka Wauketa da sunan jami an sirri.

 Junaid, daga yau karka kuskura ka ?ara Waga min kira kaji ko ? ?aga mata kai Yai alamar eh, tace yanzu zan sanya number Win a black list, hankalina zaifi kwanciya ta yi maganar a yayin da take cigaba da daddana wayar hannunta, blocking number din tayi saida ta kammala baby junaid yace
 Mommy namanta ban gaya maki ba yace wai in faWa maki daddyn um am.... natsuwa ta yi tana kallon shi,
 What ? Shine yace min wai ince maki daddyn ummm... sam ya kasa tuna sunan duk ta ?agara da sonjin ?arashen sunan
 Kai nake sauraro ka fadamin mana
 Wai ma daddyn..... girgiza kai ya Wanyi mommy kaina ya cunkushe na manta, idan na tuna zan gaya maki

Murmushine shimfiWe saman la66anta, Idanuwanta akan face dinsa

 Shikenan My baby boy, yanzu faWa mun Ina ka 6oye zoben Mahboob? Na duba cikin rigar pillow ban ganshi ba, yakamata mu maida mashi abunsa kada ayi mana kallon 6arayi

Gatsina mata hanci junaid yai haWi da murmura idanuwanshi yace tab ae Allah bani bashi, Na angel ne na 6oye shi wani wuri inda ba wanda ya sani, Allah Angel zan baimawa shi, kuma kada ki fada ma kowa in baki so mu 6ata dake,

Dariyace ?umshe abakinta kai junaid babu kyau fa, da guminsa ya sayi zoben taya zaka ce ba za ka bashi ba? Kana so Angel Winka ta sanya abun sata? Kayan haram da ba mallakin ka ba?
Girgiza mata kai yai a a mommy, to ai bani da kuWin da zan siya mata wani

Shafa sumar kanshi tayi mommynka tana da kuWi, zan siya maka wani but pls ka maida ma mahboob zoben shi kaji my boy

?aga mata kai yai Toh zan maida mashi badan halinshi ba, kuma Allah idan ya ?ara cinye min chocolate Wina saina sanya shi kuka fashewa Aneelerh tayi da dariya, ba ?aramin nishaWi yake sanyata ba.

*DAULAR ALHAJI MUSA*

Ya kasa fita ko da ?ofar Wakinsa ne, tun jiya da ya zo gidan ba?unta yake yi masu, fitowa yai daga Cikin bathroom jikinshi sanye da bathrobe fara ?yal, ya Waure igiyarta a tsakiyar cikinsa daga can ciki akwai short da ya sanya, sumar kansa ta manne ma fatarsa saboda lemar ruwan wankan daya ji?ata, Dr shureim ba dai kyau ba, ta ko ina sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikinsa, ya ji daWin dawowarshi gidan uncle Winsa baida wata damuwa, musamman tarbar da ya samu awurin Hajiya sarah, ta nuna farin cikin ganinshi kamar Wan cikinta haka take tarairayarsa.

Walking slowly ya nufi dressing mirror Don Ya kimtsa kanshi

Gyaran muryar da aka yi mashi ne yasa shi yin saurin juyo wa baya don ganin wanene

Lokaci Waya ya sauke ajiyar zuciya yana kallon uncle Win nasa
Yana daga tsaye bakin ?ofa, kayan gym ne a jikinsa, short da riga sun Wame jikinsa, mutumin akwai ?ira kamar Wan wrestling.

Da fara a akan fuskar shureim ya furta My Uncle yai maganar yayin da yake tunkarar shi, gabanshi sai faWuwa yake yi ya rasa gane dalilin dayasa a duk lokacin da ya yi tozali da uncle din nashi sai yaji faduwar gaba.

Kyakkyawar fuskar Alhaji musa, mai Wauke da ?ayataccen saje, ba murmushi sai dai yaWan sakar mashi fuska.

 Fushi nakeyi da kai shureim baka iya takowa kazo Wakina ka gaishe ni, ko dama jira kake inzo room Winka ? Cike da izza da nuna isa yake yin maganarsa.

Yawu shureim ya haWiya ba haka bane uncle, yanzu nake ?o?arin zuwa part Win naka

Yamutsa fuska Yai okey, nima na fadi ne kawai ba don wani abu ba, ko akwai abun da ka ke bu?ata ?

Girgiza kai shureim yai a a aini ka gama min komai kawuna, nagode sosai da kulawarka agareni, Allah yabarmun kai matsawa Alhaji musa yai dab dashi, Ya janyoshi a jikinshi yai hugging nashi tightly, in a whisper ya furta idan akwai abun da kake bu?ata ka sanar dani, idan ma baka Iya fadamin ka tura min ta text message, sannan akwai sa?o da za a kawo maka zuwa anjima, ya ?arasa maganar tare da raba jikinsu daga na juna.

Still face din Uncle musa ba fara a, haka Allah ya halicce shi baida sakin fuska.

 Nagode sosai uncle, tun jiya da nazo gidan nan akayi min kyakkyawar tarba naji daWin Hakan sosai

 Shureim ba ayi min godiya, next time kada ka ?ara fuskarsa a Waure yai maganar
Cikin jin shakkar shi shureim ya furta in sha Allah ya ?ara da cewa burina ka canza rayuwarka shureim, banason ganinka acikin damuwa, kaman ta duk wani abun da ya faru a rayuwarka, shiyasa na dawo dakai gidana saboda nasan zaka fi samun kwanciyar hankali, sannan Inaso naji ra ayinka, bance ka bani amsa yanzu ba, nafi so sai ka natsu kayi nazari tukunna.

Jinjina kai shureim yai, idanuwanshi na kallon ?asa, saboda ?warjinin alhaji musa bai iya jurar kallon fuskarsa.

 Bazan hana Ka Yin duk wani abu da za ka yi don jin daWin rayuwarka ba, sai dai ban goyi bayan zamanka a cikin gida ba aiki ba, abu na biyu kuma Aure, kasan shi sunnah ce ta manzon Allah SAW, Aure yana Waga darajar mutun yazamto mai cikar kamala da natsuwa, rayuwarka zata canza idan ka yi aure, Na gaji da ganinka a matsayin tazuru Yai maganar yana Waga mashi gira, da zolaya akan fuskarshi, kunyace ta hana shureim furta komai, ji yake kamar ?asa ta tsage ya shige, Yana jin nauyin uncle din nasa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login