Showing 156001 words to 159000 words out of 260999 words

Chapter 53 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

yi kamar ana ?ara gudun agogon Wakinta, hannayenta biyu ta Waga sama tana jera addu o i akan Allah Ya kawo mata mafita.

Muryar Aneelerh ce ta ratsa kunnanta Yar uwata rabin raina, tun safe baki ci komai ba, Ga abinci na kawo maki Shafa tafin hannunta tayi saman fuskarta, Rai amatu?ar 6ace ta yun?ura ta mike haWi da fuskantar Aneelerh, dake tunkarota, hannunta ru?e da madaidaicin tray, mai Wauke da plate din shinkara da ?aramar warmer ta miya, tare da lemu mai sanyi.

Kafin ta ?araso zahra ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana Aunty Aneeleeh idan kin kawo abincin nan domin in ci ne to ki maida shi kitchen! Bana bu?ata a faWace ta furta.

 Haba zahra, kashe kanki ki ke so Ki yi ne? Tun safe baki ci komai ba, Ni kaWai na damu dake, dan Allah ki kar6a ki ci

Harara zahra ta wurga mata cikin 6acin rai tace Ai ni kingama zubda girmanki a idona, tun da har kika iya bani shawarar In amince wurin aikata sa6on Allah, Kin ban mamaki aunty aneelerh, bansan haka kike ba tana magana tana jan majina.

Jinjina kai Aneelerh tayi Laifina ne zahra, Ni da na damu dake shiyasa kike gaya min magana son ranki, daga taimako? Daga yau ka da ki kuma tsammanin zan ?ara baki shawara idan har baki kar6i abincin nan ba wani Wan iskan kallo Zahra ta watsa mata, har saida ta dasa aya amaganarta tukunna zahra ta ru?e qugu kamar ana tunzurata tace Idan har kin damu dani, meyasa ba zaki taimaka mu nemi mafita atare? Saima ?o?arin da ki ka yi don ganin kin sanya ni a gur6atacciyar hanyar da zan lalata duniyata da lahirata, ke ba mai ?aunata bace aunty Aneeleeh, bana sonki kuma bana son ganin ki!, Yakamata ki nisanta kan ki dani, Idan ba haka ba zan yi maki rashin mutuncin da baki ta6a tsammani ba!!

A kausashe Ta furta maganar tana nuna Aneelerh da cazbahar hannunta kamar zata rufe ta da bugu.

GyaWa kai Aneelerh tayi tama rasa bakin magana, kalaman zahra sun bata mamaki, bata ta6a tunanin zahra zata Ya furta mata su ba.

Juyawa ta yi da sauri ta nufi ?ofar fita, adai dai lokacin Mahboob yana ?o?arin shigowa Wakin suka ci karo da Aneelerh, har gaishe ta ya yi amma ko kallon shi ba ta yi ba, hakan yasa shi tsammanin ko wani abu Ya faru ne.

Zahra na jin sallamar shi da sauri ta sanya hannu biyu ta share hawayen dake akan fuskarta, komawa tayi daga gefen gadonta ta zauna tana dubanshi.

Riga da wandon shadda ne ajikinshi, hannun shi ru?e da key din motar shi.

 Zahra Lafiya ki ke yi mini kiran talauci? Ina akan hanyar dawowa gida naga miss calls dinki, Allah dai yasa lafiya

Cikin sanyin murya tace da shi ka zauna mahboob mu yi magana zama yai da Wan mamaki akan face dinsa yace meyasa ki kuka? Naga idanuwanki sun kumbura wanene Ya ta6a ki? Ko ke da aunty Aneelerh ne ?

A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faWin bakomai, banajin daWi ne kaina ke ciwo

 Kin sha magani cikin kulawa yake yi mata magana, Waga mashi kai tayi alamar eh ta ?ara da cewa Aunty Aneelerh ce ta bani maganin

GyaWa kai yai okey, Allah ya sawa?e sister yanzu dai faWamin me kike bu?ata ne Kin dai san ban da ko sisi

Murmushin takaici tasa kar mashi jin abinda yace

 Mahboob ba kuWi zan ro?e ka ba, taimako nakeso kayi min dan Allah, bana son ka tambayeni dalili kawai ka yi abun da nace maka, kuma bana son kowa Ya sani daga ni sai kai

 Kada ki damu, Ina jin ki a ?agare Ya furta mata hakan
 Inason zan siyar da motata ne da wayata, saboda ina bu?atar kuWi ko akwai wanda ka sani da zai Iya siya a yau din nan ? Ta jefa mashi tambayar tana duban fuskarshi.

Mamakine ?arara akan fuskarshi, Har saida YaWan saki baki da ido Yana dubanta Kafin yace ke kuwa me zai ja ki siyar da motarki da wayarki? Runtse ido ta dan yi hawaye na ?o?arin cin ?arfinta tace dashi Mahboob banason tambaya! Kawai ka taimaka mun in zaka Iya in kuma ba za ka yi ba to ka tashi ka tafi kaban wuri

 Shikenan Naji, nayi shirun, amma dai kinsan kowa zai saye su sai kin faWi ko? Ba lallai asamu wanda zai siya da mutunci ba

?aga mashi kai tayi Ni wannan ba damuwata bace, indai kuWin zasu kai 4m Ya wadatar

 Okey, amma ni shawarar da zan baki mai zai hana ki bada motar da wayar taki jingina? Idan kika samu halin biyan kuWin sai ki Kar6o Kayan ki, zahra kinsan babu mai siya maki su idan kika rasa na hannunki kuma ni bazan juri ara maki motata ba Ya faWa Yana yamutsa fuskarsa, Harara ta watsa mashi da rinannun idanuwanta kai fa banza ne wlh, Ni ina ruwana da motarka? Koda zan rasa abun hawa mahboob bazan ta6a aron kayanka ba

Murmushi ya Wan saki tare da mi?ewa yace to Aunty zahra, Ni zan tafi, in sha Allah zan samu wanda zai siya, amma ki sani zamu kasa kuWin gida uku, Ki kwashi kaso biyu ni kuma Waya....

Tunkan ya ?are maganar zahra ta rarumi pillow aguje tabi shi da gudu ya fuce daga Wakin Yana ti?ar dariya muryarta asha?e take fadin wallahi mahboob ka fita idona, Ni ba tsarar wasanka bace, kuWin nan da gumina na tarasu bada gumin wani ba rai a6ace take yin maganar, bayan ta gama zazzaga mashi masifar ta juya ta koma cikin Wakinta tana faman tallabe cikinta dake yi mata kukan yunwa.

Safa da marwa ta soma Yi A tsakar dakin duk ta ?agara da jiran kiran mahboob, Fatanta Allah yasa asamu wanda zai sayi motar.

Wuraren ?arfe 8 na dare, Kiran mahboob Ya shigo wayarta jiki na rawa ta Waga ta kara a kunnanta, Anan yake sanar da ita cewa abokinsa Ya ce yana so harma sunyi cinikin motar akan miliyan uku da rabi zai siyeta, ita kuma wayar zai siyeta dubu Wari biyar idan ta bari ahakan zuwa gobe da safe zai kai mashi Motar da wayar, daga nan zai tura mashi kuWin, tsabar farin Ciki kamar ta zuba ruwa a ?asa tasha, duk da tayi asara ba kaWan, saboda an karya kuWin motar da wayar, amma hakan bai dameta, burinta ta sauke nauyin dake akanta, Bayan sun gama wayar, ta zu?unna takai goshi ?asa tana godiya da Allah, daga bisani ta mike tana ti?ar rawa, da gudu ta fito daga Waki ta nufi kitchen, ta ciko plate da abinci, ta buWe frigde ta dauko lemu mai sanyi kafin ta dawo Wakinta, ita kadai ta zauna tsakiyar gado tana ci tana sakin murmushi, ba?in cikinta Waya ta rasa damar da take da ita na zuwa Obie estate, tunawa da wannan yasata rushewa da kuka ga abinci cike abakinta.

*JOS CITY*

Dare ya tsala sosai, Gari yayi duhu, a lokacin da kowani mahalu?i yake a makwancinsa domin runtsawa, baka jin sautin komai saina kukan tsuntsaye dana karnukan Layi dake Hargowa.

A hankali take tafiya Hannunta ru?e da trolley, doguwa ce a halitta, siririya bata da ?iba sai dai tana da hips, doguwar jallabiyace a jikinta, ta sanya ni?ab ta rufe fuskarta, abun da zai baka mamaki ita kaWai take Bin santar babu alamun tsoro atattare da ita, da taimakon street light ta ke samun damar ganin ko ina, Har Allah Ya nuna mata gidan da take nema, Katafaren Villa ne Mai gingirimeman gate.

da sassarfa ta nufi gate din, tana zuwa gabanshi, Takai hannu ta soma ?wan?wasa ?ofar, tun tana yi a hankali har takai ga tsunto dutse ta cigaba da bugun ?ofar da shi kamar zata 6alle gate din

Security officers din dake tsaron gidan guda Biyu ne cikin kakinsu suka fito daga Wakunansu jiki na rawa suka ?ara so gaban gate din, da alamun mamaki akan fuskokinsu suka haWa bakin wurin furta Wanene ke buga mana ?ofa a dai dai irin wannan lokacin ! Da fargaba suka furta maganar.

Cikin shesshe?ar kuka da muryarta mai tsiwa ta furta BENAZIR CE

kallon Juna Officers din suka Yi, Waya yace Wanene kuma haka? Mutun ko aljan? Wa ki ka zo nema agidan ko dai kin yi 6atan Hanya ne

Tamkar zata fashe da kuka tace dan Allah ku buWe mun gate in shigo, ni ce benazir Wiyar Alhaji ubaid !

Ba ?aramin Waure masu kai lamarin yayi ba, kasancewar su tsoffin masu gadin gidan, sunsan wacece benazir Yarinyar uban gidansu data 6ace tsawon shekara goma sha shidda, kokwanto suka soma Yi anya kuwa itace?

Officer mai gemu yace kai, Da wuya ya zama gaskiya yarinyar da babu tabbacin tana araye kota mutu !

?ayan kuma yace Ai ni banma yarda ba gaskiya, Kusan shekara goma sha shidda da 6atanta sai Yau ?arfe sha biyu na dare zata dawo! anya kuwa ba tarko bane aka Wana mana ?

Mai gemu yace amma kuma muryarta sak kalarta hajiya layla, Har tsiwar iri Waya da tayi maganar

Jin sun?i buWe mata kofa yasa ta rushe masu da kuka mai sautin gaske a faWa ce ta ke fadin wai baza ku buWe mun gate ba, na gaji da tsayuwa wallahi idan baku buWe ba na shigo cikin gidan saina Sa an kore ku

Yawu suka haWiya atare mai gemu yace Ke baiwar Allah, ba yadda za ai mu buWe maki gate ba tare da mun sanar da masu gidan ba, dan haka ki ?ara ha?uri mu faWa masu

Kafin suyi yun?urin zuwa cikin gidan su sanar masu, ba zato ba tsammani suka ji ta bangaje ?ofar jikin gate din dake a kulle, nan take ?ofar ta buWe, hankalin su ba ?aramin tashi Yai ba, A firgice suke dubanta yayin da take shigowa ciki da akwatinta, Ko kallo basu isheta ba, da sauri ta nufi cikin gidan.

Kasa motsi suka yi Kamar an dasa masu Aya, tuni zufa ta wanke fuskokinsu, Mamakin su Taya akai ta Iya bugun ?ofa da ?arfi Har jamlock mai ?arko Ya zame kanshi! Tabbas suna hasashen ba mutun bace aljana ce, tuni suka sha jinin jikinsu.

Tana tafiya tana bin ko ina na gidan da kallo, abubuwa da dama sun canza mata ba kamar yadda ta tafi tabarshi ba.

Adai dai lokacin Zainab mai aikin gidan tana a palour hannunta ru?e da floor wiper tana goge tiles, ta saba ba tun Yau idan bata son aiki Yayi mata yawa takan fito har tsakar dare Tana aikace aikacen ta don ta rage wasu ayyukan na safe duk idan taji ?arfi a jikinta.

Tamkar da rana saboda hasken ?aton kwan dake a falon Ya gauraye ko ina, Hankalinta kwance ta du?ufa tana gudanar da aikinta ba zato ba tsammani taji an banko ?ofar falon.

A firgice Zainab ta Wago tana kallon matar da ta fado cikin falon afujajen, tsabar firgitar da ta yi har batasan sa adda ta jefar da wiper din hannun ta ba, tun daga ?asa har sama take kallonta, Hankalin ta ba ?aramin tashi yai ba, tsananin tsoro Ya kamata, Jikinta ya hau yin kerma, Muryarta na rawa ta furta baiwar Allah wacece ke? taya ya akai kika shigo gidan nan? ?arfe sha biyu na dare ? AruWe take jefa mata tambayar.

Shesshe?ar Kukan matar ne Ya ?ara firgitar da ita, ta soma Ja da baya tana ?o?arin guduwa cikin gidan don ta faWo ma Hajiya layla abun da ke faruwa sai dai kafin Ta juya muryar Matar ya ratsa kunnanta cikin harshen larabcin take faWin.

 AUNTY ZAINAB NI CE BENAZIR!! INA ABBANA! INA UMMI NA! INA MIJINA DA ?A TA!!! A jere ta jefa mata tambayoyin.

Har abada ba zata ta6a mantawa da muryar nan ba, koda kuwa amafarkine Ta jita tabbas zata shaida mamallakiyarta.

A hargitse Ta juya Tana dubanta, A hankali benazir ta Waura ziraran yatsun hannun ta farare tas ta ru?o ?asan ni?ab Win fuskarta ta Wage shi sama tsabar kiWima da ganin fuskar da tayi kimanin shekaru sha shidda ba ta yi tozali da ita bane yasa Jikinta ya hau yin kerma, tsantsar mamaki da al ajabi ne akan fuskarta, ta zazzare idonta akan kyakkyawar fuskar benazir, sam takasa yarda da abun da idanuwanta ke nuna mana gani take yi tamkar mafarki ne take Yi!!

Tayi wani irin haske Kamar ka ta6a jini ya Wigo, Fuskarta sharkaf take da hawaye ta ko ina, ga zufa dake tsastsafo mata sam babu kwanciyar hankali atattare da ita.

Tsantsar tashi hankaline Akan fuskar zainab, Muryarta adabarbarce ta furta be..be..nazir! Dagaske ke ce ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba ?

Da ?arfi ta furta Ni ce Aunty zainab! Ki amsa min tambayoyin da nayi maki !

Tana faWin hakan Nan take Ta yanke jiki Ta faWi ?asa a sume, akwatin hannunta ya kife saman floor.

Juyawa Zainab tayi da gudun gaske ta nufi Wakin hajiya layla, Hada yin tuntu6e tsabar sauri, tunkafin ta ?arasa ta soma ?wala mata kira na fitar hayyaci tamkar ma?oshin ta zai 6allo waje.

 Hajiya layla! hajiya layla

Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnuwan su daga ita har Alhaji ubaid dake kwance saman katafaren gadonsu, A firgice suka farka a lokaci Waya suka mi?e zaune suna ambaton Sunan zainab.

Doguwar jallabiya ce a jikin alhaji ubaid wuyan rigar ya karkace, Hajiya layla kuwa Rigar Bacci ce a jikinta, da sauri Alhaji ubaid ya kunna bedside lamp din Wakin.

Sam babu kwanciyar hankali atattare da su, duk sun ?ura ido suna jiran ganin ta inda zainab zata 6ullo.

Kamar daga sama suka ji ta banko ?ofar Wakin tana faman Yin haki.
Da mamaki Akan fuskar Layla tace Zainab baki da hankali ne? Ko kin makance ne? Taya zaki faWo mana Waki a irin wannan lokacin ba tare da kin nemi iznin shigowa ciki ba !

Kafin zainab ta bata amsa Alhaji ubaid Ya katse mata hanzarinta da cewa Zainab Lafiya kike ?wala mana kifa? Kowani abun ne Ya faru ?

Cikin rawar murya ta furta dan Allah kuyi ha?uri ku yafe ni, bana acikin kwanciyar hankalina ne shiyasa na faWo maku Waki ba sallama nasan bai dace ba dogon tsoki Layla Taja Ba dogon bayani na tambaye ki ba, Ki faWi min uban mi Ya kawo ki Wakin mu?

Bata kai ga ?arasa maganar ba, Alhaji ubaid Yai saurin katse ta da cewa Ya isa haka, Haba kin cikata da faWa, Kin ?i bari tayi mana bayani dangane da abunda ke faruwa tsuke fuska Layla Tayi.

Cikin sanyin murya zainab tace dama BENAZIR ce ta dawo!

Kallon juna Alhaji ubaid da layla suka Yi lokaci Waya, kafin suka dawo da dubansu ga zainab, Har suna haWa baki wurin tambayar wacece Benazir!! Tsabar ruWanin da suka shiga
Zainab tace benazir ?anwar dr shureim ?ar wurinku itace ta dawo, Yanzu haka tana acikin palour ta yanke jiki ta faWi a sume.

Girgiza kai layla tayi haWi da cewa baki da hankali zainab, dama na fara zargin kin fara shan ?waya, In ba haka ba, ta ya ya benazir da ta gudu da ?afafuwanta zata dawo gida! bazai yiwu ba.

Alhaji ubaid Yace ko dai mafarki ki ka yi ne zainab? Girgiza mashi kai tayi hada hawaye akan fuskarta tace wallahi dagaske nake yi zaku Iya zuwa palourn ku duba benazir ce da kanta ta dawo

Kusan atare suka sauko daga saman gadon, da sauri zainab ta basu hanya suka fuce har suna bange juna tsabar sauri.

Tunkafin su ?arasa falon suka soma hango mutun kwance saman floor da ba?a?en Kaya ga trolley dinta a gefe Waya, kasancewar ta yaye niqab din fuskarta hakan ya basu damar ganin fuskarta, wani irin mahaukacin bugu zuciyarsu tayi A matu?ar gigice suka furta sunanta BENAZIR adai dai lokacin gate security officers din gidan suka shigo falon da sallama sam babu kwanciyar hankali akan fuskokinsu ganin Yanayin mutanan gidan yasa suma suka ?ame suna faman zare ido.

Muryar Hajiya layla Na rawa ta furta wallahi itace Benazir Wina ce, Yarinya tace data 6ata, itace ta dawo da kanta ta ?are maganar jiki na 6ari ta nufi gaban Benazir dake kwance ta zube saman gwiwowinta tare da kai hannu ta ru?o ni?ab din fuskarta ta ?arasa cire mata shi, Kowa dake a falon saida yai matu?ar Al ajabin ganin Benazir, yalwataccen gashin kanta har gadon bayanta Ya nannaWe kamar taliyar indomie, babu alamun wahala atare da ita, sai ma hutun dake kwance saman farar fatarta, wani iko na Allah, gaba Waya Jikinta Ya ji?e da ruwan zufar dake tsastsafo mata, hatta ba?ar jallabiyar jikinta ta manne ma fatarta saboda zufar data wanketa, ga wata zufar dake kurWaWowa ta cikin sumar kanta ta ji?e sharkaf duk da sanyin A.c din falon.

Rushewa da kuka Hajiya layla tayi haWi da Waura Hannayenta biyu saman kanta tana fadin Inna lillahi wa inna ilaihirraji un! Dan Allah kuyi wani abu akai mana kun tsaya kuna kallonta, sai kace baku gane ta ba, Wiyata ce benazir Allah Ya dawo mun da ita da ranta Sautin kukan ta ya cika Wakin, Zainab ma tuni ta fashe da kukan farin ciki, security officers dake tsaye Jikinsu ya yi mugun yin sanyi, da farko sunyi tsammanin ba mutun bace amma daga bisani Bayan ta shigo cikin gidan suka dudduba ?ofar donsu tabbatar mutun ce ba aljana ba, ashe Jamlock Win ?ofar gate dinne basu kulle shi ba sun manta, shiyasa har ta samu damar sanya ?arfi ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login