Showing 237001 words to 240000 words out of 260999 words

Chapter 80 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

haWi da Waga hannayenta sama kamar yadda sukayi
Addu o i unaisah ta soma karantowa suna amsa mata da ameen ameen, bayan ta kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, kafin su zame hannayensu, kunnuwansu suka soma jiyo masu motsin buWe ?ofar dakinsu, A hanzarce suka Wago suna kallonsu.

Big guy ne ya shigo hannun shi ru?e da faffaWan tray Na kayan breakfast dinsu, Daga Bayanshi Ummin america ce, Ta Wauki wankan turkish gown launin brown anyi mata adon stones launin yellow, mayafin da tayi rolling kala Waya ne da stones din rigar, ta sanya high heels a ?afarta, daga sama rigar ta matseta ta bayyana surar kirjinta, daga bayan rigar tudun mazaunanta ya fito sosai.
Tunda batool taji ?amshin turaren ummin america hankalinta ya tashi, tasan dole ta hukuntata akan fitowar da tayi daga Waki batare da saninta ba.
A tsakiyarsu big guy ya Waura tray din kayan abincin kafin Ya soma yin magana.
 Ga auntynku nan Ummi, zata zauna atare daku don ta Webe maku kewa, idan kuna bu?atar wani abu, ita zaku faWa mawa amsa mashi sukayi da toh.

Big guy ya maida dubanshi ga ummi dake atsaye ta ru?e qugu da hannu Waya, Hadaddiyar agogon hannunta sai ?yalli take yi.

 Ummi, ki kula da su, bana so asamu matsala, malamin ne ya bu?aci a tattara sauran yaran wuri Waya sannan aja hankalinsu gudun kada suji sautin abunda zai rikitar da su
Lumshe mashi ido tayi, alamar taji mai yace, shi kanshi daurewa yake yi, domin kuwa wankan da ummi ta Wauka yaja hankalinshi, musamman shu umin ?amshin humran dake fita a jikinta.

Muryarta da kwarkwasa tace okey, baka da damuwa

Bayan fitar big guy daga Wakin.

Ummi ta kalli su unaisah, atare suka haWa baki wurin gaishe da ita.

 Ina kwana aunty ummi yamutsa fuskarta tayi lafiyalou, Ina batool ? Ta jefa masu tambayar tana kallonsu, kafin su bata amsa idanuwanta suka sauka akan yatsun hannun batul, ta 6oye kanta abayan haris, duk don kada ummi ta ganta.

Babu wanda ya fahimci wani abu, sai ita data san meya haWasu.

 Kunyarki take ji Aunty ummi, shiyasa ta la6e acewar Unaisah.
Ta6e baki ummi tayi kafin tace Ina maganin muran da boss man Ya baki ? Ta fada tana nuna unaisah da hannu.
sai lokacin ta tuna da maganin batasan tun yaushe ta jefar dashi ba.

 Kin yada kenan ? Girgiza kai tayi a a, Yana a hannuna tun Wazu, namantane ban kaiga bata ba
Juyawa baya ummi tayi tana kallon tsakar dakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Blister pack din dake ajiye ?asa, cikin takun Isa Ta nufi floor din ta zu?unna ta Wauki maganin ajiyar zuciya unaisah ta sauke ganin ta gano shi
 Ku matsa min anan zan zauna muyi breakfast, ta faWa tana nuna tsakankanin Batool da Haris, da sauri Ya matsa mata, taje ta zauna idonta akan batool data ?an?ame haris, ru?o hannunta ummi tayi tare da rabata daga jikin haris, duk tabi ta ruWe, ta?i yadda su haWa ido.

Bottle water Unaisah ta Wauka ta buWe murfin, ta tsiyaya ruwa acikin cup, ta mi?a ma ummi, kar6a tayi tare da fadin thanks kafin ta curo maganin ?waya biyu ta mi?a ma batul, yatsun hannunta na kerma ta kar6a ta sanya abaki, ta kar6i cup din hannun ummi ta kur6i ruwan ta haWiye maganin, Bayan ta gama ta ajiye cup.

 Bata da lafiya ne ? Sajeed ne ya tambaya, parveen tace Mura take Yi,

 Shiyasa naji muryarta asha?e, sis Allah ya baki lafiya amsa mashi da tayi da ameen, sauran mazan sukayi mata sannu ta amsa masu.
Kafin ummi ta fara serving dinsu, A plates ta zuba ma kowannansu abinci banda batool, Waya bayan Waya ta mi?a masu, suka kar6a suna ci, kallon Batul tayi atare zamu ci ta faWa tana sakar mata shu umin murmushi afakaice batare da su Unaisah sun gani ba.
A plate Waya ta zuba masu farfesun naman kaza, Yaji kayan kamshi ga uban romo.
Da?yar batool take iya shan farfesun, saboda Ummi ta hanata sakat, da zarar ta Wago sai ta haWa ido da ita, ta rasa gane dalilin dayasa ummi take son takura rayuwarta.


Hankalin Unaisah ba akansu yake ba, saboda damuwar data bijiro mata, ta ?osa taji me ke wakana da Danish, Malamin Ya fara Yi mashi aiki ko kuwa.......?


Shin meya faru bayan zuwan Sheikh Imam malik!?

Bayan ?arasowar motarsu akatafaren Gate din shiga gidan Owais Jami in dake driving dinsu yayi parking a agaban entry hall, Ya fito a hanzarce Ya zagaya ya buWe masu murfin motar, A hankali Prime minister hateem ya fito daga Ciki, Kafin Sheikh Imam Ya zuro ?afarshi waje shima Ya fito Yana ?arema ginin gidan kallo, ya yaba da haWuwar daular Owais, har saida ya furta masha Allah.

Kafin su ?arasa falon, Glass door dinsa ta buWe, Chief Owais Ne Ya bayyana gefe da gefenshi, Boss man ne tare da Big guy, da kuma sauran jami an isod da suka hallara domin tarbarsu.
Murmushi prime minister hateem yasakar mashi, tare da nufarshi tunkan ya isa gare shi, Chief owais Ya riga shi zuwa Ya haWa hannayenshi biyu yai hugging din uncle din nasa
Kafin Ya Wago Ya nufi Sheikh Imam Ya rungume shi, fuskar kowannansu Wauke da murmushi.

 Owais fatan na sameka lafiya, tsawon lokaci bamu haWuba, aiki ya 6oye ka, Sheikh imam ne yai mashi maganar
Calmly ya furta Ina lafiya, nayi missing dinka, amma naji dadin ganin ka yau, Ina fata uncle dina bai takura maka ba? Nasan shine Ya matsa maka akan zuwa Nigeria da zolaya ya fada,
Shekh Imam Yace kai dai bari, kamar yadda baiyi bacci ba adaren jiya nima haka ya hanani Yin bacci, babu shiri yasa na fara shirye shiryen zuwa Nigeria hada ?o?arin turamin jirgin da zai Waukoni Da zolaya yai maganar,
Hateem dake sauraronsu, baice komai ba sai dai murmushin dake akan fuskarsa bai washe ba.
Dubanshi chief yai uncle, sannu da zuwa, Mu shiga daga ciki, nabarku atsaye
Atare suka jera zuwa babban falon gidan, saman sofa mai mazaunin mutun uku, prime minister da Sheikh imam suka zauna, Chief Owais Yana daga zaune kan 2 seater, Yayin da Big guy da Boss suke atsaye sun goya hannayensu saman kirjinsu.
Kallonsu chief Yai kafin Ya soma magana Taj wannan uncle dina ne Prime minister Hateem na ?asar Canada, Kai kaWaine bakasan shi ba, wannan kuma Sheikh imam kenan, Aminin kakanmu Obie...

Cire face mask din fuskarshi Yai, Cikin girmamawa ya soma gaishe da hateem ina yi maku barka da zuwa, najima ina jin labarin prime minister awurin Owais sai dai ban ta6a ganinsa ba, ashe da rabon zamu haWu, kuma tunda naga fuskarshi raina ya bani cewar Uncle dinka ne saboda kamanceceniyar dake a tsakaninku

?ayataccen murmushi prime minister yasaki a yayin da yake kallon fuskar taj yace Nagode da karramawarka agare ni, kuma naji dadin haWuwa dakai, Ina fata zamu cigaba da yin zumunci a tsakaninmu
Tajo yace in sha Allah har cikin ranshi mutumin ya kwanta mashi, kuma Yayi mamakin haWuwarshi donshi a hoto yasanshi, kuma yayi mamakin sakar mashi fuska da ya yi a matsayinshi na babban mutun mai ru?e da babban mu?amin shugaban ?asar Canada, koda yake yasha ji awurin mutane cewa baida girman kai ko kaWan, mutunne najama a kowa nashine mai kudi da talaka awurinshi duk Wayane.

Chief Owais Ya Waura dacewa Uncle sunan shi Taj, Mahaifin Yarinyar nan, dana ta6a baka labari, ina fata ka gane shi
Jinjina kai Hateem yai da mamaki akan face dinsa yace masha Allah, ina ita yarinyar take ne? An gano ta ?

?aga mashi kai yai alamar eh.
 Na tayaka murna my son, Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Ina fata Yaya sharafudden Yasan da maganar mahaifinta da kuma ita kanta yarinyar !?

Chief owais Yace Ya sani, na faWa mashi, sai dai basu ta6a haWuwa da daddynta ba, amma na yanke shawarar zan haWasu kwanan nan idan muka shawo kan matsalar yaron nan
Ga dukkan alamu Hateem yaji dadin ganin tajuddeen, duba da yadda yake kallon shi.
Gyaran murya sheikh Imam yai masu Idan kun gama magana ina jiranku, Kun ajiyeni kamar buhun masara, Yakamata ku bari in kammala aikina inyaso kunyi firar taku gaba Waya suka sanya dariya banda Chief daya Wan murmusa.
Prime minister yace ay mana afwa ya sheikh, nayi kewar yarona, Mun jima bamu haWu ba Murmushi sheikh imam yasaki, da zolaya yace wani yaro kake nufi? Wanda yahanaka runtsawa daren jiya? ko kuwa wanda kuke Yin fira da shi a yanzu ?
Prime minister yace dukansu biyun nake kewa
Sheikh imam yace yanzu naji magana, bismillah owais Muje ka nuna min Wakin da yaron yake amsa mashi yai da okey
Atare suka mi?e tsaye tare da nufar Up stairs, tunkafin su ?arasa Wakin, suka soma jiyo kururuwar macijin Yana gurnani.
Sheikh Imam yace Da alama Yasan da zuwana murmushi kowannansu ya saki, abakin ?ofar Wakin suka tsaya kafin su shiga sheikh imam Ya dubi Chief owais naji kace akwai yarinya agidan nan Wiyar mutumin da naji ka kira da taj ko ? Kafin owais ya bashi amsa Boss man ya riga shi cewa ba ita kaWai bace, akwai sauran ?an uwanta dake rayuwa agidan

Sheikh imam yace Toh, ina bu?atar a killace su wuri Waya, sannan aja hankalinsu ta yadda baza su iya jin abun da ke faruwa cikin gidan ba, Idan ba haka ba zasu iya firgita arasa gane kansu boss man ya amsa mashi da toh.
Kafin Ya dubi big guy please kaje wajensu, ka aiwatar da abunda malam yace da sauri big guy ya nufi hanyar komawa down stairs, Ya rage saura su uku.

 Bismillah mu shiga daga ciki dafe ?ofar boss Yai, ta zuge a hankali kafin suka shiga dakin.

Jin motsin shigowarsu dakin Yaja hankalin salsabeel dake atsaye kai idonshi ga dubansu.

Hankalinsu na akan narkeken macijin dake zarya tsakiyar gadon wata irin kururuwa yake fitarwa yana huci.

Gaisawa sukayi da salsabeel, daga bisani, Chief Yai mashi alama da hannu, salsabeel Ya fahimci ?arin bayani yake nema game da halin da Giant snake din yake aciki

 Ni kaina bansan meke damun shi ba, Yanzu ya farka daga bacci, Yana huci, zai Iya yiwuwa saboda rashin ganin ?ar uwarshi akusa dashi ne

Hankalin prime minister hateem ba ?aramin tashi yai ba, sai yanzu yaga girman macijin Ya wuce misali.

Sheikh Imam Yace Saboda ni yake wannan hucin, ku dan bamu wuri zan fara aikina babu musu suka fito daga dakin, anan second floor suka tsaya suna jiran tsammani
Bayan fitarsu ya rage saura sheikh imam da Macijin a Wakin, Toilet Ya shiga jim kaWan ya fito da alama alwala ya Wauro, Bakin gadon Ya tsaya tare dakai hannu Ya dam?i bargon dake a nannaWe kan mattress, manyan Addu o i ya soma karantowa Yana tottofe bargon, kafin ya fara yin karatun al?ur ani, Yayin da idanuwanshi suke akan macijin dake ta ?o?arin saukowa daga saman gadon Hanyar guduwa yake nema sai dai ya kasa yin hakan saboda Waurewar da Sheikh imam Yayi mashi da karatun kur anin da yake yi, Bayan Ya kammala yin ?ira ar, Ya daddage Ya haye kan gadon, Ya kifa mashi bargon saman jikinshi, Ya daddanne shi da ?afafuwanshi, da hannayenshi yabi ko ina ya dafe, wata irin kururuwa macijin yake saki tamkar ana ?ona jikinshi da wuta, hatta waWanda ke a wajen Waki saida suka jiyo sautin, Har saida prime minister ya dafe kunnanshi da tafin hannun shi.
Jami an dake a kewaye da gidan da gudu suka shigo part din hannayensu ru?e da bindigu, sunyi tunanin wani mugun abunne ke faruwa, daga saman bene Boss Man Yai masu magana akan su koma bakin aikinsu hakan yasa suka juya da sauri suka bar part din.

Sheikh Imam Ya hada uban gumi, zufa ta wanke fuskarshi duk da sanyin A.c na Wakin, Ya?i Sakin bargon daya daddanne Macijin, sai ?o?ari yakeyi donya kubcema Waurin da yayi mashi.
Ma?oshin shekh imam tamkar zai 6allo tsabar yadda yake cigaba da karanta mashi ayoyin ?ur ani tare da addu o in karya sihiri, Yaci gaba da tottofe bargon da yake kudundune.
Ba zato ba tsammani, suka soma jiyo wasu irin muryoyi na ba?a?en shaiWanun aljanu suna fadin kashe ka zamuyi sheikh imam! Dole ka mutu tunda ka shiga sabgarmu, zaka mutu
Da karfin hali sheikh imam yace Idan kunga na mutu lokacin mutuwatane yayi don ubanku, Ni da Allah na dogara bada ku ba, Raina a hannunsa yake, Ku bakusa ku cutar dani ba, face da izninsa, Kunsan bana jin tsoronku tun fil azal...... bai ?are maganarba, sautin dariyarsu Ya karaWe Wakin, tamkar ana buga ganga, Hankalinsu boss man ya tashi matu?a, damuwarsu kada wani abu ya samu sheikh imam.
Cigaba da magana sukayi da kakkausar murya suke fadin mutuwa zakayi sheikh Imam, ajalinka ne Yazo, kai ka sani ba a shiga huruminmu a zauna lafiya, mun kashe ire irenka da dama waWanda suka yi ?o?arin yi mana shisshigi, Sheikh Imam kadaina janyo mana ayoyin alkurni bazasu ta6a yin tasiri akanmu ba, Mu ba kalar shaiWanun da ka saba ?onawa bane
Runtse ido sheikh imam yayi, jin numfashinshi na ?o?arin Waukewa tamkar an sha?e mashi wuyanshi, idanuwanshi suka kaWa jawur tamkar garwashin wuta, sautin muryarshi da?yar yake fita ahaka yake kokarin cigaba da yi mashi karatun kur anin..........

 Hankalina bai kwantaba, Inajin fargabar wani abu ya sami malamin nan, Mutanan nan fa ba ?ananun shaidanu bane salsabeel ne yai maganar.
Boss man yace ni kaina fargaba nake ji, gaskiya akwai matsala, kada mu jefa rayuwarshi cikin hatsari,
Duk maganganun da sukeyi akan kunnan Chief owais da prime minister Hateem, jikinsu yai sanyi babu mai magana acikin su.

Lokaci Waya bugun zuciyar Prime minister ya ?aru, arude ya furta ku buWe kofar nan ya fada yana nuna ?ofar dakin danish da sauri Bossman Ya nufi ?ofar ya sanya hannu ya dafe glass din wani iko na Allah ?ofar ta?i buWewa, gashi sunji shiru babu motsin sheikh imam da kuma kururuwar macijin.

 Babu lafiya, salsaleel zoka taimaka min mu buWe ?ofar matsawa salsabeel yayi gaban kofar, suka haWa ?arfi shida boss suka dinga bugun ?ofar ta?i buWewa.

Da ?arfi suke ambaton sunan sheikh imam shiru bai amsa masu ba, babu alamun motsinshi.

Hankali atashe Chief Owais Ya Wago da ido suka kalli juna shida prime minister.

 Bana so wani abu ya sami malamin nan, Ni ne silar kiranshi daga sudan, Idan wani abu ya same shi bazanji dadi ba, zanyi danasani Owais, Yakamata kuyi wani abu akai damuwace ?arara akan fuskar Hateem.

 In sha Allah Uncle babu abunda zai faru da shi, ka kwantar da hankalin ka chief na ?arasa fadar hakan, Ya nufi ?ofar Wakin, da sauri salsabeel Ya matsa mashi hanya, Boss man Yaja gefe Waya, bismilla ya furta da kyakkyawar niya, kafin ya daki ?ofar da kafaWarshi, nan take ?ofar ta zuge da gudun gaske, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, salsabeel yayi mamakin ?arfin owais.
An rasa wazai fara shiga dakin, kowa fargaban ganin abunda zai taras yake yi, hatta shi kanshi chief din....... =?3?=?3?=?3?





*Something Unexpected*


*WAIWAYE

*A Obie International Hospital*


Emergency room


Abun da ya faru daren Jiya da Sir mubarak Ya dauki Dr jazz zuwa asibiti, tunkafin su ?arasa Ya kira Dr fawan awaya ya sanar dashi game da zuwansu, tuni nurses sun fito da stretcher bed din da zasu dauke shi, motarsu nayin parking a harabar ajiye motocin asibitin, Sir mubarak Ya fito jiki na 6ari ya cuccu6i dr jazz ya daura shi kan gadon, A gaggauce nurses suka gungurashi zuwa Emmergency room.


Fitowa Major yai daga front seat na motar, Yabi bayan Sir mubarak dake tafiya yana nufar inda nurses din zasu kai Dr jazz, duk inda ya gifta manyan likitocin dake zarya cikin girmamawa suke gaishe da shi, a bakin ?ofar emmergency room din suka dakata da yin tafiyar, damuwar duniya ta isheshi, ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daWi, ha?ika yaji takaicin bugun da yayi ma jazz bisa rashin sani.

 Yalla6ai, ka zauna Major ne yai mashi maganar yana nuna mashi waiting seat dake jingine da bango
Girgiza kai Sir mubarak yai bazan iya zama ba, Idan har jazz bai farfaWo ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, Major ka tayani da addu a Allah yasa yarona ya farka bana so wani abu ya same shi

Cikin kwantar da murya major yace Sir in sha Allah babu abunda zai same shi, zai ji sau?i, ubangiji Allah ya bashi lafiya

 Ameen ya amsa mashi.
Tunda aka shiga da jazz cikin emmergency room, likitoci suka taru akanshi, yadda kasan zasu hana shi mutuwa idan tazo daukar shi.

After some minutes, Dr fawan Ya fito daga medical room din, sanye cikin shiga ta likitoci, fuskarshi da face mask, tunkan ya ?araso wurin su sir mubarak yai hanzarin nufarshi yana fadin fawan ya farfado? Ko hanyar yanzu ?
Calmly dr fawan yace daddy ka kwantar da hankalinka, har yanzu bamuyi nasarar farfaWo dashi ba, jazz ya bugu sosai, yanzu dai muna ?o?arin ganin munyi mashi treatment din raunukan dake akan goshinsa, In sha Allah nan badajimawa ba zai farfaWo, ina da tabbacin hakan ya ?are maganar yana duban fuskar sir mubarak, babu alamun zai kwantar da hankalinsa, fuskarshi duk ta yamutse.

Dr fawan baiyi mamakin ganin hakan ba, yasan da irin sha?uwar dake atsakaninshi da jazz, dole ya damu.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login