Showing 231001 words to 234000 words out of 260999 words

Chapter 78 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

su.


Gaba Waya ta tattara hankalinta akan Apple laptop din dake agabanta, yayin da take zaune a tsakiyar katafaren gadonta dake acikin hamsha?in Wakin kwananta daya gaji da haWuwa, ko dakin sarauniya Albarka, farace sol kamanninta sak dana Mahaifinta Hateem, yadda kasan ta macen aljanna saboda kyanta da dirinta, kamanninta sun 6aci dana Hateem, tamkar yayi kakinta, Hasken fatarta ne kadai ta dauko na mom mujeedat da doguwar sumar kanta, mace ce mai aji, mai ji da ?asaita da izza, bakowa bace wannan face NAZLI, itace first born dinsu, a ?alla zata kai shekara ashirin da takwas a duniya, tana asanye da lace Camisole daga sama ta Waura silk robe launin hot pink, a tsanake take operating laptop dinta cikin ?warewa, yayin da kyawawan idanuwanta dake a manne da farin glass suke akan screen din laptop nata, daga gefen gadon ?ayataccen round table ne daga saman shi china tea set ne, jefi jefi takan kai hannu ta dauki cup ta kur6i coffee din dake aciki, Nazli agogo sarkin aiki bata gajiya tana da haza?a da ?warewa a 6angaren Iya kasuwanci, Company guda take juyawa na mahaifinsu dake a ?asar Canada, ?amshin turaren jikinta ya buWe ko ina na room dinta, hatta sumar kanta kamshin turaren data turara ma gashinta ne ke fita, kullum ne sai ta turara jikinta da gashin kanta, Nazli badai tsafta ba.

 Assalamu alaikum Muryoyinsu ne suka janyo hankalinta ga duban ?ofar shigowa room dinta dake a kulle, daga inda take tana Iya hangen su ta cikin kofar, saukowa tayi daga saman gadon, sumar kanta ta rufe bayanta tamkar hijabi tayi mata, daura idonta tayi akan cashmere slippers dinta dake ajiye saman lallausan carpet, ta zura su cikin kafarta, kafin ta nufi kofar cikin takun izza, ta sanya hannu biyu ta ruko handle din kofar ta buWe ta.
Fuskokinsu dauke da murmushi suke kallonta, sai dai ita babu alamun murmushi akan fuskarta, haka take bata da fara a, taji dadin ganinsu amma bazaka Iya gane hakan ta yanayinta ba saboda tsabar ji da izzarta,
Cikin harshen turanci tace

 Good morning, Mom and Dad! I m so glad to see you, yau kun riga ni zuwa room dina, yanzu nake ko?arin kammala aikin da nakeyi a laptop....

Ta ?are maganar tare da matsawa ta rungume daddynta, hannu biyu ya daura saman bayanta barka da safiya daughter, Ina fata kin tashi cikin koshin lafiya

Muryarta ?asa ?asa ta amsa mashi da cewa

 I m doing well, Dad. I ve been thinking about you since yesterday. I ve missed you.

Gimbiya mujeedat tace oh shi kaWai ki ka gani shiyasa kika rungume shi ko? Da zolaya tayi maganar.

?agowa Nazli tayi tare da mi?a hannu zata rungume mujeedat, da sauri gimbiya mujeedat taja da baya tana fadin nayi fushi, ba tun yauba na lura kinfi ji da daddynki, shiyasa nima nafi ji da Yazrin daboda tafi nuna damuwa akaina

Marairaice mata fuska Nazli tayi haWi da kama kunnanta agafarce ni sanyin idaniyata, mahaifiyata abun alfaharina
Sakin fuska mujeedat tayi nayi hakuri amma kada ki ?ara yi min hakan, Daga yau ni zaki fara hugging kafin daddynki ta faWa tana kallon Hateem dake kallonsu, fuskarshi dauke da murmushi yace na fahimci kishi kike yi dani akan Nazli, Yarinya tafi son ubanta, da ni da ita ?aunace mai ?arfi, baki ga kamannin fuskarmu ba? Shiyasa take ji dani, ke kuma kije da Yazrin itace take kama dake

Farfari tayi mashi da ido batare datace komai ba, ta rungumo nazli ajikinta tana Wan bubbuga bayanta da hannu tace sannu agogo sarkin aiki, tun da sassafe ko breakfast bakiyi ba kin fara danna laptop, Ina fata na same ki lafiya ?
?agowa tayi da kanta tana fadin Ina lafiya mommy, bana so aiki yai min yawa shiyasa nake ragewa ta fada tana dubansu.

 Naji dadin ganinku, duk da ni yakama naje na sameku, ban samu damar yin hakan ba,

Prime minister yace bakomai daughter, muma munji dadin ganinki, Inaso ki shirya Zanyi ba?o ?an mintuna suka rage su ?araso, daga sudan zaizo, gaisawa zakuyi da shi,
Batare da ta tambaye shi wanene zaizo ba tace in sha Allah daddy, yanzu zan sauko down

Amsa mata yai da toh, kafin ya dubi mujeedat, muje ko ya run?o hannunta suka juyawa zuwa dakin Yazrin,

A lokacin Yazrin tana daga kwance cikin bathtub dake a bathroom dinta, ta ji?e jikinta da ruwan kumfa mai Wumi, ta lumshe idanuwanta yayin da take sha?ar ?amshin bath soft dinta daya karaWe toilet din tamkar an fesa turare, A kalla zata kai shekaru ashirin da biyar, Yazrin ?arshe ce afagen haduwa bata baro komai na mahaifiyarta mujeedat ba, launin fatartane kadai kalar na hateem, haskenta bai kai na mujeedat ba, daga ita har Yazrin babu wanda yafi wani kyau, ta inda suka banbanta Yazrin tafi Nazli sau?in Kai da iya mu amala da mutane, Ita Nazli bata son bare, ?iwuya gareta kamar ?aramar yarinya ga ji da izza, magana ma wuyar furtata take ji.

Sautin ?arar door belt ne ya katse mata jin daWinta, A hanzarce ta Waure jikinta da ruwan dumi, kafin ta fito ta ru?o towel dake sagale jikin hanger ta Waure qugunta da shi,
Shigowa Bedroom din tayi da sauri ta nufi wardrobe dinta, shaf shaf ta zura jallabiya a jikinta, ko tsane jikinta bata samu damar yi ba, sumar kanta duk ta nannaWe saman kafadunta.

BuWe kofar Wakin tayi fuskarta dauke da kayataccen murmushi, dimples dinta biyu sun lotsa

Su kansu da sukayi tozali da ita saida suka saki fara a, Yarinyar akwai shiga rai, da wuya kaga fuskarta adaure, kafin su bude baki suyi mata magana ta ware hannayenta biyu ta hadasu ta rungume tana fadin Mom dad, tunkafin nazo gaishe ku kun riga ni zuwa, kunsa naji nauyin hada ido daku

Ta faWa tare da Wagowa da kanta tana faman kare fuskarta da tafin hannunta
Dariya kowan nan su yasaki, Prime minister yace barka da safiya daughter, fatan mun same ki lafiya ? Jinjina mashi kai tayi lafiyalou daddy, amma ni baku kyauta min ba, maimakon ku bari ni in fara zuwa gaishe daku ta fada tana bubbuga ?afafuwanta da shagwa6a.

 Ladar da nake kwaWayin samu, Kun rigani kwashe ta dariya mujeedat tasaki tana fadin Wato ke har yanzu baki girma da shagwa6a ba

Hateem yace barta tayi abunta, don bata da ?anine shiyasa take yi mana shagwa6a

Nuna kanta tayi da yatsanta saboda nice auta mommy, dagani babu ?ari, kunga kuwa dole nayi shagwa6a ta fada tana ru?e masu qugu,
Ba ?aramin nishaWi take basu ba, Hateem yace baki fada mana ya kika wayi gari ba,

 Na tashi lafiya daddy, tun safe nasha coffe, yanzu haka wanka nakeyi a toilet naji ?arar knocking dinku shiyasa na fito

 Kina nufin baki ?arasa wankan ba ? Acewar mujeeda.
Yazrin tace tun Wazu fa na kammala, kawai inajin daWin kwanciya acikin ruwane

 Okey, Ki koma ciki ki shirya muna jiranku a downstairs, daddynku ne zai yi bako daga kasar sudan, yanaso ku gaisa dashine

Yazrin tace okey mom, bari na shiga ciki in shirya

Ta fada tare da kallon Daddynta, harta buWe baki zatayi mashi magana, sautin ?arar dirar motocin dake shigowa gidan nasu ya katse mata hanzarinta, muryarta tamkar tame yin raWa ta furta bakon ya karaso kenan, bari nayi sauri naje na sanya kayan mutunci ta juya da sauri ta shige cikin dakin
Murmushi kowan nan su yasaki, mujeedat tace yazrin kenan, tana bani nishaWi, sai dai narasa gane halin wa ta dauko atsakanin nida kai
Nuna ta yai da yatsa ke mana, har sai an fadi, ni dai kin san ba haka nake ba, idan kika dubi Wabi un Nazli sak kalar nawane
Hararar zolaya ta yi mashi nazli fa hada izza ta sarauta ke Wawainiya da ita, kai ina kaga sarauta? Nice na gajeta, sai dai ta 6angaren siyasa nan kafi karfi, kuma shi Wan siyasa da fara a aka sanshi, hakan na nufin halinkane yazrin ta dauko bani ba

 Gorin sarauta zaki yi min ? Ya faWa yana kanne mata ido.

Tana dariya tace ni dai bance ba, ai kafi ?arfin ayi maka gori, dani dakai babban gorone magogin ?arfe

Ta fada tare da ru?o hannun shi muje kada su jimu shiru, ina tunanin sune suka ?araso atare suka nufi down stair.

Adai dai lokacin zungureriyar motar da ta Wauko Sheikh imam daga airport, ta karaso bakin entry hall nagidan Prime minister a hankali tayi parking, gaba da bayanta motocin sojoji ne da suka dauko shi domin bashi tsaro, fitowa sukayi daga cikin motocinsu, wani ?ato daga cikinsu ya buWe mashi murfin mota, A hankali sheikh Imam malik Ya zuro kafarsa ta dama dake asanye cikin takalma na alfarma, kafin Ya ?arasa fitowa, masha Allah, magadan annabawa, kallon Waya zakayi mashi ka shaida maluntakarsa, yayi shiga ta alfarma shiga ta larabawan saudi arebiya, farar throbe ce, daga sama ya daura wata shara sharar riga, kanshi yana asanye da kufi ?ar karamar hula ta malamai, an nannaWeta da black turban, Yana da godon gemu, babban mutunne ya manyata don harya fara tsufa gashin gemunshi hada furfura ta manyantaka, duhun fatarsa mai kyau ne, kai daga ganin shi baida wasa irin malaman nan ne masu zafi akan addini, babu tsoro a idanuwanshi, mutunne mai cikar kamala, ya shahara a 6angaren wa anzartawa da yin da awa ta addinin musulunci, yayi gwagwarmaya a kasashe daban daban babu inda bai shiga, kuma yana cin nasara akan da awarsa, shaidanun aljanu kansu tsoronshi suke Ji, Suna jin shakkar zama a inda shekh imam malik yake, mutunne shi mai koyi da sunna ta manzon Allah SAW, Ya ru?e Allah Waya azuciyarshi, kainuwane shi dashen Allah, badai mutun ba sai Allah, ta ko ina jikinshi ?amshin turarensa ne mai dadin sha?a a hanci, hannun shi na dama ru?e da cazbaha.

A hankali Yake bin ko ina da kallo, Yayin da yake sha?ar kamshin iskar data gauraya da ?amshin turarensa.

 Ya mu allim, mu ?arasa shiga ciki, Waya daga cikin Sojojin ne yai mashi magana haWi da nuna mashi kofar shiga babban falon, Waga kafarshi yai atsanake yake yin tafiya, suna gab da zasu shiga falon, Prime minister ya fito tare da gimbiya majeedat, Murmushin dake kan fuskokinsu ne ya ?ara faWaWa, da sauri hateem Ya mika mashi hannu suka gaisa cikin girmamawa Marhaban bika babana, barka da sauka, ya gajiyar tafiya ya fada tare da rungumeshi, bayan sun raba jikinsu daga na juna Sheikh imam yace ai ni babu gajiya atare dani, ni da aka gatantani kamar wani basarake haka aka daukoni a privet jet, hankali akwance naci na koshi na cika tumbina Ya fada yana nuna tumbinshi da cazbahar hannunshi, gaba daya suka sanya dariya gwanin ban sha awa, sheikh imam mutunne mai son barkwanci amma fa sai idan yaso.

Prime minister yace Akara makallah ai kafi karfin basarake awurinmu, ku fa magadan annabawane, kunfi duk wani mai mu?ami a karkashin tafin kafarku Yake

Murmushi Shekh imam Yasaki, Tare da daura idanuwanshi kan fuskar Gimbiya mujeedat, kafin yayi magana tayi saurin gaishe shi cikin harshen larabci.

Da zolaya yace Hateem dama ana ganin fuskar matarka? Ya akai yau baka rufe lu u lu un ka ba ? Koba ita bace matar nan da ake yi mana 6oyanta ba? Kodai ?arce ? Kunyace ta rufe gimbiya mujeedat, Ta sanya hannu Waya ta kare fuskarta
Hatta jami an dake a kewaye da Ya shekh Imam saida suka saki murmushi .

Dariya prime minister yasaki a fakaice ya harari Jami an dake atsaitsaye suna kallonsu, jiki na 6ari suka juya kowa yakama gabanshi, don sun fahimci me yake nufi, wato suna kalle mashi matarshi.

 Ya sheikh Mu ?arasa cikin falon, mun barka atsaye gashi ka kwaso gajiya prime minister ya fada tare da ru?o hannun shi, Suka nufi babban falon Gidan, Gimbiya mujeedat tana abiye da su.

 Hateem Irin wannan daula haka? Anya kuwa kuna tunawa da mutuwa? Ka ajiye lu u lu u agidanka ga kuma kayan alatu ta ko ina, maimakon ku bari sai mun shiga Aljana muji daWi Ya faWa yana Jijjiga cazbahar hannunshi, Dariya suka sanya gaba dayansu, A saman Royal sofa kowan nan su Ya zauna, suna fuskantar juna da sheikh imam, sai faman jinjina kai yake yi yana bin gidan da kallo, duk maganar da sheikh imam zaiyi yanayin amfani da harshen turanci saboda mujeedat yasan bata jin hausa sai dai turanci da larabci.

 Yanzu kai hateem, Har kake iya kwana acikin daular nan? Wannan haWuwa haka ai sai mutun ya manta da tur6aya aka halicce shi
Murmushi suka saki suna dubanshi
Sautin takun takalman Yazrin da Nazli ne Ya janyo hankulansu ga dubansu,
Hannunsu ru?e cikin na juna suke yin tafiya suna tunkarosu, kowaccensu ta yafa mayafi akanta,
Bayan sun ?araso, Cikin girmamawa suka gaishe da shekh Imam, Abunda Ya burgeshi da yaran tarbiyarsu, A saman lallausan carpet din dake a atsakankanin Royal sofa din suka zauna kowaccensu ta nade kafafuwanta
 Masha Allah, Matan hurul aini har a duniya, Hateem, wacce zaka bani acikinsu in cike sunnah ? Ya faWa yana duban faces din Yazrin da Nazli, Yazrin sai famam sakar mashi murmushi take Yi, Nazli kuwa tunda ta gaishe dashi ta sunnar da kanta ?asa.
 Duk wadda ka za6a malam, zamu baka Ita acewar mujeedat,
Shekh imam yace Uwargida maganarnan taki bata kai zuci ba, ni nasan kin faWine kawai, taya zaku ba yarinya auran dattijo? Mai jan cazba, balle ?an matan zamani basu son auran malamai
Murmushi kowannansu yasaki, banda Nazli.
Biyu daga cikin masu aikin gidanne suka nufo falon, hannunsu ru?e da faWaWan farantai daga sama an jera drinks masu sanyi da snacks.
Tunkafin su karaso sheikh imam yace waWannan fa? Badai ni zasu kawo mawa ba? Bayan abincin da naci acikin jirgi har wani ?ari za ayi min? A a gaskiya Ni a koshe nake, Ko ruwa bana jin zai Iya wucewa ta makoshi na
Prime minister yace babana adai daure ko ruwan ne kasha,
GyaWa kai yai toh, naji iya ruwan zansha, Asaman carpet suka daura farantan, mai aikince ta zuba mashi Apple juice mai sanyi a cup ta mi?a mashi, Yasa hannu ya kar6a, Kur6a uku yai ya dawo da dubanshi gasu Nazli ?an matan hateem ina fata na same ku lafiya? Ya karatu? Ko da yake nasan kun kammala, to Ya aiki
Atare suka amsa mashi da cewa lafiyalou Alhamdulillah, jinjina kanshi yai Masha Allah, bayan ya ajiye cup din alamar ya kammala sha, Prime minister hateem Yace nasan yanzu ka kwaso gajiya, ko zamu bari zuwa anjima idan ka huta sai mu fara shiga gida ku gaisa da baba kafin mu wuce can gidan Owais din inda Yaron yake ?
Girgiza kai sheikh imam yai A a, tun da mahaifin naku baisan da zuwana ba, to ba yanzu zanje gaishe shi ba, nafi bu?atar ganin yaron, don agaskiya ni babu gajiya atare dani, ka tashi mu tafi kawai,
Kallon mujeedat Hateem yai zamu tafi, in sha Allah bazamu daWe ba, a taya mu da addu a murmushi tasakar mashi ubangiji Allah yasa ayi asa a, Ina yi maku fatan alkhairi amsa mata yai da ameen, kafin ya maida dubanshi gasu Nazli da Yazrin daughters ku tayamu da addu a, ga mommynku nan zatayi maku bayanin komai dangane da zuwa sheikh imam amsa mashi sukayi datoh, kafin ya Wago Ya kalli Ya sheik wanda tuni Ya mi?e tsaye, mi?ewa hateem yai atare suka nufi kofar fita falon, tunkafin su ?arasa Jami en dake atsaye bakin motar data dauko sheikh daga Airport Yai saurin bude masu motar, Bayan sun shiga daga ciki, jami en Ya zauna a driver s seat Ya tashi motar, atsanake Yake yin driving dinsu........

*Chief Owais
'd'*

Tun bayan daya dawo daga masallaci, Yin sallar asuba bacci ya addabi idanuwanshi, adaddafe ya shiga bathroom yai wanka, within minutes ya fito waist dinshi Waure da white towel, kan mirror chair ya zauna da niyar ya kimtsa kanshi, sai dai yakasa tabuka komai saboda kasalar data kame sassan jikin shi, idan har ba baccin nan yai ba to kuwa bazai ta6a samun sukuni ba, kyawawan idanuwanshi sunyi mashi nauyi da?yar yake iya buWe su, mi?ewa yai bai nufi ko ina ba sai saman katafaren gadonshi, Ya haye ya kwanta tare da jan bargo ya lullu6e rabin jikinsa, In a short time bacci yai awon gaba da shi.

Tsawon awanni yanata sharar baccinsa, tun karfe shida har goma da rabi ta buga, Yayin da numfashinshi ke fita cikin natsuwa da kwanciyar hankali, phone dinsa dake ajiye gaban dressing mirror ta soma yin ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, ringin din ya fara takura mashi, mutsu mutsun farkawa daga bacci ya somayi, A hankali Ya ware fararen idanuwanshi dake fuskantar ceillin din dakin nashi
Tsawon minutes, kafin Ya laluba hannunshi Cikin kasala Ya ru?o wayar ya duba sunan me kiranshi, sunan Uncle Hateem ne Ya bayyana akan screen din wayar,
Kiran harya kusa katsewa yai saurin yin picking, tare da manna wayar akan kunnansa
 My son, Ina fata ban takura maka ba
Yamutsa fuskarshi yadan kafin ya furta Barka da safiya uncle, fatan ka tashi lafiya ?
 Lafiyalou, naji muryarka da alamun bacci bai isheka ba
 Kiran wayarka ne Ya tashi ni daga bacci, Ina fata lafiya
 Banji dadiba amma kayi hakuri da takura makan da nayi, ni kaina bansan dililin dayasa na damu da yaron ba
 Ba damuwa uncle
 Yanzu haka da nakeyi maka magana Muna akan hanyar zuwa Gidan naka tare da sheikh imam
Lumshe ido owais yai har cikin ranshi yaji dadin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login