Showing 135001 words to 138000 words out of 260999 words

Chapter 46 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Sam bai lura da lace din data cire ta jefar saman floor, idanuwanshi na akan gadonta, bargon da ta lullu6e dashi sai kerma yake kamar wadda sanyi ya kama.

daddaWan ?amshin turarensa ne Ya daki hancinta, Nan take ta fahimci Ya shigo Wakin nata.

Gefen gadonta ya zauna Yana dubanta, calmly ya furta Zeenat ina son yin magana dake
Shiru tayi bata tanka mashi ba, tayi tunanin Tani ta fada mashi cewa bacci take yi kamar yadda tace ta gaya mashi.

 Nasan Kina Jina zeenatu, Ki amsa mini, nazo ne don in baki ha?uri, nasan ban kyauta maki ba, Yanzu haka da nike yi maki magana na kammala shiryawa ke nake jira mu tafi

Cikin disasshiyar murya tace yaya shureim bana jin daWin jikina, bazan iya fita ba, sai dai zuwa gobe

 am sorry zeenatu, fushi kike yi da yayan naki? Ba za ki yi mini uziri ba?

 Yaya shureim ni ba fushi nike yi dakai ba, fitarce na fasa, Bana jin daWi

Ya rasa ya zai yi ya shawo kanta don ta amince su fita.

Yanke shawarar Yaye Bargon Jikinta yai don ya samu damar lallashinta dakyau.

Tsautsayine Yakai hannun shi saman bargonta, Ya ru?o shi tare da jan shi, Ras yaji gabanshi ya faWi da sauri Ya maida mata bargon a jikinta, Yana faman jan numfashi da ?arfi da ?arfi, mi?ewa yai da wani irin Yanayi ya nufi ?ofar fita daga Wakin Yayin da la66ansa ke ambaton sunan Allah, Har ya kusa kaiwa ?ofar Wakin Muryar zeenatu ta katse mashi hanzarin shi.

 Yaya shureim kai da kanka ka faWa mini cewa baka ta6a yin soyayya ba, amma meyasa kake kallon hoton wata awayarka

Ta gaza ha?ura har saida ta amayar masa da abunda ke cikinta, shi kuwa Man din duk ya rasa natsuwarshi, tunda Yaja bargonta Yayi arba da undy din jikinta shara shara Hakan ba ?aramin tada mashi hankalin shi yai ba, ga dukkan alamu ita batasan ma ya buWe bargon ba saboda ta ?udundune kanta, idanuwanta suna arufe.

 Zeenatu, abun da na faWa maki da gaske ne, banyi maki ?arya ba, Ni ban ta6a yin soyayya ba A hankali Ya Wan Juyo yana dubanta, a lokacin ta fiddo da kanta daga Cikin bargon, Yalwatacciyar sumar kanta, ta rufe mata gefen fuskarta, Jan bakin data shafa ya dame fuskar saboda kukan da tasha, har saman kumatunta jan bakin ne, duk da kwalliyar fuskarta ta 6aci ba ?aramin kyau tayi mashi ba.

Muryarta da shagwa6a tace ka faWamin wacece ka ke kallo awayarka? Idan ba budurwar ka bace.

?ayataccen murmushine Ya bayyana akan fuskarshi, sai yanzu ya gane dalilin dayasa take haukan nan, wato kishin shi take Yi saboda yana kallon hoton wata wayarshi, aranshi ya ayyana da ace tasan hoton wacece yake kallo da batayi haukan nan ba.

 Zeenatu, dama saboda hoton wayata kike kuka ? ?aga mashi kai tayi alamar eh.
 Okey, Ki kwantar da hankalin ki, ba budurwata ba ce, ma?e mashi kafaWa tayi ni ban yadda ba yaya shureim, idan har dagaske kake yi min ba budurwan ka bace to ka nuna min hoton in gani

Lumshe idonshi ya Wanyi tare da waresu kan fuskarka, duk da tazarar dake a tsakanin su, ba ?aramin Kyau take yi mashi ba musamman yanzu daya fahimci irin zazzafan son da take yi mashi.

Ganin ya tsareta da ido, ba tare daya furta komai ba yasa tace Yaya shureim magana fa nake yi maka, kayi shiru baka ce komai ba, Ni dama nasani baza ka nuna min hoton in gani ba

Yadda take yin maganar tana jujjuya eyes balls dinta ne suka ?ara rikitar da shi.

Gyaran murya ya Wanyi kafin yace Idan har Ki ka amince zaki shirya mu fita, Ni kuma zan nuna maki wacece nake kallo awayata, zum6ura mashi baki tayi toh, amma ka fara yi min al?awari,

 Nayi maki al?awari

 Yanzu zan shirya yaya shureim, ganin tana ?o?arin mi?ewa tsaye yai saurin fuce wa daga Wakin gudun kada Ya ?ara ganin abunda zai hana shi Runtsawa.

Fitowa ya yi daga cikin gidan Ya nufi harabar ajiye motocin su, Wasu dan?ara dan?aran motoci ne na Alhaji musa a killace a ?alla sun haura goma shabiyar, kuma dukansu babu motar ?asa da miliyan talatin, Manya manyan motocine tsadaddun gaske masu numfashi.

Motarshi Ya buWe Ya shige Ciki Ya zauna a driver seat haWi da Waura kanshi jikin headrest, bakomai Yake tunawa ba face maganar da Alhaji musa ya faWa mashi akan Aiki da kuma aure, A yanzu ya fara tunanin ta yadda zai 6ullo mashi da zancen auran zeenatu, yafi bu?atar auren akan komai, saboda yanason ya samu natsuwar cigaba da gudanar da rayuwarshi, zeenatu ta kwanta mashi aranshi Wari bisa Wari, kuma yana da tabbacin zeenatu zata maye mashi gurbin abunda ya rasa.

Almost 15 mins, ?amshin turarenta Ya doki hancinsa, Nan take ya fahimci ?arasowarta, buWe motar Tayi tare da samun wuri ta zauna gefenshi Waura idonshi yayi akan face dinta, babu make up, zallar kyan da Allah yayi matane, ta canza kayan jikinta zuwa turkish gown launin black gray, Ta yafa mayafi akanta, Idanuwanta sun kumbura saboda kukan da tasha.

Kallon Juna suka somayi kamar zasu haWiye kawu nan su, Ko ?yaftawa basa yi, kunyar shi ce ta kama ta, da sauri ta daura kanta saman laps dinta.

 Zamu Iya tafiya da shagwa6a tace a a yaya shureim, nafi so ka fara nuna mini hoton in gani

Zaro wayarshi yai daga cikin aljahu Ya daddanata, Kafin Ya mi?e mata wayar kar6i ki ganta, Kyakkyawa ce tafi ki kyau, ita nike da burin aure

Gabanta na faWuwa ta Wago, tare da sanya yatsun hannunta dake kerma ta kar6i wayar da ya mi?o mata, idanuwanta rufe tabarsu, Gudun kada taga abun da zai hanata kwanciyar hankali.

Dr. Shureim dake kallonta, murmushine Wauke akan fuskarshi

 Meyasa ki ka rufe idonki ? Muryarta na rawa ta furta bana son inga abunda zai hanani bacci

 In sha Allah ba zai hanaki yin bacci ba, sai daima ya sanyaki yin bacci cikin kwanciyar hankali, now Open your eyes slowly and look at the picture,

She took a deep breath and tried to slowly open her eyes kamar yadda ya bata umarnin ta bude su a hankali.....


(KaWan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya>?#? sai dai Allah yakaimu zamu gani, Very soon In sha Allah Zamu shiga Takun ?arshe na labarin kurkukun ?addara)

*Boss Bature
'? Mu haWu Monday In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*_


~Middle step~

3,F 'DB/1d'>?
?d'


_THE PRISONERS E24=?%?=ث?_



*Daga al?alamin Boss Bature*



Confusion of the heart=ث?


lokacin da ta ware idanuwanta akan screen din wayar wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta ganin fuskarta, hotonta ne tun tana ?ar shekara goma sha Waya a duniya, tsabar farin ciki Ya hanata rufe baki, hada hawayenta saboda farin cikin ganin hotonta ne yaya shureim yake kallo, bata kawo komai aranta ba saboda ta yarda da shi.

?agowa tayi idonta acikin nashi ta furta yaya shureim dama hotona kake kallo ? ?aga mata gira yai alamar eh, ta kuma cewa yaya shureim wannan ai tsohon hotona ne a ina ka same shi

Fuskarshi Wauke da murmushi yace nima tsohuwar ajiyace a cikin memory dina, saboda inason hoton bana so na rasa shi, bama shi kaWai ba akwai sauran hotunanki a gallery Win wayar zaki Iya dubawa ki gani

Yatsun hannunta na kerma ta bubbuWe sauran hotunan tana kallonsu hada wanda tun tana jaririya akayi mata shi, abunda ya Waure mata kai gaba daya gallery na wayarsa hoton mutun biyune acikinsa daga hotonta saina ?anwarshi benazir.

 Yaya shureim tun yaushe kake kallon hotuna na ? ta faWa da mamaki akan fuskarta.

Muryarshi ?asa ?asa tamkar tame yin raWa ya furta mata tun lokacin dana fahimci kece ?addarata wurga mashi blue eye balls dinta tayi akan face dinsa.

 ?addararka? Kamar yaya kenan ? Cikin rashin fahimtar kalaman shi ta ambaci hakan.

 Lokaci zai ?ure mana zeenatu, ki bari idan muka dawo gida zan fahimtar dake abunda nake nufi amsa mashi tayi da toh, haWi da mi?a mashi wayarshi Ya sanya hannu ya kar6a, ya turata a aljhu, har cikin ranshi ba ?aramin daWi yaji ba, ganin bata kawo komai aranta ba, Duk da ya 6oye mata ainihin hoton da yake kallo.

 Allah sarki aunty benazir, nayi missing dinta Yaya shureim, tsawon lokaci babu ita, Allah dai yasa aganta da ranta da lafiyarta cikin sanyin murya zeenatu ta yi maganar, ya amsa mata da ameen.

Yana ?o?arin tada motar, ba zato ba tsammani yaji zeenatu ta kwantar da kanta saman kafaWarshi, wata irin kasalace ta soma baibaye shi sakamakon ?amshin turarenta dake kashe mashi jiki.

A hankali motarsu ta mi?i Hanyar babban gate din gidan, Gate security officers Win dake tsaron gidan suna ganin motarshi gaba Waya suka yun?uro suka nufo motarsu, hannunsu ru?e da jibga jibgan bindigu, ba arzi?i dr. shureim Yaci burki, Jin ya dakata da yin driving din yasa zeenatu Wago da kanta daga saman kafadarshi ta dube shi.

 Yaya shureim meyasa ka dakata da yin driving din

 Masu tsaron gidan nan ne suke tunkaro mota ta, ya bata amsa a takaice.

Dafe kai tayi da hannu Waya Namanta ban faWa ma daddy ba, Ni nasan da?yar zasu bari mu fita, idan har bai basu umarnin su ?yale mu ba, gashi baya agidan, Mommy ma har yanzu bata dawo daga office ba ta faWa tana faman zare ido.

 Yaya shureim ka kira daddy awaya ka sanar dashi a tsoroce take yi masa maganar don ita kanta mugun jin shakkar masu tsaron gidan nasu take ji, ?irar jikinsu kaWai abun tsoratarwa ne, sannan basa wasa da aikinsu, gashi babu annurin akan fuskokinsu.

Kafin dr shureim Ya zaro wayarshi tuni sun cimma masu, ?awanya su ka yi mata motarshi.

?aya daga cikin su ne yai knocking glass motar, da kakkausar murya yake ya ce  wanene acikin motar? Muna baka umarnin ka zuge glass din motar ka

zeenatu ce ta sauke glass din, Ya zu?unno Yana dubansu A tsanake miryarta na rawa tace yanzu zai kira daddy awaya, yayana ne shureim zamu fita yawo ne

Security guard Win yace oh, meyasa baki faWa mashi ba a fita dake waje ba tare da iznin daddyn ki ba ?

Still muryarta arude ta furta ai mantawa nayi ban fada mashi ba jinjina kai mutumin yai okey, Muna jiran umarninsa

Kusan Sau uku dr shureim yana jaraba kiran layin Alhaji musa bai Waga ba, zeenatu tace dashi ka jaraba kiran Layin mommy, idan tayi masu magana zasu barmu mu fita kiran Layin Hajiya sarah yayi ringing biyu ta Waga, bayan sun gaisa ya sanar da ita halin da suke aciki, tace dashi yaba ma Security guard din waya suyi magana da shi.

Mi?a masu wayar yai, bayan sun kar6a ya dubi zeenatu, yayi mamakin ganin zufa na wanke fuskarta duk da sanyin A.c na motarshi, ya fahimci tsoron su take ji.

 Ki kwantar da hankalinki zeenatu kina atare dani

cikin sanyin murya ya ambaci hakan, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace yaya shuriem ni bana son tashin hankali, duk laifin daddyne ni banga amfanin ajiye waWannan ?attan ba acikin gidanmu, ai Allah ne ke tsare bawansa bawai mutun ba da shagwa6a ta ?are maganar, ru?o hannunta yai acikin nashi, da sauri ta mayar da kanta saman kafaWarshi tare da lumshe idanuwanta tana faman sauke ajiyar zuciya.

Mi?o mashi wayar Security guard Win yai an baku iznin fita, amma bisa sharaWin zaku koma mazaunin baya na motar, Ni zanyi driving dinku duk inda zaku je zeenatu tamkar zata fashe da kuka tsabar jin takaicin jin abunda Security guard din ya fadi.

Dr shureim yace  ba damuwa mun gode da kulawa, ya faWa yana buWe murfin motar, fitowa su ka yi daga front seat suka koma back seat na motar suka zauna, security guard din ya shiga ciki Ya zauna a driver s seat, Ya tada motar Ya fuce dasu daga cikin gidan lokacin da suka haura saman titi, security guard din ya tambaye su ina zasu je ne, zeenatu ce ta zayyana mashi wuraren sha?atawar da zasu je, kafin dawowarsu gida sai da suka mori lokacinsu, kamar karsu dawo gida.


*EX-PRISONERSd'*

After two days (bayan kwana biyu)

Idan muka koma 6angaren prisoners sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tafiya ta kankama, tun bayan da sojoji suka ?ulla yarjejeniya da ummin america, A ranar wuraren ?arfe shidda na marece, sojojin suka zo kawo masu ziyara domin duba lafiyarsu, a Wakin hutawar dr Laura, suka tattarasu gaba Wayansu, sunyi matu?ar jin daWin ganin Yaran sun samu sau?i musamman Danish da suka barshi Yana ta faman sharar bacci, dama sun ?wallafa rai akan son ganin ya farka, duk da bai sakar masu fuska ba sai da suka ja shi ajiki, kafin tafiyar sojojin sai da dr laura ta nemi izni akan tana so abata dama ta Wauki Yaran zuwa gidanta na tsawon kwana uku, saboda tana so gobe zata kai su saloon agyara masu jikinsu da sumar kansu, sannan tana so zata siya masu suturar da zasu sanya, sojojin basu amince da bu?atarta ba, saboda chief na Isod Ya hana a fita da yaran ko ina, yace kada a kuskura a fitarsu daga asibiti sai Airport idan zasu tafi, Sun bata ha?uri akan ?in amincewa da bu?atarta sun kuma nuna mata illar yin hakan tun da su Yaran suna hasashen cutar da su akayi kuma dole asamu masu bibiyarsu, ba dan taso ba ta ha?ura, sai dai kamar yarda tace zata siya masu suturar sanyawa tayi ?o?arin yin hakan duk da Commender yace kada ta wahalar da kanta, Chief na isod Ya Wauki Wawainiyar yaran duk wani abu da zasu bu?ata a duniyar nan shi zaiyi masu, dr laura tace taji amma dole ta siya masu wani abun da zasu dinga tunawa da ita akai akai, commender yace mata ba damuwa, bayan tafiyar sojojin, tsabar farin Ciki awurin Angel kamar zata zuba ruwa ?asa tasha, dr laura ce ta faWa masu komai dangane da tafiyarsu Nigeria, da kuma dam?a case Winsu a hannun Chief of Isod, daren ranar da aka faWa masu ko bacci bata yi ba, kwana tayi tana yin Nafilfili, har sai da idanuwanta suka kumbura saboda hawayen dake fita acikinsu, ?afafuwanta suka fara yi mata zogin azaba, tukunna ta dakata dayin sallar asaman prayer mat bacci ya Wauke ta.

Tsawon kwana Biyu Kacal, a tsakani Shugaban Isod, Ya shigo birnin San Antonio Texas, Ya kama Yau kenan Monday, Kuma A yau din zasu Bar America, Da zarar ya fito daga meeting din da suka shiga ahead quarter tare da Chief of army staff, da commender da sauran sojojin dake da alhaki akan Tsintar Yaran A daji, tattaunawa ce ta musamman da zata dauki tsawon awa nni suna Yinta.

*UNAISERH ANGEL=؋?*

Mutuniyar tun da ta farka, bakinta awashe kamar wadda akayima Albishir da gidan Aljanna, sai faman zarya take Yi a Wakin ta kasa zama, jefi jefi ta kan wurga eye balls dinta kan wall clock dake a Wakin don ganin lokaci idan yana tafiya, ta ?osa su kammala meeting din azo a Wauke su, don ita a takure take da zama america.

Ta zuba hannayenta biyu acikin aljihun wandonta, bakomai take tunawa ba face Aunty Aneelerh da daddynta, ta sanyawa ranta cewa idan suka koma Nigeria, zata ganshi a gidansu.

Zame hannayenta tayi daga cikin aljihun wandonta, ta goya su saman ?irjinta, abun nayine.

 Masoyiya Angel, muryar dr Laura ce ta fargar da ita ga kallonta, har batasan lokacin da ta furta Sun gama meeting din ? Fuskar dr Laura dauke da murmushi ta ?araso ciki, hannunta ru?e da ?atuwar shopping bag.

A gefen gado ta Waura jakar kayan, tare da mi?a hannu ta rungumo Angel a jikinta.

 Zanyi missing dinki masoyiya Angel, sai dai na lura kamar ke ba za kiyi kewata ba ko ? Ta fada tana raba jikinta daga na Angel.

Du?ar dakai Angel tayi cikin jin kunyarta tace Idan nace bazan yi missing dinki ba, Nayi ?arya, ba ma ke kaWai ba, duka nurses da likitocin da suka taimaka mana wurin samun lafiyarmu, zamuyi kewarku sosai

Shafa gefen fuskarta dr. laura tayi da tafin hannunta.

Cikin karyayyar murya ta furta masoyiya Angel, saura mintuna ?alilan suka rage maku a asibitin nan, ?an uwanki duk sun shirya cikin sabbin Kayan da na Siya masu, Kema ga naki nan ta faWa tana nuna mata jakar kayan data ajiye mata saman mattress.

 Sannan akwai Waya dana siya maki, na yi maki Saving phone number dina tare dana Dr brown dana dr mark, da duk numbers na nurses da suka kula da ku, idan kin sanya layi akan wayar ki kira mu pls Da?yar ta karasa maganar, idanuwanta sun cicciko tab da ?walla, Jikin Angel duk yai sanyi, zuciyarta ta karaya.

Cikin murya tamkar tame Yin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login