Showing 159001 words to 162000 words out of 260999 words

Chapter 54 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

bangaje ?ofar ta shigo ciki.

Mamaki da al jabi sun Hana Alhaji ubaid motsawa Ya kafe fuskar ?ar tashi da ido Yana kallonta, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwanshi ha?i?a ya yi farin ciki mara misaltuwa kusan shekara goma sha shidda Yau rana Waya Allah Ya kaWo masu da hankalinta ta dawo wurinsu, Allah ne kaWai Yasan uwa duniyar data shiga.

Cikin shesshe?ar kuka zainab tace yakamata muyi wani abu akai, Benazir tana bu?atar taimakon gaggawa, ga dukkan alamu wani abunne Ya faru da ita wanda Ya haifar mata da fitar da gumi a jikinta

Da sauri Alhaji Ubaid Ya sanya Hannayenshi biyu, Ya cuccu6eta Ya juya ya nufi sofa mai mazaunin mutun uku Ya kwantar da ita, kallon zainab yai je ki Wauko min wayata a Waki ta amsa mashi da toh, da Wan gudunta ta nufi bedroom dinsu.

Jiki amace layla ta mi?e ta koma saman sofa hand din da benazir ke akwance ta zauna tana duban fuskar ?artata Kamar Ta haWiyeta haka take ji.

 Alhaji kun tabbata benazir Winmu ce ta dawo ! Mai gemu ne Yai mashi Maganar, Jinjina masu kai Yai babu shakka itace Allah ya dawo mana da ita Ajiyar zuciya kowan nan su Ya sauke tsantsar farin ciki Ne Ya kamasu.

 Muna tayaku murna, ita kuma muna yi mata fatan Allah Ya bata lafiya, Ubangiji Allah yasa ?arshen wahalarta kenan, sannan Alhaji Muna baku shawarar a kira malamin da zai dubata don yanayinta dana gani a matsayina na wanda yake da sani a 6angaren sihiri, Yarinyar ka ba likita take bu?ata ba, Malami take bu?ata saboda duk wasu alamomi na jikinta sun nuna kamar sihirine daya daWe a jikinta ya kwance !!! A firgice Alhaji Ubaid Da Hajiya layla suka Wago suna duban mai gemu da yayi maganar, jinjina masu kai yayi ba yau na fara ganin irin hakan ba, ina da tabbacin Yarinyar nan kurciya aka yi mata, amma idan kunaso ku gasgata zance na ku kira babban malamin da zai dubata sam sun kasa magana sai bin shi da kallo da su ke Yi.

Da?yar Hajiya layla Ta iya buWe bakinta la66anta na kerma tace amma benazir da ?afafuwanta ta gudu tabar gidan tajudden Bayan ta haihu tabar mashi jinjira a cikin kwamin wanka, tayaya hakan zai yiwu? Wanene zai yi mana hakan?

Girgiza kai mai gemu yai haka zakuyi tunani saboda bakusan dalilin tafiyarta ba, amma abun duba anan tayaya Uwa zata gudu tabar jinjirin Wan da ta haifa ta hanyar raya sunna!! Duk irin soyayyar dake tsakanin uwa da Wanta? Sannan idan har dagaske benazir ta gudu don son ranta tsawon shekara goma sha Waya meyasa zata dawo da ?afafuwanta ba a cikin Hayyacin ta? Ga zufa duk ta wanke suturar jikinta, Nidai shawarar da zan baku shine a tuntu6i malamin da zai dubata

Jinjina kai Alhaji ubaid ya yi shi kanshi jikin shi ya yi sanyi da zancen Mai gemu, saboda akwai ?amshin gaskiya a kalamanshi.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruke da wayar Alhaji ubaid Ta mi?a mashi, Yasa hannu Ya kar6a.

 Dare Yayi yanzu, kada mu katse ma wani baccin shi, shawarar da zan bada shine a Webo ruwa a yayyafa mata in sha Allah zata farka, zuwa asuba sai a kira malamin da zai dubata mai gemu ne Yayi maganar, muryar Alhaji ubaid a sanyaye yace Inaso zan kira Dr shureim ne, saboda a irin wannan lokacin baya runtsawa Idonshi biyu Yana tashi domin Yin nafilfilin dare ya ambaci hakan tare da Danna wayar hannunshi ya buga ma dr shureim Kira ta soma ringing.

Kallon zainab Hajiya layla tayi idanuwanta sun kaWa jawur tace Wauko mun ruwa a fridge  amsa mata zainab tayi da toh, da sauri ta nufi hanyar kitchen.

Dafe kai Hajiya layla tayi da hannu Waya, Sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, ta manta da yanayin jikinta, don ma babu wanda ke acikin natsuwar shi, hankalinsu na akan Benazir.

Bayan zainab ta dawo, hannunta ru?e da bottle water me sanyi ta buWe murfin ta mi?a ma Hajiya layla, Yayyafa mata tayi saman fuskarta, nan take ta sauke nannauyar ajiyar zuciyata muryarta da tsiwa take fadin ina mahaifiyata Ina mahaifina! Ina mijina da ?ata Ina yayana shureim, suna ina ! Na shiga uku na bani na lalace Na rasa kowa nawa, wayyo Allahna na shiga Uku wallahi gida zan koma Nabar Yarinyata cikin Jini, tajuddeen kai na bama amanar Wiyata nasan bazaka bari rayuwarta ta wula?anta ba. Dan Allah ka bani ?ata ita nake son gani

tunda ta fara sambatun nan zainab da hajiya layla suka fashe da kuka suna kallonta, ta runtse idanuwanta sai faman ciccije le6enta take Yi da ha?oranta tuni suka soma faffashewa, jini Ya soma tsastsafowa, dun?ule hannu tayi tana buge buge, da sauri zainab da hajiya layla suke rurru?eta sosai suna ambaton sunanta

*DR.SHUREIMd'*

Lokacin da Kiran Alhaji Ubaid ya shigo wayarshi, Yana a zaune saman darduma cikin shiga ta larabawa, Yayi nisa acikin karatun qur nin dayake yi Kiran Ya daki dodon kunnanshi, Hakanan yaji gabanshi Na faduwa, aranshi ya ayyana kowa ne ne ke kiranshi a tsakar daren na! ya salam, Sai da yakai ?arshen Aya tukunna Ya zabura Ya mi?e Ya nufi wayar dake ajiye saman side drawer ya Wauke ta yana duban Screen din, Hankalin shi ba ?aramin tashi yai ba ganin sunan Abie dinsa Ya bayyana, kafin Ya Waga kiran saida Ya fara kallon agogon bango ?arfe Waya da rabi na dare, picking call Win ya yi muryarshi na rawa ya furta Assalamu alaikum Daddy!!! muryar Alhaji ubaid Babu natsuwa Ya furta mashi shureim ?ar uwarka ta dawo gida daren nan cikin mawuyacin hali ! Da alamun ruWu akan fuskar dr shureim Yace bangane wa kake nufi ba daddy muryar shi da sauti mai ?arfi Yace BENAZIR!! nake nufi ta dawo gida cikin daren Nan, Gatanan kwance tana buge buge zufa duk ta wanke jikinta, mun rasa ya zamuyi da ita

Zafafan Hawaye ne suka wanke fuskar dr. shureim, tsabar farin ciki baisan sa adda Ya zube saman gwiwowinsa Yayi sujjada, sosai ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, Alhaji Ubaid Yana jiyo sautin kukan dr shureim Kamar ?aramin Yaro.

 Shureim ba kuka yakamata kayi ba, dan Allah ka natsu muyi magana, hankalin mu ba a kwance Yake ba, ?ar uwarka bata acikin Hayyacinta, Mai gemu ya tabbatar min da cewa Kurciya ne akayi mata, saboda alamomin dake a jikinta na fitar sihirine

Jin wannan maganar ta Mahaifin nasa ne yasa shi saurin Wagowa daga sujjadar, arab turban dinsa tuni ya warware Yabar saman kanshi.

Manna wayar yai saman kunnanshi da alamun kiWima ya furta Sihiri kuma!!
Alhaji ubaid Yace to haka dai mai gemu Ya faWa mana, baka ga yadda jikinta ke fitar da gumi ba kamar wadda aka tsamo daga kogon ruwa, bari na kanga maka wayar kaji haukan da take Yi mana on the other hand Alhaji Ubaid Ya matsa gaban benazir Ya saita wayar abakinta.

Muryarya ce ta ratsa kunnuwan dr shureim Ni ku sake ni, Ku ?yaleni ku daina ru?e mun hannuna, wurin Mijina zanje nabar mashi ?ata a gida ita nake son gani, wallahi ku rabu dani dole in tafi Jikin ta?aura yai la asar, a sukwane Dr shureim ya mi?e tsaye da waya kare a kunnanshi.

Muryarshi na rawa Ya furta daddy najima ina zargin hakan, innalillahi wa inna ilaihirraji un, wallahi da ina da halin da zan Iya zuwa Jos acikin daren nan da babu abun da zai hana inzo don in cece rayuwar ?ar uwata, amma duk da haka daga nan Win ma zan Iya taimakawa, Daddy Idan Aunty zainab tana akusa ka mi?a mata wayar!

Jikin Alhaji ubaid na 6ari ya mi?a ma zainab Wayar yace ta kar6a dr shureim ne ke son Yin magana da ita, da sauri ta sanya hannu ta kar6i wayar tana fadin dr shureim kaga wani ikon Allah ko? Tsawon shekara goma sha shidda Yau benazir ta dawo gida, wlh tsabar farin ciki bansan inda zan tsoma kaina ba, sai dai na damu da yanayin da take aciki

Numfasawa dr shureim Yai tare da cewa a tsanake Aunty zainab, yanzu bani da natsuwa, zuwa gobe da sassafe zan shigo Jos din, amma kafin nan ki duba Wakina a cikin drawer chest na bedside drawer gida na uku, akwai robobin ruwan zam zam da wani malamin mu na ?asar egyp ya bamu su don mu dinga yin amfani da su muna taimakon mutanan da suke fama da matsalar sihiri, ki Wauki Waya Kije ki buWe bakin benazir Ki matsa mata shi ki tabbar ta shanye shi duka in sha Allah, sauran sihirin dake ajikinta zai barta ne kafin goben mu ?araso amsa mashi tayi da toh, yace ta mi?a ma mahaifiyarshi wayar da sauri ta mi?a mata, yatsun hannun layla na kerma ta kar6i wayar.

Cikin shesshe?ar kuka tace shureim benazir Winmu ta dawo gida, sai dai kamar bata acikin hayyacinta, duk ta faffasa la66anta da ha?oranta.

Cikin kwantar da murya dr shureim Yace Ki sanya handsfree Inason daddy yaji maganar da zanyi da sauri layla ta mayar da wayar handsfree, zainab tuni ta shige Wakin dr shureim neman ruwan zam zam.

 Mommy daddy, dan Allah ku kwantar da hankalinku, wallahi Allah ne ya taimaki rayuwar baiwar Allah nan Ya Karya sihirin dake a jikinta, kuma ya dawo mana da ita da ranta, wani mugun aka samu mara imani mai zuciya irin ta kafuran farko Yai silar rabata da danginta tsawon shekara goma sha shidda, wallahi tun lokacin dana ji yanayin da benazir ta gudu tabar gida raina ya bani cewar wani abunne Ya faru da ita, ha?i?a munyi sakaci wurin kula da ita, gaba Waya mun Waura mata lafin guduwarta babu wanda ya ta6a yi mata kyakkyawan zato akan meyasa ta gudu tabar jinjira acikin kwamin wanka, Kuma bata nemi kowa ba ta kama hanya tayi tafiyarta, anyi amfani da halayanta na rashin jin magana da rashin Kunya da take dashi anyi mata abun da yasa tabar mu saboda ansan kowa zai yi tsammanin ita ta gudu dakanta tunda dama bata jin magana, da ya ke Allah ba azzulumin bawansa bane sai gashi ya dawo mana da ita a lokacin da bamuyi tsammanin ganin ta ba gaba Waya sun natsu suna sauraron muryar dr.shureim, hatta security officers din gidan duk suna sauraron shi ga dukkan alamu suna gamsuwa da bayananshi duba da yadda suke gyaWa kawunansu.

 Banaso wani daga cikinku Ya tambayeta meyasa ta tafi, ko kuce zakuyi mata faWa dan Allah kada kuyi mata hakan, Kuma kada ku faWa mata abun da ya faru da mijinta da ?arta, naji tana ambaton sunansu, ku sanar da ita cewa suna nan kuma zaku haWata da su idan ta kwantar da hankalinta, idan ba haka ba zata Iya zaucewa idan taji cewa babu su

Kamar malami da Walibansa haka shureim keyi masu magana suna amsa mashi da toh.

 Zuwa da safe kafin mu ?araso, a kira likitan gidanmu Ya duba lafiyarta, suka amsa mashi da toh.

 Mommy idan zainab ta bata ruwan zam zam din, in dai bacci bai Wauke ta ba, ki taimaka mata tayi wanka taci abinci, idan kuma tayi bacci ku ?yale ta kada ku takura mata layla ta amsa mashi da toh.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ru?e da robar zam zam ta ?ara so gaban sofa din da benazir ke akwance tana sambatu, muryarta harta disashe fuskarta ta kumbura suntum.

Zu?unnawa tayi agaban sofa din, ta cizge murfin robar, da sauri Alhaji ubaid ya rurru?e mata hannuwan Benazir, da?yar ta Iya buWe bakinta ta kafa mata ruwan zam zam din ya dinga shiga cikin ?aramin bakinta, gaba Waya ta shanye ruwan, ko mintuna biyar ba ayi ba da bata ruwan bacci mai nauyi ya Wauketa, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zufar jikinta tuni ta soma daskarewa, addu o i zainab ta dinga karantowa cikin harshen larabci tana tottofa mata saman fuskarta da jikinta, hakan ba ?aramin daWi yayi ma iyayenta ba, tuni layla tayi sallama da dr shureim ta mi?a ma Alhaji ubaid wayarshi ya sanya hannu Ya kar6a ya tura a aljihun jallabiyarshi, security office din dake atsaye bakin ?ofar falon suka yi masu sallama da niyar gobe da safe zasu dawo duba jikin benazir, Alhaji ubaid yai masu godiya kafin suka fice daga falon.

Hajiya layla ta dubi zainab kije ki kwanta mun gode sosai, dan Allah gobe da a suba ki shirya mata lafiyayyan breakfast din da zata ci amsa mata tayi da toh, ta mike ta nufi room dinta, ya rage saura Alhaji ubaid da Hajiya layla a falon, kallon juna sukayi lamarin Ya girgiza su, abun daya Waure masu kai wanene yayi masu wannan muguwar aika aikar!!!
Atare suka Waura idanuwansu kan benazir tsantsar sonta da ?aunarta ne Ya kamasu, Har cikin zuciyarsu basu ji daWin ?addarar data afka mata ba, tayi matu?ar basu tausayi ganin irin mayuwacin halin da take aciki, fatansu Allah Ya toni asirin ba?in azzulim daya yi silar barinta gida!!! yadda suka ga Rana haka suka ga dare, babu wanda Ya runtsa acikin zukatan nan guda huWu, Hajiya layla da Alhaji ubaid, Dr shureim da Zainab, akan kunnuwansu aka fara kiran sallar asubahi!!!!


Dr.shureim Tun bayan daya dawo daga sallar asuba Yake ta faman shirye shiryen tafiya jos, tuni Yayi wanka ya kimtsa cikin shigar shi ta larabawa Yabi ko ina na jikin shi Ya feshe da turare, Hannun shi Waya ruke da wayar shi Wayan hannun Yana ru?e da car key dinsa, takalmasa Ya zura a ?afa Jiki Na rawa ya nufi ?ofar fita daga Wakin bayan ya fito bai nifo ko ina ba sai part din Alhaji musa don Ya sanar mashi da zancen bayyanar benazir da kuma tafiyar da zaiyi zuwa jos, abakin ?ofar Wakin ya dai daita natsuwarshi, ya Waga murya yayi mashi Sallama, kusan sau uku kafin muryar Alhaji musa ta amsa mashi
 Wa alaikum salam shureim shigo ciki mana ajiyar zuciya ya sauke, tare da sanya hannu Ya ture ?ofar ta buWe, baiyi tsammanin zai ganshi tare da wani ba, ashe bashi kaWai bane, su biyune shi da Hajiya Sarah suna zaune saman Sofa Win Wakinshi, An jera masu kayan breakfast a saman sofa table din gabansu, mutumin babu annuri akan fuskarshi, Jallabiyace a jikin shi hajiyar tashi kuwa ta ca6a uban adon lace a jikinta, ta kashe Waurin kallabinta, wutsiyar gashin kanta ya sauka har saman wuyanta
Fuskarta da fara a take kallon shureim barka da safiya My son, fatan ka wayi gari lafiya shureim na murmushi yace yawwa mommy, ina kwananku ta amsa mashi da Lafiya lou, tare da nuna mashi wuri saman armchair ta Wakin tace bismillah ka zauna mana tun da ya shigo Alhaji musa bai Wago Ya kalli fuskarshi ba, Hankalin shi na akan abincin da Yake ci, plate ne agabanshi sha?e da farfesun nama Yaji ?ayan hadi sai ?amshi Yake Yi, a tsanake Yake cin abun shi.
Kasa zama shureim yayi idanuwanshi akan fuskar Alhaji musa Yace uncle barka da safiya kamar bazai amsa mashi ba ya furta lafiya da ido Hajiya sarah tayi alamar yayi ha?uri da halin uncle din nashi, murmushi shureim ya sakar mata yaWan jinjina mata kai
 Ko zaka Bari idan Ya gama cin abinci sai ku yi magana, don bai cika son yana cin abinci ana yi mashi magana ba hajiya sarah ce ta fada,
Kafin dr shureim ya bata amsa muryar Alhaji musa ta katse mashi hanzarinshi Shureim ina jin ka, faWi abunda ya kawo ka
Ba ?aramin daWi Yaji ba, da fara arshi ya fara magana uncle bansani ba, ko daddy ya kira ka awaya ya sanar dakai abun farin cikin daya faru a daren Jiya sai da ya ambacin hakan tukunna alhaji musa Ya Wago da ido yana dubanshi alamar yana son jin ?arashen zancen
 ?ar uwata Benazir ta dawo gida a daren Jiya ?arfe goma sha biyu na dare!!!
Tsantsar mamaki da al ajabi ne Ya bayyana akan fuskar alhaji musa, sai dai babu alamun zai furta magana sai faman jinjina kanshi yake yi.
Hajiya sarah kuwa Tsabar farin ciki mikewa tayi tsaye tare da Waga hannyenta sama tana ambaton ALHAMDULILLAH!! wayyo Allah shureim Allah Yasa ba wasa kake Yi min, dagaske Benazir ta dawo gida da ?afafuwanta ko kawota akayi ?
Shureim na murmushi yace da kanta ta dawo gida, kuma abun mamaki tana ta sambatu tana ambaton sunan daddy da mommy da mijinta da ?arta, kuma muna hasashen kurciya ne akayi mata da har ta gudu tsawon shekaru bata dawo gida ba, shiyasa nake so inje jos din Yanzu.......
Hawayene suka wanke fuskar Hajiya sarah, Muryarta na rawa ta furta shureim nima zan bika muje jos din, nasan shima uncle din naka zai je sai mu tafi atare... kafin ta ?are maganar Alhaji musa ya dakatar da ita ta hanyar cewa Ya isa haka? Kinsan bana son shouting shiru suka yi gaba Wayansu, duk suka sha jinin jikinsu.
Kallon shureim yayi ina zaka je da safen nan, naga ka shirya ga key din mota a hannu ?
Cikin sanyin murya yace jos zan tafi, Inason ganin benazir

Ta6e baki Alhaji musa yayi, tsawon mintuna Wakin yai tsita, saida ya mula yasha iska tukunna yace zanyi waya da yaya ubaid din, basai kaje jos din ba, zansa su zo nan abuja... har saida gaban shureim Ya faWi jin abinda Yace, bashi ba hatta Hajiya sarah arude take duban fuskarshi, kallon mara hankali take binshi da shi don wanna Yafi ?arfin a kira shi da izzah, Tayaya zai nuna ?arfin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login