Showing 138001 words to 141000 words out of 260999 words

Chapter 47 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

raWa, dr laura taci gaba da cewa Abu Waya da ban faWa maku ba, dama na yanke shawarar Sai mun ke6e dake in sanar da ke, saboda Na yaba da hankalin ki da kuma kaifin basirarki da wayon ki, Angel ta natsu tana sauraronta.

 Matar da sojoji suka dam?a amanarku a hannunta, Mistress ce, kai tsaye sunan Ya daki dodon kunnan Angel, cikin rashin fahimtar ma anar hakan ta maimaita kalmar mistress.

Jinjina kai Dr Laura Tayi tantiriyar ?ar bariki ce mai zaman kanta, shaidaniyace a fagen iya karuwanci, ta shahara sosai, babu wanda baisanta ba, tayi ?aurin suna a America, maca ce mai haWarin gaske, Namiji baya Iya ganinta Ya kawar da idonshi, saboda kyawun surar dake gareta, Nayi ?o?arin Fahimtar da sojojin Akan illar dam?a amanarku a hannunta amma sun?i su amince min Angel, ni nasan da wuya ta Iya baku kulawar daya ce, in ma bata gur6ata maku rayuwarku ba, Musamman ?an uwanki maza........ Hankalin Angel Ba ?aramin tashi yai ba, duk da Sanyin A.c na Wakin zufa ce ke tsastsafo mata saman goshinta, idanuwanta azazzare take kallon fuskar dr Laura dake kora mata jawabi.

 Ni damuwata depression din dake damunku, da kuma Wan uwanku mai fama da ciwon zuciya, idan har aka cigaba da ?untata maku zaku Iya rasa rayukanku, shiyasa banso suka dam?a amanarku a hannun karuwa ba, donni a sanina da matar masifaffiyace tana da girman kai, bata ta6a yin aure ba, kuma bata san ciwon haihuwa ba, abunda ta sani shine ?wacewa matan aure mazajensu tayi fasi?anci da su, matar ta zama tamkar annoba, ta raba aure da dama saboda hatsabibancinta dakatawa tayi da yin jawabin idonta akan Angel, tsantsar tashin hankali take gani acikin ?wayar idonta, Jikin Ta ?aura Yai la asar, An gudu ba a tsira ba.

Muryarta Na rawa ta furta Aunty, amma meyasa suka dam?a amanar mu a hannunta? Babu wata ne sai ita? Kuma ai mu bamu bu?atar wadda zata kula damu, idan ma akwai abunda zamu bu?ata bai wuce jami an da su bamu tsaro ba.... bata ?arasa maganar ba dr laura ta katse ta da cewa dalilin dayasa suka dam?a amanarku a hannun ummin america, kamar yarda major ya sanar dani, matar tamkar ma aikaciyarsu take, ta saba yi masu aiki wurin jan hankalin tantiran ?an ta addan da suka gagara a ?asa, suna yin amfani da ummi wurin Wana masu tarkon da zasu kamasu, kuma suna cin nasara, Masoyiya Angel ban faWa maki hakan donna tada maki hankali ba face don ki dage damtse wurin Yin ya?i da ita akan ?an uwanki, kada ki kuskura ki bari ta ke6e da Waya daga cikin Samarin dake a jikinku, Idan ba haka ba za a Iya samun matsala, saboda bata da linzami matar, duk da A yanzu ina kyautata mata zo, tun da har sojojin suka aminta da ita suka dam?a mata amanar ku, hakan na nufin sun san zata Iya ne, Bayan haka sun ?ulla yarjejeniya da ita akan baku kula ta musamman da kuma gujewa duk wani abu da zai 6ata maku rai, kamar yarda na gani dai dai da tsawa tayi maku babban laifine, don haka Zan tura maki sharuddan da sojojin suka gindaya mata akanku ta whatsapp, saboda inaso kiyi amfani da su wurin ja mata kunne idan ta sa6a maku, jinjina kai Angel tayi alamar toh ta ?ara da cewa  bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya, Allah ne kaWai zai Iya biyanki, saboda kyautatawar da kukayi mana, gashi kun Wauke mu tamkar ?a?an ku, 

Shafa sumar kanta dr Laura tayi Kada ki damu yana daga cikin aikin mu!, Yanzu ki shiga kiyi wanka, Mintuna ?alilan suka rage maku, amsa mata tayi da toh, Bayan fitar dr Laura, Angel ta nufi Jakar Kayan, zuciyarta a hautsine ta girgiza da jin wacece matar da aka dam?a ma amanarsu, ita babban abunda ta ke jima fargaba garkuwarsu, tunawa da lokacin da aka kawo masu unaiza a kurkuku, yarinyar ta ruWe shi da big boobs dinta, balle kuma matar da taji ance tana tafiya da imanin namiji saboda dirin jikinta, tashin hankalin da ba a sanya mashi date. (>?#?)

Har ta fara Imagining abun da zai faru, a gidan da zasu zaune atare da ita, tayi tunanin sun samu sau?ine komawarsu Nigeria ashe akwai sauran rina akaba.

A hankali ta ruko hannun jakar Kayan, ta zaro kayan dake acikinta, wata haWaWWiyar A-line gown ce launin red colour mai round neck ?ar ubansu awurin haWuwa, Rigar tayi mata kyau a ido, sai faman jujjuyata take yi, aranta tana ayyana yau wata rana zata sanya kaya na mutunci wanda ba uniform din prison ba, wannan abun farin ciki ne agare ta.

Bayan ta gama kallon rigar, ta Waurata saman mattress, ta zaro kwalin takalman dake a cikin jakar tare da kwalin sabuwar wayar da dr laura ta siya mata, ?irar iphone 15 pro, Takalman kuma Ankle strap ne masu tsini launin black, hada face mask da mayafi aka basu wanda bakowa bane Ya tsara hakan face chief na Isod, Lokacin da dr laura ta bukaci zata siya masu kaya Sai da aka nemi izininshi, yace ya amince bisa sharaWin idan zasu sanya kayan a haWa masu da Ni?ab ko face mask da zasu rufe fuskokinsu, a ?alla ta shafe tsawon mintuna biyar tana kallon kayan, bakomai yafi burgeta ba face wayar da aka bata kyauta, tunawa da lokaci yasa tayi saurin nufar toilet ta shige ciki, shaf shaf tayi wanka kafin fitowarta, Nurse jessica ta shigo Wakin hannunta ru?e da gift kit ?aramin akwati na kayan shafa, ta Waura shi gefen gadon Angel, ta zauna saman kujera tana Jiran fiowarta, bayan ta fito daga wankan, suka gaisa da nurse din cikin girmamawa, daga bisani tayi mata bayani game da care kit din data kawo mata donta gyara jikinta, godiya Angel tayi mata bayan ta Wauki kayan shafar da rigar ta juya ta nufi toilet dasu saboda jin kunyar kada aganta tana sanya kaya, murmushi nurse jessica tayi yayin da take binta da kallo.

Bayan ta shafe ko ina na jikinta da body oil mai tsadar gaske, skin dinta har glowing take yi, rigar tayi bala en yi mata kyau, duk da bata da jiki tana da tsawo, white in red abun ba a magana, lokacin da ta fito daga cikin toilet Win, ita kanta nurse din sai santin kyan Angel take Yi, daga saman rigar ta tsuke daga ?asanta bazace daga ta jujjuya rigar take bubbuWewa kamar ana hura mata iska, bayan ta kammala shiryawa nurse ta feshe mata jikinta da turaren desired destiny, fragrance din turaren mai daWin sha?a a hanci.

Face mask din da ta sanya black colour ne launin takalmanta, har saman karan hancinta mask din ya haura, Gray eyes dinta ne kaWai suka Bayyana.

?aura Mayafin rigar tayi asaman kanta tayi rolling dinsa, gyalen yana da tsayi ba laifi, Har saman gwiwar hannayenta yakai mata, shima launin takalmanta ne.

 Kin yi kyau masoyiya Angel, sai ki ka yi mini kama da Cinderella saboda rashin ?ibarki, ?ayataccen murmushine kwance saman fuskarta,

 Na lura kin ?osa ki bar ?asar nan, Ni kuma gashi bana son ki tafi, saboda na saba da ke masoyiya Angel, cikin sanyin murya Nurse jessy tayi maganar tana duban fuskarta.

 Dr. laura ta bani kyautar waya, kuma ta faWa min akwai phone numbers din ku aciki, zan dinga kiranku akai akai muna gaisawa saboda ni kaina bana son mu rabu don ya zamar mana dole ne mu tafi Sai da tayi maganar Nurse jessica ta wurga eye balls dinta kan kwalin wayar, zaro ido ta Wanyi haWi da cewa wow, gaskiya dr. Laura tana Ji da ke shalelenta, wannan waya haka mai kyau da tsada, Ina taya ki murna masoyiya Angel, Kuma naji dadi da ta baki wayar, Kinga zamu dinga kiran juna muna gaisawa, harma muyi video call fuskarta dauke da matsanancin farin ciki, ta nufi gefen gadon ta Wauki kwalin wayar a hannunta, tana ?are mashi kallo, Angel dai sai murmushi take saki, bakinta ya?i rufuwa kamar ta fasa ihu Haka take ji tsabar murnar yau zasu Bar america zuwa ?asarta ta gado.

 Yakamata mu tafi masoyiya Angel, ?an uwanki suna Jiranki a waje cike da ?agara Angel ta amsa mata da toh, shaf shaf ta zura takalman a ?afarta masha Allah, wankan Angel yabi jiki.

A hannu ta ru?e wayar bayan ta curo ta daga kwalin, atare suka fito daga Wakin.

Tun kafin ta Wago da idonta, Muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta Genie gamu nan ki dube mu da kyau, mun yi kyau Da sauri ta wurga idonta kansu, masha Allah har saida gabanta Ya faWi tsabar kiWima da ganin Kyawun da suka Yi acikin sabbin kayansu, jemimah da azeeza launin gown dinsu Royal blue ne, hannah da parveen launin punch pink, Ita kuma Batul launi Wayane dana Angel, red colour, kowaccensu akwai Face mask a fuskarta, Anyi masu rolling Veil a saman kawunansu, takalman kafarsu flat ne ba kalar nata ba, Waya bayan Waya take binsu da kallon mamakin Kyawun da suka Yi, mutun Waya ne ke babu a cikinsu, Mazan su huWune, kowannansu ya kimtsa cikin shiga ta mutunci ta kece raini wato shigar hadaddun Slim fit suit, sun manna mask a fuskokinsu, kwantacciyar sumar kawunansu ta kwanta luf, ?afafuwansu na sanye cikin tsadaddun takalman fata, ta ko ina ?amshin turarensu ne ya karaWe ward din da suke.

Ganin tayi tsaye tana kallonsu bata motsa ba, yasa kowan nan su sanya hannu a lokaci Waya suka Zame mask din dake a saman fuskokin su, sai faman washe mata baki suke yi, wani irin farin ciki ne Mara misaltuwa ya kamata, tun daga kan yadda suke sha?ar iskar ?an ci zaka tabbatar da kwanciyar hankali da natsuwa atattare da su, su kansu sun yaba da kyawunsu, sai faman shafa kayan jikinsu suke Kamar zasu lashesu.

Jemimah ce ta ru?o hannun Azeeza suka watso da gudu zuwa gabanta, Atare suka fada saman jikinta, Hugging dinta su ka yi suna ti?ar dariyar murna, tuni idanuwanta suka cicciko tab da ?walla, ko a mafarki bata ta6a tsammanin zata ga wannan ranar ba, yau gata ga ?an uwanta cikin shiga ta alfarma ba uniform din kurkuku ?addara ba.

A hankali Batul da sauran ?an uwan nasu suka nufo wurin Angel, Waya bayan daya take rungumo su saman chest dinta, suna matu?ar ?aunar junansu, nurses da likitocin dake tsaitsaye cirko curko sai kallonsu suke yi gwanin ban sha awa.

 Angel, Kinga yadda ki kayi kyau? Rigar nan tayi maki kyau, wlh duk munyi kyau, Batul ce tayi maganar tana shafa gaban rigarta da hannunta.

 Nayi tunanin abinci kaWaine abu mafi kyau a duniyar nan, ashe sutura ma abu ne mai ?ayatarwa, gaskiya bazan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, DaWi Nake ji kamar In buga tsalle sama in dira ?asa, Parveen ce tayi maganar, sautin dariyarsu yacika ko ina, kasancewar suna Yin firar cikin harshen hausa babu wanda ya fahimci abunda suke tattaunawa a tsakaninsu, sai dai Abi la66ansu da kallo.

 Ban ta6a ganin kalar kayan nan ba, Mun saba da Uniform kala daya na prison, Yau sai gashi mun tsinci kanmu acikin sutura mai kyan gaske, godiya ta tabbata ga Allah, domin kuwa shine silar komai, dama kin ta6a fada mana cewa maha?urci mawadaci, sannan duk tsanani Yana tare da sau?i, kuma babu yanayi na rayuwa da yake kasancewa Na dundundun, Yau mun shaida hakan Angel tun da Haris Ya fara magana Suka natsu suna kallonshi, tamkar ba mara lafiyan nan ba, Jikinshi Yayi kyau Wan black beauty da shi, Kalamanshi sun tunama Angel deeja, Yarinyar akwai tawakkali duk da bata da zurfin ilmin addinin musulci tayi imani da Allah, fiye da wani musulmin daya taso acikin musulunci, tunawa da deeja ne yasa ?wallar idonta suka soma gangarowa saman kuncinta, a fakaice ta sanya hannu ta share su, ha?i?a taji zafin mutuwarsu, ga salsabeel daya tsaya mata aranta, bawan Allah ko awani hali yake ayanzu? Ya rayu ko ya mutu? Allah masani!.

 Angel, Ina fata Yanzu hankalinki ya kwanta, babu sauran damuwa tun da yau zamu koma Nigeria Gabriel ne yai mata maganar HaWi da Waga mata gira Waya, hakan ba ?aramin dariya yaso ya bata ba, Javed yace ni fa duk atakure nake jin kaina, mutanan nan sai kallon mu suke Yi,

Naufal Yace ka gode ma Allah tun da ba Giants din kurkukun ?addara bane suke kallon ka, gaba daya suka sanya dariya cikin nishaWi.

Gabriel yace  kyau suke kallo, wankan da muka Wauka ne Ya burgesu, mu kanmu mun burge kanmu balle kuma su
Hanna tace Wannan abun da aka sanya mana a fuska yafi komai 6ata min rai, Duk ya toshe mun ?ofofin hancina, wai ba yadda za ai mu tafi batare da mun sanya shi ba ? Tana faman yamutsa fuska tayi tambayar tana kallon Fuskar Angel.

Kafin tayi yun?urin bata amsa Gabriel ya riga ta cewa saboda tsaro, shiyasa aka bamu shi don mu sanya, sunanshi face mask, Javed Yace ai na gane shi, kalar wanda tsohuwa zafreen take sanyawa ne harara parveen ta Wan jefa mashi Ni bana so kuna maganar matar nan, na tsaneta kamar mutuwa ta


 Ina danish yake ne? Shi bai fito ba ne ? Angel tayi tambayar tana le?en ?ofar room dinsa.

Haris yace Suna can Wakin shi suna ta fama dashi akan ya sanya kayanshi ya?iya, kinsan mutumin da taurin kai kamar ?ashin nama, bansan Ya suka ?are da shi ba, Har lalla6a shi nayi na nuna mashi kayan dake a jikina amma yasa kafiya akan bazai sanya ba

Mai hali bazai ta6a canzawa ba, aranta ta ayyana hakan, Kallon su azeeza tayi our twins ku sakar min rigata, zanje Wakin danish
Azeeza tace toh, mu tafi atare zamu biki Ru?o hannayensu tayi a cikin nata, suka nufi Wakin Danish, Su Haris ma suka bi Bayansu, har sun kusa shiga Muryar dr laura ta katse masu hanzarinsu.

Cikin harshen turanci take yi masu magana  Duk inda na kalla kyawawan ?an mata ne da samari nake gani, kunyi kyau sosai, Kamar in sace ku gaba Waya suka sanya dariya, Mi?a ma Haris hannu tayi zonan My baby boy, Ya jikin naka ? Zuwa yai gabanta ta sanya hannu biyu ta rungume shi a ?irjinta kamar yaron cikinta

 Allah ya ?ara maka lafiya Haris, zamu yi kewarku sosai, Ku kula mana da kanku, zamu dinga kira akai akai don mu gaisa da ku cikin karyayyar murya ta ?are maganar, tare da raba shi daga jikinta, idanuwansu duk sun ciko da ?walla.

Voice dinshi na rawa ya furta mun gode sosai da kulawarku agare mu, Kune mutune na farko da kuka fara jan mu a jiki kuka bamu kulawa ta musamman, akanku muka fara yarda cewa akwai mutanan kirki a duniya ba duka aka taru aka zama Waya ba murmushi tasakar mashi tare da kai hannu ta shafa sumar kanshi nayi magana da Angel, Nasan zata baka kulawar daya dace, duk wani abu da kakeso kayi mata magana amsa mata yai da toh.

Angel da su jemimah duk suna a tsaye da sauran nurses da doctors dake kallonsu.

Mi?a ma Su hannu tayi ku zonan my twins, Inason jin Wuminku a jikina, gaskiya zanyi kewarku da sauri jemimah da Azeeza suka isa gareta hannu biyu ta sanya ta rungume su tighly.

Bayan ta raba jikinta daga nasu ta kalli parveen da zolaya tace  Oh, Ji ra kike saina ce kizo ki rungumeni? Ko dan baki ga abinci a hannu na ba ?

Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba Wayansu da gudu parveen ta ?arasa ta rungumeta, shafa kanta dr laura tayi ki kula mun da kanki, a duk lokacin da kika ji yunwa, kiyi ma Angel magana zata baki abinci, kada ki zauna da yunwa lumshe ido parveen tayi ji take kamar karsu rabu da juna, don ba ?aramun so suke Yima matar ba.
 Pure heart, my beautiful daughter zo ki rungume mommynki ta faWa tana kallon Batul, da Wan sauri ta je gabanta ta faWa saman chest dinta sosai ta rungumeta.

 Ki kula mun da kanki, Allah ya tsare mun ku, zanyi kewarku Batul tace muma zamuyi kewarku, idan muka samu dama zamu dinga zuwa muna ganin ku, dr laura tace kada ki damu basai kunzo ba, muma zamu Iya zuwa dubaku har ?asar taku Batul taji dadin kalamanta, Waya bayan Waya sai da tabisu ta rungumesu tana mai ?ara jaddada masu akan su kula dakan su.

Lokacin da tazo kan Angel, Har ta mi?a hannu zata rungumota, Ba zato ba tsammani Garkuwa Ya fito daga room dinsa, adai dai lokacin Jami an Isod sun shigo ward din, Cikin shiga ta black suits, Hannayensu da ?afafuwansu sanye cikin ba?a?en safuna, takalman ?afarsu leather shoes ne fuskokinsu duk sun sanya face mask, ?irar su bata da banbanci data jami an kurkukun ?addara, Giants ne wani irin faffaWan kirjine dasu, na ban mamaki, suna tafiya cikin taku na ?asaita, kai daga ganinsu zaka shaida ?arfin da suke dashi damtsen hannunsu tamkar zai fasa rigar jikinsu a murmurWe suke, azafafe suke yin takunsu tamkar zakuna, Suna tafiya tsokokin jikinsu na motsawa da ?a??arfan kuzari na majiya ?arfi.

Lokaci Waya ward din Yai tsit tamkar mutuwa ta gifta, bakomai ne Ya jawo hakan ba face fitowar Danish daga room dinsa, tare da dr brown da dr. Mark jackson, Tabarakallahu ahsanul khalikin, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da mutumin da sutura ta raina kanta a jikinsa ba irin Danish !

Wankan daya Wauka na slim fit suit dinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login