Showing 165001 words to 168000 words out of 260999 words

Chapter 56 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ne, wasu haWaWun gujerune kewaye da tables din, daga saman ceilling din Wakin cin abincin ?aton kwan fitila ne ke haskaka cikinsa, ga kuma Zungureriyar floor lamp, Itama nata hasken Daban Yake, agurguje zamu le?a Cikin Bedrooms din dake a part din, A ?alla Wakunan kwanan dake a cikin part din sun kai goma sha biyar, Just for one part, ?ofar shigar kowani Waki ta glass ce sai dai baka Iya hangen abunda ke ciki idan har na cikin Wakin ya zuge curtain dinsa ba, ?ofar da kanta take zugewa da zarar mutun Ya kusance ta take sliding a hankali, Idan ka shiga Wakin idanuwanka zasu fara Yin Arba da wallpaper ta bango mai matu?ar jan hankali, kowani room Yana Wauke da hamsha?an king-side beds masu tausasan Katifu kalar wanda ko mutun bai jin bacci idan Ya hau su sai dai aji sautin minsharin shi, saman gadon shimfiWe yake da tausasan bedsheet, da jibgegen bargon lullu6a kafi mage laushi, ga jerin matassan kai daga gaban gadon.

Gefe da gefen gadon nightstands ne, wadanda ke Wauke da bedside lamps, daga bakin gadon faffaWan wooden table ne mai Wauke da drawer chest a jikin shi, ga wani haWaWWen rag carpet shimfiWe ?asa mai dumbujejen gashi gashi ajikinshi tsaf mutun zai Iya kwanciya saman shi saboda laushinshi, ga wani ?ayataccen dressing mirror gabanshi haWaWWiyar kujerace, daga can cikin Wakin akwai dressing room, aljannar duniya kamar ka shiga company saboda haWuwar Large walk in closet din daya mamaye kowani bango na dakin sanya suturar, suturun sanyawa ne an jera su, daga waje zaka Iya ganin kayan dake a cikin closet din, 6angaren Kayan bacci, dana Dogayen riguna, 6angaren english wears dana atamfofi ga laces, da jerin coat, ga 6angaren takalma kala kala, dana jakkuna, kai komai fa an zuba shi babu ce kaWai ke babu, shima Wakin Yana da nashi dressing table, mai Wauke da oval-shaped mirror, Mai Kyan gaske.

Ata?aice Idan fa nace zan tsaya zayyana daular Owais sharafudden tabbas zamu ?are littafin akan bayyana kyawunsa, sai dai mun shiga cikin labarin sannu a hankali zan ?arasa zayyana maku haWuwar wasu 6angarorin na gidan.


*CHIEF OWAIS
'*


Gajiyar tafiya ta hana shi ta6uka komai, ga6o6in jikinsa sunyi mashi nauyi, tun da ya fito daga bathroom yake a kwance saman katafaren king bed dinsa, ya lullu6e surar jikinshi da Cashmere robe launin dark navy, Iya gwiwarsa rigar ta tsaya mashi, ya Waure igiyarta daga saiting flat waist dinsa, mutumin fa akwai ?irar ?arfi, Kyawawan idanuwanshi A lumshe suke tamkar maiyin bacci, Yalwatattun eye lashes dinsa sun kwanta luf, a hankali Yake motsa soft thin lips dinsa tausasa launin pink, dogon hancinsa Yayi tsaye babu lan?wasa Yayin da yake fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali, ya zagayo da hannun shi Waya ta saman yalwatacciyar sumar kanshi, ba za ka ta6a gane a wani yanayi yake aciki ba, ya tada kansa asaman tattausan pillow.

Alert ne ya shigo wayarshi, tamkar baisan motsawa A hankali ya mi?a ziraran yatsun hannunsa na dama ya janyo wayar dake ajiye saman nightstand, da?yar yake iya buWe eyes dinshi akan screen din wayar, Doorbell alert ya gani alamar wani yana son shigowa room dinsa, unclock button ya danna, a hankali ?ofar room Win ta zuge, mutun biyu ne sanye cikin kakinsu, ba?a?en kaya, dogon wando tare da black shirt, daga sama sun Waura long coat, kowannansu ya 6oye fuskarshi da face mask, idanuwansu ne kaWai zaka Iya gani, suna da faffaWan ?irji, agaban gadon shi suka dakata da yin tafiya, cikin girmamawa suka haWa baki wurin furta

 Barka da safiya Yalla6ai, fatan ka tashi lafiya, Ya gajiyar tafiya tun da suka fara magana basu Wago da ido sun kalle shi ba, saboda a ?a ida shi ba ayi mashi magana ana kallon cikin idon shi, hakan babban laifi ne.

Bai da niyar yi masu magana, bai kuma buWe idanuwanshi ba tun da ya lumshe su, aran su su ka ayyana yau qasaitar tashi ce ta motsa, kamar gumaka Ya shanyasu a tsaye suna jiran amsar shi, sai da ya mula yasha iska kamar baison motsa la66ansa Ya furta Lafiya muryarshi tamkar ana busa sarewa.

Big Guy yace Sir, is there anything you need? ya tambaye shi ne don shi a ?a ida ba ayi mashi abun da bai ce yana so ba, ko da kuwa abinci ne ka kawo mashi duk mun yunwar da yake ji in dai bashi yace yana so ba to zai ce maka ka koma dashi inda ka Wauko shi sai in yaga dama ya ke kar6ar shi

Jin yayi shiru yasa Big Guy kuma cewa yalla6ai zamu Iya yin magana ta waya ? Sai lokacin Ya Waga mashi kai alamar eh, ajiyar zuciya Big Guy ya sauke tare da kallon mutumin dake a gefen shi wanda suke kira Boss Man, murmushi su ka sakar ma junan su, sun ?wammace su yi magana dashi ta text message saboda wahala yake basu in dai a baki zai furta masu magana.

Slowly ya ware reddish brown eyes dinsa akan screen din iphone dinsa, a tsanake yake yin typing.

Jin ?arar shigowar message ta wayar Big Guy ne yasa shi yin saurin curo wayar daga cikin aljihun coat dinsa Ya duba abun da Chief ya rubuta mashi

_I need My breakfast right now_


cikin girmamawa big guy yace  I ll bring it to you immediately,

Ya faWa tare da Juyawa ya fuce daga Wakin, Boss Man daya ya rage a tsaye ya natsu yana jiran jin me zai ce.

A lokacin da bai yi tsammani ba, muryar Chief ta katse shi Have a seat wuri ya samu saman doguwar sofa din Wakin Ya zauna
 Check your phone, I sent you a message.
Ya bashi umarni.
Da sauri Boss Man Ya zaro wayarshi daga aljihu ya soma karanta sa?on chief din nasu.

 Ya kake fatan ka tashi lafiya murmushi ya saki har saida ya Wago dakai Ya kalli fuskarshi, Yana matu?ar yin mamakin girmama shi da yake yi duk cikin waWanda ke aiki a ?ar?ashinsa shi kaWai Owais Yake gatantawa, suna mutunci da juna.

 Lafiyalou Alhamdulillah, Ina fata kaima lafiya, don na lura kamar gajiyar tafiya bata sake ka ba abaki Ya furta mashi maganar, shi kuma Ya bashi amsa ta text message.

 Nagaji sosai, amma alhamdulillah, lafiyata ?alou, Ina fata ka le?a wurin ?ar taka, 

Still fuskar Boss man da murmushi yace ban kaiga zuwa ba, Yanzu nake shirin shiga na duba ta

Text ya rubuta mashi Make sure you give her a big hug. I know you ve missed her for a long time.

Idanuwan shi ne suka cicciko tab da ?walla, tuni jikinshi yai sanyi, cikin sanyin murya ya furta in sha Allah, zanyi hakan, daren jiya ko runtsawa banyi ba saboda jiran ?arasowarku Nigeria, duk don saboda Inyi tozali da ita, sai dai ban samu damar Yin hakan ba, saboda Bayan nayi sallar asubahi a masallaci bacci Ya dauke ni, saida na shigo gida nake jin labarin ?arasowar ku...... dakatawa ya Wanyin da yin maganar, ganin text din da owais Ya tura mashi.

 Don t let the tears fall from your eyes, Otherwise, I won t let you see your daughter. fashewa yayi da dariya jin abunda yace mishi, har saida ya Wago ya dubi fuskar Owais, Hankali kwance sam idanuwanshi basa akan fuskar Boss Man Win.

 Kana da mutunci, shiyasa muke ?aunarka, wallahi tunda nake arayuwata ban ta6a ganin matashin saurayi mai wadatar arzi?i, da kyau da asali, mara girman kai irinka ba, saboda kowa naka ne, babu ruwanka ka ji daWin rayuwarka, bazan ta6a mantawa da alheran da kayi mun ba, nasan bazan Iya biyanka ba amma ina fata Allah Ya wadatani da abunda zan faranta maka da shi

Tunda ya fara magana Chief owais Ya natsu yana sauraron shi, idanuwanshi akan screen din wayarshi.

Tambaya ya jefa mashi What s her full name?

cikin girmamawa Boss Man yace UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN lumshe idanuwanshi yayi, ?amshin turaren jikinsa yana ?ara daWaWa hancinsa.

 She looks like you dariya Boss Man ya saki yana duban fuskarshi Yace tayaya akai ka sani? Kaida baka kallon mutane, Ni nasan baku haWu da ita ba

Kafin Owais Ya furta magana, alert Ya shigo wayar shi, unclock button ya danna, door room din ta zuge, Big Guy ne ya shigo da food trolley, Ya gunguro shi zuwa gaban wooden table din gadon Owais, a saman shi Ya jera mashi kayan Lafiyayyan breakfast dinsa, Bayan ya gama da zolaya Boss man yace Big Guy, mutumin fa yau baya iya cin abinci da kanshi, ko zaka mashi abaki ? Big Guy na murmushi yace If he gives me the opportunity to do that, I ll do it har wanka zan dinga yi mashi.... da?yar Ya ?are maganar ganin yadda Chief owais Ya Wago da sexy eyes dinsa akan fuskarshi, cikin jin kunyar maganar daya furta ya sunnar dakai ?asa Yana faWin afwan Sir, su6ul da baka nayi

Fuskarshi a Waure Ya furta If you ever repeat this mistake, you ll spend the rest of your life in prison. Dariya Boss Man yayi jin abunda chief yace, Big Guy na murmushi aranshi Yana fadin Ai bazan ma ?araba, Yanzun ma albarkacin boss man naci

Ajiye wayarshi yayi saman nightstand, Ya yun?ura Ya mi?e Yana faman Yamutsa fuskarshi, Big guy dake satar kallon damtsen hannun shi sai faman jinjina kanshi Yake Yi, dawowa yayi end bed din Ya zaune gaban glass table din dake sha?e da abinci.

Serving dinshi big guy Ya fara Yi, Ya mi?a mashi mug na coffee, Kafin Ya fara sha sai da Ya fara fadin Boss bismillah Man na murmushi Yace A a yalla6ai, Ni ina na isa In haWa KafaWa dakai wurin cin abinci, kaima ka sani bamai yiwuwa bane, sannan Ni a ?oshe nake, Madam ta girka min abinci na cika ciki na

Ta6e baki Chief Owais Yai, ba tare daya ?ara furta komai ba.

 Yaran fa har Yanzu bacci suke Yi yalla6ai, na lura ba ?aramin gajiya suka yi ba, musamman Kyakkyawan matashin nan dake acikinsu, mai kama dakai, yamutsa fuska owais Yai jin ance mai kama da shi.

Fresh fruit ya soma Wauka Yan sha, duk wani motsin shi akan idon Boss Man, Yaron ba ?aramin burgeshi Yake Yi ba, ?aramin mutun da halin girma, Idan kaji shekarun chief owais zaka sha mamaki, girman jikine kawai dashi da kuma babban matsayi da Allah Ya bashi, uwa uba Ya iya dattako.

Boss man Yace An kammala shirya masu breakfast dinsu, masu aiki suna can suna aikin jera masu, Yanzu su kaWai muke jira su farka don su ci ya faWa yana duban fuskar chief, Jinjina kanshi ya Wanyi batare daya Wago da idona ba ya furta hakan Yayi kyau

Mi?ewa Boss Man Yayi Ni zan shiga Cikin gidan, Ka ci abinci Lafiya our chief Ya ambaci hakan tare da Juyawa Ya fuce daga Wakin, Ya rage saura Big guy dake saving dinshi.

*>?
?EX-PRISONERSd'*

Kwance take saman katafaren gadon Wakin Danish, tun daren Jiya da suka ?araso kowannansu aka ware mashi Wakin shi, mutun biyu Waki Waya, Danish ne kaWai Aka mallaka mashi bedroom Waya saboda shine babbansu, Angel da Batul Wakinsu daban, Azeeza da jamima Waki Waya, Parveen da Hanna suma nasu daban, Gabriel da Naufal room Waya, Javed da haris a Waki Waya.

Saboda Rashin lafiyar danish yasa ta gudo daga Wakinsu ta dawo nashi tana matu?ar jin tausayinshi batasan wani abu ya same shi, gani take kamar idan tayi nesa dashi wani abu zai faru da shi, gown din Jiyace a jikinta red colour, tayi uban squeezing, hatta sumar kanta a haukece take babu gyara sunsha bacci kamar ba za su farka ba, daWin lumbutsetsiyar katifar gadonne Ya sanya suka shagala, daga ita har shi garkuwan, ya cire suit jacket din jikinshi Iya farar shirt dince Ya bari, da gajeran wando fararen laps dinshi kamar ka ta6a jini ya Wago tsabar hasken fatar, ya Waura kanshi saman wuyanta, yayin da hannayenshi biyu ke a ru?e da waist dinta, zafin jikinshi ya daidaita bakamar da suna acikin jirgi ba zazza6i ya lullu6e shi, Yanzu ya samu sau?i numfashinshi na fita cikin kwanciyar hankali, Sanyin A.c din dakin ya ?ara masu ?aimi wurin Yin baccin nasu kamar matattu.

Mutsu mutsu ya soma yi alamar zai farka, wata irin matsiyaciyar yunwace ta addabe shi, tun Jiya baici ko mai ba, ko ruwa bai gifta ma?oshin shi ba, Dogon numfashi yaja idanuwanshi sunyi mashi nauyi Ya gaza buWe su, da wata irin kasalalliyar murya ya soma ambaton sunanta My Angel! My Angel badan la66ansa na akusa da wuyanta ba da kuwa zaiyi wuya ta iya jin muryarshi.

Kamar an zungureta, a firgice ta farka tana faman zare gray eyes dinta haWi da ambaton sunanshi Danish are u okey? Ko jikin ne ?

Da?yar Ya iya janye head dinsa daga saman wuyanta Ya daura shi saman tattausan pillow, a hanzarce ta yun?ura Ta mi?e zaune tana faman mutsistsike idanuwanta da hannunta donta samu damar ?are mashi kallo.

 My man, yunwa ko ? Tun kafin ma ya faWa mata abunda Yake Ji ta riga shi faWi.
?aga mata gira yai alamar eh, murmushi ta Wan sakar mashi har dimple dinta Ya lotsa Danish banga ka yaba kyan Wakinka ba, ko da yake baka acikin hayyacinka, saboda kana Jin Yunwa, bari naje naga ko zan samo maka abunda zaka ci, kafin in dawo ka shiga toilet kayi wanka, sai ka canza kayan jikinka kamar ?aramin yaro haka takeyi mashi magana.

Wurga eye balls dinshi yayi akan katafaren Wakin nashi, kamar na Wan shugaban ?asa tsabar haWuwarshi.

Saukowa Angel tayi daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon shi, daWi kamar ya kashe ta, ha?ika taji daWin canjin rayuwar da suka samu, har ta fara tsara masu irin rayuwar jin daWin da zasuyi, sai dai ta Wan shafa a da zancen kurkukun ?addara.

Tun da ta fito daga Wakin take faman ?wala ido tana kallon haWuwar katafaren falon, Cikin sanWa take Yin tafiya kamar 6arauniya, fararen ?afafuwanta babu takalma, bata nufi ko ina ba sai Wakin su Azeeza a hankali ta zuge ?ofar ta faWa cikinsa, tayi mamakin ganinsu a tsaitsaye saman bed mattress kowacce ta ru?e pillow a hannunta, sai tsalle suke Yi suna fadin gamu agidan daddyn Genie dariyace ta kusa kubce mata da sauri ta toshe bakinta da tafin hannunta, wato su duk a tunaninsu gidan daddyn Genie ne aka kawo. yara sun zama ?an hutu. Fitowa tayi daga Wakinsu ta nufi Wakin Parveen tana shiga ta sameta a zaune tsakiyar gado, bacci ya?i sakinta ga yunwa tana ji sai faman yin hamma take Yi, sumar kanta kamar ta mahaukaciya duk ta yamutsata, ta gimtse eyes dinta, hannah na akwance gefenta sai sharar baccinta take Yi.

?umshe dariya Angel tayi da sauri ta fito ta nufi Wakin su Haris don ta duba su, lokacin data shiga Wakin gaba Wayansu bacci suke yi daga shi har javed duk sun cire suit jacket dinsu sunbar shirt da gajeran wando.

Fitowa tayi dakinsu ta nufi, Wakinsu Naufal, adai dai lokacin Gabriel Ya fito daga wanka, daga shi sai short, Ya ru?e short toilet Yana tsane sumar kanshi, Naufal kuma yana zaune saman mirror chair Ya ?ura ma madubin ido da alama gabriel din Yake jira ya fito daga wankan shima Ya shiga.

Gaba Waya basu lura da Angel ba, da zolaya gabriel Yace mutumin kyau kake kallo a madubi naga tun Wazu ka tasa shi agaba ko ?yafta ido baka Yi

Ba tare daya juyo ya dube shi ba yace Kai nake jira ka fito daga toilet din nima wankan nake son Yi

Gabriel Yace amma dai kasan toilet din nan ba kalar na prison bane, akwai ruwan zafi dana sanyi kada kaje ka ?ona fatarka, kazo in nuna maka Yadda zakayi amfani da shi

Harara Naufal Ya watsa mashi bana bu?ata, nima zan Iya dakai na gabriel na dariya yace bana so ka yi danasani mi?ewa naufal yai ya nufi toilet din Ya shige, shigar shi ko minti Waya ba ai ba sai gashi ya fito Yana haWe rai Ya kalli gabriel nifa bangane komai ba dariya ce ta kufce ma Angel gaba Waya suka juya suna kallonta, har ta juya zata gudu Gabriel Yai saurin zuwa ya ru?o hannunta Sister yaushe kika shigo? Ba sallama?
 6atan Hanya nayi, ni banma san na faWo Wakinku ba

Naufal Yace kindai shigone yi mana le?en asiri, kuma kinga abunda kikeson gani, gashi har kina dariya girgiza kai tayi wallahi ni ba abunda nashigo gani, ba ri ma in tafi ta faWa tare da Juyawa da sauri ta fuce daga Wakin,

Kallon Naufal Yai muje ko sai da ya fara murguWa mashi baki, kafin Ya Juya suka nufi toilet din, Ya nuna mashi yadda zaiyi amfani da komai, kafin Ya baro shi a cikin toilet din.

Tana cikin tafiya Muryar Batul ta katse mata hanzarinta Angel a firgice ta Juya tana kallonta, buWe baki tayi haWi da zare idonta, ganin Batul ta fito tana faman Yin hamma haWi da Yin mi?a duk a lokaci Waya
 Yaushe kika tashi ?
 Yanzu, na duba Wakin banganki ba ashe kina anan tunda ta fara magana idonta ba akan Angel Yake ba, Katafaram Falon take ?arema kallo, kamar maijin tsoron shi, sai faman ?yaf?yafta idanuwanta take Yi, bakinta hada Miyan bacci, kwata kwata babu natsuwa atare da ita, musamman sumar kanta tafi komai haukacewa.

Mi?a mata hannu Angel tayi idan zaki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login