Showing 213001 words to 216000 words out of 260999 words

Chapter 72 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

kan giant snake din

Tamkar yana ?ara tunzurata, kuka take yi na fitar hayyaci.

Big guy dake amanne da earbuds, muryar Chief ce ta janyo hankalinshi ga sauraronshi

 Tell her to stop crying, I don t want to hear it.(Ka faWa mata ta daina kuka, bana son ji ) amsa mashi yai da toh, kafin ya Waga murya yace da salsabeel ka lallashi ?ar uwarka, tadaina yin Kuka, umarni ne daga chief
Jinjina mashi kai yai, da karyayyar murya ya ambaci sunanta Unaisa, Ki daina kuka, danish baya jin dadi, ya fadamin idan baki daina ba shima zai fara kukan saboda kina ?ara tayar mashi da hankali jin wannan maganar yasa tayi saurin haWiye kukanta, a hankali ta dago da kanta tana duban fuskar salsabeel, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, kumatunta sunyi jawur, pink lips dinta sunyi suntum dasu, tasha kuka baiwar Allah.

Cikin shesshe?ar kuka take fadin Sal... Sal... Sabeel, ka fadamin ya akai ka tsira daga gidan kurkukun ?addara? Ina ?an uwana suke? Ina deeja take da mubeen? Suma sun rayu ko sun mutu? Inaso nasani, gaba Waya na rikice

Shafa gefen fuskarta yai da hannun shi, Cikin sanyi murya yace Unaisah, ki kwantar da hankalinki, yanzu bana acikin natsuwar da zan Iya yi maki bayanin komai, nayi maki al?awarin zan fayyace maki komai idan Danish ya dawo mutun, amma fa sai kin daina yin kuka, kin kuma natsu jinjina mashi kai tayi alamar zata daina.

 Danish yana yi min magana, yanzu haka ba ta yi mamakin jin abunda yace ba, tunawa da cewa shima giant ne, abune mai yiwuwa suyi magana ta sirri acikin zuciyoyinsu harma su Iya jin juna, big guy ne kadai al ajabi ya cika shi, tun yana daga tsaye har yakai ga samun wuri saman sofa din dakin ya zauna yana dubansu
 Ina son jin me yake fada maka acewar big guy
A lokacin Unaisah ta mayar da kanta saman kirjinshi, ya tallabeta da hannu Waya, zazza6i jikinta sai ?ara nunkuwa yake yi.
Calmly Salsabeel Ya soma faWa masu tattaunawar da suke Yi da danish.

 Ya faWamin bayason unaisah tana yin kuka, Zuciyarshi tana karaya, sannan yana ro?ona akan in taimaka mashi ya rikiWa ya koma mutum baya son ganinshi a suffar maciji, yana jin ?yan?yamin kanshi, yana acikin mawuyacin hali na ?unci da raWaWi, idan har ya Wauki tsawon lokaci bai dawo mutum ba Giant s heart dinshi zata motsa ne, idan kuwa ta motsa gaba Wayanmu zai Iya cutar damu, saboda awannan matakin babu wanda zai Iya sarrafa shi har ita unaisah hankalin Unaisah ba ?aramin tashi yai ba jin abunda salsabeel yake fadi, ita azatonta giant s heart dinshi ne ya motsa shiyasa har ya iya rikiWa ashe ba zuciyar bace ta motsa.

Ba ita ba hatta big guy ya Wan girgiza da jin kalaman salsabeel, har saida ya daura eye balls dinshi akan macijin dake a nannaWe saman gadon har yanzu bai Wago da kanshi daya daura saman laps din salsabeel.

Cigaba da yin magana yayi danish yana acikin damuwa, ina jin shesshe?ar kukanshi, ro?ona yake yi akan mu taimaka mashi ya canza halittarshi ya gaza rikiWa baisan ya zaiyi ba, bayason ?an uwanshi su guje shi, idan kowa ya ?yamace kamar yadda ya ?yamaci kanshi hakan zai yi silar motsawar giant s heart dinshi kuma idan ta motsa zai nesanta kanshi da kowa saboda baya son ya cutar da mu, zai koma inda yasan baza a ?yamace shi ba, yana nufin tushen shi gidan kurkukun ?addara.... tunkan salsabeel Ya ?are maganar, Unaisah ta tari numfashinshi  A a danish, ka daina fadin zamu ?yamace ka, Ni yanzu ma nafara ?aunarka saboda ina tausayin rayuwarka nasan cewa bayin kanka bane, mugayan mutanan can ne suka assasa faruwar hakan duk don ka koma garesu, sunyi maka hakanne don mutane su guje ka kai kuma kaji ka ?yamaci kanka saboda sunsan ta wannan hanyarne kadai zakaje gare su, Ni kuma wallahi bazan ta6a bari hakan ta faru ba, Yanzu nafara sonka, Danish ba maciji ba, kowace irin halitta zaka koma a duniyar nan ina atare dakai, har abada har ?arshen numfashina, kai koda ace zaka dinga cutar danine bazan rabu dakai ba, sai inda ?arfina ya ?are, akanka babu gudu babu ja da baya wallahi bazan barka ba....... kukane yaci ?arfinta har ta kasa ?arasa maganar.

Macijin yana sauraron duk abunda take cewa, ya Wago da kanshi daga saman laps din salsabeel, mitsi mitsin idanuwanshi na fuskantarta.

Big guy bazai Iya jurar tausayinsu da yake ji ba, Jikinshi yai sanyi la?was kamar wanda aka zare ma laka.

Duk abunda ke faru Chief Owais Yana sauraronsu, yayin da yake a kwance cikin bedroom dinshi saman gadonshi, Muryar unaisah ta cika mashi kunnuwanshi tamkar agabanshi take Yin kukan, A hankali ya dauki wayarsa daya daura saman broad chest dinshi ya dawo da ita saitin kunnanshi, don yaji dadin sauraronta dakyau.

Shafa sumar kanta Salsabeel yai da hannunshi Ki daina kuka yace min in fada maki bayaso da sauri ta hadiye kukanta tana fadin toh na daina, bazan ?ara ba my Man, ta faWa tana kallon macijin har girgiza mata kai yake yi, batasa sa adda tasaki murmushi ba, ta fahimci lallashinta yake yi.

 Abun da Unaisah ta faWi gaskiya ne, tsammaninmu yazo Waya, azzaluman kurkukun ?addara ne suke sarrafashi ta ?arfi da yaji bada son ranshi ba, kuma sunayi mashi hakanne don mutane su ?yamace shi kowa ya gujeshi, shi kuma zaiji ya tsani kanshi saboda ?yarar da mutane suke yi mashi, daga haka zai fara tunanin komawa prison wannan shine abunda suke ?o?arin yi

Tun da yafara magana big guy yake jinjina kanshi alamar gamsuwa da jawabin shi, Muryar chief ce ta sa shi dakatawa yana sauraronshi, babu mai iya jin voice dinshi sai shi da yasanya abun sauraron akunne.

Cikin harshen turance yace  Ka faWa mashi, muna atare dashi, bazamu ta6a rabuwa dashi ba har iya ?arshen numfashinmu, babu wanda zai ?yamace shi, duk runtsi zamu kasance atare dashi don mu bashi ?warin gwiwa kuma zamu tallafa masa don ganin mun raba shi da miyagun dake atare dashi, in sha Allah komai yazo ?arshe ya kwantar da hankalinshi

Jinjina kai big guy yai ha?i?a yaji daWin kalaman Chief owais, magana yasoma yi masu chief yace in isar mashi da sakonshi zuwa ga Danish ..... mayar da hankalin sukayi akanshi suna sauraronshi, a tsanake ya faWa masu abunda chief yace.

Wani irin farin cikine ya lullu6e Unaisah, har cikin ranta taji daWin kalaman shi duk da batasan wanene shi ba, ba ta ta6a ganin fuskarshi ba, ko Wazu da taji an dauketa lokacin data lullu6e Danish da bazar rigarta batasan wanene ya dauketa ba saboda bata acikin hayyacinta, idanuwanta sun makance.

 Wanene chief? Yaushe ya faWa maka sakon ? Ta jefa ma Big guy tambayar yayin da take dubanshi.

Nuna mata earbuds din kunnanshi yai da yatsan hannun shi, nan take ta gane abun jin magana ne a ear dinshi tanan suke yin communicating da shi.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke muryarta adisashe ta furta idan na samu natsuwa zaka kaini wurinshi muyi mashi godiya Big guy yace a a shi ba ayi mashi godiya, sai dai idan kinason ganinshi zan nema maki izni daga gare shi, amsa mashi tayi da toh inaso

Kallon salsabeel Yai menene mafita? Muna son musan wani hali yake aciki kafin ya bashi amsa unaisa tayi saurin cewa nayi magana da boss man, na fada mashi inda na ajiye wasi?ar adreshin gidanku daka bani, inda zamu samu ruwan zam zam din

Fuskarshi da matsanancin damuwa yace ai babu zamzam din nan! Tun lokacin da kuka faWa hannun sojin america suka dam?a case dinku hannun hukumar Isod, nasan da zamanku, munyi ?o?arin samu ruwan zam zam saboda gudun kada giant s heart dinsa ta motsa, sai dai kash lokacin da muka je gidanmu na kaduna tare da jami an isod bamu samu komai ba, Gidan ma an canza mashi kamanni, magada ne suka koma da zama cikinshi, su kansu da mukaje basu san Wanene ni ba, munyi ?o?arin yi masu bayani amma sai suka fada mana cewa babu komai na habibullah dayai saura agidan.... aruWe Unaisah tace ya zamuyi yanzu ? Ta faWa tana zazzare idanuwanta.
Salsabeel yace akwai hanyoyi da dama, da zamu Iya samun ruwan zam zam sai dai bamusan wasu irin addu o ine ko ayoyin al?ur ani ake amfani dasu ba wurin tofe ruwan ba ya faWa yana dubanta.

 da za a samu babban malamin addini kamar mahaifina habibullah ina da tabbacin zai iya taimaka mashi

Shiru suka Wanyi suna kallon kallo atsakanin Salsabeel da Unaisah, ga macijin yayi kwance saman jikinshi daya nannaWe.

Chief Owais dake a kwance saman bed matress dinsa Yana sauraronsu, ?arar shigowar message ce ta janyo hankalinshi ga buWe eyes dinshi, phone dinsa Ya Wago da ita yana duban screen din.

Text message ne aka turo mashi, yayi mamakin ganin sa?on Uncle dinsa, A irin wannan lokacin ?arfe biyu da rabi na dare, hakan na nufin bai runtsa ba.

Karanta text message din Ya soma yi acikin zuciyarshi.

_ My son, I can t sleep because of that child, I don t know why I m so worried about him. Please help me. I want to see him before I go back to Canada next week. na jaraba kiran layin Sheikh imam munyi magana dashi ashe baya kasar ya tafi sudan, na nemi alfarmar inason ganinshi da gaggawa, yace min in sha Allah zai dawo ?asar a gobe, sa?o daga Prime minister Hateem Obinna_

Bayan kammala karanta message din, Owais Yai mashi reply kamar haka

_ Nima ban runtsa ba kawuna, saboda yaron, ?o?arin da muke Yi kenan don ganin mun taimaka mashi ya canza halittarshi zuwa ta suffar mutane, amma inaso ka kwantar da hankalinka ka yi bacci, in sha Allah zaka haWu dashi kafin komawarka kanada, har ma kuci abinci atare _

Tura mashi sakon yai, within minutes saiga wani sakon daga prime minister

_thank u, sai mun hadu gobe da wuri zan shigo gidan naka idan sheikh iman ya ?araso_

Lumshe ido owais yai, A hankali ya furta sunan big guy, on the other hand big guy ya amsa mashi da na am yalla6ai

 Sako ya shigo min daga Uncle Hateem, Zuwa gobe da safe Sheikh Imam zaizo Nigeria, yayi tafiya ne zuwa sudan, ka yi ma brother din yaron nan magana ya tambaye shi idan yana jin yunwa ya fadi me zai iya ci akawo mashi amsa mashi yai da toh.
Ya mayar da dubanshi ga su salsabeel tun da yana jin maganarka ka tambayar mana shi me zai Iya ci akawo mashi, sannan pls kace mashi ya kwantar da hankalinshi zuwa gobe insha Allah sheik imam zai shigo Nigeria, shahararran malamin addinine muna da tabbacin zai Iya taimaka mashi

GyaWa kai salsabeel yai ay yana sauraronka, Yanzu haka magana yake yi min.

 Meyasa kuka harbe shi? Duk da harsashin bai fasa jikinshi ba yayi mashi illah saboda babu kakin giant a jikinshi

Hankalin Unaisah dana Big guy ya tashi matu?ar, muryarta na rawa ta furta meya faru dashi? Yaji ciwo ajikin shi
 Bazan Iya sani ba, sai ya dawo suffarshi ta mutane tukunna zamu ga illar da yayi mashi, sannan ya fadamin yana son kayan marmari su kadai yake sha awar sha

Damuwace ?arara akan fuskar Angel meyasa bazai Iya cin abinci ba ? Ta fada tana duban salsabeel.

 A halin yanzu Danish dinki, ba mutun bane Giant snake nake, bazai Iya cin kalar abincin mu ba, har sai ya dawo cikakken mutun.

Kwa6e fuska tayi tana duban kan macijin, har yanzu bai dagoba tunda ya kwantar da kanshi saman jikinshi daya nannaWe.

Mi?ewa tsaye big guy yai ka zauna atare dasu, zan je na kawo mashi kayan marmarin amsa mashi salsabeel yayi da toh.

Bayan fitar big guy, ta ?ura ma salsabeel ido, har yanzu mamakin ganinshi take yi, abubuwa dayawa sun cunkushe mata brain dinta, tana son jin ya akai ya tsira daga kurkukun ?addara? Shin ya sauran ?an uwansu suka ?are sun mutu ko sun rayu? Tayaya Akai Ya haWu da jami an da suke kula dasu? Ko dai dama shima jami insu ne!? ta Waura mashi alamar tambaya, tadai ha?ura ne har zuwa time din da danish zai rikiWa ya dawo mutun donjin amsar tambayoyinta, kamar yadda take kallon Salsabeel haka shima yake kallonta, yayi kewarsu sosai, kuma yaji dadin ganinsu, da ransu da lafiyarsu, bakomai yake tunawa ba face ranar daya fara haduwa da ita har yakaita dakin da suka tattauna, da kuma ranar da ya ceci rayuwarta lokacin da matsafa sukayi mata wanka da jini, ranar da ta azabtu ta galabaita, Allah kenan mai yadda yaso mai jujjuya al amurra, yanzu tamkar ba ayi ba, tayi haske abunta gwanin kyau har girma ta ?ara mashi akan yadda suka yi rabuwar ?arshe a kurkuku.

Murmushi yasakar mata, itama ta mayar mashi da martanin murmushin, ya fahimci a?agare take da son jin labarin ?an uwanta daga gare shi.

*PRISONERS=ؔ?
'?*

Tun bayan fitowar Batul daga Wakin Ummin america, a tsakar dare ta nufi down stair, baiwar Allah tana tafiya jikinta na kakarwa, hatta ha?oranta kerma sukeyi suna hadewa jikin juna, tsoro take ji ita kaWai kamar aljana, sai faman firgita take yi gani take yi kamar macijin zai kawo mata hari.

Da?yar take iya taka ?afarta saman floor din falo, ga wani azababban tari daya farmata.

Sam ba ta ji takun tafiyar mutum ba, saboda hankalinta ba akwance yake ba, sai ?an waige waige take yi tana faman hadiyar yawu.

Yayi mamakin ganin Waya daga cikin yaran tana yawo a tsakar dare, babu mayafi a jikinta, ?ura mata ido yai a ?o?arinshi naya gano wacece acikinsu, ya rasa gane batul ce ko Unaisah, saboda launin gashinsu kala Waya ne ga kuma nannaWewar sumar kan nasu daya kasance iri Waya, zuciyarshi ce ta raya mashi cewa Unaisah tana adaki fa ya barota tare da salsabeel wannan ba ita bace sai dai ko ?ar uwarta ce Batul.

Da ?arfi ya ambaci sunanta Batul rass taji gabanta Ya faWi, a firgice ta waiwayo don ganin wanene, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar big guy dake sanye cikin face mask,l.

Tsabar tsoro da ruWu yasa ta zabura zata watsa da gudu, sai dai kafin tayi hakan yai saurin haura ?afa ya dam?o damtsen hannunta ya janyota zuwa jikin shi, ?an?ame shi tayi atsorace ga tari da take yi.

Lamarin ya Waure mashi kai, Wago da kanta yai daga saman ?irjinshi ya furta ke! Daga ina kike? Ya akai kika fito daga Waki ?
Da?yar ta Iya buWe baki tace sanyi nake ji babu bargo shine na fito zani Waki in Wauko
 Awani Waki kike ?
 ?akin aunty ummi, boss man ne yace muje can mu kwana, saboda munajin tsoron kwana ana mu dakin

 Meyasa baki tambayeta ta baki bargo ba ?
A tsoroce take yi mashi magana tayi bacci ne, kafin ta kwanta ma saida nace ta taimaka ma parveen da kaya ta sanya saboda tayi ma nata fitsari sunji?e sharkaf amma ta?i bata sai dai ni na cire nawa muka yi musanya ta bani nata, kuma Wakinta sanyi sosai
Tunda tafara magana Big guy yake jinjina kanshi, ga dukkan alamu ya fusata matu?a, bashi ba hatta chief owais dake acan room dinsa yana sauraron maganganunsu.

Ru?o hannun Batul yayi acikin nashi ya juya da ita suka nufi Wakin.

A lokacin Ummin america tana ?o?arin fitowa daga cikin toilet, ta gama she?e ayarta da gardin daya kirata awaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zura ?afarta keda wuya hasken Wakinta Ya kama, a firgice takai idanuwanta kan masu shigowa ciki, tunda tayi arba da big guy tare da batul gabanta yai mugun faWuwa.

Wani irin kallon tuhuma yake jefa mata, ranshi amatu?ar 6ace ya soma magana.

 Ke baki da hankaline? Kin ajiye yara aWaki kin kure masu sanyin A.c ? Idan ?a ?ankine na cikinki zaki Iya yi masu haka ?

Muryarta adabarbarce tace am..ba haka bane ni ai bansan basu iya jure sanyin A.c din ba, na saba kwana..... bata ?are maganar ba, Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, sakin hannun batul yai ya matsa kusa da ita, abunda wani Wa namiji bai ta6a gigin yi mata ba, da yatsan hannunshi ya nuna ta ki shiga taitayinki, This is the last time I ll warn you. Don t be reckless in your work. We don t accept mistakes, koda gigin wasa kada ki kuskura ki ?ara maimaita laifin nan yana huci ya faWa
 Yarinya harta fara mura tana tari! Ke ko ajikinki ai nayi tunanin zanzo na sameki kina bacci ashe idonki biyu hakan na nufin da gangan kika kure sanyin A.c din dakinki, Ke bari kiji bana so gobe da safe inji yarinyar nan tana yin mura, ki san yadda zakiyi ta dawo daidai, bama itaba hatta sauran ?an uwanta kada ki bari Waya daga cikinsu ya tashi da mura, idan ba haka ba zaki fuskanci hukunci mai tsanani daga hannun chief..  hankalin ummin america ba ?aramin tashi yai ba, duk tabi ta susuce musamman daya ambaci sunan owais, muryarta na rawa take fadin na kar6i laifina bazan ?araba, kuma aini bansan sanyin zaiyi masu illa ba... bai bari ta ?are maganar ba ya dakatar da ita ta hanyar Waga mata hannu bana sonji,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login