Showing 168001 words to 171000 words out of 260999 words

Chapter 57 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

bini taho mu tafi, Nima kitchen nake nema, danish ne Yake jin yunwa da sauri batul ta ?arasa ta nufeta ru?o hannunta tayi acikin nata, Har sun Waga ?afa zasu motsa kwatsam muryar Ummin america ta katse masu hanzarin su Where are you all going? Wa ya Baku iznin fitowa daga Waki ? Har saida gabansu Ya faWi, duk suka sha jinin jikinsu, A hankali take saukowa down stairs, kimono robe ce a jikinta har ?asa rigar takai mata, Tabi shape din jikinta, takalman ?afarta high hills ne, hair wing din dake akanta launin black ne.

Tana tafiya Hips dinta na jujjuyawa kamar ana kaWasu, agabansu ta tsaya haWi da Goya hannayenta saman tudun kirjinta tana kallonsu, idan ta kalli Angel sai ta kalli Batul, kamar wasu munafukai sunyi wu?i wu?i da ido, musamman Batul duk tasha jinin jikinta, saboda mugun jin shakkarta take ji, har ?wara Angel ashirye take da tayi mata rashin kunya idan har ta ?etare iyakarta.

 Ke! Meye sunanki ! Ta jefa ma batul tambayar, muryarta na rawa ta furta BATUL ! ta6e baki ummi tayi tare da daura idonta kan Angel ke fa ?
?aure mata fuska Angel tayi kamar bazata tanka mata ba tace UNAISAH
 Me kuke nema ne ?




Angel ce tayi ?arfin halin bata amsa da cewa Wan uwana ke jin yunwa, shine na fito don in sama mashi abun da zai ci
Ta6e la66a ummi tayi An shirya maku breakfast din ku a dining, dama ku nake jira ku farka ta faWa tana nuna masu dining room da hannunta, atare su ka kai idonsu ita da batul suka kalli Wakin.

 Ku koma ku tada sauran ?an uwan naku, su fito mu yi breakfast, idan mun kammala inaso zanyi magana da ku


Amsa mata su ka yi da toh, da sauri suka juya suka nufi bedrooms din ?an uwansu, tana a tsaye tana bin bayansu da kallo, bakomai yafi bata mamaki da yaran ba face doguwar sumar kansu data lullu6e bayansu kamar hijabi, aranta ta ayyana Wawainiya da yaran nan ba abune mai sau?i ba, gyaran gashin kansu kaWai wata wahalar ce mai zaman kanta, gashi an faWa mata babu shige babu fuce balle tace zata kai su saloon, kuma babu damar a gayyato masu yi din suyi masu, dole sai dai ita ce za ta gyara su.


Daya bayan Waya suka bi Wakunan yan uwansu suka shiga domin tada wadanda basu farka daga bacci ba, saida suka taimaka ma Azeeza da jamimah suka wanke fuskokinsu da bakunansu, tukunna suka fito daga Wakin, Kayan jiya ne a jikinsu sai mayafin da suka yafa akansu, Hankalin su ba ?aramin tashi yai ba, musamman azeeza tun da tayi tozali da ?wan fitilun falo jikinta Ya hau yin kerma, duk ta firgice, Parveen kuwa baki ya?i rufuwa kamar lefen sakarai sai faman zazzare idanuwa suke Yi, saboda yanzu ne suka samu damar ganin ko ina na cikin gidan dakyau, Hanna kuwa da?yar take taka tiles din floor, da takalmi ta fito amma saboda tsabar ruWu a hannu ta ru?e takalman ta rungumesu a ?irjinta, gani take kamar in ta taka ?asan da takalman zai fashe, Naufal da Javed har tuntu6e suke yi garin yin kalle kalle gidan yayi matu?ar ruWar dasu, shi ko Haris jiki sai kerma yake yi basa ban ban, shima crystal Chandelier din ceilling ne Ya ruWar da shi ga sanyin A.c da yayi mashi yawa, hatta gabriel dake da wayewa yau dai an ?ure shi, sai faman jinjina kai Yake yi yayin da yake bin katafaren falon da kallo, abunda zai baka mamaki jamimah hankalinta kwance babu abunda ya ruWe ta koya tsoratar da ita, sai faman washe baki take Yi komai ta kalla saita nuna shi da yatsa tace menene wancan ta ishe su da tambaya kamar rainon Wan jarida, Ummin america dake a tsaye bakin ?ofar shiga dining room din, lamarin ya Waure mata kai, tayi matu?ar yin mamakin ?auyancin su, gasu dai a halitta kamar ?a ?an masu kuWi, tafiya suke yi tamkar suna jin tsoron taka floor, sun?i maida hankali su shigo su ci abinci, sai faman ?an kalle kalle suke Yi kamar wuyansu zai cire.

Mutum Waya ce babu acikinsu, Angel da ta tafi bedroom Win Danish, Batul dai tana atare da su Haris.

Gyaran muryar da ummi tayi masu ne ya janyo hankalinsu ga kallonta.
Da hannu ta nuna masu ?ofar shiga ku zo ku shiga ba tare da sun tanka mata ba, suka nufi Wakin cin abincin, koda suka shiga sai suka koma suna bin ko ina da kallo, Parveen ce ta furta La ha ilah! Wannan duk namune ? Ta jefa tambayar tana nuna kayan breakfast din dake a jere saman zungureran table.

Ummi ce ta bata amsa da cewa naku ne, kowa ya samu wuri ya zauna su parveen anga banza, tuni taja kujera ta zauna, Waya bayan Waya kowannansu Ya samu wuri ya zauna, sai faman baza ido suke Yi suna bin komai da kallo, jamimah tana jinjina kai tace Yau zamu ci daWi, wallahi munji daWi muma mun zama ?an gayu, gidan daddyn genie akwai abinci da kayan wasa

Azeeza ta?i Wagowa dakai, ta ?an?ame jikinta saman kujera, ita kwan fitila ne damuwarta, na Wakinsu bai kai na falo dana dining room girma ba, sun hanata sakat, Gabriel dake kallonta cikin muryar raWa ya ambaci sunanta My azeeza Wagowa tayi da ido tana kallon shi sai faman yamutsa fuska take Yi
 Meke damun ki ?
Da index finger ta nuna mashi saman ceilling ba tare da ta kalla ba, muryarta ?asa ?asa tace zai Iya faWowa saman kanmu

Murmushi ya sakar mata ki kwantar da hankalin ki, ba zai ta6a faWowa ba, idan ma zai faWo sai na tare maki shi, hakan yayi maki ? Sai lokacin ta Wan saki murmushi jin abun da yace ta jinjina mashi kai alamar eh.

Parveen sai faman haWiyar yawu take yi ta ?osa su fara ci, sai dai sun gaza sanya hannu ganin yadda Ummin america ta tsare su da ido ko kyaftawa ba tayi, tana daga tsaye bakin glass door din dakin, ta lura basu cika ba shiyasa ta tsaya tana jiran sauran su ?araso don su fara ci.

 Menene wannan abun jamimah ce tayi tambaya tana nuna wata roba
Kallon robar Gabriel yai a jikinta an rubuta Honey.

 Zuma ce a ciki, kin ta6a sha ? Girgiza mashi kai tayi alamar a a, ta kuma nuna dafaffan ?wai tace wannan luluyayyan abun fa ? Harara ya dan jefa mata ?wai ne, pls ki daina yi min tambaya baki ga ana kallon mu ba ? Ta6e mashi baki tayi to aini inason in sani ne ko, har tayi shiru can kuma kamar an cikare ta tace Gabriel kace ?wai ne, to shima kamar ?wan fitila mai bada haske Yake shiru yayi yana kallonta ba tare daya furta komai ba,

(abun da yasa take tambayarshi saboda bakomai ne suka sani dangane da nau ikan abinci, ko a kurkuku snacks da nama suke ci da kayan marmari, haka zalika a asibiti da suka zauna bakomai ne suka sani ba yawanci duk kalar abunda suke ci a prison ne, yau sunci karo da wasu nau ikan abincin dana sha wanda basu ta6a yin tozali da su, shiyasa jemimah ta tsare shi da tambayoyi kamar ?ar jarida)

Batul dai sai satar kallon ummi take yi ita kanta ummin ta lura da kallon ?urullan da Batul take Yi mata, shiyasa ta tsaida idonta akanta, tunda tayi hakan batul ta saddar da kanta ?asa cikin jin kunyarta.

Abun da Ya faru, Lokacin da suka kammala tada ?an uwansu Angel ta nufi Wakin Danish, shigarta keda wuya ta taras dashi atsaye gaban mirror Yana faman yin haki Ya dun?ule tafukan hannayensa kamar wanda zai yi dambe, Kafin ta buWe baki ta tambaye shi lafiya, idanuwanta suka sauka akan madubin daya fasa, ?wa??waran naushi ya kai mashi gaba Waya ya zube ?asa ya tarwatse.

Rass taji gabanta Ya faWi, a tsananin tsoroce ta furta Na shiga uku! danish meyasa zaka fasa masu madubi? Kasan kuwa tsadar dake gare shi? Wai meke damunka ne? So kake kaja mana bala i daga zuwa gidan mutane har ka fara yi masu 6arna hankalinta atashe tayi maganar tana duban bayanshi.

A hankali Ya jiyo yana kallon cikin sanyin murya ya furta mutun na gani aciki Yana kallona, shiyasa na naushe shi Zaro ido waje tayi can kuma ta tuntsire da dariya hada dafe ciki, Waure mata fuska yai ganin tana yi mashi dariya.

Nuna shi tayi da yatsa tana fadin mutumin da ka gani acikin madubin kaine ba wani ba, ai saida naso in nuna maka kanka a mirror amma ka?iya, ka nuna baka son kallon shi gashi nan Yanzu ka fasa masu madubi mai tsada, Ni dai ba ruwana ta faWa fuskarta da murmushi.

Kallon rashin fahimta yake binta da shi, ya rasa gane me take nufi, kamar bata fahimci abunda ya faWa mata ba.

Gudun kada wani ya shigo ya taras da 6arnar da Danish yayi yasa tayi saurin juyawa tana yan dube dube cen idonta ya sauka kan wani abu yayi mata yanayi da tsintsiya da sauri ta Wauko ta tattara broken glass din ta turasu kasan gadon shi dan bataga dust bin a dakin ba ajiyar zuciya ta sauke

Kafin ta Wago tana dubanshi kai kaWai muke jira, zamu yi break fast, ka shiga toilet ka wanke face dinka da bakinka, idan mun gama cin abincin sai kayi wankan toilet door Ya nufa, har ya kusa kaiwa ?ofar ta tuna da madubin toilet, da karfi ta furta dakata danish cak ya tsaya da tafiya, da sauri ta nufi ?ofar toilet din ta buWe ta shige ciki, towel ta Wauko ta rufe madubi, saboda tsaro tasan zai Iya Fasa shi kamar yadda ya fasa na room dinsa.

Fitowa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya ta dubi fuskarshi nasan idan ka shiga ciki zakaga towel na lullu6e wani abu dashi, kada ka buWe shi, madubi ne bana so ka fasa shi kamar yadda ka fasa na Wakin ka, Idan ba haka ba zasu ce saika biya su ne kuma kaga bamu da kuWi, kai ba kama san menene kuWi ba, Ni zaka bari da aikin biyansu ta faWa tana yamutsa mashi fuska, bawan Allah yayi tsaye yana kallonta.

 Ina jiran ka, kada ka daWe ka yi sauri ka fito suna jiran mu

Amsa mata yai da toh, kafin ya bude kofar ya shiga, ?an mintuna ya fito daga ciki, har yayi brushing teeth dinsa, daga kasa har sama take bin shi da kallo, a ganinta basai ya tsaya sanya kaya ba tun da ba wanka yayi ba, Ru?o hannun shi tayi acikin nata kamar wani ?aninta muje ko ? Ta faWa tana ?o?arin janshi.

Adai dai lokacin da suka sauko falon, ?ofar shigowa cikinsa ta zuge a hankali, atare Angel da Danish suka juya baya jin takun tafiyar mutun.

Basu san wanene ba, amma saida taji gabanta Ya faWi, ganin kakin dake a jikinshi na ba?a?en Kaya, kuma ya rufe fuskarshi da face mask, 6oyewa tayi bayan Danish ta ?an?ame shi tana le?en mutumin da ke tunkaro su.

Bugun zuciyarta na ?aruwa kamar zai fasa ?irjinta.

Mi?a ma Danish hannu yai da niyar su gaisa, Danish Ya?i bashi hannu saboda rashin yardar da shi, gyaran murya ya Wanyi kafin ya soma magana a tsanake zaku Iya kira na da Boss man, ina Waya daga cikin masu kula da ku, ya faWi hakan ne don su saki jiki da shi.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke, jin muryarshi ta kamilallun mutane.

Dawowa tayi daga gaban shi ta tsaya tana dubanshi, ido cikin ido suke kallon juna ba tare da ?yaftawa ba.

Tsawon mintuna kafin ta furta Ina kwana, ya amsa mata lafiyalou Angel, kin tashi lafiya? Ya kuma gajiyar tafiya
Tace lafiyalou, gajiya tabi jiki, mun gode da kulawa da alamun jin daWin maganarta ya furta Naji daWin ganinki da ranki da lafiyarki, ina fata baki da wata damuwa maganarshi taWan so ta ruWar da ita, amma sai ta basar tace nima haka da ?yar ta furta ganin irin kallon da yake binta dashi, duk saita sha jinin jikinta, ta rasa gane kallon menene yake yi mata, dauriyace kawai yake yi, yaso ace zai iya bayyana mata kanshi a yanzu sai dai bazai yiwu ba.

 Ciki zamu shiga Ni da Danish, suna jiranmu a dining ta fada don ta samu damar guduwa daga kallon da mutumin yake binta da shi.

?agowa yai da ido ya dubi fuskar danish, har saida yaWan ji gabanshi ya faWi ganin yadda ya Waureta tamau babu annuri, dama tunda ya shigo falon yake mamakin kyawunshi da body structure dinshi don shi sai yanzu ya samu damar ganin shi, abakin abokan aikinsa yaji suna zuzuta kyan yaran da kamanninsu da Chief dinsu.

 ?an uwan naki bai magana ne? Ya?i bani hannu mu gaisa murmushin ya?e tasakar mashi rashin sabone, Yana da wuyar sha ani amma idan kuka saba zai saki jiki da kai

Jinjina kai boss man yai okey, mu shiga ciki, Nima can zanje a fakaice ta yamutsa fuska, aranta ta ayyana wannan mutumin zai takura mata ga shi da kallon tsiya kamar zai lashe mutun a fili kuma taja hannun dashi suka nufi dining room din, Boss man na abiye da bayansu, kwata kwata babu alamun ?auyanci atattare da Danish, sai dai jefi jefi yake satar kallon kayan alatun dake acikin katafaren falon.

Lokacin da suka shiga dining room din da sallama abakunansu, gaba Waya hankulansu Baful Ya dawo kansu, Ummin america tuni ta samu wuri ta zauna, ganin Angel da suka yi da danish nan fa suka fara sakin murmushi kamar wasu zautattu, kujera taja ma danish ya zauna Yana fuskantar ummi, ita kuma Angel ta zauna daga gefen shi, Sai daga bisani su Gabriel suka lura da Boss man daya shigo, kallon juna suka yi da alama sun Wan tsorata da ganinshi saboda dressing din jikin shi yayi shige dana Giants din kurkukun ?addara.

Sai da Angel tace ku gaishe shi, sunan shi Boss man, Yana Waya daga cikin waWanda zasu dinga kula da mu har suna haWa baki wurin furta mashi gaisuwa, a mutunce ya amsa masu yaji daWi yadda Angel tayi masu bayanin wanene shi.

Ummi ta dube shi awayance tace barka ya amsa mata da yawwa ya kike fatan kin wayi gari lafiya a yayin da yake ?okarin zama gefen kujerar dake a kusa da ita, wadda ke fuskantar Angel, don yaji daWin kallonta.

Ummi tace  Lafiyalou, daga haka ta mi?e ta soma yin serving dinsu, a plates ta zuzzuba ma kowannansu abinci, ta dauki cups ta tsirara masu tea dake acikin flask, Bayan ta gama ta koma ta zauna

Yatsun hannun parveen har karma suke yi wurin Waukar cup din tea, duka ta kur6e shi, ta soma cin wainar kwai hannu baka hannu ?urya.

Batul kuwa wani sabon salon ?auyanci, tunda ta dafi plate din noodles tasha romo da kayan haWi, da hannu take Waukar indomie din tana Jujjuyata kafin ta turata abaki, Waya bayan Waya Angel ke kallonsu, Kunya duk ta kamata, koda ta daura idonta kan Jamimah robar zuma ta Wauka ta dinga matsata a tafin hannunta ta sanya harshe tana lasa hada tanWar baki, Angel ji take kamar ta fasa ihu.

Ummin america da boss man duk suna kallonsu sai faman sakin murmushi suke Yi.

Gyaran murya ya yi masu jamimah ta dago tana kallon shi yace kidaina shan zumar ita kadai, ga mahaWinta nan ki zuba asama sai ki ci ya faWa yana nuna mata plate din pancakes da robar yougurt washe mashi baki tayi tana fadin wallahi za?i gareta, kunnuwana har motsi suke yi gaba daya suka sanya dariya, Ummi kamar zata sha?e tsabar dariya, Angel dai abin duniya ya isheta, ita ala dole mai aji kada a zubda mata mutunci su kuwa ba ruwansu bayin Allah basu san ma menene ?auyancin ba.

 Malama, ki dauki spork da shi zakiyi amfani ki ci noodles din ba hannu ba ummi ce tayi maganar tana nuna batul da spoon din hannunta, bata Iya cin abinci da cokali ba cos sunfi sabawa da hannu, jiki asanyaye batul ta ke faman ?an kame kame ta rasa ina zata Wauki cokali, Angel ce ta Wauko shi ta mi?a mata, ta kar6a ta tsoma shi cikin indomie din batasan yadda zata kwasota ba, ganin yadda ummi take yi masu dariyar sha?iyanci yasa ran Angel ya 6aci ta haWe rai, muryarta a?ula tace da batul idan bazaki Iya ci da shi ba, Ki ajiye shi ba dole kallonta ummi tayi aikuwa ta galla mata harara, mamaki ya kama ummi ganin abun da Angel tayi mata.

Batul kuwa ta ajiye cokalin taci gaba da ci da hannunta,
Maganar Angel ta burge boss man, sai ?ara dubanta yake yi, abinci yake ci amma hankalin shi na akanta.

Haris dai tun da ya dafi chips babu maijin motsinshi, sai idan anyi magana ya Wago da ido Ya dube su.
Mutun Wayane baya cin abinci, Ya rasa sukuninsa, saboda mutun biyu dake zaune acikinsu, bayason ba?uwar fuska, uwa uba ummi dake ta kallon shi jefi jefi take bin shi da kallo kamar zata haWiye shi.

Sam Angel bata lura da yanayin da yake aciki ba, sai da Boss Man ya furta meyasa baka cin abinci ne ? Tukunna ta Wago ta dubi Danish don ta gane dashi yake magana.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login