Showing 228001 words to 231000 words out of 260999 words

Chapter 77 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

haka, kamar don ita aka sa?a kayan, bata sanya hular ba, yalwatacciyar sumar kanta ta sauko har gadon bayanta dark brown.

Sai faman ?an?ame jikinta take yi, ganin yadda ummi ke kallontane yasa ta du?ar da idanuwanta ?asa, duk tasha jinin jikinta.

Batasan ya akai ta tsinci kanta dayi ma fuskar batul kallon sani, sai dai tarasa tuna dawa take yi mata kama.
Matsawa tayi kusa da ita, takai hannu ta ru?o hular rigar ta sanya mata ita, sai taga ta ?ara yi mata kyau.

 Ki daina ganin ina kallonki, ba kyau kikayi min ba, Munin fuskarki nake kallo shiru Batul batace mata komai ba, bayan ta kammala gyara mata hular rigar, ta nuna mata gado ki koma ki kwanta, har zuwa time da muryarki zata dawo dai dai kinji ko ?
Ma?e mata kafaWa batul tayi ni bazan kwanta ba, dan Allah kibarni in tafi daki wajen ?an uwana, Inason ganin Unaisah muryarta sha?e ta furta maganar.
 Wato saboda kinga makwancina shiyasa kika fara rainani ko? Har kina da bakin fadin Bazaki yi abu ba idan nasaka ki, Dalla ni wuce ciki ko inyi ball dake

?in matsawa Batul tayi, gani take kamar ummi zata iya kasheta, furucin da tayi mata jiya sun firgitar da ita, sun kuma tsaya mata aranta.

Zabura tayi da niyar ta nufi kofa don ta gudu, ai kuwa azafafe ummi ta dam?ota kamar Wiyar roba haka ta Waga ta sama, ta nufi gado ta jefar da ita, ta kuma janyo bargo ta lullu6eta tana fadin idan kika kuskura kika le?o koda kankine saina mur?ushe?i
Muryar batul da shesshe?ar kuka take fadin aunty ummi dan Allah kibarni in tafi, banason kwanciyar, ni wajen ?an uwana zanje ummi dake tsaye tana kallon bargon tace idan kina son fita daga dakin nan to ki fara gyara muryarki

 Ai ni bansan yadda zan gyarata ba, ki bani magani in sha

Ta cikin bargo batul take Yi mata magana.

Tunani ta somayi aranta, ina zata samo mata maganin mura? Tasan ba a rasa dakin ajiye magani a gidan tun da na jami ae ne kuma yaran an tanadar masu komai da zasu bu?ata saboda rayuwar kullece aka shirya masu.

Boss man kadai take da contact dinsa, awayarta, daukar wayar tayi dake ajiye on bedside drawer ta danna ma Boss kira, cikin sa a ya Waga kiran.

Cikin girmamawa ta gaishe da shi barka da asuba yalla6ai
On the other hand muryar boss ta amsa mata da cewa wa alaikum salam, ummi barka da safiya
 Yawwa barka, Allah yasa dai ban katse maka baccinka ba

 Kada ki damu, idona biyu yanzu nake shirin zuwa cikin gidan, ko akwai wani abu da kike bu?ata ?

 Taimako nakeso kayi min in ba takura, maganin mura nake bu?ata

 Wanene ke baida lafiya ? Da sauri tace nice zan sha, Yaran dake atare dani lafiyarsu ?alau amsa mata yai da okey, idan zan shigo gidan zan taho maki da shi

 Nagode katse kiran tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, Batul dake a ?umshe cikin bargo, abun duniya ya isheta.

Muryarta shake tace aunty ummi banyi sallar asubaba, kuma ina jin yunwa
Guntun tsoki ummi taja kiyi min shiru malama, ni ma ai banyi sallar ba, kuma ina jin yunwar bawai bana ji ba

Ta fada Tare da samun wuri daga gefen gadon ta zauna tana gadin Batul, hannunta ru?e da wayarta, chatting ta kama yi, batul tayi shiru cikin bargo tana faman matse ?walla.




A katafaren Villa Mallakin Hateem Obinna, haddadiyar daula kuma aljannar duniya wadda idan ka zura ?afarka acikinsa sai ka yi tsammanin ?asar dubai ka shiga, Hamsha?in Gidanshi a kewaye yake da Jami ae sojoji da ?an sanda, mugun tsaro ake yi mashi, babu wanda ya isa ya ?etare gidan hateem cikin sau?i idan ba Mahaifinsa ba da yayyansa, amma bayan wadanda kafin mutun ya samu iznin shiga ciki sai ya ci ba?ar wahala don kuwa daga ?asa har sama zasu bincike ka da na ura, har ?wara mutun ya shiga masarauta yafi mashi sauki, akan Gidan prime minister, tsaruwar ginin gidan kuwa da haduwarshi ba a magana, gaba Waya Obie estate babu gidan da yakai Na prime minister In ka cire Villah din Owais.


*Gimbiya Mujeedat=?Q?*



A kishingiWe take saman Katafaran gadonta na alfarma, kalar na sarakuna waWanda suka gaji Arzi?i, gadon a kewaye yake da labulaye launin royal blue, an ?awata shi da lallausan zanen gado fari ?yal, haWi da matassan kai launin blue and white, gefe da gefen gadon bedside drawers ne suma launin royal blue, daga saman su Fitilune masu bada haske launi daban daban, an zuba mata tsadaddun furniture a Wakinta, ya ?awatasu sosai da kayan alatu.

ta Waura kanta saman pillow, Rigar dake a jikinta Silk robe ce launin ice blue, tabi shape dinta ta bayyana dirarran dirin jikinta, A halitta Gimbiya Mujeedat doguwace, fara sol tana da dogon wuya, hutu ya zauna mata ta ko ina Allah Ya hore mata, Kyau kamar ita ta zana kanta, fararen idanuwanta tamkar an Wiga masu zaiba, launinsu dark black ne, ga tarin ziraran eye lashes dinta da suka ?awata kewayen idanuwanta sun yi mashi rumfa, dogon hacinta a tsaye yake babu lan?wasa, siraran la66anta launin ja tamkar na jarirai tsabar ?arantarsu da laushin fatarsu, tana da yalwatacciyar sumar kai ba?a wulik mai santsi da silbi, har gadon bayanta, Tabarakallahu ahsanul khalilin Gimbiya mujeedat ma?urace afagen kyau, uwa uba ta fito daga tsatson masarautar daular larabawa, bugu da ?ari First Lady ta ?asar Canada, ajin farko ce ita, zan iya cewa baba Hateem Ya more mata =? ?

Ziririyar sar?ar wuyanta ta zallar diamond ce, haka zalika Ziraran yatsun hannunta na dama suna sanye da Ring set na Gold komai nata me tsadane ita kanta lu u lu un ce.

Yanayin yadda ta kwanta da alamun kasala atattare da ita, ta Wan lumshe idanuwanta, fuskarta sam babu walwala, kamar akwai wani abu dake damunta.

A lokacin da bata yi tsammani ba, muryar prime minister Hateem ta karaWe kunnuwanta, sallama ce yai mata yayin da yake shigowa dakin, Cikin shiga ta jallabiya launin maroon, daddaWan ?amshin turarenta dana ?amshin turaren wuta ne Ya daki hancinsa Har saida Ya lumshe idanuwanshi, mutunne shi ma aboci son ?amshi, sai kuma Allah Ya haWa shi da mace ma abociya son kamshi da son ado, shiyasa a kullum take ?ara shiga ranshi, soyayyarsu bata tsufa, Idan suna atare da juna daukar kansu suke Yi tamkar sabbin ma aurata.


Bata samu damar amsa mashi sallamar shi ba, da?yar ta iya buWe idanuwanta da sukayi mata nauyi, launinsu ya rikiWa zuwa ja, saboda rashin baccin da batayi ba adaren jiya kuma shine sila, Ya hanata sukuni, bai ta6a burkice mata ba irin Na jiya, ?iri ?iri Ya takura kanshi, Ya hana kanshi runtsawa, kuma yaki fada mata abun da ke damun shi, daga ita har shi jiya babu wanda ya runtsa, saboda ta maida damuwarshi tata.


Koda ya shigo dakin, a hankali ya daura idanuwanshi kan fuskarta, sai yaji ba daWi har cikin zuciyarshi yasan bai kyauta mata ba, tunda ya riga da yasan halinta na damuwa da damuwarshi.

Daga gaban gadon Ya dakata dayin tafiyar, ya goya hannayenshi on his broad chest yana fuskantarta.

Ba zato ba tsammani, yaga ta galla mashi harara haWi da murguWa mashi ?aramin bakinta.

Nan take ya fahimci fushi take yi da shi, ranta ya 6aci.
Cikin harshen turanci tace Sannu da dawowa

Ta inda gimbiya mujeedat take burge shi, duk mun fushin da zatayi dashi hakan bai hanata kula da shi

 Yawwa, fatan na same ki lafiya

Yamutsa fuska tayi fuskarta babu annuri ta soma magana tamkar bata son furtata.

 Mijina baka kyauta min ba, ka hana kanka runtsawa nima kuma ka hanani runtsawa, nayi ko?arin faranta maka duk don na kawar maka da damuwarka amma babu abunda ya canza, Ka jefa ni cikin wani hali daga daren Jiya zuwa yau, meyasa ba zaka fadamin meke damunka ba? Ko ban isa nayi maka magani bane? Nasan ka yarda dani, sannan baka 6oye min komai, sirrinka nawa ne amma meyasa jiya ka?i fadamin damuwarka sautin muryarta tamkar ana busa sarewa tsabar daWinta.

Idanuwanta aruntse take yi mashi magana, don ta fahimci idan tana kallon cikin idanuwanshi bazata samu ?warin gwiwar yi mashi magana ba

Sauke hannayenshi yai daga saman kirjinshi, ya zagayo ta gefen da take a kwance Ya zauna, yana duban fuskarta
?ayataccen murnushine kwance kan la66ansa, yasan ta kan mace, idan ranta ya 6aci cikin sau?i yake faranta mata

 Uwar gida sarautar mata, Gimbiyata, Ina neman afwarki ranki shi daWe, bai kamata gimbiya tana fushi da bawanta ba, Ni fa a karkashin inuwarki nake, da taimakonki nake samun natsuwa da kwanciyar hankali, taya zanso na 6ata maki rai? Bayan kece linzamin dake sarrafa ni....
Tun da yafara gaya mata daWaWan kalamansa, ta fara sassauta fushin fuskarta,
A hankali ta buWe idanuwanta kan fuskarshi, da sauri ya kama kunnuwansa Yana fadin Am sorry My wife, na gane kuskurena
Ta6e mashi baki tayi Ni so nake ka fadamin meke damunka? Da har yai silar hanaka runtsawa, kalli fuskarka duk ta yamutse, idanuwanka sun ?an?ance saboda rashin baccin da baka yi ba ta faWa tana faman 6ata fuska, yayi shiru yana kallonta batare daya furta mata komai ba.

 Kai nake sauraro! Meke damunka? Sannan naji kana waya Wazu, akan za a tura da jet zuwa sudan, wa za a Wauko ? Ta jefa mashi tambayar cike da son jin amsar shi.

Ya rasa amsar da zai bata, Ta kafe shi da ido.
Gyara muryarsa yadanyi kafin yafara magana a tsanake.

 Sheikh imam nake son gani, baya a ?asarne ya tafi sudan, Ina bu?atar ganinsa da gaggawa akwai taimakon da zaiyi mani

Fuskarta da alamun mamaki ta furta meyasa kake son ganin shi? Wani kalar taimako zaiyi maka

 Wani matashin yarone yake fama da aljanu sun hana rayuwarshi sakat, jiya ina zaune tare da baba muna yin firar yaushe rabo, a lokacin da bamuyi tsammani ba, yaron ya faWo falon gwanin ban tausayi, duk mai imani idan yaji irin jarabtar da yaron yake fuskanta sai ya tausaya mashi..... tun da ya fara magana gimbiya mujeedat ta yun?ura ta mi?e daga zaune tana dubanshi, Ya fayyace mata komai sai dai bai faWa mata da suffar da ya ga yaron ba.

 Na yanke shawarar yin magana da sheikh Imam akan halin da yaron yake aciki, Ina da tabbacin zai taimaka mashi In sha allah, yanzu haka da nake yi maki magana, sheikh imam Yana akan hanya, Ina tsammanin nan da ?arfe goma jirgin daya Wauko shi zai yi sauka a nigeria.

Yanayin fuskartane Ya canza, yayin da take kallonshi, Ya rasa gane kallon menene take yi mashi, har dai yagaza jurewa jin shirun yayi yawa yace baki fahimci abunda nake fadi bane? Ko bakiji dadi bane ?
Girgiza mashi kai tayi ko Waya mijina, wani abune yadan bani mamaki, nasan halinka ne yin taimako, indai abune daya shafi aikin Allah kana akan gaba, amma tunda nake arayuwata ban ta6a ganin tausayi da ya kai wannan ba atare dakai, saboda yaron jiya ba ka yi bacci ba, aduk lokacin da ka dawo gida a yanayi na damu nasan yadda zan shawo kanka in kwantar maka da hankalinta harma kayi bacci, amma adaren jiya saboda damuwar halin da yaron yake, waWannan dabarun nawa basuyi maka aiki ba, bayan haka ka tura da jirgin da zai dauko malamin da zai duba shi daga Sudan zuwa Nigeria, saboda kana bu?atarshi da gaggawa don ya duba yaron.... ta faWa fuskarta da alamun ruWani, yayin da Hateem ya natsu yana sauraronta abunda bata sani ba ayanzun ma da take yi mashi magana hankalin shi yafi karkata kan agogon dake sanye a wrist din hannun shi, burinshi goma ta buga.

 Abunda yafi Waure min kai mijina, wanene yaron? Menene ala?arka da shi? Yanayin yadda ka nuna damuwa akanshi ko Wan cikin ka sai haka


Jim ya Wanyi kafin ya furta bani da ala?a da shi, bansan shi ba! Kuma ban ta6a ganin shi ba, kamar yadda na faWa maki adaren Jiya idanuwana suka fara yin tozali da shi, tun daganan sai naji ?aunarsa ta kama ni, har naji ina son na taimaka mashi, sai nake jima kamar nike da alhakin ciwon shi, idan har ban taimaka mashi yaji sau?i ba Allah zai iya kamani da laifin ?in tallafa masa da banyi ba

Murmushin gefen fuska Gimbiya mujeedat ta sakar mashi har fararen hakoranta suka bayyana.

 Kai din na dabanne mijina ta faWa tana matsawa kusa dashi, ta Waura hannunta na dama saman sumar kanshi.

 Samun miji kamarka a duniyar nan abune mai wuya, kana da tausayi da jin?an na ?asa dakaina, sannan kowa naka ne, burinka ka faranta ma wanda yake acikin kunci koda ta silar hakan kai zaka rasa naka farin cikin, ni kaina ina ilmantuwa da kyawawan Wabi unka da halayanka, shiyasa nake alfaharin mallakarka da nayi a matsayin mijina lumshe idanuwanshi ya Wanyi kalamanta ba ?aramin faranta mashi suke Yi ba, tamkar tana ?arfafa mashi gwiwane.

Zame hannunta tayi daga kan sumar shi zuwa gefen fuskarshi idanuwansu cikin na juna
 Kamar yadda ka sani, duk abunda kakeso nima inason shi, koda bana son shi saina yi kokarin koya ma kaina yadda zanso shi saboda mijina yana son shi, don haka nima ina goyan bayanka akan Yaron, Allah ya baka sa a mijina ya cika maka burinka na ganin yaron ya samu lafiya, A shirye nake dana bada gudummuwata wurin ganin mun inganta rayuwarshi
Murmushine ya bayyana akan fuskar prime minister, kallonta kadai da yake yi natsuwa yake samu, musamman idan tana ?arfafa mashi gwiwa da daWaWan kalamanta.
 In sha Allah zamuyi nasara, yaushe zaka bani iznin zuwa ganin yaron ?

 Na yanke shawara idan yaji sau?i, zan gayyace shi zuwa gidan mu, zamu shirya mashi dinner.

Tsantsar farin cikine akan fuskarta naji dadin jin hakan mijina, wallahi har na ?osa naganshi, duk na kagu gashi bazamu daWe a ?asar ba, kwanaki kadan suka rage mana ta fada tana 6ata fuska alamar bataso hakan ba.
Dam?o hannunta yai da take kokarin shafa wuyanshi, fari sol dashi, ga wani shu umin kamshi dake fita sako da lungu na jikinta, sumbatar tafin hannu yai, ba tare da ya sake shi ba ya dago da reddish eyes dinshi akan fuskarta yaron marayane bashi da kowa, Owais ne ke kula da su, zan nemi alfarmar yabar min shi mu tafi canada atare, inaso ya maye min gurbin abunda narasa sai yanzu ta fahimci damuwarshi.

Tausayinshi ne ya kamata, tuntuni tasan yana da burin samun Wa Namiji, yaso ta ?ara haifa mashi ?a ?a sai dai shiru babu alamun zasu sake samun ?aruwa, kuma lafiyarta ?alau saboda shi yasa bata yin tsarin Iyali, Allah ne bai nufa zata ?ara haihuwar ba.

Kafin ta buWe baki tayi mashi magana, wayarsa dake ajiye cikin aljihun shi ta soma yin ringing, ya riga da yasan wanene Ya kirashi.
Da sauri Ya saki hannun Gimbiyarsa, Ya zura hannu ya zaro wayar picking call din yai tare da karata a kunnanshi, gimbiya mujeedat ta kura mashi ido tana kallon shi
 Alhamdulillah, Allah ya kawo ku lafiya, iya abun da taji ya furta kenan, zame wayar yai daga kunnanshi yana dubanta yace sun sauka lafiya
Gimbiya mujeedat tace shiyasa naga farin ciki akan fuskarka, sheik imam ya?araso kenan, bari nayi magana da masu aiki su shirya maku breakfast dinku
Ta fada tana kokarin daukar phone dake ajiye on nightstand da sauri ya ru?o hannunta, ta dago da ido suka kalli juna
 An shirya mashi breakfast dinshi, tun acikin jirgi, ina da tabbacin babu yunwa ko gajiya atare da shi, nafi bu?atar idan ya ?araso mu tafi gidan Owais din
 Amma kaifa? Baka ci komai ba, Yakamata kayi breakfast dinka, zaka fi samun kuzari
Girgiza mata kai yai Bana bu?ata, saboda bani da natsuwar cin abinci, Idan har yaron nan bai dawo dai dai ba, nafi son idan Ya samu sau?i, muci abincin atare da shi
Tsantsar mamakin kalamansa ne ya daure mata kai, bata ta6a ganin ?auna kalar wannan ba, Ko a shirin film.

 Amma kasan bana iya yin breakfast ba atare dakai ba, idan har baka ci ba, nima bazan ci komai ba, har sai ka dawo gidan cikin tausasa harshe tayi maganar.

 Yau kawai, Kiyi hakuri kiyi breakfast tare da su Yazrin, bazan jima ba, in sha Allah atare zamu yi lunch dinmu

Kwa6e mashi fuska tayi hadi da marairaice mashi tamkar zatayi mashi shagwa6a ta furta bazan takura maka ba, Na kar6i uzurinka

 Ki tashi ki shirya inaso ku gaisa da shekh imam kafin mu wuce gidan owais amsa mashi tayi da toh, kafin ta sauko daga saman gadon, shima ya mi?e yana bin bayanta da kallo, har ta 6ace ma ganinsa, jim kadan ta fito sanye da Abaya launin Maroon tayi rolling mayafi akanta, ru?o hannunta yai acikin nashi, suka nufi kofar fita daga dakin.
Lokacin da suka shigo babban katafaren palourn gidan, masu yi masu hidimane suke ta gudanar da aikace aikacen su, kowan nan su sanye da uniform ba?in wando da farar shirt, matasan ?an mata, duk inda Suka gifta jiki na 6ari suke gaishe dasu cikin girmamawa, yayin da su kuma suke amsa masu da fara a.

Yanke shawarar zuwa bedrooms din ?a ?an su suka Yi, kafin ?arasowar Ya sheikh, Yana da bu?atar suma su kasance cikin shiri donsu yi mashi kyakkyawar tarba.

elevator suka hau ta daukesu zuwa upstairs, bayan ta sauke su suka fito batare da sun saki hannayensu da suka ru?e acikin na juna ba, kaitsaye suka nufi bedroom din ?an matan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login