Showing 162001 words to 165000 words out of 260999 words

Chapter 55 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

iko akan Yayanshi? Waye ya dace yazo gidan wani? Almost 16years yarinya ta 6ace sai Jiya ta dawo ?arfe sha biyu na dare ko kaWan bai nuna danuwarshi ba, kuma babu alamun zai je ya taya yayanshi murnar ganin yarsu da suka yi?
Muryarta na rawa ta furta am..amma hakan bai dace ba, nayi mamaki daka furta wannan maganar, kodai baka ji abunda shureim Yake faWi bane? ?ar wurin Yayanka benazir ce data 6ace tsawon shekaru ta dawo gida a daren jiya ?arfe goma sha biyu na dare Yakama ka tashi ka shirya mu tafi da buWar bakinshi sai cewa yai Umarni kike bani ? Da ?arfin hali Ta furta A a kawai ina ?o?arin faWa maka abunda Ya dace ne tamkar zaki Haka ya yun?ura ya mi?e Ya dubi fuskar shureim da mamaki Ya gama kamashi
 Nace bazaka je jos ba, ka koma Waki ka zauna, zansa Iyayen naka su zo tare da ?ar uwar taka abuja gyaWa kai dr shureim yayi jiki amace yace toh uncle, na hakura, zan jira su zo Win ?walla ce ta ciko idanuwanshi da sauri Ya juya ya fuce daga dakin.
Bayan fitarshi Alhaji musa Ya nuna Hajiya sarah da Yatsan hannunshi koda gigin wasa kada ki kuskura ki ?ara shiga tsakanina da shureim idan muna magana, abune da ya shafeni da dangina banaki ba, don haka ki kiyaye yana gama fadin hakan a fusace yakai hannu ya yago tissue ya goge bakinsa ya nufi cikin dakin.
Jiki asanyaye hajiya sarah ta zauna saman sofa din, lamarin Ya Waure mata kai, wannan rashin adalcin har ina? Meyasa zai dinga iko da yayanshi? Ko dan Yana da dukiya ne? girgiza kai tayi ahankali ta furta wannan ba adalci bane ta faWa haWi da mi?ewa ta nufi hanyar fita daga Wakin.
Bawan Allah dr shureim abun duniya ya isheshi, Uncle musa Ya bashi mamaki, bai ta6a jin haushinshi ba sai yau daya nuna ?arfin iko akan iyayenshi, Ya fahimci ma bai damu da dawowar benazir ba saboda babu annuri akan fuskarshi duk da yasan halin shi ne hakan, amma yaji Waci aranshi, don me zai dinga juya mahaifinshi son ranshi bayan shine agaba dashi, ko a shekaru Alhaji ubaid Ya zarce Alhaji musa nesa ba kusa ba saboda shi ba wasu shekaru gare shi ba, shiyasa ko a jam iyarsu ake kiranshi da ?araminsu babbansu. Abun ya Waurewa Dr. Shureim kai, har ya fara tunani kodan Yana da dukiyane shiyasa yake sarrafa kowa yadda yake so? In banda rashin ta ido har zai Iya buWe baki yace zai kira iyayan nashi suzo abuja maimakon shi ya tattara iyalansa suje can jos din su tayasu murnar dawowar ?ar su, Anya kuwa Uncle musa bai fara shan ?waya ba ? Sa?e sa?e zuciyar shureim take Yi mashi hakanan ya samu kanshi da kokwanton uncle din nasa.
 Shureim dan Allah ka yi hakuri da abunda uncle dinka Ya faWa maka, wallahi banji daWi ba, bai kyauta ba, wannan ai ba adalci bane, bansan meyasa yake yin haka ba
Muryar Hajiya sarah ce ta katse mashi zancen zucin nashi, har ya kusa shiga Wakin shi Ya ci burki tare da Juyowa baya yana dubanta
Damuwace ?arara akan fuskarta, kamar yadda shima tashi fuskar damuwarce
Murmushin ya?e ya ?a?alo akan fuskarshi da karyayyar murya ya furta kada hakan ya dame ki mommy, da ace bansan halin uncle din nawa bane, amma nasani, shiyasa nake yi mashi uziri, bakomai zan jira su zo din kamar yadda ya fada
GyaWa kai hajiya sarah tayi har cikin ranta bataji daWin abin daya faru ba
 Bari na kira maka zeenatu, nasan zata Webe maka kewa, kafin isowarsu still da murmushi akan fuskarshi Yace toh, zan jirata
Bayan tafiyarta, Ya shiga dakin shi, asaman gado ya jefar da key din hannun shi, Ya tu6e arab tur6an dinsa Ya jefar saman gado, Ya zauna daga gefe hannu bibbiyu ya zabga uban ta gumi takaici Ya ishe shi, mahaifinshi Yafi 6ata mashi rai saboda shine silar komai, da ace tun farko bai bari uncle musa ya raina shi ba da duk hakan bata faru ba.
Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar Zeenatu ta katse shi
 Yaya shureim Wina a hanzarce ya Wago da ido yana dubanta, ta zumbula dogon hajibi har ?asa Yake ja, ta ru?o round plate mai Wauke da mug, sai faman sakar mashi murmushi take yi, kwata kwata babu natsuwa atattare da ita, kafin shigowarta Wakin mommynta ta faWa mata xancen ganin benazir shiyasa take ta yin farin ciki, ita fa tun da take bata ta6a ganin benazir ba a hoto kaWai tasanta saboda kafin guduwar benazir tana ?ar jinjirarta.
Ganin yadda take tafiya babu natsuwa yasa shin saurin motsa la66ansa da niyar ya dakata da ita, sai dai ina kafin yai yun?urin yin hakan tuni tayi tuntu6e da takalmanshi daya cire a tsakar Wakin, Mugs din data dauko yai tsalle sama Ya dira daman ?afarta ruwan coffee mai zafi Ya Walli ?afarta, zafin da tajine yasa ta jefar da plate din hannunta, ta du?e saman floor tana kuka, da sauri Ya mi?e ya ?arasa gabanta, ya zu?unna tare da kai hannu ya dam?i ?afafuwanta Ya soma tottofe su da addu o i, ta dage sai kuka take yi mashi, abunka ga farar fata wurin da ruwan coffeen Ya ta6a yayi jawur kamar zai fashe.
Kukanta duk Ya cika mashi kunnuwanshi, a hankali ya Wago Yana dubanta, hawaye sun wanke fuskarta, lokaci Waya ya soma tariyo sambatun benazir tuni yaji jikinshi yai sanyi, ha?i?a Yana matu?ar tausayin rayuwar ?a mace, fuskar benazir ce ta dinga yi mashi gizo akan fuskar zeenatu, har baisan sa adda Ya rungume ta a kirjinshi Ya zagoya da hannanyeshi saman bayanta, Yana Wan bubbuga shi cikin sigar lallashi, ?an?ameshi zeenatu tayi kamar zata koma cikin cikinsa, daddaWan ?amshin turarenshi ba ?aramin kashe mata jiki yayi ba, tuni ta haWiye kukan da take yi, tayi kwance abunta sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, dr. Shureim sam ya manta dawa ya rungume a jikinshi, kewar benazir duk ta addabe shi, Ya jefa zeenatu cikin yanayi najin shau?in shi, yayin da shi hankalinshi nacan wani wurin daban...............

Idan muka koma 6angaren zahra, tun wuraren ?arfe shidda Mahboob Ya shigo mata da jakar kuWin motarta da wayar da aka saida mata, shaf shaf ta shirya cikin jallabiya ta yafa mayafi akanta, tace da mahboob ya taimaka ya kaita gidan Hajiya falmata, yace zai kaita amma bisa sharadin zata bashi nashi kason, tunda ai yayi mata ?okari, a lokacin ta?agara da taje tace mashi ta amince su tafi kawai, kafin su bar gidan saida ta fara cire miliyan Waya ta ajiye su cikin drawer, ya rage saura 3m dai dai kuWin da zata bata.
Tana zaune a back seat na motar mahboob, yayin da shi kuma yake zaune a mazaunin driver, a tsanake yake yin driving har Allah Ya kawo su gidan Hajiya falmata.
A parking space mahboob yai parking din motar yace da ita ta shiga yana jiranta, ta amsa mashi da toh, ta buWe motar ta fito ta nufi ?ofar shiga babban falon gidan
Murmushin gefen fuska Mahboob ya dan saki yayin da yake bin Bayan zahra da kallo, ya zuro ?afarshi daga cikin motar daya bar murfinta abuWe
Wayarshi ce tayi ringing daga cikin aljihu da sauri Ya zura hannu ya duba mai kiranshi sunan Aunty Aneelerh ne Ya bayyana
Picking call din yai ya kara wayar a kunne Babbar yayanmu, mun karaso gidan fa, Yau zahra zata sha mamaki, wallahi bakiga yadda take ta zubda uban gumi ba, kamar wadda tayi ma sarki ?arya fadawa suka kamo ta tuntsirewa yayi da dariya,
Muryar Aneelerh da sautin dariya tace baiwar Allah, ina fata yau hankalinta zai kwanta, naji daWi da nasarar da muka samu, ubangiji Allah Ya ?ara tsare mata ita ya amsa mata da ameen

Ta kuma cewa Idan kuka dawo gida, ka faWa mata cewa motarta da wayarta jingina ka bada su, idan tanaso ta baka kuWin za a dawo mata da su, sannan please bana so tasan cewa jiya munje gidan hajiya falmata, ya amsa mata da toh, daga haka sukayi sallamar.

Tun da zahra ta shiga gidan, takasa zama, tana a tsaye tana jiran fitowar hajiya falmata don ta mi?a mata kuWinta, mai aikin gidan ce ta fito daga part din dakin nata ta dubi zahra ki zauna mana gatanan fitowa galla mata harara zahra tayi ba zama nazo yi ba murmushi mai aikin tasaki kafin ta wuce ta nufi kitchen
Jim kaWan, Hajiya falmata ta sauko down stairs, sleeping dress ne a jikinta riga da wando ta yafa mayafi akanta.
Fuskarta babu walwala ta dubi zahra zauna mana tayi maganar tana nuna mata sofa
Harara zahra ta watsa mata ba zama nazo yi ba, kuWinki na kawo maki tayi maganar a fadace ta ajiye mata jakar gaban kujerar da take a zaune
Har ta juya zata fita muryar hajiya falmata ta katse mata hanzarinta
 Zahra! Dan Allah ki zauna inaso muyi magana badan halina ba
Batayi mata gardama ba tace dan kin haWani da Allah, shiyasa zan zauna badan haka ba wallahi ko kallo baki ishe ni ba murmushi hajiya falmata tasaki.
Bayan zahra ta zauna tana faman haWe rai tace ina sauraronki sauri nake yi in tafi
 Nasan zakiyi mamaki zahra, kuma ba lallai ki yarda da abunda zan faWa maki ba, abunda Ya faru a tsakanina dake badagaske bane, jarabaki nayi saboda wani dalili nawa.... da mamaki zahra take dubanta, jinjina kai hajiya falmata tayi tabbas ba halina bane, nayi ?o?arin jan ra ayinki ne don insan dawa ?ata take tarayya
Tunkan ta kare maganar zahra tasaki dariyar rainin wayau tana fadin dallah malama dakata! Banason zancen banza, harni zaki raina ma wayau? Ki gama zubda mutuncinki agabana kuma ki dawo kina fadin jarabani kikayi akan me kenan? A tsiwace ta furta hakan
Numfasawa hajiya falmata tayi zahra dalilin dayasa nayi maki hakan, Mun samu sabani nida wata aminiyata hajiya naja at akan ?arta dake bin mata, ta la?afa mun sharrin cewa ?ata fatima ce ta koya mata, saboda ita kaWaice suke tarayya, sannan ita taba yarta tarbiya tasan bazata ta6a aikata hakan ba, faWa sosai mukayi da ita, ta zageni taci mutuncina, damuwar duniya ta isheni, lokacin dana dawo gida narasa ya zanyi in tuhumi fatima saboda nima ina tsoron ace ?ata tana aikata kalar abunda Yarinyar aminiyartawa take yi, nasan zaiyi wuya fatima ta faWa min gaskiya, kinji dalilin dayasa na yanke shawarar yi maki hakan saboda nasan ke kaWaice aminiyar fatima, duk wani abu da zatayi saida shawararki, atare kuke yin komai, Ni a tunanina ta hanyar dana 6ullo maki zan samu abunda nake nema na gano abunda ?ata take aikawata ashe ba haka bane nayi babban kuskure zahra, dan Allah Ki yafe min fashewa tayi da kuka hawaye nabin fuskarta, baiwar Allah zahra tuni zuciyarta ta karya, sam bata kawo komai aranta ba, ta yadda da kalaman hajiya falmata, cikin shesshe?ar kuka tace Amma meyasa zaki yi jarabawar dani? Kin hanani bacci kin hanani cin abinci, kin jefa rayuwata cikin matsanancin tashin hankali, babban abun takaicina shine karya min zuciya da kikayi saboda na Wauke ki tamkar mahaifiyata ina ganin girmanki, ashe dama duk plan ne kika shirya min ?
Hajiya falmata na matsar ?walla tace kiyi hakuri zahra nasan ban kyauta maki ba, dan Allah ki rufe min asiri kada kowa Yaji maganar nan, saboda banaso ayi tsammanin nima ina aikatawa ne sannan, maganar kuWin da nake binku ni tuntuni na yafe maku, wallahi na bar maku su babu abunda zanyi dasu, sannan maganar yin order na kaya daga dubai in sha Allah gobe zasu iso Nigeria, inaso kuci gaba da gudanar da aikinku a companyna ke da fatima, don bazanso in rasa mace mai nagarta da tawakkali irinki ba, komai kuke so zanyi maku zahra, ni dai fatana ki manta da duk wani abu daya faru a tsakanina dake, Ki cigaba da daukata tamkar mahaifiyarki
Rushewa zahra tayi da kuka, kamar ranta zai fita, bata ta6a tsammanin komai zai zo mata da sau?i ba, harta fidda ran cigaba da aiki a companynsu da kuma damar zuwa obie estate ashe da rabon mafarkin ta ya zama gaskiya.
Cikin shesshe?ar kuka tace In sha Allah mommy babu wanda zaiji maganar nan, komai Ya wuce amma dan Allah kada ki ?ara yi min wasan nan, ni kaWai nasan raWaWin da naji acikin zuciyata
Jinjina kai hajiya falmata tayi da karyayyar murya tace bazan ?araba zahra, nima nayi danasani, dan Allah ki tsaya mu yi breakfast atare kada kice zaki tafiya
Zahra tace sauri nake yi wata rana zan dawo, Ina fatima take ? Hajiya falmata tace bata nan, jiya ta tafi gidan uncle dinta amma yau zata dawo saboda aikin da zakuyi tare murmushin farin cikine Ya bayyana akan fuskar Zahra, sai faman washe bake takeyi harta fara tunanin irin rashin mutuncin da zatayi ma Aneelerh idan ta koma gida,
Godiya sosai hajiya falmata tayi mata, itama zahra tayi mata godiya da fara a suka rabu.
Ta ru?o jakar kuWinta a hannu, tana fitowa daga falon da gudu ta nufi motar mahboob tana dariya haWi da yin rawa tana jujjuya,
Mahboob tamkar baisan komai yace zahra kin haukace ne? Lafiya kike dariya kamar wadda ta zauce ga hawaye akan fuskarki da sauri ta share hawayen da gyalen jallabiyarta
Tace dashi bro ka tayani murna yau ina cikin farin ciki, amma fa kada ka tambayeni meyasani shiga yanayin nan
Mahboob na murmushi yace shakuruminki aini ba Wan jarida bane da zan tsareki da tambaya, Yanzu dai shiga mota muje gida muyi magana akan ha??ina,
Da farin ciki tace ai mahboob kamar yadda Allah Ya rufa min asiri kaima zan rufa maka asiri, kai dai muje gidan ta faWa haWi da shiga motar, ya tada suka nufi Hanyar komawa gida.



*EX-PRISONERS>?s?*

*At abuja Nigeria=???*


Alhamdulillah Matafiya sun samu damar sauka Lafiya basu wayi gari ba sai acikin Katafaren Luxury Villa Mallakin Chief Owais sharafuddeen Obinna! haWaWWiyar Daular arz?i ce wadda zamu Iya kiranta da Aljannar duniya saboda Kayan alatun dake acikin ta, Katafaren gini ne mai girman gaske ta 6angaren tsayi da faWi Yana Wauke da Sassa Uku acikinsa, a Waya daga cikin Part din gidan aka yima Prisoners masaukinsu, A hankali nake bin ginin da kallo domin in ?arasa ga cikinsa, ta ko ina na kalla ?yal?yalin gilassai ne suke kashe min idona da kyawunsu, wasu irin haWaWWun floor-to-ceiling Glass windows ne masu mamaye bango, daga ?asa har sama glass ne, Kana Iya hangen Katafaren Main falo din dake acikin sashen ta glass windows din, Ga wasu sliding doors ?ofofi masu zuge kansu da zarar sun gama tantance mutun saboda gidan Yana da mugun tsaro ba iya mutane ba hada na urori ke sarrafa shi, ba za ka ta6a Iya ?etare Gingirimeman entry way din gidan ba tare da An tantance ka ba, daga ?asa har sama, bana tunanin ko aljani zai Iya shiga salin alin ba tare da na ura ta haska shi ba, salon kuma ace nayi karya (=??)

Dafa ?ofar glass din Nayi da hannuna Waya, Na ura ta tantance ni aka bani iznin shiga ciki, Slowly glass din Ya soma zugewa, Na baza ido ina kallon tsaruwar Falon da kallon shi kaWai zai Iya faranta zuciya, launukan painting cikinsa black, gold and white, An ?awata shi da manya manyan sectional Chersterfield sofas, saiti biyu ne a palourn, ?an ubansu masu numfashi masu tafshi da daWin zama ga jerin Throw pillows launuka daban daban saman kowace sofa, daga tsakiyar Katafaren falon wani faffaWan Glass table ne daga saman shi an Waura flowers Vase, Furannin har ?yalli suke Yi masu launi daban daban, bayan haka a kowani sofa hand din akwai Round glass table, mai dauke da kayan ?yale-?yale na ado, daga saman jigunan ceilling din falon wasu ?ayatattun Crystal chandeliers ne masu girman gaske, An ?awatasu da ado, kusan guda Uku ne a saman silin din, Haskensu Ya mamaye ko ina tamkar da rana, Idan ka kalle su sai ka yi tsammanin zasu rubzo maka saman kai, sobada girman su, ga wata faskekiyar flat screen tv wadda idan kana kallo da ita sai ka yi tsammanin mutanan ciki zasu fito waje saboda girmanta, Bayan sofas din falon akwai hamsha?an armchairs har guda biyu, hatta saman floor din falon Kayan adone aka Waura samansu, sparkling floor lamps ne ajiye a kasa suna bada nasu hasken mai ?yal?yali, akwai Kayan jin sauti, Ga Dogayen labulaye dake kewaye da falon an zuge su, A ?alla Part din Yana Wauke da Faluka sun kai Uku, bayan wanda na zayyana ma ku, daga cikin falon farko kana Iya hangen furniture din da ke a cikin falo na biyu ta hanyar Glass window, komai zaka Iya gani, Gidan fa Ya haWu Ga glass elevator gefen twins stairs din dake a falon, ta ko ina sanyayyan sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikin bil adama mai ni imar gaske, bayan haka ta cikin glass din falon zaka Iya hango Sashen da tan?ameman swimming pool din gidan Yake, ruwan dake acikinsa launin sky blue ne, da wasu kujerun sha?atawa a gefenshi, da sauran ababen more rayuwa, Idan muka koma Dining room wato Wakin cin abincin gidan abun ba a magana, shima a kewaye yake da floor-to-ceilling glass windows, kana Iya hangen abubuwan dake wakana daga wajen Wakin cin abincin, An ?awata shi da haWaWWun dining tables, na farko zungureren table ne mai mazaunin mutun goma sha biyu, da me mazaunin mutun shidda, da kuma tabur mai mazaunin mutun uku, kowan nan su saman shi an ?erashi da zallar glass, ?afafuwansu kuma wooden legs


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login