Showing 24001 words to 27000 words out of 260999 words

Chapter 9 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Sautin muryar matashiyar budurwa.

Nauyin bacci ya hana ta buWe idanuwanta sai ma ?ara ?udundune kanta da ta ke yi acikin lallausar bargonta, faWowa cikin Wakin ta yi Tabarakallahu ZankaWeWiyar budurwa jawur da ita, Jikinta na sanye da egyptian gown launin shuWi, Ta yi rolling veil akanta, Light make up ne akan fuskarta daga ganinta ba ?aramar wayayyi bace a jin farko, Takalman ?afarta high hills ne launi Waya da Mayafinta white colour, hannunta na dama na asanya da Tsadadden agogo silver colour. ?amshin turaren Jikin ta mai matu?ar sanyaya zuciya, wayar da ke a ru?e a hannunta ?irar i phone 15 pro ce.

Agogon bangon da ke a Wakin ta kalla ?arfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga ?wayar idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta Wanyi fuskarta Wauke da ?ayataccen murmushi tace Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje da zolaya ta yi maganar a yayin da take ?arasa shigewa Cikin bedroom Win, Cikin sanWa take tafiya tana tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, Waukar shi ta yi saboda mugunta ta ?ure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke ?ara nannaWe kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yun?urin buWe ido da sauri Zahra ta rage sanyin a.c ta ajiye remove Win saman drawer, ta ru?e qugu tana binta da kallo.

Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse, Tunkan ta buWe ido ta soma surfa masifa tana faWin junaid bana hana ka ?ara min sanyin a.c ba? Saboda ka raina min wayau ko?wlh idan ka bari na dam?i hannun ka sai ka gane ba ka da wayau, Sullu6iyo kawai...... Bata ?arasa maganar ba ta soma Jin sautin dariyar Zahra, hakan yasa ta yi saurin ware idanuwanta tare da wurga su kan fuskarta.

Gwalo ta yi mata tare da Waga mata gira tace Ba junaid bane yayar shi ce mai irin halin shi,  Harara Aneelerh ta shiga watsa mata kamar ?wayar idon zata faWo kasa.

Zahra tana dariya tace Iya hararar ne kawai idan mutun ya isa ya sanya hannu ya dake ni, kai da ka zo ba?unta gidan mutane ka ishe su da baccin lalaci..... bata samu damar ?arasa maganarta ba, Aneelerh ta rarumi pillow a zafafe da duro daga saman gadonta, zaro ido zahra ta yi kafin ta juya da gudu ta nufi ?ofa cikin rashin sa a ?afarta ta jirkice ta fasa ?ara zata kife ?asa da sauri Aneelerh ta janyota zuwa jikinta, sosai ta ?an?ameta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi ta firgita sosai.

 Rasa kunya 6eran tanka, Yanzu ga ki a hannuna, mai ?watarki yau sai Allah Kokoyi su ka soma Yi kamar ?ananun yara, Zahra sai ?walawa Umminta kira ta ke yi tana faWin tazo ta cece ta daga hannun Aunty aneelerh zata kashe mata ?arta, Aneeleh na dariya tace Nima ai ina da uwar sai in kirata tazo taga idon mara kunya ta ambaci hakan tare da ?walawa Maminta kira.

Sun sha?e junansu sai nishi su ke yi gyalen Zahta tuni ya jima da zamewa saman tiles, gashin kanta ba?i wulik anyi mata kitson kalaba ya sauko har kafaWarta.

 Aunty Aneelerh Am sorry wlh na mi?a wuya, zan maki biyayya na tufa bazan ?ara ba Azabar zafin da taji ne yasa ta furta mata hakan donta ?yale ta.

Sakinta Aneelerh ta yi don itama ta gaji da kokawar Sai haki ta ke yi, A nan ?asa suka zauna saman floor suna kallon juna.

 ?auko mun ruwa mai sanyi in sha harara zahra ta Wan jefa mata Baki da hannu ne ? Zaro ido Aneelerh ta yi tare da cewa bugun da nayi maki bai ishe ki ba Jin haka yasa zahra yin saurin mi?ewa hannunta Waya dafe da qugunta, Binta da kallo Aneelerh tayi fuskarta Wauke da murmushi fucewa tayi daga Cikin Wakin, after some minutes ta dawo hannunta Wauke da glass Win ruwa me sanyi, ta mi?a ma Aneelerh hannu tasa ta kar6a tare da kafa ruwan abakinta Kur6a uku tayi mashi ya ?are, Janye shi tayi daga bakinta tadan kalli zahra da ke tsaye tana gatsina mata hanci.

 Ki gama yi mini rashin kunyar ina nan ina jiran ki, in dai ni ce za ki zo ro?ona in faWa maki ?iyamil lailin da za ki yi don ki mallaki Zuciyar matashin saurayin nan da ki ka ?wallafa rai akan shi, meye ma sunan shi? tai tambayar tana kallon Zahra, Dariya ta saki tare da kai hannu ta kar6i glass cup din hannun aneelerh, Cikin kwarkwasa ta Juya ta nufi ?ofar fita daga Wakin tana faWin Heart beat of Obinna Murmushi Aneelerh tasaki tare da cewa Ehem shi nake nufi, zakiyi bayani ne bayan fitar zahra mi?ewa Aneelerh ta yi tare da juyawa har ta kusa shiga toilet Muryar zahra ta katse ta Bafa tafiya nayi ba, taimakon nan dai da aka saba aunty Aneelerh,  Juyawa aneelerh ta yi tare da kallonta, Fuskarta Wauke da murmushi.

Harara ta jefa mata ?ar wahala wanka zan shiga idan na fito zamu tattauna Zahra tace idan ma shekara za ki yi zan zauna in jira ki ta6e mata baki Aneelerh ta yi a yayin da ta ke shigewa cikin toilet taja ?ofa ta datse.

Daga gefen gadonta Zahra ta zauna tana jiran fitowarta, almost 15 mins Aneelerh ta buWe ?ofar toilet ta fito jikinta sanye da rigar wanka fara ?yal, ganin yadda zahra ta tsare ta da ido yasa ta murguWa mata baki  Tubarkallah Dariya Zahra ta sa ki kafin ta tsagaita da yin dariyar tace Masha Allah Iyayen mu sun Iya haihuwa girgiza kai Aneelerh ta Wanyi Allah ya shiryeki Zahra, Yanzu dai ta shi ki fuce zan sanya sutura, Ki jira Ni a palour  ma?e mata kafaWa zarah tayi Nifa ba ?aramar yarinya bace da zaki kore ni, Menene aciki don kin sanya kaya agabana, sai kace wani gardin ?ato Nima fa macace kamar ke komai ki ke dashi ina da..... Kafin ta ?arasa maganar Aneelerh ta nufeta da gudu Zarah ta bar Cikin Wakin tana dariya.

Kaitsaye ta nufi Cikin Hadadden palourn gidan mai girman gaske. Tun kan ta ?arasa ta hango mami da ummi zaune saman sofa suna fira, kowaccen su na sanye da atampha riga da zane ba ?aramin kyau su ka yi ba.

 Gani nan tafe kamar daga sama suka ji miryarta.

Atare suka Wago suna kallonta, mami tace yaushe kika dawo gidan ?

 Ban jima da shigowa ba, Na shiga Wakin Aunty Aneelerh ne, Na same ta kwance Tana bacci, Tai maganar a yayin da ta ke zama saman sofa mai mazaunin mutun Waya.

 Nasan kin kwaso gajiya, Tun asuba sai yanzu aka kammala aikin decoration Win, Kin ci abinci kuwa ? cikin Kulawa mami ta yi mata maganar, Fuskarta Wauke da murmushi tace mun aikatu Mami, Uban aiki kamar zamu shekara muna Yi, kinsan hidima idan akace maki ta Hamsha?an attajiran masu kuWine komai dagaske ake yin shi basu ?aramar harka, Mami zanso Kije Gidan nan zaki sha mamaki wlh, HaWaWWiyar Daular arzi?i ce.... tun kan Zahra ta rufe baki Ummi tace Ae Obie estate Aljannar Duniya ce Mai zaman kanta, Idan fa ki ka shiga gidan Sai ki rasa gane Awace ?asa kike, tsabar kayan alatun da ke a cikinsa, Yasin in mutun mai ?aramin Imani na rayuwa acikin tuni zai daina Sallah..... Dariya mami ta saki Yayin da take sauraron su, daga uwar har Wiyar gwanaye ne wurin Iya bada Labari.

 Aunty duk yadda zan kwatanta maki HaWuwar Kayan alatun dake acikin Estate Winsu Ba zaki Fahimta ba, Gani da ido yafi abaka Labari, Obinna family duniyace mai zaman Kanta, Ranar dana ta6a zura ?afa ta cikin gidan wlh Sai da gabana ya faWi, nace Anya ko Mutane suna tunanin duniya? Yo abu kamar baza a mutu ba, wannan ae sai mutun ya manta cewa da tur6aya aka halicce shi Dariya sosai Mami ta ke yi tana kallon Aunty Ummi da ke kora mata jawabi, Zahra ta Waura da cewa Ni wlh Naso Daddy ya sama mun Ko aikatau ne agidan su, tun ranar da naji Salary din masu aikin gidan da dollar ake biyan su, Ci da sha da suturarsu duka A kyauta ake yi masu, ai duk wanda Ya haWa ala?a Da Wan familyn Obinna kakar shi ta yanke sa?a, Shi da talauci sun raba Jaha.... in serious matter za a ta ke magana, Ummi taci gaba da cewa Shiyasa naso mahaifin ki ya kutsa ki cikin danginsu tun da dama Wan bangar siyasa ne, Ni ko wannan Yaron ne *DR JAZZ* kisamu ki aure shi, ko mun samu muma mu dangawali arzi?i ta ?arasa maganar tana dariya, tur6une fuska zahra tayi Jin abunda Ummi tace haba ummi, dr Jazz fa meye haka, Ni da na ke harin bugun zuciyar Family Win gaba Waya, Taya zaki haWa ni da yaron da har yau ba asan waye ubanshi ba acikin family Win da mamaki akan fuskar Mami tace kamar ya ba asan Ubanshi ba ? Zahra tace Waya daga Cikin ma aikatan gidan su ce tazo dashi aikatau, Matar ma farar fata ce, ba ki ga yaron ba kyakkyawa ga son mutane, ni bazan Iya auran mara asali ba, Ta ya Ummi zatai min fatan auranshi? Ga gwarazan samari a family din kyawawan gaske masu kama da kakansu Obinna.... tana magana tana turo baki.

Ummi tace Saboda nasan baza ki Iya samun wanda kike so ba, Haukan banza ki ke yi a kan shi, ke kin sani Ruwa ba sa an kwando bane, Babban Goro sai magogin ?arfe, Wutsiyar ra?umi tayi nesa da ?asa, In banda haWama irin ta zahra taya zaki nace wa mutumin da yafi ?arfin ki nesa ba kusa ba? Shiyasa nace ?wara Dr Jazz Win shine dai dai da ke, Waure fuska Zahra tayi jin abunda Umminta take faWi, ta haWe rai sosai, Muryarta a ?ule tace Mami kinga ni ko? Ita fa mahaifiyata ce amma bata min fatan naci ka burina, Kullum sai dai tayi discouraging Wina, meyasa ta ke yi min haka ne ? a bun ka ga me saurin kuka tuni idonta sun ciko tab da ?walla.

Fuskar mami Wauke da matashin murmushi ta soma magana a tsanake kwantar da hankalin ki zahra, Ai duk kyan takalmi ?afa ce ke taka shi, kuma idan Allah ya ?addara cewa shi Yaron wanda kikeso Mijin ki ne duk min mu?amin shi duk mun izzar shi da kyanshi wlh da kanshi zai nemo ki a duk inda ki ke, Ai shi so bashi a matsayin mutun, mai kuWi ko talaka Zahra kuma ta haWa komai da duk wani Wa namiji zaiso zama da ita a matsayin matarshi,... Tunda mamin Aneelerh ta soma magana zahra ta washe baki tana zabga uban murmushi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, Tsabar murna batasan sa adda ta sauko daga saman sofa Win da ta ke zaune ba, ta dawo ?asa saman carpet, Ta kafe mami ido tana kallonta kamar wadda ta samu Tashar Bolly wood, Hakan ba ?aramin dariya yaso ba Ummi ba, Ganin yadda zarah ta ke sakin murmushi jin ana yabanta.

 Mami ni ba ina kushe Zahra bane, Just bana so ta ?wallafa rai akan abunda ita kanta tasan bazata ta6a mallakarshi ba, Yakamata ta run?a tuna matsayinta, Mahaifinta fa Wan bangar siyasa ne ba wani shege ba, Ta ya ya ta ke tunanin zata Mallakin Hamsha?in mutun kamar *OWAIS SHARAFUDEEN OBINNA*!? Bazan iya lissafi ma matan da su ka yi hauka akanshi ba, Daga cikin hada ?iyar Chancellor na ?asar Germany bayan ita akwai ?ar sarkin saudi arab, Ga Wiyar shugaban ?asar America..... Lamarin ya Waure wa mami kai, Baki asake ta ke kallon Ummi sai da ta kai ?arshen maganar tukunna tace Ni ko zanso In ga wanene wannan Namijin hurul ainin, Farin Jini sai kace Wan gwal yo wannan koda lu u lu u aka ?era fatar Jikin shi sai haka, Dariya su ka saki gaba Wayan su.

 Saboda Farin Jinin da Allah ya yi mashi kakan shi Ya toshe duk wata ?ofa da za a Iya ganin shi, Zaiyi wuya ki samu hoton shi a social media, shahararre ne sosai babu inda ba asan shi ba, Da zarar kin ambaci sunan shi awuri sai an girgiza Ummi ce ta kora mata jawabi, Al ajabi Ya kama Mami Na ?osa Inji tarihin Family Winsu, Najima Ina jin zancensu abakin mutune da kuma labaransu a gidan radio, Nasan fuskokin Ya yanshi a tv sai dai bansan Komai dangane da su ba

Gyara zama Ummi ta yi Jinin Nasara shi ne sunan da akeyiwa family Winsu la?abi da shi saboda wadatar Arzi?in da Allah yayi masu, Suna Waya daga cikin Most richest family in the world, shahararru ne na bugawa A jarida, shi Obinna da ki ka ji ana faWi Kakan su ne tsohon Wan siyasa ne wanda yai gwagwarmaya ya ru?e mu?amai da dama tun daga ?asa Nigeria har zuwa ?asashen waje, Allah ya yi su da farin Jini, matan shi biyu a yadda naji labari, amma dukansu basa araye yanzu, shi kaWai ne ya rage, ?a ?an shi bakwai kaf Winsu suna ru?e da manyan mu?amai, su ke ru?e da ?asar nan, Manyan ?a ?an shi ?an Uku ne sune first born Win shi numsafawa Ummi tayi kafin ta soma zayyana mata sunayen su kamar haka.

 SENATE PRESIDENT LATEEF OBINNA, bayan shi akwai CHIEF OF ARMY STAFF SIR MUBARAK OBINNA, cikon Na ukun su shine HIS EXCELLENCY ABDUL RAZAK Obinna Gomnan Jihar Lagos, waWannan sune yan ukun shi, bayan su akwai ?annan su maza HIS EXCELLENCY DEEN OBINNA Gomnan Jihar kaduna state, mai bi mashi PRIME MINISTER HATEEM OBINNA Shugaban ?asar Canada Shi ne ya ke auran Gimbiya mujeedat ?ar Sarkin Dubai..... Tun da Ummi ta soma bata labarin Mami ta baza kunne tana sauraronta, ga dukkan alamu al ajabi ya kamata duba da yadda ta saki baki tana kallonta

 Bayan Hateem sai mai bi mashi SHARAFUDEEN OBINNA Current president na ?asar Nigeria, Adalin shugaba hawan shi mulki da wata biyar kacal ba a ?ara jin Wuriyar ?an ta adda ba Fuskarta Wauke da murmushi ta yi maganar Kada ki ji Ina yabon shi ya cancanta ne, matan shi biyu Uwar gidan shi Wiyar Sarkin Yarbawan Jihar lagos ce, Ta biyun kuma ?ar gidan Alhaji wada ce, ?anwar former Gomna na Jiharku Jos Murmusawa mami ta yi fuskarta da alamun mamaki tace Wai Alhaji Ubaid ki ke nufi surukin tajudden? Dama ?anwarshi ke auran Sharafuddeen ? Dariya ummi tayi haba dai kada ki ce min ba ki da masaniya, watsa hannu mami tayi taya za ae in sani? Ni da ba shisshige masu na ke yi ba, In banda ma abun ki ae bani da ala?a dasu da ya wuce ?awancen Benazir da Aneelerh, Makaranta ce ta haWa kuma Yanzu sun rabu, amma duk da haka Na yi mamaki,

Ummi tace Auran su shekara goma sha Waya kenan A lissafi na, kada ki yi tunanin ina sanya masu ido ne, Kinsan in mutun nada Arzi?i da Waukaka a kyauta ake bin diddigin shi.... ta ?arasa maganar tana dariya Mamin ma dariyar ta ke yi.

 Nasan zakiyi mamaki Idan na faWa maki cewa Duk irin wadatar Arzi?in dake gare su da Waukakarsu Basu da yawa family Winsu, Jikokin Obinna Goma sha Biyar A Wan ruWe mami tace kai! Wai dagaske ? Jinjina kai mami tayi ?warai kuwa, Saratu Obinna ce kaWai ta ke da ?a ?a Uku, twins zaid da zain sai autarsu Faryat Obinna, Na manta ma ban faWa maki ita a jerin ?a ?an shi ba, Saratu obinna Itace Autarsu, tana ru?e da mu?amin Minister of health Mijinta Pravin Obinna Wan ?asar india ne silar zuwanta karatun likitanci india Allah ya haWa ta dashi..... Ummi bata ?arasa maganar ba, Zahra tai saurin cewa Cin Arzi?i ya kawo shi, tsabar son banza mami ya canza sunan ubanshi ya maidashi na Obinna, Sai ki rasa gane Wa ne ko suruki a gidan tun da suka fara magana sai Yanzu ta tsoma masu baki hannunta ru?e da wayarta da alama chatting ta ke yi.

 To ke ina ruwanki zahra? Na rasa meya tsone maki ido da mutumin nan, ya fa riga daya zama Wan gida, yafi ?arfin a kira shi da suruki sai da Wa Ta6e baki zahra tai Haba Ummi haka ake surukuntaka, mutun ya tare a gidan surukai don kawai yana auran yar shi, nifa Pravin sam baya burgeni mutun kamar Wan ta adda mami sai kallonta take yi, ta fahinci bata ?aunar mutumin.

Ummi na ?o?arin buWe baki don ta yi magana Muryar Baby Junaid ta katse masu firar tasu.

Mommy! I m back! I really missed u, Na maki tsaraba Gaba Waya suka Wago suna kallon shi, shigowar shi kenan Cikin Falon Jikin shi sanye da suit Na yara Black colour, Madarar kyau, Ya ?ara girma ayanzu yana acikin shekara ta biyar a duniya. hannun shi na aru?e da Farar leda ta shopping, ba shi kaWai ya shigo palourn ba, Yana atare da Mahboob ?anin Zahra, Kamar su sak kamar tagwaye shi da ita, Crazy Jeans ne a jikin shi, daga sama Ya sanya farar t shirt, Sumar kanshi kwance luf tasha gyara, Mi?ewa zahra tayi da gudu ta nufi baby junaid tana ware mashi hannu don yazo ta rungume shi, tunkan ta ?araso ya girgiza mata kai Yana faWin Na mommy ne wlh, Wayo kike so ki min dan In Wan maki tsarabata Dariya suka saki,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login