Showing 126001 words to 129000 words out of 260999 words

Chapter 43 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

maganar tana hura mashi kiss.


 Yaro ne Commender ne yace haka,
Ummi tace Ai shi namiji baya kaWan, especially idan abunsa ya ru?a, a wurina wannan ba yaro bane Namiji ne murmushi suka saki, basu damu da abun da tace ba saboda sun san halinta, bata mu amala da matasan samari, Sai mazan da su ke da aure waWanda tasan idan ta bibiyesu za ayi bala i idan matansu suka kamata.


Bayan Ya wuce hoton Naufal Ya buWe mata hoton Gabriel, tunda ta kafe shi da ido bata ?yaftaba sai faman jinjina kanta take Yi alamar mamaki

Can dai ta numfasa tare da cewa Allah Ya yayi halitta, gaskiya idan aka bani rainon yaran nan tamkar kun ba kura ajiyar nama ne, major idan akwai wani hoton nuna mini na ?osa na ?arasa ganinsu

Lokacin da Major Ya hasko mata hoton Danish daga zaune ta zabura ta mi?e tsaye tana duban fuskarsa data cika screen na laptop din, duk suna akwance akayi masu hotunan idanuwansu arufe.

Muryarta tamkar tame Yin raWa ta furta  Speechless! Major Ina kuka samun Kyakkyawar matashin nan mai kama da Wan sarkin aljanu? Anya Cikakken mutunne? Ko dai A cikin Dajin da kuka tsintosu Aljana ta haife shi Ta yada dariya kowan nan su ya saki jin sambatun ummi dama sai da ransu ya basu zata ruWe idan taga hoton shi.

Major yace sai ma kin ganshi a zahiri, ba ?aramin kyaune da shi ba

Ko da ta koma ta zauna, sam takasa Wauke idonta daga kan fuskar Danish, Yayi matu?ar tafiya da imaninta, aranta har ta fara Ayyana koya surar shi zata kasance a zarihi?

Muryar Commender ce ta fargar da ita ga dubanshi dukansu ne muka nuna maki, shin kin canza ra ayinka akan kula da su ko kuwa har yanzu kina akan bakanki

Shiru ta Wanyi tana yanke shawara da zuciyarta, duk sun ?agara da son jin amsarta.

 Yanzu haka case din Yaran mun mi?a shi hannun shugaban isod, shine zai cigaba da jan ragamar bincike akansu, jiya muka samu amincewarshi na kar6ar case din nasu, sai dai ya nuna baya bu?atar 6ata lokaci yanason ya tafi tare da yaran can nigeria a jet dinsa, a satin da zamu shiga

Lokaci Waya ummin america ta canza fuskarta zuwa 6acin rai, da farko tayi murnar jin cewa Case din Yana a hannun chief na Isod, daga bisani daya furta komawa Nigeria ne taji komai ya fita aranta.

 Naji kin yi shiru, baki ce komai ba
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta soma magana ranta a6ace Idan har kuna so in ru?e Yaran a hannuna, they should stay in America. I will not follow them to Nigeria,

Commender yace amma meyasa? Ke kanki fa ?ar ?asar Nigeria ce why baki son zuwa ?asar Ki

Girgiza kai Tayi still fuskarta da 6acin rai ta furta Ni ba ?ar nigeria ba ce, asalina ne acan, amma Ni black american ce, tun da nace banaso mubar maganar kawai, Ni zan koma gidan idan ka gama maganar ka

Yanayin fuskarta Ya canza sosai, 6acin raine tsantsa, sun fahimci kamar akwai wani abu daya ta6a faruwa da ita wanda har yajawo silar barinta ?asar, kuma batason Anayi mata maganar komawa can

Ganin yadda ta haWe rai babu annuri ko miskala zarratin akan fuskarta, Yasa Commender cewa Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ba zamu takura maki ba, Zaki Iya tafiya ba don yaso ba ya ambaci hakan, duk basu ji daWin canzawarta ba, muryarta a disashe ta furta thank u ta yun?ura ta mi?e ta nufi ?ofar fita daga office din, Har ta kusa ficewa Muryar Commender ta katse mata hanzarinta duk da bansan abunda ya faru dake a ?asarki ba da har yasa kika tsani jin an ambaci sunanta, da akwai wani abu da nike so in faWa maki ummi yayi maganar tare da mi?ewa hannun shi ru?e da mug na coffee, Ya kur6a kafin ya Waure da cewa wannan dama ce agare ki, da zaki koma ?asarki a karo na farko ki nuna ma waWanda sukayi silar barinki ?asar cewa Kina araye kuma kinsamu cigaba a rayuwarki ba kamar yadda sukayi tsammani ba, inaso ki basu mamaki ummi, sannan zuwanki Nigeri bana dundun bane na Wan lokacine zaki dawo nan da zarar Mun samu nasara akan binciken Yaran, zamu dawo dake nan, saboda mu kanmu ba zamu so mu rasa nagartacciyar mace irinki ba, ke kanki kin sani muna ?aunarki kuma muna daraja ?imarki a idanuwan mu, ba zamu so abunda zai 6ata maki rai ba ummi, kina da damar da zaki Iya zuwa gida ki zauna ki yi tunani akan maganata kafin ki yanke shawara.

Kalaman shi sun Wan ta6ata, tuni zuciyarta ta fara sassautowa, ita kanta zataso wannan damar ta zuwa Nigeria ko dan taba waWanda sukayi silar barinta mamaki.

Numfasawa ta Wanyi kafin a hankali ta juya tana kallon commender dake tsaye abayanta, kamar bata son furta maganar tace babu bu?atar yanke shawara, Na amince Zan bi su zuwa Nigeria, Kuma nagode da karramawarku agareni, da zarar na gama aikin, zan dawo ?asata

Murmushi major da commender suka saki, Jin abunda tace, har yanzu bata yadda ta kira Nigeria da sunan ?asarta ba.

Sun ji daWin amincewarta, ba tare da 6ata lokaci ba, Commender ya dauko mata kundun dake Wauke da bayanansu Angel, duka takardun akwai Signature dinsu a jiki, saura sanya hannunta suke bu?ata, cikin ?an?anin lokaci su ka ?ulla Yarjejeniya ta (guardianship agreement)atsakanin su da ita, sai da ta natsu ta karanta sharuWWansu dalla dalla akan irin rainon da suke so tayima yaran kafin ta sanya hannu a takardun, bayan ta kammala sun bata wasu takaddun yarjejeniyar da zata ru?e a hannunta.

Bayan tayi masu sallama, Ta fito daga office din, tana tafiya Sojoji Na binta da kallo, Yayin da ita kuma hankalinta na akan takaddun dake a hannunta, Fatanta Allah yasa Ru?on Yaran da za ta yi da kuma zuwan ta Nigeria Ya zama alkhairi agare ta.

Tun kafin ta ?arasa gaban motarta da ta bari a harabar ajiye motocinsu, ta hango sojoji dadda6e sun kewaye motar suna jiranta, murmushin gefe fuska tasaki har dimple dinta Ya lotsa, ta fahimci tunda ta shiga office din commender suke ta jiran fitowarta don su yi mata magana, bata tsaya sauraron su ba, da?yar ta samu suka ?yaleta ta shiga mota, a tsanake ta tada motar, Ta juya sitiyarin da gudu ta fuce daga head quarter din.

*EX-PRISONERSd'*

Tun Wazu da safe kowan nan su Ya farka daga bacci, sun wayi gari da jin kyakkyawan labarin farkawar Danish, saboda zumuWin zuwa ganin shi babu wanda ya nemi breakfast acikinsu, gaba Waya sun Hallara a room dinsa, tun daga kan Haris, Javed, Naufal, Gabriel, Batul, Hannah, Jamimah, Azeeza, ?wansu da kwarkwatarsu sun yi tsaitsaye cirko cirkon suna kallon shi, fuskokinsu Wauke da Annurin farin Ciki, ?aya bayan Waya Danish Yabisu ya rungume su a ?irjinshi, kamar sunyi shekara basu atare da juna, Haris hada kukanshi saboda murnar ganin Danish Ya farka.

Sun tasa shi gaba suna kallonshi kamar zasu lashe shi, Musamman Azeeza da Jemimah, daWi suke Ji Danish Winsu Ya farka.

Muryar jamimah da shagwa6a tace munyi fushi ma sai yau zaka farka, kullum sai munyi kukan rashin ka, ko bacci bamu Iya yi abincin ma ba mu ci Harara Azeeza ta watsa mata wlh ?arya take yi Danish kullum sai taci abinci sau uku, kuma tana Yin bacci Murmushi ya saki yana binsu da kallo, Haris dake zaune gefen gadon Danish ya ru?e hannunshi a Cikin nashi ji yake kamar za a kwace mashi Wan uwanshi.

 Meyasa Angel Jiya daya farka baki tada mu daga bacci ba? Bayan kinsan irin ?agarar da muka Yi na son ganin shi Hanna ce tayi maganar, Gabriel Yace Ni dai ba abunda zance sai godiya, saboda ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, Yau babbar rana ce agaremu Wan uwanmu abun alfarinmu Ya farka da ranshi da lafiyarshi yana daga tsaye yake yin maganar Ya goye hannayenshi saman ?irjinshi.

 Allah sarki Rayuwa kenan, Har na tuna kokawar da Ku ka yi kaida Danish akan nace zan dire taga gaba Wayansu suka sanya dariya.

Batul tace ai mu bamusan abunda ya haWa su faWa ba

Parveen dake tsaye gefen Naufal hannunta ru?e da Ayaba sai ci take Yi, Kunnuwanta akansu ta natsu tana sauraransu.

Labari Angel ta basu na abunda ya faru lokacin da zata dire taga, ba ?aramin nishaWi su ka yi ba.

Azeeza tace munyi kuka lokacin sosai, Munyi tsammanin Danish Winmu zai rasa idonshi Waya, sai gashi Allah ya dawo mana dashi da ranshi da Lafiyarshi, gaskiya munji daWi da farin ciki akan fuskarta ta ?are maganar, idanuwan Danish akan faces dinsu, ita da Jemamah.

Parveen tace ni banaso muna tuna baya, nafi so inji muna magana akan abunda zai faru agaba

Jemimah tace Genie yaushe zamuje gidan daddyn naki? Ni na ?osa mu koma can, waWannan mutanan masu jan kumatun, kullum sai sun tsira mana allura a Wuwawun mu ta yi maganar tare da nuna ass dinta da indext finger dinta, gaba Waya suka tuntsire da dariya, Azeeza tace Kai jamimah ki ji tsoron Allah, Jiya fa ba ayi mana allura ba, nurse ta faWamin an gama yi mana ita, sai dai magani da zamu dinga sha na tsawon one month turo mata baki Jemimah tayi
Javed yace Kufa baku gajiya da abun magana, Kun Cika Wan uwanmu da surutu, Ko so kuke yi ya koma baccin atare suka zaro ido haWi da Wan buWe baki A a wlh bamu so Ya koma bacci,

 Alhamdulillah, Tun da yanzu mun haWu mu dukanmu, Yakamata Muyi wa Allah godiya Angel Ce tayi maganar, Tare da ?aga tafin hannayenta sama, Da sauri suma suka Waga nasu zasu yi addu a, Mutun Waya ne bai Waga nashi hannun ba, Hatta Gabriel da ya ke Christian sai da ya Waga hannunshi don su yi addu ar atare, Don shi a yanzu baida za6in addini, yafi ?arfi ta 6angaren musulunci saboda Angel.

Kallon fuskarshi Angel tayi danish zamuyi addu a, ba zaka Waga hannu ba
Girgiza mata kai Yayi alamar a a, Waure mashi fuska tayi sai yayi tamkar baisan tana Yi ba
Cikin sanyin murya Haris yace Danish meyasa har yanzu baka goyan bayan addinin musulunci ?

Shiru danish bai yi magana ba, Kuma babu alamun zaiyi ta.
Damuwace ?arar akan fuskokinsu
 Pls danish just for today ka Waga hannu Muyi addu a Muyar Angel tamkar zata fashe mashi da kuka Tayi maganar.

Marairaice mashi fuska Azeeza da jemimah sukayi Bro pls, let pray together,

Runtse idanuwanshi Yai, ba tare daya buWe su ba Ya furta I can t, ku daina yi mini magana akan Inyi, bana so

Sai lokacin Batul ta sanya baki tun da ya nuna bayaso mu ?yaleshi, damu da shi duk abu Wayane, ko da ace baiyi ba mu zamu yi mashi, hakan ma ya wadatar Angel bata ji daWi ?in Yin addu a da yai ba, addu oi ta soma karanto masu suna amsa mata da ameen ameen, idanuwanta sun cicciko tab da ?walla, bayan sun Kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, banda Angel maimakon ta shafa addu ar da tayi saman fuskarta, sai ta shafa ma danish saman sumar kanshi, a hankali ya Wago da idanuwanshi yana duban fuskarta, harara ta watsa mashi tare da murguWa mashi baki, hakan da tayi ba ?aramin ?ayatar da shi yai ba, muryarshi ?asa ?asa ya furta mata thank u ta6e mashi baki tayi kada ka yi tunanin na damu dakai, ?ayataccen murmushin gefen fuska yasakar mata, Su Batul sun natsu suna kallonsu.

Muryar Dr. laura ce ta katse masu hanzarinsu Congratulation! My lovely Children Ina tayaku murnar farkawar Wan uwan ku daga bacci, banjima da shigowa asibitin ba, dr Harry ke faWamin cewa Wan uwanku Danish Ya farka, wannan abun farin Ciki ne ta ?arasa maganar, a yayin da take ?arasowa Gaban gadon Danish. Fararen idanuwanta dake asanye cikin farin glass ta Waura su kan face dinshi.

 An sanar dani cewa Baya kula kowa sai ?an uwanshi, dagaske ne masoyiya Angel? Tayi tambayar tare da kallon Angel

Da fara a akan fuskar Angel ta amsa mata da cewa  Jiya ne amma yau ya saki jiki, zai Iya magana da kowa

Dr laura tace Anya kuwa? Naga ko kallona baisan Yi, danish Ya jikin naka? Ko akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka ? Tayi tambayar cikin ?agara da son jin muryarshi
Cikin raWa Angel ta furta mashi danish pls kayi mata magana, sun taimake mu, kuma suna da mutunci kamar wanda akayi ma dole da?yar ya iya motsa lips dinsa ya furta da sau?i babu inda keyi mini ciwo,

Dr Laura taji daWin maganarshi ina fata kaci abinci babu yunwa atare dakai ? ?aga mata kai yai alamar eh
Ta furta okey, amma meyasa jiya baka ba likitoci damar duba lafiyarka ba ?
A takure yake yi mata magana saboda lafiyata ?alau, bana bu?atar a duba ni, Jinjina kai ta Wanyi tayi mamakin Halinshi, basu ta6a samun patient irin shi ba.

Muryar Angel ce ta janyo hankalinta ga dubanta Aunty, mun gode sosai da kulawarku agaremu, Allah ne kaWai zai Iya biyanku, tayi mata maganar ne don ta mantar da ita zancen yi ma Danish maganar duba Lafiyar Jikinshi.

 kada ki damu masoyiya Angel, aikin mun e kula da lafiyarku kuma Alhamdulillah, Naga Jiki yayi kyau Allah ya ?ara Lafiya, ta ?are maganar tare da kallon Azeeza da jemimah My twins, Ya jikin naku atare suka haWa baki da sau?i kafin ta Waura idonta kan Parveen da sauri ta 6oye Ayabar dake a hannunta, dariya dr laura ta Wan saki hmm ai na gani dama kin daina wahalar 6oye mini du?ar da kai Parveen tayi fuskarta Wauke da murmushi.

Kallonsu Gabriel Tayi ?an samari, Jiki yayi kyau, badan sister dinku ta matsa akan son komawarku Nigeria ba, da a gidana zan killace ku, In cigaba da rainonku, murmushi kowan nan su ya saki.

 Zan Koma Office, Ku kula mun da kanku har ta juya zata fuce Angel tayi saurin cewa Aunty, har yanzu sojojin basu kira ba naji su shiru basu zo sun duba mu ba

Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba zato ba tsammani, Suka hango Dr. Mark tare da dr. brown sun nufo ?ofar Wakin, Kusan a tare suka shigo.

Gaisawa suka Yi da dr laura, Cikin girmamawa su Angel suka gaishe da su, Bayan sun amsa masu, suka tayasu murnar farkawar Wan uwansu

Kafin daga bisani Dr Mark Ya soma Yin magana Dr. Ke muke nema, Sojojin nan sun Kira Awaya, idan ba damuwa zamu Iya zuwa office muyi magana

Amsa mashi tayi da toh, ba tare da 6ata lokaci ba suka fuce daga Wakin.

Hankalin Angel ya?i kwanciya burinta taji me zasu tattauna, fatanta Allah yasa su amince da maganar maidasu Nigeria.

Bayan fitarsu Wakin kaitsaye office din dr Laura suka nufa, kowan nan su ya samu wuri saman kujera Ya zauna suna fuskantar Juna da ita

 Ina sauraronku, me sojojin suke ce ne ? A ?agare ta tambayesu
Dr mark Ne ya soma kora mata jawabi Commender dinsu ne Ya kirani awaya, Ya sanar dani cewa Chief na Isod Ya Amince zai kar6i case din Yaran.... tunkan Ya ?arasa maganar, dr laura tasaki murmushin farin ciki

 Bayan haka, sun ?ulla Yarjejeniya tsakanin ita ummin american da su sojojin, zuwa Anjima zasu zo asibitin domin shirya yaran, zasu Wauke su zuwa gidanta, sai dai zamuyi kewarsu saboda Commender din ya faWamin next week chief na isod zai bar ?asar tare da yaran ya ?arasa maganar idonshi Akan dr laura, mood din fuskarta ya canza zuwa damuwa, ba ta yi tsammanin zasu bar ?asar da wuri ba, zaman da su ka yi da su na kwana huWu ba ?aramin sabo su ka yi da juna ba, sai dai ta wani 6angaren taji daWi kodan saboda Angel da ta ro?e ta akan ta taimaka masu su koma ?asarsu.

 Dr lafiya? Naga kamar yanayin fuskarki Ya canza? Ko baki ji daWin maganar bane ? dr. Mark ne yayi maganar ganin ta haWe fuska, Murmushin ya?e tasakar mashi
 No ba haka bane, Na saba da yaran ne, banaso su yi nesa dani, banyi tsammanin zasu bar ?asar da wuri ba, inaso zan nemi alfarma abar mana su ko da one month ne su yi anan kafin su tafi

Dr brown yace ba zai yiwu ba dr, da ace case dinsu a hannun sojojin yake zamu Iya neman alfarmar abar mana yaran su zauna a wurinmu, sai dai kash sun riga da sun dam?a case din hannun chief na isod, kuma kinsan shi ba Wan ?asar nan bane, A ?asar shi yake zaune Aiki ne mai muhimmanci ya kawoshi america, tun cikin weekend daya wuce yaso barin ?asar, saboda case din Yaran Ya fasa tafiya, yanzu haka da nakeyi maki magana, yana shirye shiryen barin Washinton zai shigo garin mu saboda ya haWa kan yaran ya tafi dasu, mutumin babu wasa a aikinsa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login