Showing 87001 words to 90000 words out of 260999 words

Chapter 30 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

mashi Ya mi?e zaune Bayan ta sanya mashi pillow a tsakankanin bayan shi da headboard na gadon.

Sun natsu suna kallon shi, azabar ciwo tasa shi canza kamanni, fatarshi ta yi haske Ya rame sosai, hakan ba ?aramin Kyau ya fiddo mashi ba, sumar kan shi a cukurkuWe kamar mahaukaci sabon kamu, Waya bayan Waya ya ke binsu da kallo Yana ambaton sunansu da raunatacciyar muryarsa
 Angel, Batul, Azeeza, Jamimah, Hannah, Javed, Naufal, Gabriel.. Numfashi Yaja Kafin ya furta sunan Deeja Ya akai banganta ba? Ina aka kaimin deejana? Baku zo da ita ba ? Idanuwanshi acike tab da hawaye yai masu maganar

Cikin sanyin murya Angel tace Haris pls ka daina sanya damuwa aranka, dubi kaga yadda ka rame, tamkar ba Haris Win mu ba, duk kabi ka zauce, Why pls? Bama Jin daWin canzawar da ka yi, gashi baka da ?oshin lafiya

da?yar sautin muryarshi ke fita Bazan Iya jurewa bane Angel, inason deejana ina jin tsoron ace narasa ta, donni inaji araina tana araye tun da har su azeeza basu mutu ba, Itama sumane tayi

 Haris idan har baka kwantar da hankalin ba, Ta ya ya zamu Iya samun ?warin gwiwar fallasa asirin masu kurkukun ?addarar har muci nasarar Wauko sauran ?an uwanmu da suke acan idan basu mutu ba? Dole fa sai ka bamu haWin kai ka danne damuwar dake aranka tukunna zamu Iya Cin galaba akan su ! Angel ce ke yi mashi magana cikin kwantar da murya

Gabriel ya Waura da cewa Kin faWi gaskiya Angel, Haris pls ka taimaka ma kanka muma kuma ka taimake mu sannan ka taimaki rayuwar su Deeja Rashin lafiyarka shi zai tarwatsa mana shirin mu, Nurse ta faWamin abunda ke damun ka, Ciwon zuciyane Haris kuma nasan bakomai ne ya jawo hakan ba face Deeja!! kaga yanzu mun ku6uta daga Daji muna acikin mutanan duniya, Nan inda muke asibiti ne Inda ake duba marasa Lafiya sune suka bincika lafiyarka kuma suka tabbatar mana da cewa damuwace ta silar wani abu daka ?wallafa rai akan son shi, pls Haris Ka taimaka mana! Idan har ba ka ji sau?i ba Likitocin nan bazasu ta6a bari mu koma Nigeria ba gidan daddyn Angel tunda Gabriel Ya fara magana Haris Yake bin Wakin da suke da kallo, sai lokacin Ya gane ba adaji suke ba, shifa gaba Waya baya acikin hayyacinsa baisan ma a ina yake ba, idanuwanshi sun makance.

Azeeza sarkin tausayi tun da ta tsareshi da ido, Hawaye ke bin fuskarta.
Cikin shesshe?ar kuka tace Dan Allah haris ka yi ha?uri, In sha Allah deejan mu bata mutu ba da sauran ?an uwanmu Zamuje mu Wauko su

Batul tace kwanciyar hankalinka kawai muke bu?ata Haris, idan ba haka ba kaga zaka mutune kafin muyi nasarar dawo da su deeja, me kake tsammani idan Ka mutu muka gano deeja araye ya za ta ji? Ka mutu saboda ita? Kaima ka sani yadda take ?aunarka itama mutuwa zatayi tabi ka

lumshe idanuwanshi yai, ?an uwanshi ba ?aramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba, sai kwantar mashi da hankali suke yi duk don su samu ya wartsake

 Ina Wan uwana ? yai tambayar yana kallom faces dinsu
 Danish bai farka ba Haris Har yanzu, bacci yake yi,  Angel ce ta bashi amsa, damuwace ?arara akan fuskarshi
 Angel wani irin bacci ne wannan Har yanzu bai farka ba? Ina jin tsoro wani abu yasame shi girgiza kai Angel tayi a a Hairs ba abunda zai same shi, Ni inaji araina Lafiyar danish qalou, Bacci ne kawai ya ke yi kasan ya Wauki tsawon lokaci bai runtsa ba shiyasa bai farka ba

GyaWa kai yai Allah yasa hakane,
.  Haris ka ci abinci ko kana jin yunwa ? Kallon parveen yai bana Jin yunwa parveen, Naji daWin kulawarku agare ni, sannan Ina tayamu murnar barin kurkukun ?addara murmushi kowan nan su Ya saki, shima ya ?alalo murmushi akan fuskarshi

Muryar Jemimah da shagwa6a tace Idan ka ji sau?i, zamu ga deeja ma har kuci abinci atare da ita, kana bata abaki itama tana baka abaki, agidan daddyn genie Wita gaba Wayansu suka sanya dariya, Nurse rebecca dake tsaye tuni ta zauna saman chair tana dubansu sam bata gajiya da kallon Yaran burgeta suke Yi kamar ta sace su take ji.

Haris Ya ji daWin maganar Jemimah har saida yaWan murmusa
 Sannan Haris zai dinga wanke ma deeja gashin kanta yana sharce mata shi, Batul ce tayi maganar, tsabar daWin maganarta har saida fararen ha?oransa suka bayyana.

 Bayan haka zai dinga goyata a saman bayanshi Suna yawo acewar Hannah sosai Haris ya fashe da dariya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri akan fuskarsa, Lamarin ya Waurewa rebecca kai, mamakinta yadda yaran suke matu?ar ?aunar junansu, wani abu da ya ?ara burgeta yadda suke ta sanya shi dariya tabbas su ka Wai suke Iya sarrafa junansu.

 In sha Allah Haris our dream will come true lumshe idanuwanshi yai tare da buWe su akan fuskokinsu sai ya dinga ganin tamkar Deejar sa ce zaune a tsakiyar gadon tana sakar mashi murmushi, hakan yasashi sakin murmushi kamar wani zautacce

 Haris ka kwanta ka huta, kada mu cika ka da surutu, zamuje Wakin Danish mu duba shi

 Nima inaso naganshi Angel, muje atare

Kallon Nurse Win tayi pls sister zamu Iya tafiya da shi Wakin Wan uwanmu ?
Smilling gently, nurse rebecca tace badamuwa, zamu Iya tafiya da shi ta yi maganar tare da mi?ewa Ta nufi gaban gadon, da taimakonta Haris ya sauko daga saman gadon tace mashi ya dafa shoulder Winta don ya samu damar yin tafiya, Rurru?eta yai da hannayenshi a haka suke Yin tafiyar, Su Angel suna abayansu har suka ?araso Wakin da aka kwantar da garkuwa, Jikin Angel har 6ari yake yi saboda tsabar zumuWi, tun kafin su ?arasa shiga Wakin suka hango Danish Baje saman gadon, kamar matacce, lallausar sumar kanshi ta tarwatse saman mattress Win gadon, da sauri Angel ta nufi gadon Ta haye daga gefe Idonta akan Kyakkyawar fuskarshi, Har kullum kamar ana ?ara ninka mashi kyawunshi, fatarshi tayi smooth fara sol Ko tabo babu, Sun canza mashi uniform Winshi wanda ke a jikin sa Yanzu kalar nasu ne Riga da wando light blue, rigar tayi tighting Winsa, gajeran hannu ne da ita Hakan ya bayyana ?a??arfan Damtsen hannun shi, Likitoci sun sha wahala wurin canza mashi kayan Jikinshi saida suka haWa ?arfi tukunna su ka samu damar raba shi da su.

A hankali take bin Shi da kallon so da ?auna tun daga saman sumar kanshi har i zuwa kan Long eye lashes Winsa, dogon hancin nan nashi yayi sam6al babu lan?wasa, full lips Winsa sun ciza launinsu, slowly ta sauke idonta akan Zanan tattoo dake a gefen dogon wuyanshi Yayi bala in yi mashi kyau
A gefe da gefen gadonshi kowannansu Ya samu wuri ya zauna hada haris da nurse ta zaunar dashi, natsuwa su ka yi a yayin da su ke kallon Wan uwansu, daWi kamar zai kashe su
Angel ta shagala da kallonsa ji ta ke kamar ta faWa saman chest Winsa ta ?an?ame shi ko ta samu sassaucin kewarsa da ta ke yi, Muryar Haris ce ta fargar da ita.

 Angel zuciyarshi tana bugawa ?

A hanzarce ta kwantar da kunnanta saman chest Winsa saitin heart Winsa nan take taji bugun zuciyarshi na harbawa a tsanake
?agowa tayi fuskarta Wauke da murmushi tace dasu zuciyarshi tana bugawa, bacci ne yake yi

Jin haka yasa Kowan nan su Ya matsa kusa da shi, Waya bayan Waya suke Waura kunnuwansu saitin zuciyarshi, nurse rebecca dake a tsaye murmushine Wauke akan fuskarta

hankalinsu ba ?aramin kwanciya yai ba, jin zuciyarshi na bugawa

 Sai yaushe zai farka? Baccin yayi yawa Javed ne yai maganar, Naufal yace may be saiya Wauki adadin kwanakin da yayi bai runtsa ba tukunna zai farka zaro ido Angel tayi haWi da girgiza kanta in sha Allah ba zai kai wannan lokacin ba zai farka.

Ta ?are maganar tare da ru?o zira ziran yatsun hannun Danish na dama acikin nata, sosai ta runtse su (nima kuma na runtse al?alamina)



*Boss Bature
'? Mu haWu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*



_~*BossLadiesWriters*~_


_*KURKUKUN ?ADDARA*_


~Middle step~


_The Prisoners E17=?%?=ث?_



*Daga al?alamin Boss Bature*




A ?alla sun shafe kusan 30 minutes a Wakin Danish, Ji suke kamar abarsu su kwanta a Waki Waya saboda haka su ka saba kwana a kurkuku, daga bisani Nurse tace dasu zasu tafi zuwa gobe zasu Iya zuwa su ?ara duba shi jiki asanyaye suka mi?e suna tafiya suna waiwayon shi musamman Angel ji ta ke yi kamar ta koma ta rungume shi.

Bayan fitar su daga Wakin, Nurse Ta raka kowan nan su room da aka kwantar da shi, ba su so aka raba su ba, har yanzu tsoron mutanan su ke ji, ba dan Angel ta lalla6a su ba da ko babu inda zasu je, a Wakinta zasu kwana, musamman Azeeza da jemimah Wa?yar Angel ta lallashesu ta lalla6asu don ta fahimci dokar asibitin ce haka ba a haWa mutun fiye da Waya a Waki, wata ?il sai idan ya kama dole, sau?in ma kowan nan su akwai nurse Waya da ke kula da Wakin shi, duk wani abu da zasu bu?ata zasu yi masu, hatta toilet suna raka mutun In ya bu?aci hakan musamman gasu da basu san yadda zasuyi amfani da wasu abubuwan ba.

A daren ranar sun yi kwanan farin ciki basu da wata damuwa.

*Daular Alhaji Musa wadata*

idan nace zan tsaya zayyana maku zunzurutun Kayan alatun da ke a gidan Alhaji musa daga ni har ku zamu koma Yin Mafarkinsa ne, wato HaWaWWiyar Daular arzi?i ce, Katafaren Villa ne Wanda Idan ka zura ?afarka acikinsa tamkar ka Bar Nigeria ka shiga Dubai ne, Aljannar duniyace ?ar ubansu, A ?alla security din dake tsaron Kafcecen Gate Win shiga gidan sunkai su goma shabiyar, Wasu gabza gabzan Garada Masu ?irar sadaukan Ya?i, Babu wasa akan fuskokin su, Bana tunanin ko aljani zai Iya gifta gate din gidan salin alin ba tare da sun cafke shi ba, Shantalelen titi ne zai sadaka da Cikin gidan kai tsaye daga bakin babban gate Win, yadda kasan da zallar goal aka ?era ginin saboda Waukar idon gilassan ?ofofin da Windows, ko gidan shugaban ?asa albarka, Babu ce kaWai ke babu agidan Alhaji musa, komai na gidanshi babu made in Nigeria, an zabga almubazzarancin dollar wurin ?era ginin, don hatta sample dinsa da ?wararrun da suka ginasa kaf aikin turawa ne.

Mamaki da al ajabin dukiyar Uncle din nasa Ya hana shi Kwantar da hankalinsa, Tun Bayan da escords suka Wauko su daga airport, Motocin suka shigo gidan gabanshi ke ta faWuwa, saboda sabon gini ne baya a ?asar Uncle Win nasa Ya mallake shi, shiyasa komai yake Waure masa kai, Kafin shigarsu gidan Saida shureim Ya dinga jero addu o i acikin zuciyarshi Yana neman tsari akan Allah ya kare shi daga shagalar duniya, Idan har zaman shi gidan ba alkhairi bane, Ya ro?i Allah da ya yi mashi silar barin shi cikin sau?i ba tare daya sha Wahala ba.

Tun da suka shiga gidan Kamar wani ba?auye Haka ya dinga bin ko ina da kallo, wasu matsiyatan Chandeliers saman ceilling Masu ?yal?yali tamkar zasu rubzowa mutun saman kanshi, Ga wasu HaWaWWun twins stairs, masu Wauke da Glass Elevator a gefensu. Idan ka shiga cikinta Kana iya hangen mutanan dake zarya a palourn Yayin da take Yin sama dakai ko take dawowa dakai ?asa.


A katafaren Palourn gidan kuwa Wasu Jigunannun Royal Sofas set ne ?an ubansu masu numfashi Ga Arm chairs kalar Na sarakuna, A gefe da gefen kujerun Sofa table ne, Tiles din palourn baida banbanci da Mirrored tiles Kana kallon Fuskarka acikinsa Idan kana Tafiya, zallar haWuwa, An zuba komai na more rayuwa, Idan nace zan tsaya zayyana haWuwar Komai dake acikin Gidan Tabbas zamu ?are middle step da last step acikin gidan Alhaji musa (>?#?)

Babu wanda Yasan da zuwansu, Hatta Iyalinsa Ba su san da dawowar shi a yau ba, yana Waya daga Cikin Halayan Alhaji musa, Idan zai yi tafiya babu wanda ke sani Matar shi ko ?a ?anshi, Haka zalika Idan Zai dawo sai dai su ganshi, saboda zuwan ba zata Ya ke yi masu.

A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta ?udundune kanta acikinsa, daga gaban dardumar Qur anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon gaba da ita a yayin da take Yin karatun al ?ur ani mai girma.

 Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin ta Wago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare ?al launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya Ware na mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde har saman fore head Winta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da ?aramin baki launin pink, Ba ta da ?iba ko mis?ala zarratin siririya ce, abu Wayane ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon.

 Zeenat! Bacci ki ke Yi ? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta zabura ta mi?e tare da wurga ?wayar idanuwanta kan Mai shigowa Wakin, babbar macace mai cikar kamala, Ta Wauki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan fuskarta, baturiyace Siririya bata da ?iba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta Waure kanta da kallabi, hakan bai 6oye doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace Win wuyanta da earrings Winta na zallar diamond ne sai ?yal?yali suke Yi da Waukar ido.

Muryarta Adisashe ta amsa mata mommy karatun ?ur ani nike Yi bacci ya Wauke ni bansani ba ta yi maganar tana Yin mi?a haWi da yin hamma

 Ba ki ji dirar motoci ba ne ? Ras Taji gabanta Ya faWi, Muryarta na rawa ta furta dad... daddy is he back  ?

Ta6e baki Hajiya Sarah tayi ya dawo tun Wazu, yanzu haka yana a Wakinsa, yace baya son takura, kinsan halinsa

Hankalin Zeenat Ba ?aramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko ba?in Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so da ?auna.

Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa ya naga kamar baki farin Ciki da dawowarshi ? A hanzare ta girgiza kai  I m so happy he s back, na yi murna ai shi Winne baya son takura

Murmushi tasakar mata Albishirinki !
Da mamaki ta tsayar da eye balls Winta kan face din momyn nata
 Goro !
 Fari ko ja
 Fari
Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin raWa ta furta mata Ba shi kaWai ya dawo ba, Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom Win da aka ware masa Tun kafin Hajiya sarah ta ?arasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da Waura goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta

 Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada Wagowa Zeenat Tayi, tare da mi?ewa tsaye Hijab Win jikinta sai Ja da ?asa Yake yi.

 Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa tsantsar farin cikine akan fuskarta

 No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai ki je ki kai mashi a Wakinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci hausawa

Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta ?agara don a kwaWaice take da son ganinsa
 Na faWa maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko Wan gyalene ki yafa a kafaWa, turo baki zeenat tayi da ?ar shagwa6a tace Mommy ae shima Yaya shureim Win yafi son mace mai sanya dogon hijabi

 To ai bance bayaso ba, tun da acikin gidane ki samu gyale ki yafa ta ?are maganar da zolaya ta furta Muslimatun matar limam Dariya Zeenat ta sanya tana kallon mommyn nata.

 Zan koma kitchen, Ki tabbatar kin shirya da wuri

Amasa mata tayi da toh

Bayan fitarta, da sauri Zeenat ta cire hijab Win jikinta, ta nufi toilet ta shige, cikin ?an mintuna ta fito Sanye da bathrobe (rigar wanka) fara ?yal a jikinta, hannunta ru?e da short towel tana tsane sumar kanta, Bayan ta kammala tsane gashin, a gaban tafkeken dressing mirror ta zauna saman chair tana Gyara Jikinta, Hair dryer ta kunna Ta busar da sumar kanta, Bayan ta gama ta soma shafa tsadaddun Mayukan shafawarta dake a jere gaban madubin.

Zeenatu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login