Showing 153001 words to 156000 words out of 260999 words

Chapter 52 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

mashi na birthday dinshi ?

 Eh, na tambayi yayanki akan ya faWa min me yafi so, kinsan halin shi, cewa yai shi baisani ba, Duk abunda yayi mini in siya mashi, Ni kuma nafi son abun zai burge shi sosai

Dariya hajiya saratu tayi tana fadin Gaskiya baba ni kaina bazan Iya cewa ga abunda yafi so ba, amma kwanakin baya naji yana magana da abokinshi akan yana son suturar su na al adar inyamurai, tun lokacin dai banji sun ?ara magana ba, kuma ba akawo kayan ba, idan har kika shirya mashi su a matsayin gift dinsa, Nasan zai yi farin ciki sosai kuma zaiyi mamaki

 Okey, Send me his measurements through WhatsApp, and please don t let anyone know. I want to surprise him. ta amsa mata da toh nima agaida mun da yayan nawa, ko na kira shi sai yaga dama yake Wagawa, Ina nan ina jiran shi zamu haWu ne sautin dariyar hajiyarne ya cika kunnanta da ba a tace Ai kin fi kowa sanin yayan naki, sai dai ki ba wani labari Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama, Ajiyar zuciya ta sauke, tana ?o?arin zama gefen gadonta, Muryar Hajjaty ta katse mata hanzarinta, tayi mamakin jin sallamarta, don koda gigin wasa bata ta6a tako ?afarta zuwa Wakinta ba, Jim ta Wanyi kafin ta furta Wacece ta fada tamkar bata gane me magana ba

 Hajjaty ce jinjina kai Hajiya saratu tayi tuni mood din fuskarta Ya canza, jim ta Wanyi kafin tace zaki Iya shigowa

A hankali ta turo ?ofa ta shigo Wakin, tun daga ?asa hajiya saratu ta soma binta da wani matsiyacin kallo, pakistan ne ajikinta farare, ta ca6a uban ado, sai dai babu ?amshin turaren nan, sai ka matsa kusa tukunna zaka Iya jin shi, hannunta biyu ru?e da wooden tray, kayan abincine sha?e asaman shi.

Lamarin ya Waurewa Hajiya saratu kai, tayi sototo tana kallon ta
Muryarta na Wan rawa ta furta Ina wuni yamutsa fuska tai da ban wani ba kin ganni, shin wai ma me ya akawo ki room dina? Makuwa ki kayi ne ? Fuska adaure ta mata maganar.
Duk tasha jinin jikinta, adabarbarce ta furfa am..umm...dama abincine na kawo maki, Ni na girka shi da kaina abincin ?asar mu ne... da?yar ta ?are maganar a tsananin tsoroce.

Murmushin ya?e hajiya saratu ta sakar mata dama ke ce kike kawo min abinci? Ina masu aikin gidan ne? Ko sunyi yaji ne

 Suna a kitchen suna aiki, kawai nayi ra ayin in kawo maki ne da kaina, nasan zaki ji daWin girkin tun da baki saba cin kalar shi ba hankalin ba akwance ba take yin maganar,
Ru?e ha6a hajiya saratu tayi tana faman jinjina kai tace To fa, sabon salo, tanan kika biyo? An gaya maki bani da hankali ne da zanci abincin da kika girka da hannun ki? Wato bokan ki ya haWo ki da maganin barbaWe kin zuba min aciki shine ki kawo mun don inci in mutu saboda kinsan abinci ne lago na ko ?

Hankalin Hajjaty ba ?aramin tashi yai ba, cikin sanyin murya tace Allah shine shaidata, tun da nake arayuwata ban ta6a takawa naje wurin boka ba, kuma ni banzo da niyar in cutar dake ba, abincine kawai na kawo maki, dan Allah ki kar6a ki ci...... Kafin ta ?arasa maganar, Hajiya saratu ta dakata mata tsawar data firgitar da ita, jikinta ya kama kakarwa, nuna mata hanyar fita tayi daga Wakin Fuce min daga Waki tunkafin Inyi ?wallo da tray din hannun ki, ?ar rainin wayau, wallahi na fi ?arfinki ba za ki ta6a cin galaba akaina ba, tunda can baki ta6a girka abinci kin kawo min don inci ba sai yau da kika shirya kashe Ni ?

Tuni idanuwan Hajjaty sun cicciko tab da ?walla, cikin shesshe?ar kuka tace meyasa kika tsaneni? Laifin me nayi maki? Duk cikin masu aikin gidan nan ni kaWaice ke bakiso, idan laifi nayi maki ki faWa min sai in gyara

A tsawace Hajiya saratu tace wai ke baki da hankali Ne? Kin manta wacece ni acikin gidan nan? Ko kin fara shaye shaye ne? Ni narasa gane wani tsautsayin ne ya kawo ki cikin Wakina, I don t know where you get the nerve to talk to me face to face, ke ga ta6ararra dallah fuce ki ban wuri

Juyawa Hajjaty tayi da sauri ta fuce daga Wakin, Kamar zatayi tuntu6e, gutun tsoki Hajiya saratu taja tare da samun wuri ta zauna gefen gado, tana mai mamakin ?arfin hali irin na Hajjaty.



_~*
'=؋?BossLadiesWriters=؋?
'*~_





~The return of Benazir~


3,F 'DB/1d'>?
?d'











Bayan fitar Hajjaty daga Wakin Hajiya saratu, zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta, taji Wacin maganganun da saratu ta faWa mata, ita har ga Allah bada nufin komai taje kai mata abincin ba, dama Pravin ne ya bata shawarar ta rin?a kyautata mata, wata ?il ta fara ?aunarta, saboda ta faWa mashi tana son su dinga shiri da matarshi.

Kafin tabar ?ofar Wakin sai da ta ajiye tray din ?asa, ta share ?wallar fuskarta, tukunna ta Wauka ta nufi Wakin twins da niyar ta kai masu abincin wata kil su ci.

A lokacin Zayn yana zaune saman gado Ya tasa laptop dinsa agaba Yana operating dinta, zaid kuma Yana a kwance gefenshi hannun shi ru?e da Wayar shi Yana daddanna ta.

Sallamar hajjaty ce ta janyo hankulan su ga duban ?ofar Wakin.

Zayn tamkar bai ji ba yai shiru ya?i amsawa sai zaid Ne ya amsa mata tare da bata Iznin shigowa ciki, A hankali ta shigo da tray muryarta asanyaya tace barkan ku da hutawa, fatan kun wuni lafiya da fara a akan fuskar zaid ya ce lafiya lou auntyn mu, yau ke ce da kan ki ki ka zo kawo mana abinci ? Ya yi maganar tare da ajiye wayar shi ya sauko daga saman gadon Ya nufe ta, zayn ko kallo bata ishe shi ba, baiwar Allah taji daWin sakar fuska da zaid ya yi har cikin ranta taji ta ?ara ?aunar shi.

 Abincin ?asar mu ne, ni na girka shi da kaina, na kawo maku ne don ku WanWana hannu biyu zaid yasa ya kar6i tray din Daga hannunta yana fadin gaskiya kina ji da ?a ?an nan naki, wallahi munji daWi, kamar kinsan kuwa yunwa muke ji, Yanzu nake shirin kira akawo mana abinci mu ci

Asaman table ya Waura tray din, sai faman sakin murmushi take Yi yayin da take kallon fuskar zaid, buWe warmer ya fara yi, ?amshin Abincin ya daki hancinsa, Jinjina kai yai tare da Wago da ido Ya kalle ta Aunty, Ya sunan wannan haWin ?

 Chicken tikka masala ta faWa still da murmushi kan face dinta.

 Daga jin ?amshin abincin zai yi daWi, balle ma daya kasance hannu mai albarkane Ya girka sa ya fada yana nade hannun rigarsa.

 Zaid! Kada ka kuskura ka ci abincin nan! Kai baka da hankaline ? Ras taji gabanta ya fadi jin abun da zayn yace.

Fuskar zaid a Waure ya dube shi kaga bana son zancen banza, babu ruwanka dani, Kaja baki kayi shiru idan bazaka ci ba

Ya ?are maganar tare da maida dubansa ga hajjaty  mun gode Aunty, Idan nagama cin abincin zaki ji feed back dina jiki asanyaye ta amsa mashi da toh, da sauri ta fuce daga Wakin tana faman sauke ajiyar zuciya.

?amshin Abincin da Zaid ke ci duk Ya cika mashi hanci da ma?oshi, dauriya ce kawai Yake yi, Yana danna laptop HaWi da satar kallon Zaid, da gangan yake cuko spoon da abincin Yana turawa abaki, hada sambatun shi wannan abinci kamar a aljanna aka dafa shi? Kai ka ji wani WanWano mai daWi, gaskiya duk wanda baici abincin nan ba an barshi a baya Harara Zayn ya watsa mashi sam bai lura ba, saboda Ya bashi Baya.

Ajiye spoon din ya yi cikin abincin, ya tsiyaya lemu mai sanyi acikin glass, Ya Wauka Yasha rabi, Ya ajiye.

 bari na Wan shiga toilet ya faWa hadi da mi?ewa da sauri Ya nufi toilet door ya shige, shigar shi ke da wuya Zayn ya janye laptop dinsa, cikin sanWa Ya rarrafa saman mattress din zuwa gaban table din, Yana faman yamutsa fuska Ya Wauki spoon Ya zura a plate din abincin aranshi yana fadin ba lallai ma abincin yai daWi ba, mutuminka tun da yayi one spoon abaki, Tsabar daWi kunnanshi har motsi suke yi, Yana ci yana satar kallon ?ofar toilet gudun kada Zaid Ya riske shi Yana cin abincin Hajjaty, a ?arshe Ya ajiye spoon din Ya duma hannu ya Wauko cinyar kaza Yadinga cizga Yana ci, Kusan Rabin abincin plate din ya cinye, ya Wauki lemu Ya kur6a, Jin motsin za a buWe ?ofar toilet Yasa shi yin saurin sauke glass din lemun saman table, ko hannun shi bai goge ba, Da sauri Ya koma can saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard ya Wauki laptop dinsa Ya cigaba da operating dinta.

Fitowa zaid Yai daga toilet, Yana faman yarfa hannun shi, Satar kallon fuskar zayn yayi, mutumin Ya haWe rai babu annuri, Sai dai Ya manta bai goge bakinshi ba, yayi dama dama da mai?on abincin da ya ci.

?ayataccen murmushi zaid ya saki aranshi ya ayyana babyn mommy ai nasan zaka aika, shiyasa na shiga toilet don na baka damar ka ci, Wan rainin wayau anaso ana kaiwa kasuwa Ya faWa Yana zama bakin gadon, da zolaya yace Zayn ya akai naga abincin dana rage an ci shi ?

Muryar zayn ba wasa yace ka tambayi wanda kaba ajiya, Ni meye ruwana aciki ? Gumtse dariya Zaid yai amma dai da kunya wallahi, Ni dai nasan babu 6era agidan nan rai a6ace zayn yace ban san iya shege zaid, Uban waye 6eran ?

 Ai ni ban kama suna ba, kawai nayi maganata ne dogon tsoki Zayn yaja yana faman hura hanci, Aranshi ya ayyana Ina ma zaid Ya rage abincin da kuwa ya cinye shi duka, don ba ?aramin daWi yayi mashi ba.


*SIR MUBARAK>?
?*


A Hankali Yake tafiya Yana tunkarar Wakin Dr. Jazz, Daga shi sai short A jikin shi da singlet, Tura ?ofar Yayi baiga kowa a Wakin Ba, shiga Ciki Yai Yana bin ko ina da Kallo zanin gadonshi a hargitse Takalman shi Yashe saman floor, tunani ya shiga yi aranshi ko ina ya shiga? Ko dai yana a toilet ne Ko ya shiga Garden, Yanke shawarar zuwa garden Win ya yi don Ya dubo shi, Ahanzar ce Ya juya da niyar ya fuce kwatsam Muryar Jazz ta katse mashi hanzarin shi.

 Oh tsayawa za ka yi Kana kallonta? Babu abun da zaka Iya yi mata? Sai kace ba ka san Hanyar da zaka kashe ta ba idan haukanta Ya motsa ! wani irin bugu zuciyar Sir Mubarak Tayi Jin Kalmar Kisa, A firgice ya juya baya Yana bin toilet door Win Wakin da kallo, don Ya fahimci acikin toilet yake Yin wayar, Cikin tafiyar sanWa Sir Mubarak Ya nufi ?ofar toilet ?in Ya kanga kunnan shi Yana sauraron shi.

 Ai ba dole Saina zo ba, Kaima zaka Iya sarrafata, Idan ta?iya Kawai ka bi Hanyar da nace maka, ka kashe ta kowa Ya huta, shiru Ya Wanyi can kuma yaji yaci gaba da cewa ba yadda za ai inzo, Ina tsoron asirina Ya toni, hmm bakasan halin da nake aciki ba, ko jiya saida na kamo Hanya zanzo gidan, ganin ana bin motata yasa na karya kwana na nufi asibiti, saboda raina ya bani akwai wanda ke bin diddigina dole Inyi takatsantsan

Hankalin Sir Mubarak Ba ?aramin tashi yai ba, sai faman jinjina kanshi yake Yi, Bai ta6a tsammanin Jazz Yana da wayau ba sai Yau, Har yasan Ana bibiyarshi wato shine Ya canza Hanya, Hakan ya ?ara tabbatar mashi da zargin shi akanshi.


 What are you doing here, baby?

Muryar Turai ce ta ratsa kunnanshi, Hatta dr Jazz dake a toilet, Sai da Ya ji sautin muryar mutun a Wakin shi, a yayin da yake atsaye gaban sink, wandon crazy jeans ne da shirt a jikin shi, da sauri Yai rejecting call din Ya tura wayar cikin aljihun wandon shi, Jikinshi Ya hau Yin kerma, Tsananin fargabane Ya kama shi, A hankali Yake tafiya yana nufar ?ofar fita, Kafin fitowarshi da sauri Sir Mubarak Yai wuff Ya nufi Turai dake kallonshi da mamaki akan face dinta ganin Yadda ya ke yima Jazz la6e a Waki, Harta buWe baki zata ?ara yin magana ya yi saurin sanya faffaWan tafin hannunsa Ya toshe mata bakinta, tare da janta zuwa wajen Wakin.

Lokacin da Jazz ya fito daga toilet din zufa na bin fuskarshi, ya dubi ko ina baiga mutun ba, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, har wajen Wakin Ya le?a bai ga kowa ba, Hakan yasa shi kokwanton wata ?il Kunnuwanshi ne suka jiyo mashi ba dai dai ba, hankalinshi ya kwanta, komawa ya yi cikin Wakin Ya kwanta saman gadonshi, yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, ga dukkan alamu wani abu yake tunanowa wanda yasa shi fitar da ?walla a idon shi.


A bedroom Sir mubarak Ya shigar da turai suna tsaye suna kallon juna, kallon tuhuma take bin shi da shi.

 Nayi mamakin ganinka a Wakin Jazz kana yi mashi la6e, meyasa ?

Fuskarshi a murtuke babu annuri yace laifi ne don uba ya shiga Wakin Wanshi ? AruWe tace ba laifi bane, amma meyasa kake yi mashi la6e ? Shiru ya yi yana duban fuskarta, A yadda suke atsaye suna fuskantar juna, Ko kafaWarshi bata kai ba, saboda ?arantarta, doguwar rigace a jikinta ta shan iska, ta tufke blonde hair dinta da ribbom.

 Ka tsare ni da ido kana kallona, Baka bani amsar Tambayata ba ! a ?agare ta faWa, Ya rasa ya zaiyi ya kawar da hankalinta daga tambayar da take yi masa.

Dubara ce ta faWo masa, da sauri Ya sanya Hannu biyu ya ru?e waist dinta, sama ya Waga ta kamar Wiyar roba Ya kwantar da ita saman gadon shi Rumfa ya yi mata da faffaWan kirjin shi, tuni tasha jinin jikinta.

 Kin tsareni da tambaya ke ga mai Wa ko? Ni da ke waye yafi wani iko da shi? Yawu ta haWiya muryarta na Wan rawa ta furta kai

 Kinsan da hakan shine kike yi min tambayoyi kamar ?ar jarida ? Shiru tayi mashi tana faman zazzare green eyes dinta.
 Jibarki ?ar mitsila dake kamar in matseki nake ji dariya ce ta kubce mata, natsuwa yai yana kallon fararen ha?oranta.

 Yanzu dai faWamin me kike shiryawa a birthday din Baba? Ba za kiyi kitso da ?unshi ba ?

 Idan zaka kai ni inda za ai min kitson da ?unshin inaso, sai dai anko din da zasu sanya nasan hajiya saratu bazata barni in shiga cikinsu ba ko da na siya a marairaice ta ?are mashi maganar.

Jan hancin ta ya yi da hannun shi Ina ruwanki da ita? Ai ba dole sai kin shiga cikinsu ba, babban tarone fa za ayi akwai manyan ba?i da zasu zo, kema zaki samu ?awaye acikin su

Da shagwa6e ta furta baby ba zaka gane ba, hajiya saratu bata son ganina, ita fa haryan zu kallon ?ar aiki take Yi mini, hada faWa min wai ba ata6a canzawa tuwo suna, ni dai inajin fargabar ta disgani acikin su, ?wara Inyi zamana acikin gida zai fiye min kwanciyar hankali da?yar ta ?are maganar ganin yadda ya tsare ta da ido, kallon so da ?auna ya ke yi mata.


 Meyasa kike kira na baby? Ko kunya bakya ji? Nayi maki kama da ?aramin Yaro ne? fuskar shi a Waure yai mata maganar.
Kashe mashi ido Waya tayi I call you baby because you re like a baby to me, and I still take care of you kuma ina feeding dinka Wan zaro mata ido ya yi da sauri ta rufe baki tana faman zazzare mashi ido.

Da zolaya ya furta raini ya fara shiga tsakanina dake, saboda ina tu6e kaya agabanki ko ? Runtse mashi ido tayi tana faman ti?ar dariya.

Jinjina kanshi yai ki saurare dakyau, daga yanzu idan saratu ta faWa maki magana ki dinga mayar mata da martani, ki daina nuna kina jin tsoronta shiyasa ta rainaki, Kina jina ko ? Tana faman zumbura mashi pink lips dinta tace ni bazan Iyaba, saboda ta girmeni ko a shekaru kuma ?anwarka ce,

 Umarni nake baki ba shawara ba, kada na kuskura na ?ara ganin kin dawo gidan nan kinayi min jan ido akan saratu tayi maki wani abu, idan ba haka ba zaki kar6i horo mai tsanani daga gareni, muryar shi a kausace yake yi mata maganar
Kama kunnanta ya yi da yatsan hannun shi Idan kunne Ya tsira ? Da sauri ta ?arasa mashi karin maganar Jiki Ya tsira My baby murmushi yasaki tare da manna mata kiss saman soft lips dinta.

*GIDAN ?AN IYA*

Zahra ce zaune saman prayer mat, ta zumbula dogon Hijabi, fuskarta sharkaf da hawaye, tun da ta kammala sallar Magrib bata motsa ba, hannunta ru?e da cazba sai faman janta take Yi, damuwar duniya ta isheta, tun Wazu data farka daga bacci ta kasa Yin wanka ko abinci bata ci ba, babu kuma wanda yai tunanin ya le?o ta, tayi trying kiran layin mahboob ya?i picking call din, har yanzu bai le?o cikin gidan ba, ga lokaci yana ta tafiya gani take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login