Showing 6001 words to 9000 words out of 260999 words

Chapter 3 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ya Wauke ta abayan Gabriel, hankalinta kwance sai sharar bacci ta ke Yi, Jemimah kuwa Idonta biyu Sai faman baza ido ta ke yi Hannunta na a ru?e dana Angel.

"Me yakamata Mu yi yanzu don ganin An dawo mana da Wan uwan mu Danish"! Haris ne yai maganar

"I'll go and get him back tonight!" da ?warin gwiwa Angel ta yi maganar.

"Ta yaya hakan zai yiwu? Angel muna jin tsoron wani abu ya same ki, Me zai hana mu tafi gaba Wayan mu"! batul ce ta yi mata maganar fuskarta da alamun damuwa

"Zan bi ki Angel Mu tafi atare"! Gabriel ne Ya yi maganar" girgiza kai ta yi"Bana so wani abu ya samu Waya daga Cikin ku, Bazan bari ka bini ba Gabriel ni kaWa nake so na jefa kaina cikin hatsari Zan ro?i Allah ya tsare ni....." muryarta na Wan rawa ta ambaci hakan kamar akwai rauni atattare dani, tabbas tana matu?ar fargabar abu biyu, Na farko tafiyar da zata Yi tabar su da jimamin Awani hali take a ciki, Na biyu HaWuwarta da garkuwar kurkuku, Wani irin azababben tsoron shi ta ke ji tun kafin ta yi tozali da shi.

"Genie Pls don't leave me Ki tafi dani..." cikin shesshe?ar kuka Jemimah ta yi maganar tana ?ara dam?e hannun Angel dake ru?e da nata.

"Wlh Angel hankalin mu ba'a kwance ya ke ba, Gani mu ke kamar wani abu zai faru da ke idan kika tafi kika barmu" Deeja ce ta yi maganar, ta fahimci kowannan su atsorace ya ke da tafiyarta.

"Angel bazamu ta6a yafewa kan mu ba idan har wani abu ya faru dake ta silar taimakon mu da ki ke ?o?arin Yi,"

Javed ne yai maganar, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin kowannan su, La66anta sai kerma su ke yi sam ta kasa buWe baki ta yi masu magana sai binsu ta ke yi da ido, Zuciyarta ba ?aramin karaya ta yi ba, Ita kanta tana ji a jikinta cewa wannan karan zaiyi wuya ta dawo cikin su ba tare da wani mummunan abu ya faru da ita ba.

"Idan har muka ji kin daWe baki dawo ba, Zamu biyo ki ne"! Hibba ce tai maganar hawaye kwance saman kuncinta

Da?yar Angel Ta iya tattara natsuwarta tare da cewa"Ku daina sanyawa ranku cewa wani abu zai faru dani, idan ma ya faru dani to ku sani ?addarata ce wadda ban isa in sauyata ba, Ni da Allah na dogara wani mutun ko Aljan Waya daga cikinsu bai isa ya cutar dani ba face da izninsa, ?an uwana addu'arku kawai nake bu?ata akan Allah ya bani Sa'a akan abunda zan je nema......." Sautin shesshe?ar kukansu ne ya gauraye ?akin tsohuwa.

Muryarta adisashe tace"Tunkafin ma na tafi kun fara kuka? Meyasa? Dan Allah ku daina kamar fa kuna discouraging Wina ne, Nafi so inga kuna ?arfafa mini gwiwa, ganin hawayenku da nake yi ba ?aramin raunata mini zuciya ya ke yi ba.

"Ba zamu iya jurewa rashinki atare damu ba Angel, wlh muna ?aunarki fiye da yarda muke son kanmu, bamu son wani abu ya same ki, saboda mu kike ?o?arin jefa kan ki ga halaka taya ba zamu yi kuka ba? Angel ke uwace agare mu, Kin fiye mana iyayenmu da su ka yi watsi damu, Dan Allah Angel karki bari mu rasa ki" Sosai suka sanya mata kuka

Itama ta fashe masu da matsanancin kuka mai cin rai tamkar ana zare ranta Cikin muryar kuka take magana

"Shiga prison Ya zamar mun dole, Idan har ban je ba rayuwar mu tana a cikin haWari, sannan Al?awari ne na Wauka Dole na cika shi ku daina raunata mun zuciyata kada kusa Na gaza......" Kasa ?arasa maganar ta yi saboda raWaWin da ta ke ji a cikin zuciyarta.


Tsawon lokaci suna kallon kallo a tsakanin su kafin ta tsagaita da yin kukan tace da batul"Ga amanar jemimah, Ki rungume mun ita a ?irjin ki har sai ta yi bacci, da zarar na dawo zan kar6i abuna" cikin sanyin murya batul ta amsa mata da cewa In sha Allah zan bata kyakkyawar kulawa har ki dawo Angel, murmushin ya?e ta ?a?aro kan fuskarta tare da kallon su Parveen da ke atsaitsaye tace"Zan tafi ba za ku rungume ni a jikin ku ba"? Jin haka yasa da sauri suka matso kusa da ita, ?aya bayan Waya suka dinga rungumeta a ?irjin su, kamar karsu sake ta, a ?arshe Ta Soma tafiya tana ja da baya tana kallon su idanuwansu akanta, Jiki amace ta juya tare da buWe ?ofar Wakin tsohuwa tamira, Da gudun gaske Cikin duhu ta nufi sashen toilet Winsu tana faWowa Hasken sauran fitilun dake a cikin toilets Ya haskaka idanuwanta, buWe ?ofar toilet Win ta yi tare da shigewa Ciki. Yatsun hannunta na kerma ta sanya jamlock ta datse ?ofa don kar su yi gigin cewa zasu bi bayanta, A jikin ?ofar ta jingina bayanta sosai ta fashe da kuka gudun kada su ji sautin kukanta yasa ta toshe bakinta da tafin hannunta, tsawon mintuna goma shabiyar tana sharar ?walla kamar ruwan hawayenta zasu ?are sai da tayi mai isarta kafin ta soma tafiya tana tunkarar Tagar da zata dura, har zata gifta tukunyar fulawar nan ta Wan dakata da yin tafiya kafin a hankali ta kalli inda ta ke a jingine jikin bango, duk da halin da take aciki na fargaba sai da tayi mamakin ganin an maida tukunyar a mazauninta na asali, shiyasa Wazu tsohuwa Zafreen bata samu damar ganin ?ofar ba saboda an toshe ta, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe idunuwanta daga bisani ware su sosai akan furen Danish da ganyayyakin shi su ka bubbuWe gwanin ban sha'awa, Kyakkyawar fuskarshi ta ke imagining acikin idanuwanta, aranta kuwa tana ayyana koya Zata Ganshi a yanzu daya koma Giant? Da wannan tunanin Angel Ta ?arasa gaban glass window Win Ta janyo bokitin Ta haye sama A hankali ta 6a66ako glass Win tare da curo shi ta dire shi ?asa kafin ta daddage ta haura Saman tagar bakinta Wauke da Bismillah.

Zu?unna tayi a jikin bangon da ta faWo, wani irin Sanyi ne ya mamaye sassan Jikinta, Ga tsoro daya mamaye zuciyarta, Biji biji take ?arewa doguwar hanyar kallo, duhu sosai babu haske sai dai da alamun haske a ?arshen hanyar Inda Babban filin nan ya ke.

mi?ewa Tayi tsare tare da Sanya hannayenta Biyu ta ru?o duguwar sumar kanta tare da nannaWeta ta jefar da ita saman gadon Bayanta, tunawa da addu'oin da ta karanta a jiya da tayi fitar nan yasa a yanzu ma ta soma ambaton su acikin zuciyarta, A yayin da take tafiya tana nufar cikin kurkukun........

*Boss Bature
'? Mu haWu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game neman ?arin Bayani Ya tuntu6i Layina na whatsapp 08103884440 banda Kira just message=?
?*

_~*
'=؋?BOSS LADIES WRITERS=؋?
'*~_


*KURKUKUN ?ADDARA*



_The Prisoners 2=?%?=ث?_

*Daga al?alamin Hafsat Bature*


~Middle step~



_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty=ؔ?._





Bayin Allah su Batul zullumi da fargabar Halin da Angel zata shiga Ya hana su runtsa a daren ranar, A Wakin tsohuwa Tamira su ka zazzauna saman floor, zuciyarsu na harbawa da faWuwar gaba, Sun yi shiru kowa da a bun da ya ke sa?awa acikin ranshi. Deeja ce tai ?o?arin tunasar dasu akan su yi mata addu a. Su ka amsa mata da toh, nan fa kowan nan su ya soma karanto addu o in da Angel ta koya ma su.

Dare ya nutsa sosai Azeeza tuni ta koma bacci, a saman ?irjin Gabriel ta kwantar da kanta, Hannun shi na dafe da bayanta kamar zai mai da ta cikin sa.

Jemimah tana a kwance saman cinyoyin Batul ta ?i yin bacci, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta runtse idon ta ta yi bacci amma ta kafe akan sai Genie Winta ta dawo, a ?arshe ma da su ka matsa mata sai ta sanya masu kuka, Tsananin tausayinta ne ya kama su, Haris yace ku bita a hankalin ni banga laifin ta ba, saboda ita yarinya ce ta saba kwana rungume da Angel dole taji ba daWi, Rarrashin ta ya kama ta mu yi, Amsa mashi su ka yi da toh, atare su ka haWu suna rarrashin jemimah da?yar su ka shawo kanta.

Parveen sai hammah ta ke yi Ga yunwa ga Bacci, Naufal da ke zaune a gefenta Yace da ita Ki kwanta ki yi bacci mana, Kin ishe ni da hammah harara ta Wan jefa mashi tare da cewa in yi bacci fa ka ce? Sai kace bansan ciwon kaina ba, Ta ya zan iya runtsawa bayan yan uwar mu tana acikin kurkuku.... ta6e la66ansa Yai Naji daWi da ki ka yi Hankali bata tanka mashi ba sai ma Waura kanta da ta yi asaman laps Winshi.

 Batul mu tashi mu bi Genie mu Wauko ta Muryar Jemimah ce ta yi maganar Fuskar ta ta yi sumtum saboda kukan da tasha, Lallashinta Batul ta yi Ki yi ha?uri kin ji, In sha Allah zata dawo Cikin Mu, Badajimawa ba, Zumbura ba ki ta Wanyi  Toh idan ta dawo zamu gudu ko ? gaba Waya hankalinsu Haris ya dawo kanta

Murmushi Batul ta sakar mata Eh mana da zarar ta dawo zamu gudu mubar kurkuku.... tunkan ta kai ?arshen maganar Jemimah ta katse ta da cewa Zamu koma gidan daddyn Genie Ko? In da zamu sakata mu wala mu yi rayuwar mu babu takura Allah yasa genie Win mu ta dawo da wuri na ?osa muje inga gidan daddyn ta

farin cikin da su ka gani akan fuskar jemimah a yayin da ta ke yin maganar yai matu?ar karya masu Zuciya, Har sai da suka ji hawaye sun cika idanuwansu, cikin rauni na murya Deeja tace da ita

 Jemimah Pray for Her! Tana bu?atar addu ar mu, mu dage da yi mata addu a har sai ta dawo Cikin mu jinjina kai jemimah ta yi tare da cewa tom zan mata addu a ta ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta, acikin zuciyarta tana ambaton Ya Allah ka dawo min da Genie Wita in dai kana son farin ciki na....


 Gabriel Ka tada azeeza ta tashi Mu haWu mu duka wurin yi mata addu a ba yadda za ae muna acikin tashin hankalin nan ita tana bacci, ko dai jemimah da ta ke ?arama a cikin mu ta kasa runtsawa balle ita Rubina ce ta yi maganar, Girgiza mata kai Gabriel yai alamar Bazai tayar da ita ba

 I m sorry to say I can t wake her I don t want to worry her, Just Let her sleep. Waure fuska Rubina ta yi jin a bun da yace, ita haushinta yadda suka tashi hankalin su akan Angel amma ita Azeeza ta lafe jikin shi Hankalin ta kwance ta ke sharar bacci.

 Akwai matsala fa! Dare Yana ?ara nutsawa babu alamun Angel zata dawo Sarah ce ta yi maganar tana daga zaune Ta jingina bayanta jikin bango, Ta saki dogayen ?afafuwanta ?asa.

 Duka yaushe ta tafi da har za ki fara tunanin akwai matsala! Pls mu yi mata fatan Alkhairi, Ni gajan ha?uri ke bana so acewar Haris.

To jama a abu fa kamar wasa A ?alla Angel ta Wauki tsawon awanni babu ita babu alamarta, Idanuwansu sun kaWa sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa ga zullumin rashin ta atare da su, sun dage sai addu a Su ke Yi mata, Ba zato ba tsammani Hasken ?akin su ya gauraye ko ina, ta jikin ?ofar Wakin tsohuwa da bata ?arasa datsewa ba su ka hango hasken da ke kurWaWowa, Hankalinsu Ba ?arami tashi yai ba, A kiWime su ka mimmi?e tsaye hatta Azeeza da ke bacci sai da ta farka tana faman murza idanuwanta da yatsun hannayenta.

kallon kallo suka shiga jefawa junansu fuskokinsu Wauke da matsananciya damuwa
 Innalillahi wa inna ilaihirraji un; shine kalmar da ta fara fitowa abakunansu Deeja, Yayin da su ke a tsaitsaye cirko cirko, Bakomai ne ya tayar masu da hankali ba face ganin Safiya ta yi ba tare da Angel ta dawo ba. Nan ta ke ransu ya basu cewar wani abu ya faru da ?ar uwarsu.................

Shine meke Faruwane ata 6angaren Angel!?

Ai tun lokacin data watsa da gudu ta nufi Cikin kurkuku, Sautin kururuwa
Mai ?araji da gurnani ya cika kunnuwanta, ga wani azababben San yi da ya addabe ta, kamar jaura ta gifta Cikin duhu ta ke gudu

Adai dai lokacin da ta Waura ?afarta saman ground floor Win nan Inda ke kewaye da dogayen benaye Ba zato Ba tsammani idanuwanta su ka sauka akan ?afafuwan Tsohuwa Zafreen Lamarin yai matu?ar gigitar da ita, sam Ba ta yi tsammanin Zata ci karo da wani abu ba ita kawai ta sanyawa ranta cewa Danish ne kaWai mutumin da zata haWu da shi.

Mummunar faWuwa gabanta yai, ?irjinta ya hau bugu da ?arfi da ?arfi A firgice ta Wago da idonta akan tsohuwa zafreen da ke a ru?e da sanda, Kasancewar Filin Yana da Fitilu masu haske can saman silin ya gauraye ko ina, daga ?asa har sama shigar Jajayen kaya ne a jikinta kamar kullum Fuskarta na asanye da takuntumi.

 Ya Allah saida nayi addu a kafin in fito but why na fara Cin karo da mummunar tsohuwar nan Ina lillahi..... acikin zuciyarta ta ambaci hakan, Kafin ta yi wani yun?uri tsohuwa Zafreen ta soma tunkarota sautin takalmanta ?was ?was har cikin dodon kunnan Angel, Duk ta ku Waya idan ta yi sai gaban Angel Ya faWi, tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba.


Ko da ta ?araso gabanta, Bata tanka mata ba, Sai bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo irin na marasa imani, ShuWayen idanuwanta sun Ciza launinsu.

 Ban yi mamakin Ganin ki ba Unaisah! Ina ji arai na ba yau ba ne rana ta farko da kika fara ?etare Iyakar Ki, Taurin kan ki da kafiyar ki da kuma rashin tsoron ki su ne suka ?arfafa maki gwiwar shigowa Cikin prison! Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoner Win da ya ta6a ?etare Iyakar shi ba sai Akan Ki !

Magana ta ke yi muryarta na fita da sauti mai amo.

yawu Angel ta haWiya, tuni tasha Jinin jikinta, Ido ya raina fata sam ta kasa magana, Zufa sai tsastsafo mata ta ke yi kan fuskarta har WiWWiga ta ke a ?asa.

 Ko za ki Iya faWa min menene Ya fito da ke? Kuma Ta yaya akai Kika tsaga bangon Wakin ku kika fito ? Muryar Angel na rawa ta soma magana Tsautsayi ne da ?addara, dan Allah kada ki cutar dani, Zan koma inda na fito, Kawai Inason ganin Wan uwana Danish ne shiyasa na fito neman shi..... kasa ?arasa maganar ta yi sakamakon sautin Dariyar tsohuwa zafreen da ya tari numfashinta.

Tsagaitawa ta yi da yin dariyar, ta soma matsawa tana ?ara kusanta kanta da Angel, A tsananin tsoroce Angel ta ke Ja da baya tana girgiza mata kai

 Tun jiya dana shigo Wakin ku Raina ya bani cewar Wani abun ku ke shiryawa kuma ke ce jagora a cikin tafiyar, Saboda prisoners basu da wayan da zasu Iya ta6uka wani abu, Unaisah ke ce ?warin gwiwar su, Babban kuskuran da ki ka aikata shi ne ?etare Iyakarki! Hakan Ya sa6awa dokar Kurkuku! Na yi imanin babu mai Iya ?watarki daga hannu na! Saina rushe duk wani sashe na Jikin Ki da ke da ?arfi zuwa mai rauni...... Zazzare ido Angel ta yi tamkar ?wayar zata faWo ?asa Jikinta sai kerma ya ke yi.

 Kin jama kan ki bala i da masifa! Not only u! Hatta ?an uwan ki da Ki ka baro Waki, suna cikin masifa, Zanje gare su Bayan na gama da ke, duk saina tarwatsa farin Cikin da ku ke da shi Muryarta a kausashe ta ke furta maganar.

Hawayen da su ka taru a cikin idonta ne suka soma gangarowa saman kuncinta da wani irin rauni na murya ta furta duk horon da za ki yi mani kada ki haWa da ?an uwana, Ni ce mai laifi don haka Ni za ki hukunta

Fuskar Tsohuwa Zafreen a murtuke ta jinjina kai tare da cewa  Umarni ki ke Bani? In yi abunda kike so ? A ruWe Angel ta girgiza kai ba tare da ta iya furta mata komai ba.

 Zan jaraba Ki inga idan zaki Iya ceton Kanki, Nasan baki ta6a sha?ar ?amshin mutuwa ba amma yau zansa ki sha?eta sosai, waWannan Idanuwan naki launin ruwan toka yau zansa su koma launin Ja, Hawayen da ke fito wa ta cikinsu zansa su janza launi zuwa na Jini, La66an ki da su ka saba gaya wa Mutane magana Ayau Win nan zan canza masu kamannin..... Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi tarasa gane inda kalaman tsohuwa Zafreen suka dosa.

Ja da baya tsohuwa zafreen ta soma Yi yayin da ta ke sakin Shu umin Murmushin nan nata na tantiran ?an duniya waWanda su ka ga jiya su ka ga yau

Juyawa Baya ta yi tare da nuna ma Angel Third floor da sandar hannunta

 ?an Uwan ki da ki ke nema Yana a hawa Na Uku, Za ki Iya zuwa gare shi, Fatan Nasara Kalmar ?arshe da ta furta mata kafin Ta buga sandar hannunta ?asa, Nan ta ke hayaki Mai kamar an watsa tiya gas Ya cika idanuwan Angel, bata Iya ganin komai amma taji aranta cewa tsohuwa Zafreen ta 6ace daga wurin da ta ke a tsaye, a hanzarce ta kamo sunan Allah taci gaba da ambaton duk wata addu a da tazo bakinta, Cikin ?ankanin lokaci ?urar ta washe Idanuwan ta suka dawo dai dai. A lokacin ta riga ta yanke shawarar komawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login