Showing 117001 words to 120000 words out of 260999 words

Chapter 40 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

mashi Mommyn nasa, wani lokacin tun kafin ta farka daga bacci kiran su ke shigowa wayarta saboda jarabar junaid.

Tayi zurfi cikin tunaninta, Wayar Zahra ta soma yin ringing, Kafin ta wurga idonta kan inda zahra ta ajiye wayar saman drawer, da ?arfi taji sautin buWe ?ofar toilet, Ras taji gabanta Ya fadi ganin zahra ta watso aguje, jikinta duk kumfa daga ita sai gajeran towel tayi Waurin gaba da shi, hatta fuskarta kumfar sabulu ce, mi?a hannu tayi ta rurumi wayar, tsabar zumuWin ganin wanene ke kiranta, fatanta Allah yasa hajiya saratu obinna ce, cikin sa a idonta yai mata nuni da sunanta akan screen, sai ?o?arin Waga kiran takeyi kumfar hannunta ta hana touching din yin aiki, kamar zata fashe da kuka, sai da aneelerh ta taimaka mata wurin answer mata call din tukunna ta samu natsuwa, a Hands free ta sanya kiran don suji me zata je
Cikin girmamawa zahra tayi mata sallama Assalamu alaikum kamar tana agabanta.
On the other hand sautin muryar hajiya saratu ya karaWe kunnuwansu
 Wa alaikum salam
 Ina kwana hajiya, fatan kun tashi Lafiya, wlh bana a kusa da wayar ne, kunata kira bansamu damar Wagawa ba, da yake na Wan shiga toilet ne

Aneeleeh dake zaune saman gado, dariyace ta kubce mata da sauri ta cakumi pillow ta toshe fuskarta dashi don kada sautin Ya fita, bakomai ne ya sanyata yin dariya ba face yadda zahara keyin waya kamar ?ar maro?a, ga kumfa a jikinta.

 Bawani abu ai, nayi maki uziri, dalilin dayasa na kira layin ki, last time da kukayi mana decoration aikin ku ya yi mana kyau, muna so za a ?ara Yi mana wani next week, sannan muna so za a fidda mana anko wanda zai dace damu

Da sauri zahra ta kar6e da cewa in sha Allah hajiya komai kuke so za ayi yadda ya dace, hada ?unshi da kitso idan akwai mai bu?ata

Hajiya saratu tace okey, You can send me the list of your services and I ll add what I want to the list, through text message zaki tura min


 Toh hajiya in sha Allah, Mun gode sosai, da kiranmu da ku kayi, kuma in sha Allah zaku same mu masu biyayya ga duk abunda kuke so, bayan sunyi sallama da Hajiya saratu, Zahra ta sauke nauyayyar Ajiyar zuciya, Ta fasa ihu Tana faWin Alhamdulillah! lokacin Yin arziki na Yayi, wai yau ni ce Aunty saratu ta kira awaya? nayi mamaki wlh, matar tana burgeni bata Waukar raini, akwai harkar arzi?i.


Ta saki baki sai sambatu take yi, Kumfar Jikinta duk ta bushe har ?asan tiles ruwan ke zuba, sautin dariyar Aneelerh ne Ya fargar da ita, da sauri ta jefa wayar saman mattress din, ta ruga da gudu ta faWa toilet tana dariya.

Da?yar Aneeleeh ta samu ta tsagaita da yin dariyar. Ta Wago da kanta daga jikin pillow ta jingina bayan jikin head board.
 Aneelerh muryar Mamie ce ta ratsa kunnanta, zumbur ta sauko daga saman gadon ta nufi kofar Wakin, shigowa Wakin Mamie Ta yi suka ci karo da ita oh dama kina anan? Inata kiranki na duba ko ina ban ganki ba Aneelerh na murmushi tace mamie kema kinsan bani da wurin zuwa a gidan nan inba Wakin ?ar uwata zahra ba
 Okey, ina zahran ?

 Ta shiga toilet yin wanka, amma takusa fitowa

Mamie tace Okey, idan ta fito, muna jiran ku a dining, ku zo muci abinci

Ta amsa mata da toh, bayan fitar mami Wakin, komawa ta yi gefen gadon zahra ta zauna, bada jimawa ba zahra ta fito chest dinta daure da towel, da zolaya Aneelerh tace Lashe money an fito lafiya ? Tuntsirewa zahra tayi da dariya tana fadin aunty aneelerh kuWi duniyane, Dole inso kuWi, saboda sune maganin talauci, maganin ?as?anci da wula?anci, idan kina da kuWi kin fi ?arfin raini wlh, girmama ki za a dinga yi kamar wata basarakiya, taya mutum bazai so kuWi ba? Yanzu fa ko a dangi masu kuWi sune masu faWa aji, idan baka da kuWi toh baka da banbanci da Allon bango

Fashewa Aneeleeh tayi da dariya, zahra ta za?e sai kora mata jawabi ta ke yi dangane da kuWi.

 Zahra wasu kuWinfa ba alkhairi bane, suna kai mutun ga shagalar duniya har ya halaka

 Aunty Aneelerh, nima ai bana ro?on Allah yabani kuWi kaitsaye batare da nace Allah yabani masu albarka ba, kuma ni burina inyi arzi?i don al umar annabi su amfana da ni, Ina kwaWayin inga na taimaki marasa ?arfi.... .

 Zahra Allah ya dubi kyakkyawar niyarki, inayi maki fatan Alkhairi
 Ameen auntyna

Shaf shaf ta kammala shiryawa, cikin riga da skirt, ta dawo gefen Aneeleerh ta zauna bayan ta Wauki wayarta

 Ki tashi muje muci abinci, su mamie suna jiran mu a dining
 Inaso ne in fara turama aunty saratu list na abunda mukeyi, zaki Iya zuwa kada su ji mu shiru mi?ewa Aneelerh tayi daga gefen gadon ta fuce daga Wakin.

Through text message ta tura mata sa?on kamar haka

Here s a list of services that  Zahra s World of Beauty could offer:

- Bridal makeup and hairstyling
- Event planning and decoration
- Haircuts, color, and styling
- Manicures and pedicures
- Facials and skin care treatments
- Massage and body treatments
- Waxing and other hair removal services.

Bayan ta kammala rubuta sakon a ?alla saida ta maimaita shi yayi sau ashirin gudun kada ace tayi kuskure kafin ta tura mata, fuskarta Wauke da murmushi ta ajiye wayar saman pillow, ta mi?e ta nufi falo domin Yin breakfast, fatanta Allah yasa Hajiya saratu ta mayar mata da martanin sa?on da wuri, taci buri sosai akan zuwa estate dinsu, ko dan ta haWu da Owais idan Allah yasa lokacin ya dawo ?asar.


*KURKUKUN ?ADDARA*

*AN YANKA TA TASHI &?=?y?*

Babban Wakin tarone mai girman gaske, wanda akeyiwa la?abi da fadar matsafa, Mallakin shuwagabannin kurkukun ?addara, ta ko ina manya manyan matsafane ma?il acikin fadar, zazzaune saman kujeru dake a jere tsakiyar fadar, kowannansu yana sanye cikin shiga ta ba?a?en dogayen riguna masu huluna, sunyi 6adda kama ta yadda mutun bazai ta6a Iya ganin koda ziririn gashin kansu bane, Hannayensu da ?afafuwansu ba?a?en safunane, Yayin da fuskokinsu sun sanya masu mask me suffar ?warangwal gwanin ban tsoro, sa?o da lungu ta fadar, Wasu Gabza gabzan giants ne daga masu ?aramin mi?ami har izuwa manyansu masu star uku a gaban kakinsu, wata irin ?ira garesu mai matu?ar ruWarwa, rikitarwa da razanarwa da kuma tsoratarwa, kallonsu kaWai zai Iyasa zuciyar mutun ta buga, Ga tsawo da Allah yayi masu tun daga kan tsayuwarsu zaka tabbatar babu Wigon imani akansu.

Daga can saman karagar fadar, wasu jigunannun arm chairs ne guda shidda ?an ubansu, mutane shiddan dake zaune saman kujerun dogayen rigunane launin jajaye na maza a jikinsu masu huluna, baka ta6a Iya tantance suffarsu saboda sun 6oye ko ina na jikinsu, hannyensu na ru?e da Sanda wadda aka ?erata da zallar zinari, daga gabansu zungureran teburi ne, samanshi ma?il Yake da kayan ciye ciye dana shaye shaye daga ciki hada Jinin mutun da farfesun naman mutun ga zungura zunguran kwalaban giya, da Kayan marmari nau i kala kala, da gasasshen nama na dabbobi daban daban.

Komai na fadar matsafan tun daga kan ?ofofi da tagogi da fentinta da jan carpet din dake shimfiWe ?asanta, gaba Waya Launin ba?i da Ja ne, saman rufin fadar wasu haWaWWun fitilune masu haskaka cikinta.

Zanunnukan dake a jikin bangon fadar, na kan ?warangwal ne, da yatsun hannun shaiWanu masu akaifu za?o za?o da sauran zanunnuka masu ban tsoro.

Daga gefe Waya tacan 6angaren da Arm chairs din nan suke Tan?ameman madubine wanda suke Kira da Allon tsafi, gaba Waya Hankalin matsafan yana akan Allon tsafin nasu, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, ga dukkan alamu wani abu suke kallo wanda yai silar Wauke masu hankulansu..........


(Nima kuma na Wauke al?alamina)




*Boss Bature
'? Mu haWu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*_


~Middle step~


_The Prisoners E21=?%?=ث?_



*Daga al?alamin Boss Bature*




A ?alla sun shafe mintuna suna kallon Allon tsafin, ga dukkan alamu sun girgiza da ganin abun da idanuwan su ke gane masu, Hankulan su sun yi matu?ar tashi, abun ya yi mugun Waure masu kai, bakomai bane suke kallo acikin Allon tsafin face Garkuwar kurkuku tare da Angel, duk wani motsinsu akan idonsu tamkar video haka suke ganinsu, lokaci Waya Allon tsafin yayi duhu hoton fuskokin su ya 6ace.

Kowan nan su ya sauke Ajiyar zuciya, sun natsu suna jiran jin bayani daga bakunan shuwagaban nin su.

?aya daga cikinsu ne yai gyaran murya, da wata irin kakkausar murya mai sautin gaske tamkar bata mutun ba, ya soma Yin magana Cikin harshen su na shahararrun matsafa ni kuma ina fassara maku.

 Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu mi?e tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoners Win da suka tsira daga kurkukun ?addara ba, su ne na farko kuma sune na ?arshe, da farko sunyi nasarar ?etare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahalu?in da ya isa ya iya ?etare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya Wauke shi munyi nasarar yi mashi abunda ya dawo gare mu sai dai wani abun al ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi, kamar yadda kuka gani a allon tsafin mu, shin me ya jawo hakan ? Yai tambayar yayin da yake gyaran zaman shi.

Mutumin dake a gefenshi, Ya Waura da cewa Yarinyar da ke atare da shi itace silar komai, kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, Cewa itace za ta yi silar tarwatsa tarihin kurkukun ?addara, gangancin da mu ka yi shine HaWa su wuri Waya da garkuwar mu, sakamakon sha?uwar da sukayi a tsakanin su, taja shi ga faWawa tarkon sonta, mu kan mu bamu ta6a tsammanin Garkuwar prison zai Iya kamuwa da matsanancin so irin haka ba dakatawa yai da yin maganar yana motsa yatsun hannunsa, kafin ya cigaba da cewa

 Sai dai har yanzu bamu rasa power Winmu ba, Garkuwa namu ne har abada, mu ke ru?e da masarrafin da zamu Iya sarrafa linzamin shi, mu kaWai ne mu ke da iko da shi, ba zamu ta6a yin danasanin ?aura shi amatsayin magajin kurkukun ?addara ba, kuskure Waya da muka tabka shine sakacin da mu ka yi da har ya samu nasarar guduwa daga kurkuku, Ni ban damu da sauran Yaran da suka ku6uta ba, saboda basu da amfani a wurinmu, mun ci moriyar su, mutun ukun ne sune rauninmu, Na farko Garkuwarmu dole sai da shi za a Iya Cin galaba akanmu, Na biyu ?addarar kurkuku, yarinyar ta fi sauran hatsari tun da har ta Iya Jan hankalin garkuwarmu, wanda nayi imanin da ace babu ?auna a tsakanin shi da yarinyar ba zai ta6a taimakon sauran ?an uwan shi don su gudu daga tarkon mu, Ya faWa yana mai jan dogon numfashi Ya fetsar da shi, ya cigaba da faWin  Itace silar komai, kuma itace kaWai zata Iya sarrafa shi bayan mu, idan kuwa hakan Ya faru zai Iya fallasa mana sirrin mu ya kuma taimaka wurin ruguza kurkukun ?addara ! Da ?arfi Ya ambaci hakan Yana mai nuna fusatar shi.

 Yarinya ta ?arshe itace bugun zuciyar kurkukun ?addara, kamar yadda ya zo mana a allon tsafin mu, idan har muka samu nasarar Cire Zuciyarta daga ?irjinta zamu samu ?arfin Iko fiye da wanda muke da shi a yanzu, Ita kuma ?addarar kurkuku dole mu dawo da ita cikin mu idan har muna son ta zamar mana ?addara mai kyau, barin ta awaje shi zaisa ta zamto mummunar ?addara agare mu Tamkar mayunwacin zaki haka yake kora masu jawabi yana fitar da huci.

Bayan ya rufe baki Na gefen shi ya soma magana da wata irin murya ta dattawa waWanda suka Shahara a fagen zalunci.

 Tun fil azal, Banso Muka dam?a amanar mu ga tsohuwa tamira ba, dama tun lokacin Sai da na musa akan hakan, Ni dama nasani Jinin Habibullah ba zasu ta6a zama amintattun mu ba, sai gashi sun yaudaremu sunci amanar kurkuku, sun kashe mana Zafreen Waya daga cikin shuwagabannin mu, babu wanda ya ta6a tsammanin zasu Ci amanar mu ita da Wanta Salsabeel, sai da suka bari mun basu yarda mu su kuma suka butulce mana, ha?i?a Nayi takaicin rasa gangar jikin tamira, da ba abun da zai hana mu azabtar da ita, mu sa6ule naman jikinta sannan muyi farfesun shi muba ma Karnuka su shanye roman, amma duk da haka bamu makaro ba, Zamu huce haushin mu akan Wanta Salsabeel mutumin da yayi maganar babu Wigon imani akansa.

Bayan ya dasa aya a maganar shi, wani daga cikin shuwagabannin Ya numfasa tare da cewa Garkuwa ya yi mana mummunar 6arnar da ba zamu Iya gyarata ba, bamu ta6a tsammanin zai Iya yi mana haka ba, sai dai ba zamu Iya hukunta shi ba, saboda shi jinin mu ne, abu Waya da zamu Iya yi mashi shine mu hana shi jin daWin rayuwarshi da Yarinyar, mu shiga tsakaninsu, horon da zamu bashi kenan, sannan zamu ci gaba da sarrafa shi wurin azabtar da mutane, kafin muyi nasarar dawo da su Cikin mu, hikmar yin hakan mutane zasu fara tsoranshi suna nuna mashi ?yamata, zai ji duk duniya kamar ba a sonshi ne, kunga anan zai yi tunanin mu kaWaine gatanshi, kurkukune kaWai inda zai zauna yayi rayuwarshi ba tare da ?untata ba, daga lokacin daya fara wannan tunanin mu kuma zamu samu damar kwashesu su ukun mu dawo da su cikin mu ! Ya kai ?arshen maganar tare da buga hannun arm chair Win da yake a zaune, gaba Waya matsafan suka fashe da dariya mai sautin gaske tamkar ana bubbuga ganga, jikinsu har jijjiga ya ke yi saboda tsabar yadda suke yin dariyar kamar dokuna.

 Mun Fi ?arfin mutun, Ko mutuwa tsoron tunkararmu take Yi, shiyasa muka daWe muna she?e ayarmu, shan jinin mutune da cin tsokar naman su yanzu muka fara, Rainon Yara ba zamu fasa ba, zamu cigaba da tarasu a cikin kurkukun ?addara muna biyan bu?atarmu dasu domin samun ?arfin ikonmu Ihu suka dinga Yi sunayin shewa sautin muryoyinsu tamkar zasu fasa bangon Fadar, kusan atare matsafan suke mi?e tsaye suna taka rawarsu ta matsafa, kowan nan su, ya Wauki abunda yake ra ayin ci asaman table wasu giya, wasu farfesun naman mutun wasu jini wasu kuma naman dabbobi suke ci, Yayin da wasun su a tsaye suke saduwa da junansu kamar dabbobi wa iya zubillah.

*DAULAR OBIE ESTATE*

*Dr. jazzd'*

?udundune yake acikin bargo, saman katafaren gadonshi na gidan Sir mubarak, cikin muryar raWa yake yin magana a wayar shi.

 I m not working today, I m at home. yanzu haka da ni ke yi maka magana Ina akwance saman gadona shiru ya Wanyi yana sauraron mutumin da suke yin wayarshi, can yaci gaba da cewa Boss Man kasan bana wasa da aikin ka, idan ka bani umarni jiki na rawa nike yin shi, ko jiya na shiga gidan gonar na duba lafiyar kajin, sai dai muce Alhamdulillah, Jikin su yayi kyau baka ga yadda suke tafiya ba tsokar jikinsu har girgiza take yi saboda ?oshin lafiyar dake gare su ya ?are maganar muryarshi da sautin dariya

 My Boss Man, Amma dani da kai zamu Wubi na azumi ko? Ko zamu bari sai sallah Ayi layya da su ? Tuntsirewa yayi da dariya jin amsar da mutumin ya bashi muryarshi cikin harshen turanci yake yi mashi magana.

 Amma ai kasan nayi ?o?ari, tun da na fara kiwon kajin nan wlh ko Waya ban ta6a gigin kamawa don in yanka ba, kuma miyau na ya biya fa da shagwa6a ya ?are maganar.

Abun da bai sani ba, tun da ya fara yin wayar, Sir mubarak Ya shigo Wakin jikinshi sanye da kakin sojoji, Hannunsa biyu ru?e da faffaWan plate, daga saman shi an jera Chocolate raspberry cupcakes.

Ya shigo Wakin ne da niyar ya faranta mashi, tun lokacin da turai ta faWa mashi game da gorin da Hajiya saratu ke yi mashi akan cewa shi ba mahaifin shi bane sai yaji ya ?ara ?aunar yaron yana matu?ar sonshi.

Lamarin Ya Waure mashi kai, ba tun yau ba, Ya jima yana mamakin wayar da dr jazz ke yi akan Kajin gidan gona, cikin tafiyar sanWa Sir mubarak Ya ?arasa shiga Wakin ya zauna gefen gadon shi hannun shi ru?e da plate din, Ya kasa kunne Yana sauraron tattaunawar jazz da Boss man din shi.

Jin shiru Jazz bai ?ara yin magana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login