Showing 129001 words to 132000 words out of 260999 words

Chapter 44 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Baison 6ata lokaci.

Jikin dr. laura ba ?aramin sanyi yai ba, tana son su Angel, ganin duk ta damune yasa Dr mark kwantar mata hankali Tafiyarsu ba yana nufin mun rabu da su ba, Kada Ki manta Sojojin ?asarmu ne suka tsince su, bayanan su da komai Yana a hannunsu, kuma zasu cigaba da bibiyar rayuwar yaran, wannan dalilinne ma yasa suka haWasu da Ummin america.

GyaWa kai Dr Laura Tayi Ni damuwata depression din dake damun yaran, da kuma Yaron dake fama da ciwon zuciya, Hankalina bai kwanta da Ummin america ba, Shin zata Iya bamu su kulawar da zata sanya su manta da damuwarsu? nafa santa bata da mutunci macace mai izza kuma ta shahara wurin Iya karuwanci..... Damuwace ?arara kan fuskar dr laura, idanuwanta tuni sun ciko tab da kwalla.

 Yaran sunfi bu?atar kulawar mace wadda tasan ciwon haihuwa, bawai karuwa ba! Wadda ta saba ?wacewa matan aure mazajensu tana fasi?anci da su! Yakamata Kuyi tunani akan hakan, Ni zanyima Commender din nasu magana, akan su canza masu wadda zata raine su, Yara fa har goma sha Waya za a damka ma karuwa, gaskiya basuyi tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su ranta amu?ar 6ace take Yin maganar.

Cikin kwantar da murya Dr mark yace ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba

Dr brown ya Waura da cewa sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na karuwa ne, su kuma a matsayin ma aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a dam?a mata amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba

GyaWa kai Dr Laura Tayi Shikenan na ha?ura, bazan yi masu magana ba, amma inaso zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai kai

 Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da ?aunarsu, Har na fara jin kewarsu acewar dr. Mark

Dr brown yace aini har ?asarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda damuwa, muna atare da su

Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin aikinsa.


*DAULAR ALHAJI MUSA*

*Dr Shureimd'*


?an kwanakin da yayi a gidan Uncle Win nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr. Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa, kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman Waki yakan fito ya zagaye gidan tare da zeenatu, yana matu?ar jin daWin kulawar da take bashi, sun sha?u da juna kamar sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta faWo Wakin shi yana cikin kallon hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece yake yawon kallo? Don ta fahimci ba ?aramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba.

A KishingiWe yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko ina ba, ko ?ofar bedroom dinsa bai le?a ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba Waya hankalinsa na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya Waura saman pillow,

Sam bai ji takun tafiyarta ba, saboda hankalinshi baya atare da shi, wankan swiss lace ne a jikinta, launin ash colour riga da skirt sunbi shape din jikinta, kamar a jikinta aka Winka kayan, duk da bata ?iba kayan sunyi bala en Yi mata Kyau, Tani da Lami ne sukayi mata Make up, hatta Waurin Wan kwalin kanta sune suka Waura mata shi, ziririyar sar?ar wuyanta ta diamond ce, stone din jikinta sai ?yalli Yake Yi, ta yafa gyale a saman kafadarta, hannunta ru?e da handbag, fragrance din turaren jikinta mai daWin sha?a ahanci.

Hankalinta ba akwance yake ba, tun kafin ta shigo Wakin tayi mashi sallama bai amsa bata ba, har ta gaji da yin sallamar shiyasa ta yanke shawarar shigowa don ta ga ko bacci yake yi ne
Tun kafin ta ?araso gaban gadonshi blue eye balls dinta suka sauka akan screen din Laptop nasa

Ras taji gabanta yai mugun faWuwa, zuciyarta tamkar zata faso ?irjinta saboda zafin da take yi mata, zeenatu tana da saukin kai sai dai tana da zuciya idan ta hasala, ranta ya 6aci sosai ganin abunda yake kallo, hoton da ta tsana a duniyar nan duk da batasan hoton menene yake kallo ba, ranta ya bata cewar budurwarsa ce yake kallo.

Idanuwanta sun makance, bakomai suke hango mata ba face dr shureim Winta rungume da mace a kirjinsa.

Runtse ido tayi da karfi ta fasa wata irin gigitacciyar ?ara wadda tayi silar firgitar da shi, da sauri Ya mi?e tare da wurga idonshi Kanta, tuni ta saki jakar hannunta ?asa, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta.

Hankalinshi ba ?aramin tashi yai ba, a hanzarce ya sauko daga saman gadon ya nufeta fuskarshi da alamun ruWu ya furta zeenatu! Lafiya? Meya faru?

Girgiza mashi kai tadinga yi tana faWin kada ka matso kusa dani yaya shureim, inna lillahi wa inna ilaihirraji un gaba Waya ta gama rikitar dashi zeenatu ki natsu kiyi min bayani meya faru dake? Ko wani abu ne ya tsoratar da ke?

Cikin shesshe?ar kuka tace yaya shureim bazan Iya jurewaba, zuciyata zata Iya bugawa, tun Wazu mukayi magana dakai akan zamu fita yawo atare, kace min inje in shirya kafin in dawo kaima za ka shiga wanka ka kimtsa, ashe baka yi komai ba, ko wankan ma bakayi ba, ka zauna kana kallon hotonta saboda tafi ni mahimmanci awurinka, ba tun yau ba kullum ne saina ganka kana kallonta, wai wacece wannan ne? Dame tafi ni? Numfashinta na fita da hucin zafi ta ?arasa maganar, tare da juyawa da gudu ta fuce daga Wakin nashi.

Hankalin shi ba ?aramin tashi yai ba, idonshi akan bayanta harta 6ace ma ganin shi.

Dafe kanshi yai da hannu Waya, har cikin ranshi baiji daWin kalamanta ba, baiso yai silar 6ata mata rai ba, duk da bai fahimci inda maganganunta su ka dosa ba, lumshe idanuwanshi ya Wanyi kafin ya ware su a hankali, yayin da zuciyarshi ke tariyo mashi furucin da tayi mashi, yasan bai kyauta mata ba, ta ?walla fa rai akan son su fita tun Jiya shi da kanshi yai mata al?awarin yau zai Wauke ta a sabuwar motarshi su fita yawo.

Cikin sanyin murya ya furta am sorry my zeenat,  da sauri Ya nufi toilet don yai wanka.



*Boss Bature
'? Mu haWu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_*=؋?KURKUKUN ?ADDARA=؋?*_


~Middle step~

3,F 'DB/1d'>?
?d'


_THE PRISONERS E23=?%?=ث?_



*Daga al?alamin Boss Bature*



Confusion of the heart=ث?



Sir mubarak ne zaune Cikin Motarshi, da su ka yi parking dinta a harabar ajiye motoci na asibitin Obinna,Tan?ameman asibiti ne Ya haWu tamkar ba wurin Jinyar marasa lafiya ba, An zuba dukiya wurin gininsa, suna da ?wararrun ma aikata na gida Nigeria dana ?asar waje.

Su biyu ne acikin motar, Shi yana a back seat na motar Ya zauna a hakimce, A yayin da Driver-operator dake driving dinsa Yana zaune saman driver s seat kowan nan su na sanye ciki kakinsa na sojoji, sun yi shiru, Sanyin A.c din motar na ratsa fatar jikinsu, ga dukkan alamu wani muhimmin abu ne ya kawo su asibitin, akwai wanda suke Jira Ya ?araso, tsawon mintuna Biyar, wani kyakkyawan matashin likita Ya nufo motar da saurin shi kamar zai yi tuntu6e.

A gaban motar su ya dakata da yin tafiyar, ya kai hannu yai knocking glass din motar, turo ?ofar da a kayi ne Yasa shi yin saurin gyara natsuwar shi, Sam hankalin shi ba a kwance ya ke ba, tun da sir mubarak ya kira shi awaya ya sanar da shi game da zuwan shi asibitin gaba Waya ya rasa natsuwar shi, saboda sanin matsayin shi a ?asar.


 Dr fawan, shigo ciki mana  muryar Sir mubarak ce ta fargar da shi, Jiki na rawa ya shiga motar, ya zauna yana faman zazzare idonshi yace daddy, ina wuni Ya gida ya Iyali sir mubarak yace lafiya lou fawan, Ya aiki ya fama da marasa lafiya tun da ya fara magana bai Wago Ya daura idonshi akan fuskar fawan ba, Hankalin shi na akan Wayar hannun shi da yake daddanawa.

Still muryarshi na rawa ya furta Lafiya lou daddy, sai ga kiranka, Na Wanyi mamaki sai da ya ambaci hakan sir mubarak Ya Wago da ido ya kalli fuskar fawan, duk da sanyin A c na motar, abun mamaki zufa ce ke tsastsafo mashi, kallon tuhuma sir mubarak yake jefa mashi, saboda zufar daya gani a saman goshin shi.

 Ya akai naga kana zubar da gumi? Ko baka da lafiya ne ? Yawu fawan Ya haWiya tare da cewa babu komai, Lafiya ta ?alau


Ta6e baki Sir mubarak Yai Okey, Inaso ka kaini gidan kajin da kuke kiwo kai da Jazz, da alamun ruWu akan fuskar dr Fawan yace Gidan kaji? Daddy ban fahimci abunda kake nufi ba, waye ya buWe gidan kaji yanayin yadda ya furta maganar, babu alamun yasan da zancen.

Fuskar sir mubarak a Waure tamau yace You know who I am. I don t need to explain this to you, Don haka kada ka 6oye min gaskiya, wani gidan kaji ne kuka buWe kai da jazz? Da kanshi ya faWa mini cewa kun zuba jari don kuyi kiwon kaji, kusan kullum ne saina kama shi yana yin waya akan gidan kiwon kajin ku

Hankalin dr fawan ba ?aramin tashi yai fa, Muyarshi na rawa ya furta `wallahi thumma tallahi daddy bansan da zancen gidan kaji ba, sai dai ko ?arya dr jazz yayi maka, ka ji na rantse maka da Allah... Lamarin ya Waurewa Sir mubarak kai, Sojan dake zaune a driver seat Ya natsu Yana sauraron su, ta cikin ear-view mirror din motar Yake kallonsu.

 Fawan, Ka faWamin gaskiya, ni nasan Jazz ba zai ta6a yi mini ?arya ba, na lura gaba Waya baka acikin hayyacin ka, idan ma saboda ni ne to ka kwantar da hankalin ka, babu abun da zan yi maka, ni dai buri na shine ka kai ni gidan Kajin ku, inaso in gansu, nayi maka al?awarin idan ka rakani na gansu zan ?ara maku jari

cikin ruWu dr fawan ya girgiza kai yana fadin bazan yi maka ?arya ba daddy, ina ganin ka tamkar uba agareni saboda ?aunar dake a tsakanina da Jazz, wlh Daddy ni bamu ta6a yin maganar buWe gidan kaji da dr jazz ba

Da kakkausar murya Sojan dake a gaban motar yace Sir, this boy isn t telling us the truth. Why don t we take him to the headquarter? Maybe if we do, he ll tell us the truth. (yalla6ai Yaron nan bazai fada mana gaskiya ba, Me zai hana Mu shiga dashi headquarter Wata ?il idan mu ka je can Ya faWa mana gaskiya)

Zaro ido waje dr fawan yai, jin ance za aje dashi headquarter, sir mubarak yace kada ka damu ai basai munje headquarter ba, akwai bindiga a ?uguna,  yai maganar tare da sanya hannu ya zaro bindigar Ya Waurata saman laps dinshi, tsabar tashin hankali ne tsantsa akan fuskar fawan.

Sir mubarak yace idan na kashe ka na kashe banza, sai dai idan munje lahira ayi mana hisabi, don haka ka faWa min gasiya, idan ba haka ba zan tarwatsa kanka da bindigar hannuna bawan Allah dr fawan duk sun tsoratar dashi da barazanar su, ?an hanjin cikin shi sun kaWa.

Hawaye tuni sun soma wanke fuskarshi, cikin sanyin murya yace ko da zaka kashe ni daddy, bazan fasa faWa maka gaskiyata ba, wlh rantsuwar Wan musulmi bani da masaniya akan maganar gidan kaji, daddy banyi niyar fada maka ba, amma don in kare kaina zan sanar dakai wani abu da baka sani ba Hankalinsu gaba Waya yana akan fuskarshi.

Numfasawa yayi kafin ya Waura da cewa  Daddy, jazz baya zuwa aiki, yau kusan wata Waya da sati, bansani ba ko kunsan da hakan, Ni kaina na damu da canzawarshi, . Zuciyar Sir mubarak a hautsine Ya furta idan kuwa har hakane Dr fawan baka kyauta mini ba! Meyasa tuntuni baka kira awaya ka sanar dani cewa baya zuwa aiki ba? Kusan kullum sai na ganshi ya shirya zai je asibiti, hakan na nufin ba aiki yake zuwaba wani wurin daban ya ke tafiya? Ya jefa mashi tambayar yana mai jin Waci acikin zuciyarshi.

 Ka yi hakuri daddy, Bana son in shiga tsakaninka da shi, sannan ni bansan baku da masaniya akan hakan ba

 Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Sir mubarak ne ya furta hakan, zuciyarshi tayi matu?ar karaya da jin cewa jazz baya zuwa aiki, Ya fara zargin shi akan ?arairakin da ya ke yi mashi, bai ta6a tunanin Jazz zai yi mashi haka ba, duk da irin ?aunar da yake nuna mashi.

Idanuwan shi tuni sun kaWa jawur, zuciyarshi ta motsa.

 Bana so Jazz ya san cewa nazo asibitin nan! Ko nayi magana dakai! Kaja baki kayi shiru, dr fawan ya amsa mashi da toh daddy, in sha Allah bazan faWa mashi ba.

 Ka share hawayen ka, da sauri dr fawan ya zaro hanky ya soma goge fuskarshi.

 Dr fawan, Na yarda da jazz sai dai a yanzu na fara zargin shi, wallahi If I find out that he s doing something wrong, sai ya WanWani kuWar shi, rai a6ace ya furta maganar, ya ?ara da cewa  dr fawan nagoda da bayanan da ka bani, zaka iya komawa bakin aikin ka jiki na rawa dr fawan ya fito daga cikin motar, Bayan yayi masu sallama Ya nufi cikin asibitin yana faman sauke ajiyar zuciya.


Shiru su ka yi babu wanda ya ?ara magana acikin motar, Lamarin ya Waurewa Sir mubarak Kai, Mamakin shi ?aryar da jazz yai mashi na cewa Sun buWe gidan kaji, da kuma zuwa aikin da yake yi ashe duk ?arya ne.

Driver-operator, Ya fahimci halin da sir mubarak ya shiga na damuwa, cikin kwantar da murya yace Sir, pls kada hakan ya dame ka, nasan ba daWi mutumin daka yarda dashi ya sa6aka, sai dai fa har yanzu bamu da tabbacin abun da dr jazz ya ke yi, mu kyautata mashi zato, sannan shawarar da na ke so in baka yalla6ai, me zai hana mu fidda rana Waya, Mubi bayan shi ba tare da sanin shi ba, a lokacin da ya shirya zai tafi aiki,

Ta cikin mirror din motar Yake duban sir mubarak, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon drivern yace  Ka kawo shawara mai kyau, tabbas inason sanin me jazz yake aikatawa, nagode da shawararka, zamu Iya tafiya

Cikin girmamawa Ya amsa mashi da toh, sannan ya tada motar Ya fito da ita daga cikin harabar ajiye motocin, atsanake ya ke yin driving har suka haura saman titi, sir mubarak bai dai na cizon yatsanshi ba, saboda Ya damu da jazz, ?aunar da ya ke yi ma mahaifiyar shi ce ta shafe shi, ko ?a ?an shi da ya haifa bai jin su kamar yadda yake jin jazz, hankalin shi ba zai ta6a kwanciya ba idan har bai gano abun da ya ke aikatawa ba, ya jima yana danne zuciyarshi akan ?in amincewa da zargin yaron da ta ke yi, abun da ya jawo shi ga bincikar shi a yanzu ya fahimci aduk lokacin daya kama jazz yanayin waya da zarar Yaganshi yake rasa natsuwarshi, Jikinshi ya hau kerma, shiyasa ya fara suspecting dinsa.

d'ANEELERHd'

Tun kafin ta sallame sallar azahar wayar ta dake ajiye saman drawer take ta buga ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, sai da ta kammala sallar ta Waga hannu tayi addu a ta shafa a fuska, kafin ta mi?e da sauri ta nufi drawer ta Wauki wayar, murmushi ta saki ganin sunan surukar arzi?i ya bayyana akan screen din wayar, aranta ta ayyana halan baby junaid ne ya matsa a kirani awaya.

Bayan ta Waga kiran ta manna wayar a kunnanta, kafin ta furta sallama muryar junaid ta katse mata hanzarin ta.

 Mommy, baby junaid ne, ni ne na kira ki awayar granny, har sai da ta ji gabanta Ya Wan faWi, da mamaki tace junaid da gaske kai ka kirani? Ina mommy adama? Ko dai itace ta baka wayar don ka yi mini magana

muryarshi da shagwa6a yace mommy ai bata nan, suna a falo, Ni kaWai ne a Wakin... tun kan ya ?arasa maganar tace Junaid bana hana ka Waukarwa mutane waya ba? FaWamin ya akai ka iya buWe mata waya ?

 Mommy wasa nake maki, itane


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login