Showing 3001 words to 6000 words out of 260999 words

Chapter 2 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Allah!....' Azeeza ce ta yi su6ul da baka, da sauri Gabriel Ya toshe mata bakinta da hannun shi, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwansu, duk sun ?agara su ji wani hukunci zata yanke masu tun da ta gano plan Winsu.


Walking magestically ta ?araso gabansu Tare da tsaida sandarta a ?asa, Daya bayan Waya ta ke kallon su tsawon mintuna Uku kafin ta soma magana atsanake

"Furennin da ku ka shufka sunyi kyau sosai, Wanene ke basu ruwa A cikin ku? Zaro ido su ka yi akan fuskarta Mamaki Ya kamasu, Aransu suka shiga ayyana cewa" ko dai bata ga ?ofar ba ne? Ko kuwa Allah ne yaji kokensu ya hanata ganin komai.

"Kun yi shiru baku bani amsa ba"? Yawu Angel ta haWiya Muryarta Na rawa ta ce"am..um..ni..nice..Ni nake bata ruwa, tare da ?an uwana,"

Murmushi tsohuwa zafreen ta saki tare da cewa"Ku cigaba da bata ruwa inason furenni, Nan da wani lokaci zan Wauke tukunyar fulawar in mayar da ita Wakina..." tsabar zalama tunkan ta ?arasa maganar Angel tai wuff wurin cewa"idan ma kinaso Yanzu saina Wauko maki ita ki tafi da ita, ai mu mun fi son duk wani abu da zai faranta maki rai" kallonta tsohuwa zafreen ta yi da tsoffin idanuwanta"Kamar baki da gaskiya? Ina magana kina katse ni"! A kausashe tayi maganar.

Sunnar dakai ?asa Angel tayi a tsananin ruWe Batul ta Waura da cewa"Ae tun lokacin da aka canza mana abinci zuwa ganye, Angel ta soma Fita hayyacinta, sam babu natsuwa atattare da ita, Hakanan zaki ga ta zauna tana sambatu ita kaWai" ta ?arasa maganar hada murmushinta,

(Yara sun zama ?an wasan kwaikwayo)

"Eyyah Hakane ashe, " jinjina kai Angel tayi"dama ni tun ina agida idan na ci abincin da aka haWa da ganye zaucewa nake yi, Bana son Cin ganye yana affecting Wina" Fuskarta amarairace ta yi maganar.

Shiru tsohuwa zafreen ta yi a yayin da ta ke ?are masu kallo kamar tana son gano wani abu da ke 6oye akan fuskokin su sai dai Allah bai bata ikon fahimtar komai ba, Abun da ya Waure mata kai yadda su ke yi mata magana ba tare da jin shakkarta ba.

"Da za ki bamu dama Yau na rana Waya kawai, Ki zauna muyi fira da ke, A matsayin ki na kakarmu....." gaba Waya sun ruWar da ita, sai kallonsu take yi tana faman jinjina kai kamar ?ar ?adangaruwa

Sun kashe mata bakin magana, A hanzarce ta juya ta nufi bene Giants dake take mata baya suka juyawa tare da bin bayanta, Suna jiyo sautin rufe ?ofar Wakinsu, Gaba Waya suka daka uban tsalle tare da rungume junansu fuskokinsu Wauke da farin Cikin nasarar da su ka yi akanta, yau sun kashe tsohuwa zafreen da mamaki

"Alhamdulillah Ya Allah, Mun gode da taimakon ka agare mu, " Angel ce ta furta hakan.

"Mun ji jiki yau Allah, ba kiji yadda gaba na ke faWuwa ba, tun da ta shigo hankalina ya?i kwanciya" acewar Yasmin, Hibba tace"Ae ba ke ka Wai ba, ni kaina ?iris ya rage in saki fitsari a wando, matar can bala'e ce' Kowa yana tofa albarkacin bakin shi

"Amma wai ya akai da ta shiga toilet din bata ga komai ba? Kuma har ta ga Tukunyar fulawar"? Naufal nai yai tambayar mamaki ya ishe shi

"Ae Allah muka ro?o shine ya makantar da ita, shiyasa bata ga komai ba" Deeja ce tai maganar,

"Pls kudaina maganar nan kada Suji mu tunda suna ganin mu, Inaso mu yi magana amma dole mu jira zuwa anjima idan marece Ya nutsa, sai mu shiga sashen toilet dinmu saboda idan su ka ga zaryar Tayi yawa zasu fahimci wani abu" Atare suka hada baki wurin furta mata "Toh"

"Yanzu kowa yaje ya kwanta, Inaso ku huta, kafin zuwa anjima " Waya bayan Waya suka nufi gadajen su tare da haye saman suka kwakkwanta, Mutun uku ya rage a tsaye, Zuciyoyin A cunkushe suke da tunanin taya zasu Iya 6alle murfin ?ofar nan? Taya zasu iya Gano Danish? Fatansu Allah yasa adawo masu da shi ba tare da sun sha wahala ba, A tunanin su Haris kenan su da basu san komai game da zamanshi giant ba.


Mutun uku da suka rage atsaye Gabriel ne sai Batul tare da Angel, Sun?i tafiya ga dukkan alamu suna bu?atar jin wani bayani ne daga gare ta.

Kallon su ta Wanyi kafin ta soma magana "Gabriel nasan me ka ke son ji, Ka ?ara ha?uri zan yi maka bayanin komai" amsa mata yai da toh tare da juyawa ya nufi gadon shi.

"bugun zuciyata me kike tunani ne"? Lumshe ido batul ta yi tare da ware su kan fuskar Angel"har yanzu ban fahimci komai ba, dangane da abunda ya faru da Wan uwana Danish, hankalina bai kwanta da abunda kika faWa mini ya faru dashi,"

Matsawa Angel tayi kusa da ita sosai har numfashinsu na kokawa dana juna

"Kin damu dashi"? Jinjina mata kai tayi alamar eh, ta ?ara da cewa"taya bazan damu dashi ba Angel, bakisan yadda nake jin shi acikin zuciyata ba, da ace ina da hanyar da zanbi inje gare shi nothing would stop me from going."

Angel ba ta yi mamakin jin abunda batul tace mata ba, saboda sanin irin sha?uwar dake a tsakaninsu, Hakan yasa ma ta?i sanar da ita cewa Ya zama Giant, gudun kada ta sanya damuwa

Ruwan hawayen da ya taru acikin idonta ne yaci gaba da gangarowa

"Ki kwantar da hankalin ki bana son kina shedding tears din ki, Ko dan saboda farin Cikin ki zan yi ?o?ari wurin ganin Danish ya dawo gare mu," kwantar da kanta tayi saman kafaWar Angel taci gaba da yin shesshe?ar kuka tana faWin"Amma ai bashi da lafiya, An cire mashi ido Waya, bansan awani hali yake ciki ba, "

"Ki daina kuka batul so kike hankalinsu Ya ?ara tashi? Nace ma ki lafiyar shi ?alau shi da kanshi Ya faWa mini cewa babu abunda ya samu idonshi"

lallashinta Angel taci gaba dayi har saida ta samu ta lafa, Abun da yaWaure ma Angel kai, zazza6in da taji a jikin batul lokacin da ta kwantar da kanta saman kafadarta, Jikinta zafi sosai.

Hannayenta biyu ta Waura saman shoulders Win batul, ta Wago da kanta, Idanuwansu acikin na juna,

"Baki da lafiya ne?naji jikin ki da zafi"? Muryarta adisashe ta ce"Lafiyata qalou, idan ma bani da lafiya damuwar rashin Danish ne" shiru Angel tayi kamar an Wauke mata sautin muryarta, ta rasa tunanin me za ta yi, Ru?o hannun batul tayi acikin nata

Calmly tace "You need to take a bath, mu je in raka ki toilet, girgiza kai batul tayi"A'a bana iya wanka, nafi so na kwanta zuwa anjima idan na tashi zanyi,"

GyaWa kai Angel tayi"shikenan muje mu kwanta da anjima nima zanyi wankan"

Atare suka nufi gadajen su, tafiya su ke yi kamar waWanda aka zarewa laka, babu kuzari a jikin kowaccensu, Ita dai Angel akwai wani abu dake damunta acan ?asan zuciyarta, Fatan ta Allah yasa hasashenta karya zama gaskiya don kuwa ba ?aramar matsala za'a samu ba.

Ta yi niyar ta kwanta asaman Gadon Danish ganin Jemimah kwance saman nata gadon, sai dai kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta batul ta riga ta kwanciya saman gadonshi, da ido ta bita da kallo ganin ta rungume pillow dinshi a ?irjinta tare da lumshe idanuwanta, Jiri Angel ta gani acikin idanuwanta kamar zata faWi kasa adaddafe ta nufi gadonta da?yar ta haye gefen jemimah ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya, lokaci Waya ta ji yanayin jikinta ya canza zuwa zazza6i, hakan yasa ta soma ambaton sunan Allah, sama sama ta fara jin bacci yana fisgarta har ya ci nasara akanta sosai ta nutsa tana bacci...............


?akin ya yi tsit babu mai magana a cikin su, kamar masu bacci alhalin kuwa likimo su ka yi, sai da marece ya nutsa Angel ta umarce su akan su je su yi wanka saboda wunin ranar jikin su baiga ruwa ba, ba tare da 6ata lokaci ba kowannansu Yayi wanka, ta Wauko masu sababbin uniform Winsu kowa ya zura nashi a jikin shi, tsaffin kuma suka cire su Angel ta kar6esu ta ninke su ta ajiye saman table.

Lokacin da dare ya gabato, dubara su ka yi wurin kashe Floor lamps Win da ke a ?asan Wakin su, Duhu Ya mamaye idanuwansu, saboda sabon da su ka yi da Wakin yasa su ke iya gane hanya ko a cikin duhu, Kamar yarda Angel ta tsara masu mutun Uku ne zasu HaWa masu kayan su A cikin akwatin da zasu gudu da shi, Rai da burin sufa shirin matafiya su ke yi tun kafin su gano Makullin BuWe ?ofa, Babu wanda yai bacci acikin su Hatta Jemimah idonta biyu tun Wazu da marece da ta farka Angel tayi mata bayanin komai dangane da gano ?ofa da kuma shirin su na guduwa, abunda yasa tayi mata bayani don kada ta basu matsala, da ya ke yarinyar tana da wayau ta fahimce ta sosai, yanzu haka suna kwance saman gadon Angel ita da azeeza sun rungume juna sunata sa?a wasi?ar jaki game da rayuwar da za su yi agidan daddyn Genie Winta.

Sauran ?an uwan nasu duk suna a zaune gefen gadajen su, duk wani motsin su Angel akan kunnuwansu.

"Bamu san Girman ?ofar ba Angel Kada mu gaza wuce wa da akwatin kayan mu" Gabriel ne yai maganar, Cikin duhu suke magana, zurfin tunani ta yi acikin kwakwalwarta, A Labarin da Salsabeel ya bata Na mahaifin shi habibullah ya tabbatar mata da cewa ?ofar sai da rarrafe mutun zai Iya giftawa ta cikinta, mutun zai Iya rarrafawa ko ya zauna, Amma babu zancen mi?ewa tsaye, abun zai zo masu da sau?i tun da basu da girman jiki, yawancinsu dogaye ne amma babu ?iba, haris Win ma da ke da jiki yanzu ya zabge ya koma kamar su Javed.

"Ae akwatin zamu Iya kwantar dashi mu dinga tura shi ta cikin hanyar, Ni abunda nake Jiye mana kada mu kwasa mu tafi zai Iya kasancewa ?urmin daji ne bamusan ya weather Win shi zai kasance ba, Zafi ko Sanyi, Zamu sha wahala akwai sanyin da ma zai Iya kisa Haka zafi ma, Ni nafi so mu tafi da bargunan mu saboda tsaro, shiyasa nake so mu Wauki akwati Waya sai Backpack Win Unaiza dole mu tafi da ita saboda gadon mu ce.

Duk maganganun da suke tattaunawa cikin duhu akan kunnan ?an uwansu da ke zaune gefen gado Sun natsu suna sauraron su.

"Mu fara Waukar uniform Win mu jera su ciki, " batul ce tai maganar, Angel tace"Ki je toilet ki Wauko mana fitila Waya amma ki fara kashe ta tun acan dan kada su gan mu, a Wakin tsohuwa tamira zamu aiwatar da komai" ta amsa mata da toh, kafin ta nufi hanyar sashen toilet Winsu cikin duhu har ta samu ta cimma ?ofar makewayin nasu, da hannu ta tura ?ofar ta kutsa kai ciki ta shiga ta Wauko fitilar tare da kashe ta, Kafin ta dawo Wakin tunkan ta ?araso tace dasu gata nan tafe, Ru?o hannunta Angel tayi acikin nata ta kuma ru?o hannun Gabriel da Wayan hannun atare suka shige Wakin tsohuwa tamira,

"Ki kunna fitilar yanzu, Ni kuma zan shiga Waki In Wauko Akwatin kayan mu da backpack Win" ta amsa da toh, Batul na kunna fitilar Haske Ya gauraye ko'ina na Wakin tsohuwa Tamira, Zazzaro ido su ka yi ita da Gabriel da mamaki akan fuskokinsu suke bin Bedroom Win da kallo, basu ta6a sanin haka ya ke ba, Yau ne rana ta farko da batul ta fara shigowa Wakin tsohuwa tamira. Kallon Juna su ka yi ita da Gabriel Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu ba tare da sun yiwa juna magana ba.

Turo ?ofar Wakin akayi da sauri suka kalli mai shigowa, Angel ce janye da akwati Waya na kayansu, Ta goyo back pack Win Unaiza saman bayanta sai ta yi tamkar ?alibar makaranta, A tsakiyar Wakin tsohuwa tamira ta ajiye akwatin saman floor, ta kwanto jakar bayanta ta Waura ta saman table.

"Angel Har yanzu ba ki yi mana bayanin ta ya ya akai kika gane inda ?ofar nan ta ke? Waye ya faWa maki kiyi amfani da ruwan zafi don shafen wurin ya tsage? after that Mun yi mamakin yadda akai kika buWe Wakin tsohuwa Tamira ko dai itace duk ta faWa maki hakan"? Batul ce tayi mata tambayar a ?agare da son jin amsarta.

"Zan baki amsar tambayarki amma kafin nan inaso ki kira mini su Haris su shigo ayi komai agabansu" har ta juya zata fuce da fitilar hannunta da sauri Gabriel Ya cafko damtsen hannunta tare da janyo ta baya yana fadin"So kike asirin mu ya tonu? Ina zaki da fitila"? Murmushi ta Wan saki tare da cewa"Na shafa'a ne" kar6ar fitilar yayi ita kuma ta fuce Jim kaWan Su kaji an turo ?ofar Haris Ne agaba Deeja na abayan shi dasu Hibba a jere suka shigo Hada azeeza Hannah ce ta ru?o hannunta.

"Wa ya ce ku zo da Azeeza? Ba a kwance ta ke ba"? Gabriel ne yai maganar Yana kallonta, Naufal yace"kasan halinta da rigima tafi son komai za'ayi ayi agabanta mutun na fama da makantar dare,"

Ranta ne ya 6aci sosai jin abunda suke cewa, fusge hannunta ta yi daga ru?on da Hanna tayi mata, A ?asa ta zu?unna tana rera masu kuka.

Angel tace"Dan Allah ku rarrashe ta idan ba so ku ke ta tona mana asiri ba" Gabriel ne ya nufi wurin da ta ke a zu?unne ya kai hannu Waya ya Wago da ita kamar jira ta ke yi ta faWa saman laps Winshi tana cigaba da kuka, Murmushi ya saki yana kallonta har mamakin ?arantarta ya ke yi,
"Its ok Share hawayen ki My Azeeza, kinsan bana son zubar hawayenki, Ko so ki ke Ajiyo sautin kukan ki asirin mu ya tonu"? Muryarta da shesshe?ar kuka tace"A'a" yace"okey wipe ur tears, zan Goya ki abayana don bana son kisha wahalar neman Wan jagora," yai maganar tare da mi?a ma Batul fitilar hannun shi, bayan ta kar6a ya zu?unna Azeeza ta haye bayan shi ta ?an?ameshi sosai, Ya mi?e Wauke da ita"

Angel na ?o?arin fara yi masu bayani muryar jemimah da suka bari ita kaWai acikin Waki ya karaWe kunnuwansu ta kware baki Tana ?wala mata kira"Genie! Genie! " da sauri Angel ta nufi ?opar ta buWe ta fuce, Bayan fitarta Hankalinsu Ya koma kan Wakin da su ke a ciki na tsohuwa Tamira Sai faman wurwurga ?wayar idanuwansu su ke yi, Parveen Acici Tana Hango Wannan Tea pot Win da ?an kofuna biyu jiki na rawa ta nufi table Win dake Wauke dasu, ta zauna saman kujera tare da Waukar pot Win tana jijjigata don taji idan akwai ruwan shayi aciki,

"Kada ki kuskura ki ce zaki sha, Kawai daga ganin abu bakisan tsawon lokacin daya Wauka a ajiye ba kin Wauka zaki sha da ya ke ba ki da linzami indai akan abinci ne" Deeja ce ke yi mata magana, Saboda kafiya irin ta parveen ko kallo bata isheta ba hada cewa"dama kin daina wahalar da kanki wurin yi mini magana don wlh saina sha tea Win nan" Tsawa haris ya daka mata"Zaki tashi ko saina 6ata maki rai"? MurguWa mashi ?aramin bakinta ta yi"Wai ku ina ruwan ku dani ne? Cikina ne ko naku"? dafe kai Hannah ta yi tare da cewa"ku ukun nan kunfi kowa jaraba dake da Azeeza sai waccan ?ar jemimah, Ni inaga Idan mun tashi tafiya mu bar su a kurkukun domin kuwa nan yafi da cewa dasu, in ba haka ba zasu ja mana ne" Jin maganar Hannah yasa azeeza dake kwance bayan gabriel ta ?ara fashewa da wani sabon kukan, saboda ance za'a barsu a kurkuku

"Pls Hannah stop saying that, na samu na rarrasheta gashi yanzu kinsa ta kuma fashewa da wani kukan" acewar Gabriel, ta6e baki hannah ta yi ba tare da ta tanka mashi ba.

Da?yar ya samu yashawo kan Azeeza ta daina yi mashi kuka, Parveen kuwa harta Tsiyaya Shayin A cikin Cup hada lashe baki zata fara sha, Kamar daga sama taji an dam?i wuyan rigarta daga baya, da sauri ta Wago don taga wanene, dama saida ranta ya bata cewar shi ne

Harara ta shiga jefa mashi tare da murguWa mashi baki, Ya Waure fuskarshi sosai babu annuri

"Tashi ki bar wurin" kaitsaye ya bata umarni, tasan halin shi sarai mi?ewa ta yi ranta a6ace, bata so ya hana ta shan tea din ba, ta ?wallafa rai.

Acikin hannunshi ya ru?e nata sosai don kada ta kufce mashi ta koma shan shayin, Naufal kenan.

"Angel shiru bata dawowa ba, Tabar mu atsaitsaye cirko cirko, Ni bari ma in haye saman gadon tsohuwa in kwanta"

Rubina ce ta yi maganar, bata kai ga zuwa ta hau gadon ba, Angel ta turo ?ofar hannayenta biyu rungume da uniform dinsu, Jemimah na kwance saman bayanta, Ta ?an?ameta da hannayenta, abunda ya jawo har suka daWe Jemimah ce ta bu?aci ta rakata toilet zata zazzage cikinta, Shiyasa basu dawo da wuri ba, Sai da Angel ta jira ta gama tukunna ta kamota suka dawo Wakin.

Ata?aice Cikin daren suka jera uniform Winsu acikin akwatin kayan, Hada barguna Deeja ta Wauko masu guda takwas da?yar akwatin ya iya Wauke su, Har saida suka rage uniform din dake a ciki suka turasu cikin backpack Win Unaiza tukunna ya ishe su, Bayan sun kammala sanya kayan suka datse shi, daga cikin abubuwan da suka dauka bayan uniform da barguna hada cotton scarves dinsu da Hulunansu sai rigunan sanyi da takalmansu, A cikin jakar unaiza suka saka Madubin da tsohuwa Tamira ta basu kyauta, ba su bar cikin Wakin ba saida Angel ta fayyace masu komai dangane da tattaunawarsu da Salsabeel.Abu Wayane bata fada masu ba komawar Danish Giant bata so su sani gudun kada su tayar da hankulansu. Ha?i?a tsohuwa tamira ta kafa tarihi acikin zukatansu, A yau ta amsa sunanta na mahaifiyar su wadda ta raine su, basu ta6a yarda cewa tana sonsu ba sai yau da Angel ta labarta masu komai dangane da taimakon da ta yi masu, sun ji ?aunarta sosai har suna fatan Allah ya haWa su da ita kafin subar kurkukun, sai da su ka kammala shirya komai tsaf na kayansu, Angel ta kalle su Waya bayan Waya Azeeza tuni bacci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login