Showing 225001 words to 228000 words out of 260999 words

Chapter 76 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Ya juya mata baya, bata Iya ganin fuskarshi da kyau, batasan ya akai ta tsinci kanta da yi mashi kallon kurulla ba, bakomai take son gani ba face fuskarshi, sai dai kash takasa ganinta, faffaWan bayanshi kadai take kallo, Ba ?aramin jikine da shi ba, murdadden damtsen hannayensa take kallo, da alama Ya ru?e wani abu yana sha a cup, duba da yadda hannun shi na dama ke motsi, yayin da Wayan hannun nashi ya zura shi a shorts pocket dinsa.

Aranta ta ayyana ko wanene wannan mutumin? daga gani yana da ?arfi da tarin dukiya, komai nashi cikin ?asaita yake yin shi, dai dai da yanayin tsayuwarshi abun kallo ce, yaWan jingina bayanshi jikin benan.

Hankalinta ya karkata akanshi, ta manta da hijabin da zata je daukowa, ta tafi wani tunanin daban, ita so take taga wanene shi? Ranta yafi bata cewar Chief din da taji ana fadi ne,

 Unaisah firgigit ta Wauke idonta daga kallon chief da take Yi, Jin muryar Boss, da sauri yake tunkarota shigowarshi kenan part din, jallabiya ce a jikin shi, Ya sanya face mask a fuskarshi, tayi mamakin ganinshi a irin wannan lokacin, abunda bata sani lokacin da boss Ya ambaci sunanta, Chief owais Ya juya don ganin wanene ke magana, dai dai sa adda ita kuma ta kawar da kanta, Natsuwa yai yana dubansu daga can saman second floor.

 Ba ki yi bacci ba ? Tambayar da boss ya jefa mata kenan a yayin daya ?araso gabanta yaci burki ya tsaya yana kallon fuskarta.

 Banjima da farkawa ba, amma meya hana ka bacci ta tambaya tana kallon rinannun idanuwanshi masu dauke da tsantsar damuwa
 Taya zan Iya yin bacci? Bayan kema bakiyi ba
Matashin murmushin ta Wan saki, har cikin ranta taji dadin maganarsa, shi kuwa ji yake kamar ya rungumeta ko dan yaji sanyi aranshi, ya damu da halin da suke aciki ita da Wan uwanta, tausayinsu ya hanashi sukuni har ya gaza runtsawa shiyasa ya fito don yazo ganin su.

 Yakamata ka kwanta ka huta boss, na fahimci ka damu dani, meyasa ?
 Taya bazan damu dake ba? Kefa jinina ce, jinin dake yawo ajikina shi yake yawo ajikin ki..... da sauri Ya katse maganar, Jin su6ul da bakan da yai, murmushin gefen fuska tayi mashi, ga dukkan alamu taji dadin maganarshi

 Boss kayi shiri baka ?arasa zancen ba? Ni wallahi idan kana Yi min magana sai inji kamar mahaifina

 Meyasa kikace haka ?

 Saboda Yana ?aunata fiye da yadda yake kaunar kansa, ya sadaukar da farin cikinshi saboda ni, nayi rashin ji a?uruciyata, na azabtar da daddyna amma duk idan na tuna ayanzu sai inji haushin kaina...... sambatu take yi mashi sam batasan me take furtawa ba, abune ya haWe mata ga radadin da zuciyar ta keyi mata shiyasa take yi mashi zuba, tana magana hawaye na taruwa acikin idanuwanta.

 Amma meyasa kike jin haushin kanki ayanzu ? Muryarshi araunace ya furta mata maganar.

Shesshekar kuka ta soma yi mashi tana fadin saboda nagane cewa bani da masoyi a duniyar nan daya wuce shi, bani da tamkar shi har abada, Har yau idan na tuna cewa shine silar duk wani abu dana koya aduniyarnan ba ?aramin dadi nake ji ba..... kasa ?arasa maganar tayi, sakamakon janyota da yai zuwa jikinshi ya rungumeta sosai, haWi da daura hannayenshi saman bayanta yana lallashinta, bata kawo komai aranta ba, sai dai bugun zuciyarta da taji ya ?aru, tajima tana mamakin yanayin da take tsintar kanta idan Boss yana akusa da ita, sakankancewa takeyi taji kamar daddyn ta ne ya dawo.

 Ya isa haka, ki daina kuka Unaisah, In sha Allah, daddynki zai bayyana, bama ke kadai ba da sauran ?an uwanki duk zamu binciko maku danginku

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, takasa raba jikinta daga nashi, tamkar zata koma cikinshi.

Duk wannan abun dake faru atsakanin Boss Man da Unaisah, akan idon chief owais, yayin da yake kur6ar coffee dinsa.

Tunawa da Hijabin da zata daukone yasa tayi saurin furta boss namanta, alwala nayi zanje daki na dauko hijabi da prayer mat, yakamata na tafi idan danish yaji na dade zai Iya biyoni, yanzuma da ?yar ya bari na fito ta fada tana raba jikinta daga nashi.
 Nagode da kulawarka agaremu,
 Kada ki damu, muje na rakaki Wakin,
 Banaso na takura maka, naga idanuwanka sun kaWa jawur, baccine a idonka yakamata kaje ka kwanta ta fada tana kokarin kakaro murmushi
Ru?o hannunta yai acikin nashi da zolaya yace saifa na biki Allah, ai tunda baki runtsa ba nima bazan yi bacciba, zan zauna atare daku har sainaga abunda ya turema buzu naWi
Dariya tadan saki jin maganarshi ta ?arshe, atare suka jera zuwa bedroom din nasu.
Koda suka ?arasa dakin, arude ta furta Boss babu batool fa ! Ta fadi tana faman zare ido akan gadonsu.

 Calm down ur mind, nasan inda suke, ba sace su akayi ba, abunda ya farune dazu ya tayar masu da hankulansu, shine na rakasu dakin Ummi, nasan yanzu haka sunyi nisa acikin baccinsu ajiyar zuciya ta sauke, har taji sanyi aranta.

 bayin Allah, nasan da?yar suka Iya runtsawa, musamman Azeeza tafi kowa tsoro a cikinsu ta furta hakan tare da kama hanyar closet dinsu, bin bayanta yai da kallo harta 6ace ma ganin shi.

Maganar amininshi ce ta fado mashi aranshi, a ranar daya kira shi video call yana daga kwance saman gado shida Angel dinsa.

Tuni idanuwanshi suka cicciko tab da ?walla, ha?i?a yayi babban rashin da bazai ta6a samun mai maye mashi gurbinshi ba
A hankali Ya furta Allah Yaji?anka aminina
 Boss mu tafi muryar unaisa ce fargar da shi ga kallonta, Harta zura hijabin ajikinta launin milk, Iya gwiwa ta tsaya mata, hannunta a ru?e da prayer mat.
Lokaci Waya annurin fuskarta ya Wauke, dama ranta babu daWi, dauriya kawai take Yi,
 Meyasa kika 6ata fuska ?
Zumbura mashi baki tai kafin tace kaine mana, ka?i jin maganata ni nasan baccine ke addabarka, amma ka?i zuwa ka kwanta, kalli idanuwanta har sun canza launi sun yi jawur da su... cikin kulawa tayi maganar
In a cool voice ya furta karki damu dani, babu bacci atare dani, idona ne keyi min ciwo, kafin na fito daga gida saida na Wiga magani
Unaisa sarkin tausayi, duk sai taji ba dadi, jin baida lafiya.
 Allah yabaka lafiya boss, amma dan Allah kaje ka kwanta kayi bacci
Bakomai ya tuna ba face maganarta lokacin da tana yarintarta, Idan baida lafiya ya kwanta don yai bacci, saman jikinshi take hayewa tana fadin ai wallahi bazan bari kayi bacci ba, ka jira sai lokacin da nima zanyi sai muyi atare, idan ta fadi hakan to bai isa yai bacci ba, dole yajira har zuwa time da zata gama wahalar dashi tukunna suyi bacci, yayi zurfi acikin tunanin shi muryarta ta dawo dashi
 Ka ?ura min ido kana kallona, ko nayi maka kama da wanine ? mamaki take bashi idan tana magana.
Adabarbarce ya furta um...bakomai mu tafi kawai
Ya ru?o hannunta acikin nashi, Suka nufi ?ofar fita daga dakin.

Kafin dawowarsu dakin danish, Tuni Big guy ya kawo mashi fresh fruit, a faffadan tray ya ajiye mashi saman mattress, abunka ga maciji, Wai Wai yake Wauka da baki Yana lunkuma shi, Cikin ?an?anin lokaci Ya shanye kayan marmarin, bayan Ya kammala ci, Big guy ya tambayi Salsabeel Ina Unaisah take? Yaga babu ita adakin salsabeel Yace ta fita dauko hijabin sallah ne, amsa mashi yai da okey, kafin Ya dauki tray din Ya juya yabar dakin.

Adai dai lokacin daya sauko down hannunshi ru?e da tray, Unaisah da Boss man suna kokarin nufar benan,
Da mamaki big guy ya furta wa nake gani kamar Boss namu? Me ye hana ka runtsawa ?
Fuska asake Boss Ya nufe shi yana fadin abunda ya hanaka runtsawa nima shi yahana in runtsa

Dariya big ya saki kai dai fadi gaskiya mutumina, nasan me ya hanaka yin bacci, damuwace ta isheka da fargabar kada maciji ya sari ?arka, koba haka ba ? Ya faWa yana Wage mashi gira da zolaya.
 Baka da dama Big guy, ai dole na damu, ita kaWaice fa ?wallin ?wal, bugun zuciyar, ya fada idanuwanshi akan unaisah wadda tuni Ta haura saman bene don ta isa ga dakin danish
 Na fahimci ba ?aramin so ka ke yi ma yarinyarnan taka ba, nima kuma inasonta, me zai hana ka bani auranta?da zolaya yai maganar
Harara Boss Ya watsa mashi shima da zolayar yace ka dai bi a hankali, kada mamallakinta Yaji ka, kaima kasan me zai biyo baya,
Da sauri Big guy ya toshe baki yana fadin au namanta, ashefa ka bayar da ita, balle ma nasan koda baka bada ita ba da wuya ka bani ita, don na fahimci kafison inda zata huta dariya boss yasaki yana fadin kamar ka sani, kaima din ai ba daga baya ba, sai dai kayi mata tsufa, ina laifin ka nemi ummi mana zata dace dakai..... tunkan ya ?are maganar, Big guy ya galla mashi harara Allah Ya kiyaye, in rasa wazan nema sai karuwa
Boss yace abar dai kaza cikin gashinta, kaima din ai tubabbe ne, nima labari naji
 Ina ganin girmanka man, mu bar maganar, bana son tuna baya, Ni bansan ma wani munafukinne yabaka labari ba, wallahi da zan sani saina takaita jin dadinsa
Dariya Boss yai ganin yadda ya 6ata fuska.

 Sorry mutumina, zolayatace kawai, ni bansan komai ba, kaine ka kama kanka,

 Next time idan ka ?ara min wannan wasan, A jikin ?arka zaka gani Ya fada tare da bi ta gefen Boss Ya wuce yana dariya, shima Boss din dariyar yakeyi
 Ai kai ?aramin Wan iskane, sai dai ka cika baki indai akan Angel dinane, don kuwa kasan ko kallon banza kayi mata a jikinka zaka gani,
Big guy bai juyo ya dube shi ba, Yai tafiyarshi.

Bayan komawar Unaisah dakin, a kishingiWe ta samu salsabeel harya gaji da zama, macijin yana nannaWe gefenshi.

Tayi tunanin bacci yake yi hakan yasa ta soma yin sanWa tana tafiya duk don kada ta farkar dashi, shimfida dardumar hannunta tayi, kafin ta daidaita natsuwarta, ta kabbara sallah.

Boss na kokarin shigowa dakin aka fara kiraye kirayen sallar asuba, daga bakin kofar ya tsaya yai gyaran murya, salsabeel daya lumshe idanuwanshi jin gyaran muryar da Boss yai mashine yasashi bude idanuwanshi
 Sannu da kokari, Mun hana ka bacci, yamutsa fuska salsabeel Yai, bacci yana neman yaci ?arfin shi
 Baku kuka hanani bacci ba, ni na hana kaina saboda Wan uwana ya fada yana duban macijin.
Kallon shi Boss Yai, gwanin ban tausayi ya langwa6e kansa, bawan Allah takaicin duniya ya ishe shi.
Shiga cikin Wakin Boss Yai, a bakin gadon ya dakata da yin tafiyar yana kallon Giant snake din
 Bacci yake yi ? Ya jefa ma salsabeel tambayar
 Bazai Iya runtsawaba, idan har ba ?ar uwarshi tana atare da shi ba, sai kuma idan ya dawo ainihin halittarsa
Cikin tausayawa boss yace kayi hakuri, wata rana sai labari, In sha Allah ?arshen wahalarka ne Yazo, wadanda suka yi silar ?untata rayuwarka, bi iznillahi ajalin su ne yazo, zasu WanWani kuWarsu har sai sunji dama ba a halitto su a duniyar nan ba, sai sunyi danasanin rayuwarsu..... kalamai masu dadi da kwantar da hankali Boss yake fada ma giant snake din, yayi lamo yana sauraronshi.

 Naji an fara kiran sallar asuba, Bari nashiga toilet inyi alwala, idan na fito kaima saika shiga ka yi mu tafi masallaci, yai magabar yana duban salsabeel.
Batare da 6ara lokaci ba, Boss ya shiga toilet ya dauro alwala, bayan ya futo salsabeel Ya shiga shima yai alwalar,, sallama sukayi ma Unaisah dake zaune saman darduma, kafin suka tafi.

Kamar jira take Yi, subar Wakin, jiki na 6ari ta mi?e ta nufi gadon ta haye gefen shi tana kallonshi, ta fahimci bacci yake ji, hakan yasa ta janyo bargo ta lullu6asu don ta taimaka mashi yai bacci.

*EX-PRISONERSd'*

Lokacin da Batul ta farka daga bacci, jikinta duk ba daWi, tamkar mai fama da zazza6i, mura tayi mata mugun kamu, muryarta da?yar take fita, fitowa tayi daga cikin bargon idanuwanta sunyi luhu luhu, ?o?ari take tabar dakin duk don kada ta ?ara haWa ido da ummi, tayi tsammanin zata ganta asaman gadon sai ganinta tay kwance saman carpet, ta lullu6e half body dinta da bargo, tafi ?arfin ta haWa shimfiWa da su shine ta dawo kan carpet ta kwanta.
Muryar batul kasa kasa ta ke ambaton sunan parveen,
Da?yar ta samu parveen ta farka daga bacci, tana faman yin mi?a haWi da yin hamma, juyawa tayi 6angaren su Jemimah ta soma tada su daga bacci Waya bayan Waya suka farka suna faman mutsustsuke idonsu.

Cikin muryar rada take yi masu magana ku tashi mu tafi Waki, lokacin sallar asuba yayi, ru?o hannun jemimah tayi ta sauko da ita daga saman gadon, Parveen ta ru?o hannun Azeeza suka sauko.

 Bana so ta farka ta ganmu, kada ku yi surutu mu lalla6a mu bar mata Wakinta ta faWa tana dubansu, Jinjina mata kai su ka yi alamar toh.

Cikin takun sanWa suka nufi ?ofar fita dakin, sai da suka fita Batul ta tuna da kayan ummi dake a jikinta, dafe kai tayi da hannu Waya nashiga uku ashe ban cire mata kayanta ba, Parveen ki ru?e hannun Aziza dana jemimah ku tafi Wakin mu zan biyo ku daga baya

Ma?e kafada jemimah tayi ni tsoro nake ji, idan abun nan ya ganmu fa ?
 Kada ki damu, babu shi ai, waWannan mutanan sun kashe shi da?yar batul take Yi masu magana
 Batul baki lafiya? Idanuwanki sun kumbura jawur, muryar ki kamar ba aji sosai Azeeza ce tayi magnar.

Kafin batul ta bata amsa parveen tace sanyine ya kamata, sai da na hana ta kar6i rigata amma ta kar6a tasaka

 Amma ai aunty ummi ta bani kaya na saka, Kawai bana jin daWine bawani abu ke damuna ba, Ku tafi Waki zan biyoki Ta faWa tare da juyawa ta nufi Wakin.

A tsananin tsoroce suke tafiya suna tunkarar benan, parveen tana aru?e da hannun azeeza dana jemimah, har yanzu basu daina jin fargabar macijin ba.

Bayan batul ta koma dakin Ummi cikin sanda take tafiya, harta ?arasa gaban gadonta, ta cire mata kayanta, ta Wauki doguwar rigar parveen data jefar ?asa, ta zura a jikinta, Juyawar da zatai keda wuya, taji sautin datse kofar Waki, rass taji gabanta ya fadi ganin ummi atsaye bakin kofar ta goya hannayenta kan ?irjinta, fuskarta a murtuke babu annuri, idanuwanta sun ?an?ance.

Hankalin batul ya tashi matu?a, agigice ta furta aunty ummi ina kwana
Harara ta galla mata daban kwana ba kin ganni atsaye? Kilbabba uwar iyayi

Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace Ai na cire maki kayanki, gasunan kan gado, Ni dakinmu zan tafi, wajen unaisah

 Idan kinga na ?yale ki kin fita daga dakin nan, to kuwa kin gyara sautin muryarki ne, wallahi baki isa kija min bala e ba, Har kayan sanyi na baki, na kuma kashe sanyin a.c, saboda ba?in hali irin naki saida kika bari mura tayi maki mugun kamu duk don kija min masifa ko ?

Hawayene suka soma wanke fuskar batul, muryarta na rawa tace ba haka bane aunty ummi, nima bayin kaina bane, bansan mura ta kamani har haka ba, dan Allah kibarni in koma cikin ?an uwana

Shu umin murmushi ummi tayi mata,
 Zan barki ki tafi, amma kafin nan saina fara kawar maki da murar nan, don haka mu shiga toilet inyi maki wanka da ruwan zafi

Zazzare ido batul tayi hadi da girgiza kanta dan Allah aunty ummi ki ?yaleni, ai ni ba yarinya bace, da zaki min wanka, ni kawai ki rabu dani nayi maki al?awarin babu wanda zaisan ina yin mura

?aure mata fuska ummi tayi zaki wuce mu shiga toilet ko saina 6ata maki rai ?

Cikin jin ?unar rai, batul ta ma?e mata kafaWa ni bazan shiga ba, Na fada maki banaso, ki ?yaleni, atakure take Yi mata magana, makoshinta radadi yake yi mata.
Ganin ummi na tunkarota ne yasa ta soma ja da baya tana kuka, kokarin kubce mata tayi da sauri ummi ta dam?o sumar kanta, tajata ta ?arfi ta shigar da ita toilet tana fadin Ke har kin isa ki kufce min, ?aramar ?ar shila dake, me zan gani a jikinki? da har kike fadamin ke ba yarinya bace sautin kukan batul ya cika dakin ummi, gigitacciyar tsawar data kwatsa matane yasa tayi saurin jan baki tayi shiru, hawaye na cigaba da bin fuskarta.

Ummi tafi ?arfinta, da girmanta da komai, Tayi mata wanka da ruwan zafi, tamkar zata sale mata fatarta, fitowa ummi tayi daga cikin toilet din, ta nufi closet din kayanta, tana faman sakin murmushin mugunta, riga da wando ta dauko masu kyan gaske, na sa?a launin pink, waWannan kayan tsohuwar ajiyace tuntana ?ar shekara sha bakwai a duniya take 6oyansu, tana matukar son kayan, rigar tana da hula hannunta dogone.

Komawa toilet din tayi kamar yadda tabar batul haka ta sameta, ta ?an?ame kanta jikin bango, dan pant ne ajikinta, hannunta biyu tallabe da kirjinta ta kakkare boobs dinta.

Jefa mata kayan ummi tayi da sauri ta kar6esu.

 Ina jiranki aWaki, salon kuma ki daWe, idan kika ?ara mintuna wani wankan zan sake yi maki cike da isa ta furta maganar, kafin ta juya ta fuce daga toilet din, abakin ?ofar ta dakata tana jiran fitowar batul.

Jin motsin buWe toilet door dinne yasa ummi kai idonta ga dubanta, har saida taji gabanta ya fadi, ganin kyan da kayan sukayi ma batul, rigar tayi mata daidai, wandonma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login