Showing 195001 words to 198000 words out of 260999 words

Chapter 66 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

hankali kada ku bari yaganku yaron wayau ne dashi, yanzu zamu biyo diddiginku tunkafin maijor ya amsa mashi yai saurin yin rejecting call din, Ya dannawa driver dinshi Kira bugu Waya ya daga Ina jiranka abakin entry hall na gidan baba, kazo da mota ka daukeni
Ya ?are maganar tare da kashe kiran, Jikin shi har tsuma yake yi fatan shi Allah ya basu nasarar kama jazz don ganin menene yake aikatawa,
Badajimawa ba ba?ar mota ?irar Range rover ta shararo da matsakaicin gudu bata nufi ko ina ba sai bakin entry hall adai dai nan Tiger Yai parking dinta, Jiki na rawa sir mubarak Ya buWe front seat na motar ya shige tare da bashi umarnin su tafi, reverse yai kafin ya karya kwana Ya nufi tan?ameman gate din fita daga estate din dake a kewaye da jami ai, tunda suka hango sir mubarak ta tagar motar basu yi gigin dakatar dasu ba, kaitsaye motarsu ta haura saman titi, da gudun gaske tiger yake driving dinsu tamkar zasu tashi sama, sir mubarak yai amfani da phone dinsa wurin bin diddigin su major, cikin sa a suka samo location din da suke, dare ne tamkar da rana saboda hasken street light daya gauraye ko ina, hanyar da suka biyo kwata kwata babu mutane, sababbin gine gine ne a unguwar, wani ginin ma ba a kammala shi.

Rage gudun motar tiger yai ta hanyar glass din motarsu suka hango motar major tana tafiya a hankali ga dukkan alamu sun ?araso inda dr jazz Yake shiyasa suka rage speed din motar, bayan major yai parking din motarsu, kusan atare suka fito shida wani matashin saurayi dukansu suna asanye cikin kakinsu na sojoji, daga bayan motarsu Tiger yai parking din tasu motar, fitowa sukayi atare shida Sir mubarak, koda su Major sukayi arba dashi a hanzarce suka buga ?afa tare da sara mashi, Jinjina masu kai Yai yayin da yake bin gine ginen da kallo Ya ce ina ku ka ga jazz din Ya shiga ? Ya jefa masu tambayar cikin ?agara da sonjin amsarsu.

Major yace Wancan gidan mai jan gate Ciki Ya shiga yai maganar yana nuna wani katafaren gida, Da sauri Sir mubarak Ya nufi gate din, Major da Army din da suke atare kowannansu Ya zaro bindigarshi, shima Tiger Ya curo tashi pistol din, gefe da gefen sir mubarak Suka Jera sun saita bindugunsu saboda tsaro gudun kada akawo masu hari tunda basusan adadin miyagun da yake mu amala da su ba, Cikin sanWa suke tafiya suna bin ko ina da kallo, ta ?ofar jikin gate din da aka bari abuWe suka shiga, babu kowa abakin gate din tamkar anyi shara, Sir mubarak yace Anya major akwai mutane acikin ginin nan? Naji shiru babu motsin komai, kodai kunyi kuskurene ? Girgiza kai major yai Yalla6ai tabbas cikin ginin nan ya shigo, ba mu yi kuskure ba, akan idonmu ya fito daga cikin motarshi Ya buWe gate kafin Ya koma ciki Yajata zuwa cikin gida
GyaWa kai sir mubarak Yai okey mu ?arasa ciki kaitsaye suka nufi katafaren ginin da suke tsammanin zasu samu hanyar shiga cikin gidan, adai dai bakin wata ?ofa, suka dakata A hankali Major Ya turo ?ofar cikin sa a suka sameta abuWe, Waya bayan Waya suke shiga, Hadadden palour ne An ?awata shi da furniture, ga sanyin A.c ta ko ina mai ratsa fatar jikin mutun.
Sunyi mamakin ganin babu kowa a palourn, ko motsin mutun babu, daga cikin falon akwai bene da zai kai mutun up stair, yanke shawarar haurawa saman benan sukayi, Cikin sanWa suke tafiya kowa ya saita bindigarshi saboda tsaro, a second floor suka dakata da yin tafiyar suna bin ko ina da kallo, ?ofofin Wakunane ta ko ina, Sam sun kasa motsawa saboda sunfara kokwanton anya akwai mutane agidan
Tiger yace shirun yayi yawa, kada fa ace tarkone aka Wana mana don mu afka
Major yace ai shi soja da kasada akasanshi, Idanma tarkon ne suka shirya mana to bamu bane zamu rufza aciki ba, sune zasu afka, wata kil watan tonuwar asirin su ne Ya kama

Sir mubarak Ya natsu Yana sauraronsu, ya rasa madafa sam bayason suyi kuskuren shiga gidan mutane, don ya fara kokwanto.
Army yace yakamata mu fara dudduba Wakunan nan wata ?il mu same shi aciki Ya furta hakan tare dakai hannu Ya buWe ?ofar Waki ?aya, karaf idanuwanshi suka sauka akan matasan ?an matan dake akwance saman bedmattress, cikin shiga ta kayan bacci a matu?ar ruWe ya juya yana kallon Sir mubarak Ya furta yalla6ai ?an matane kwance saman gado, Anya kuwa bamuyi kuskure ba ! Matsawa sukayi zuwa bakin ?ofar da Army yake a tsaye, kowan nan su Ya le?a Sun yi mamakin ganin kyawawan ?an mata kwance suna sharar baccinsu farare tass dasu kamar jinsin larabawa.
Rai amatu?ar 6ace sir mubarak ya dubi Major kace min nan jazz ya shigo to yana ina? WaWannan ?an matan alamace dake nuna cewa Gidan wani ne muka faWo
Tuni major yasha jinin jikinshi, Muryarshi adabarbarce ya furta yalla6ai wallahi da idona naganshi Ya shigo gidan nan, Ga army nan ka tambaye shi, ai tare dashi muka shigo, kuma shima yaga jazz din Yai maganar yana nuna army da hannun shi
Kallon Army sir Mubarak Yai, da kakkausar murya ya furta idan har kukasa naji kunya wallahi zakuji ajikin ku ne hankalinsu ba ?aramin tashi yai ba, Jin abunda yace masu, Guntun tsoki Yaja tare da juyawa da niyar Ya fuce daga gidan, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka soma Jiyo masu shesshe?ar Kukan mace cikin murya mai ?araji take fasa ?ara tana fadin Bana so! Ka ?yaleni Nace maka banaso, Ni ka ?yaleni, ka sake ni ka rabu dani.... sautin gigitacciyar ?arar data fasa gaba Waya Ya cika ginin, Kallon juna sojojin sukayi kafin da gudun gaske suka nufi Hanyar da suke jiyo sautin kukan Yarinyar, Sir mubarak kamar zai yi tuntube, cikin zafin nama suka haWa ?arfi wurin bangaje ?ofar Wakin, A tsiyace ?ofar ta bude, Hankalin sir mubarak Idan yai dubu to ya tashi, A matu?ar gigice sojojin suke kallon abun da ke faruwa, Lamarin yai matu?ar Waga hankulansu, musamman Sir mubarak Ya gaza yadda da abunda idanuwanshi suke nuna mashi, Tuni zufa ta soma wanke fuskarshi,
Sam baiji motsin shigowar mutane Wakin Ba, Ya du?ufa akan abunda Yake aikatawa, Rigar shaddar shi da wandonshi gaba daya suna asaman floor, Singlet ce kaWai a jikinshi sai gajeran wando Fari, Ya haWa uban gumi, matashiyar yarinyar daya danne saman gado sai kuka take Yi, tana bugun bayanshi da hannayenta, A wahalce take harba ?afafuwanta cikin fitar hayyaci kamar ranta zai fita, ta gama galabaita, tuntana kukan neman agaji har muryarta tafara disashewa, wani irin kukan kura sir mubarak Yai cikin zazzafan taku Ya kutsa kai Cikin Waki, da hannayenshi biyu ya dam?o wuyar singlet din Jazz da ?arfin gaske Ya wurgar dashi kasa gaba Waya ya kife kanshi ya daki tiles, Jiki na kerma ya Wago yana dubansu Waya bayan Waya kafin ya tsayar da idanuwanshi akan fuskar Sir mubarak dake tsaye kanshi tamkar mayunwacin zaki, hankalinshi yai matu?ar tashi da ganinsu duk yabi ya ruWe ya susuce, jikinshi ya hauyin kerma, sai faman zazzare idanuwanshi yake Yi, Muryarshi na kakarwa ya furta daddy.... bai ?arasa maganar da zaiyi ba, Sir mubarak Ya dam?o wuyanshi ya Wago dashi tsaye cikin rauni na murya ta wanda ya karaya yake fadin Jazz ka kasheni, Ka cuceni, dama abunda kake aikawata kenan? ?an mata kuke tarawa acikin gida, donku lalata rayuwarsu sannan ku kashe su? Nasha kama ka kanayin waya kana fadin kaji ashe mutanene kajin, Inna lillahi wa inna ilaihirraji un cikin jin ?unar rai yace Wallahi baka isa ka Waura min hawan jini baa, Kafin ka kasheni ni zan fara kasheka don ubanka, Mugu azzalumi fasi?i, Jazz ka bani mamaki, ka cuce ni kuma ka cuci mahaifiyarka, Cikin shesshe?ar kuka Sir mubarak Yake furta maganar, Ya sha?e wuyan Jazz sai faman mutsu mutsu yake Yi, don ya ?waci kansa.

Yayin da sojojin suke a kewaye da gadon da yarinyar take, duk tabi ta tsorata jikinta sai kerma yake Yi, short gown ce a jikinta, yalwatacciyar ba?ar sumar kanta duk ta rufe gefe da gefen fuskarta, tamkar wadda tasha gudu sai faman yin haki take Yi.
Sautin ?arar da jazz Ya fasane Ya janyo hankulansu ga duban shi, wani irin radadin azabane Ya ziyarce shi sakamakon buga kanshi da sir mubarak Yai jikin Mirror din dakin, gaba Waya madubin Ya zube, Jini Ya wanke fuskar Jazz hatta gaban farar shirt din jikinshi Yayi ca6a ca6a da jinin shi, daddafe kanshi yai da hannu bibbiyu cikin mawuyacin hali Yake sambatu  Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Daddy ka kashe ni, Na shiga uku na bani na lalace, daddy ka rabani da rayuwata
Yarinyar dake zaune saman gadon, ganin yadda suka raunata shi yasa ta fasa ?ara da ?arfi ta furta yaya Jazz, Wayyo Allah na kun kashe min shi, mugaye azzumai baiyi maku laifin komai ba amma kuna cutar min dashi Da gudun gaske ta duro daga saman gadon ta kife ?asa, sam babu natsuwa atare da ita, da rarrafe ta ?arasa gabanshi, Ta sanya hannu biyu ta Wago dakanshi ta daura saman laps dinta, Cikin shesshe?ar kuka take fadin Wallahi Allah bazai barku ba, Ku baku da burin daya wuce ku cutar da rayuwar waWanda basu ji ba basu gani ba, Sai Allah ya saka mashi, ku dukanku sai kun shiga wuta ta fada tana nuna su da yatsan hannunta, kallon juna sojojin sukayi, sunyi matu?ar girgiza da jin kalaman Yarinyar, sun fara kokwanton Anya kuwa Zargin da sukeyi mashi gaskiya ne? Tayaya yarinyar da ake cutar da rayuwarta, kuma take fada don an ta6a mutumin dake ?o?arin rabata da mutuncinta!! Fashewa tayi da kuka Hannayenta tuni sun 6aci da jinin dr jazz tana kuka tana ambaton sunanshi yaya jaz dan Allah kada ka mutu kabarmu, wallahi idan ka mutu nima saina kashe kaina
Zuciyar sir mubarak ce ta soma harbawa da ?arfin gaske, Jiri ya soma ?o?arin kwasarshi, Gaba Waya ya gama rikicewa, Hankalinshi atashe Yake kallon Kwalaben alluran dake ajiye saman bedside drawer tare da sirinji, hada magunguna, Adaddafe Ya nufi drawer din da niyar Ya duba kwalaban don ganin na menene, sautin ringin wayar Jazz ne Ya dakatar da shi, da sauri ya daura rinannun idanuwanshi inda yake jiyo sautin daga cikin aljihun wandon shaddarshine, Major ne yai saurin daukar wandon Ya binciko wayar cikin aljihun, Ya mi?a ma sir mubarak, yatsun hannun shi na kerma ya ru?e wayar, batare daya duba sunan mai kira ba Yai picking call din Ya sanya kiran handsfree.

Sautin muryar mutumin dayaji tayi matu?ar gigitar dashi, har baisan sa adda Ya saki wayar jazz ta fadi saman floor, sojojin dake atare dashi duk sun sha jinin jikinsu, kallon kallo suka soma Yi a tsakaninsu, cikin matsanancin tashin hankali, sautin shesshe?ar kukan matashiyar ya cika dakin, dr jazz tuni Ya jima da sumewa.

*EX-PRISONERS=ؔ?*

Gaba Wayansu sun hallara a dining room, domin cin abincin Dinner dinsu, mutun Waya ne ke babu acikinsu, Yana can dakin shi, mazan suna fuskantar matan, sunyi shiga kala Waya wandon jeans da farar shirt,matan kuma dogayen rigunane a jikinsu, Aunty ummi ce kaWai ta banbanta dasu, riga da skirt ne ajikinta sun matseta, shape din jikinta Ya bayyana muraran, babu mayafi akanta, sa6anin su Batul da sukayi rolling veils.

tunda suka zauna Unaisah ta kasa samun sukuni, yanayinta tamkar na mara lafiya, sai faman jujjuya spoon take Yi acikin plate din gabanta, da ke sha?e da abinci, damuwar duniya ta isheta, sam babu sukuni akan fuskarta, A hankali ta Wago da ido tana duban fuskokin ?an uwanta, tun daga kan Sajeed dake fuskantar Azeeza, suna cin abinci suna kallon juna, har zuwa kan Haris dake fuskantar Hannah, kafin ta kawar da idonta daga kansu ta maida su kan fuskar Naufal da javed, sun natsu suna cin abincinsu, hasken musulunci ya fara shigarsu, komai nasu cikin natsuwa suke yin shi, mayar da idanuwanta tayi akan face din jamimah, bakinta duk ya 6aci da mai?o, ta samu cinyar kaza saici take Yi kamar tsohuwar mayya, ta cinye tsokar naman, ?ashin take gwaigwaya kamar babu sauran naman alhalin gashinan saman tray guda aka jera masu chicken legs, girgiza kai tayi kafin ta mayar da dubanta kan Batul dake gefenta, ita dai duniya babu abunda ke burgeta irin taliyar indomie, tun ranar farko data fara cinta, kullum ne in zasu ci abinci saita ci ta, sam bata gajiya, da hannu take nannaWota kafin ta tura abaki, rantane ya raya mata ana kallonta, dai dai time dinda ta tura taliyar abaki ta Wago da ido suka kalli juna ita da Angel, da sauri ta haWiya taliyar, cikin muryar raWa ta tambayeta lafiya take kallonta? Ko tayi ?auyancine ? Girgiza kai Angel tayi babu komai kawai burgeni kikeyi idan kina cin noodles da hannu
Gyaran murya ummi tayi masu atare suka Wago suna kallonta.
 Unaisa tun Wazu na lura kamar bakya jin daWi, meke damunki ne ? Murmushin ya?e ta sakar mata babu komai aunty ummi, ko kinga wani abu ne Waga mata gira tai ?warai kuwa, tun da gashinan kin kasa cin abincinki
Kafin unaisa ta ?ara furta wani abu, Muryar Haris ta katse su
 Kodai Danish bashi da lafiyane? Tun jiya da rana ban ?ara ganin ya le?o waje ba, naso naje na duba shi sai dai karatu Ya mantar da nayi yin hakan
Cikin nuna damuwa Sajeed yace wallahi yana araina, tun Wazu da muna awurin kar6ar karatu nake ta tunaninshi, bansan dalilin dayasa baya son zuwa cikin mu cin abinci ba, naga dazu da rana ke kika kai mashi lunch dinshi a dakin shi ya faWa yana nuna Unaisah da spoon din hannunshi.
Naufal Yace to me zai hana mu tashi muje Wakin nashi mu duba su? Ni abunda ke damuna da danish baya son sakewa cikin mutane Yai maganar fuskarshi dauke da damuwa.
Javed yace ai halinshine tun fil azal, kaima kasan Danish bai cika son zama cikin mutane ba, baison surutu kuma baison ana kallon shi
Gyaran murya Ummi tai masu, Hankalinsu Ya dawo kanta sun natsu suna jiran jin me zatace
 Koda ace halinshi ne hakan bai kamata ku ?yale shi ba, cos barinshi acikin Waki zai Iya haifar mashi da wata damuwar, duk da naga Unaisah tana ?o?arin dubashi, amma a ?alla yakamata kuma kuna zuwa wurinshi kodan ku dinga Webe mashi kewa, kafin zuwa lokacin da zai saki jikinshi, nasan rashin sabone ke damun shi
Jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da bayaninta, Sajeed yace ku tashi muje dakinshi Inyaso sai mu tafi da kayan abincin mu ?arasa ci acan Yai maganar tare da mi?ewa, da sauri Unaisa tace a a basai mun tafi mu duka ba, Ku zauna ni zanje in taho da shi amsa mata sukayi da toh, da sauri ta mi?e ta nufi ?ofar fita daga dining room din
Mi?ewa Batul tayi Ummi tace Ina zuwa? Cikin sanyin murya tace ina so zanbi Unaisah ne
 Ki koma ki zauna, ai tace zasu dawo atare dashi ko ? Amsa mata tai da toh jiki asanyaye ta koma ta zauna.
Shiru suka Wanyi, abincinma sun dakata da cin shi, hakanan suke jin zuciyoyinsu na bugawa, Jemimah kadaice ke cin abinci ta cika masu kunnuwa da sautin taunar abincinta, da gangan take yi duk don ayi mata magana.
Harara Azeeza ta watsa mata dan Allah ya isa haka, ba zaki Iya ci a hankali bane ? Hanna tace ki daina wahalar da bakinki, dagangan take yi duk don ayi mata magana tuntsirewa tayi da dariya tana fadin Eh din kuma gashi kunyi min maganar ba girgiza kai ummi tayi fuskarta dauke da murmushi take dubanta, hankalinta kwance take yin magana. Kallon da naufal ya jefa matane yasa tai shiru tana ?an ?un?uni.
 Kuna burgeni, gaba Wayanku ta fada tana nuna su da spoon din hannunta.
Batul tace aunty ummi, kina nufin kina sonmu ? Jinjina mata kai tayi haka nake nufi, murmushi su naufal suka saki jin abunda tace,
Parveen na faman siWar hannu tace Aunty ummi ke baki haifi ?a ?a bane, kamar yadda daddyn unaisah ya haife ta? Ko kuwa ita mace bata haihuwane sai maza ? Da mamaki Ummi ta dan zaro ido tana kallon parveen da tayi maganar, sam babu wasa akan fuskarta ita bilhakki take Yin maganarta.
 Amma baki da hankali parveen, Kin manta labarin da unaisa ta ta6a faWa mana ne? Macace take haihuwa ba namiji ba, itama Mommyntane ta haifeta ta jefar da ita cikin wannan abun kalar na toilet din gidan nan, namanta sunanshi Batul ce tai maganar,
Azeeza tace eh kuwa hakane, Macace ta haifi unaisa ba namiji ba, to aunty ummi ke kin ta6a haihuwa ? tayi tambayar tana kallon ummin america wadda mamaki da al ajabi suka cikata, sai kallonsu take Yi Waya bayan Waya, sajeed Ya du?ar da kanshi ?asa sai faman sakin murmushi yake Yi jin wautar parveen.
 Aunty ummi kinyi shiru baki ce komai ba, kina ta kallonmu Hanna ce ta jefa mata tambayar, ta ?ura masu ido tana binsu da kallon mamaki,
 wai kuna nufin bakusan komai ba, game da zamantakewar aure?
Atare suka haWa baki wurin furta Aure kuma ? Gudun kada suyi wata 6aran 6aramar yasa Sajeed yin saurin cewa aunty Ummi, Yakamata mu maida hankali akan abunda muke Yi yanzu, Ta6e baki taWanyi kafin ta furta okey,  ta fahimci baison maganar dama ta lura yafi su hankali shida Unaisah, bata ta6a ?agara da sonjin labarinsu ba sai yau, tabbas tana son tasan tarihin rayuwarsu! Ya akai har suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login