Showing 234001 words to 237000 words out of 260999 words

Chapter 79 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

jin zuwan Sheikh imam
 Ina yi mashi barka da zuwa, Allah ya kawo ku lafiya Hateem Ya amsa mashi da amen mun gode son, daga haka sukayi sallama da juna.
Daura wayar yai saman side drawer ya sauko daga saman gadon Ya nufi dressing room din dakin shi, badajimawa ba ya fito sanye da jallabiya launin sky blue, tayi bala en yi mashi kyau, Gaban dressing mirror din dakin ya tsaya tare dakai hannu cikin jerin turarurrukansa Waya bayan Waya yake dauka yana feshe jikinshi, tuni ?amshinshi ya karaWe dakin.
Diamond wrist watch din shi dake ajiye gaban mirror ya dauko Ya zura a hannunsa, Kafin Ya mi?a hannu Ya dauki Phone dinsa, A tsanake Yake pressing dinta, Layin Boss Ya danna ma Kira, Bugu Uku Yai picking, gaisawa suka farayi kafin Ya furta Sheikh Imam Ya ?araso, Ina bu?atar ganin kowannanku a main falo, domin mu tarbesa

Boss Ya amsa mashi da Toh, In sha Allah, Yanzu zan sanar da su daga haka Yai rejecting kiran.

A dai dai lokacin, Unaisah ta kuma farkawa daga baccin da yayi awon gaba dasu ita da giant snake din, Cikin sanWa ta sauko daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon gadon, ta kudundune shi da bargo, ta ?agu da son ganin ?an uwanta shiyasa zata fita taje gare su, batasan a wani hali suka kwana ba.
Bayan ta fito daga dakin down ta sauko, Moving quickly ta nufi Hanyar da zata hau bene taje dakin ummi, Har ta kusa haurawa saman staircases miryar boss man ta katse ta Unaisah ! Cak ta tsaya haWi da waiwayowa tana dubanshi,
 Ina zakije ne ?
Muryarta adisashe ta furta dakin aunty ummi, Inason ganinsu batul ne, ai ka fadamin acan suka kwana
 Hakane, Nima dakinta zani je, amma tunda gaki bari in baki sako ki kai mata ya fada tare da zura hannu cikin aljihu ya curo maganin mura ya mi?a mata.

 Wanene bai da lafiya ? Hankalinta atashe ta fada tana bin maganin da kallo.

 Ummi ce ke bata jin dadi, mura ce ta kamata Ajiyar zuciya Angel ta sauke tayi tunanin ko cikin ?an uwanta wani ke bai da lafiya.

Kar6ar maganin tayi, har zata juya muryarshi ta dakatar da ita Sheikh imam yana akan hanyar zuwa gidan nan, malamin da zai duba Wan uwanku danish Waro ido waje tayi lokaci Waya ta fashe da dariyar farin ciki, Murmushi yasaki Dama ya fada matane don ya faranta mata rai.??
Idanuwanta cike tab da ?walla take fadin Alhamdulillah, wayyo Allah wallahi naji dadi, fatana Allah yasa ayi asa a danish Wina yaji sau?i ya dawo kamar kowa

Boss yace in sha Allah zamuyi nasara, yanzu kije ki kai mata maganin, idan kin fito ki same mu a falo,
Amsa mashi tayi da toh, jiki na rawa ta nufi benan ta haye sama, burinta takai mata maganin sannan ta kwantar masu azeeza hankalinsu kafin ta dawo falon don taga sheikh imam

Abakin ?ofar dakin Ummi ta dakata tare dakai hannu ta dafi glass door din A hankali kofar ta buWe, Zura kafarta keda wuya sukayi kicibus da batul, sam hankalinta ba akwance yake ba, ganin ummi ta shiga toilet tsawon lokaci bata fitowa ba shiyasa ta yi dabarar guduwa daga dakin don ba ?aramin takura tayi ba, baiwar Allah suna haWa ido da Unaisah, ta faWa jikinta, Hannu biyu ta ?an?ameta dasu kamar zata koma cikinta, tun daga kan yadda ta rungumeta ranta ya bata cewar babu lafiya, A hankali itama ta zagayo da hannayenta saman bayan Batul.

 Meke damunki sister? Baki da lafiyane ? Ta fada batare data raba jikinsu daga na juna ba
Muryar batul asha?e da mura ta furta babu komai, Mu tafi dakinmu, Ni kadaice na rage su azeeza sun tafi tun Wazu, Ni ko sallar asuba banyi ba
Hankalin Unaisah ba ?aramin tashi yai ba, Jin muryar Batul asha?e kamar an Waure mata makoshi, A hanzarce ta raba jikinsu, ido cikon ido suke kallon juna, ta Wanyi mamakin ganin kayan dake ajikinta masu kyan gaske.
AruWe ta furta batul! Dama kece baki da lafiya ba aunty ummi ba? Garin yaya mura tayi maki mugun kamu ?
Shiru batul tayi mata batare data furta komai ba, saboda tana jin tsoron ummi taji ta fada ma wani.
Da sauri ta canza akalar maganar tasu Meke damunki? Naga fuskarki ta kumbura idanuwanki sun yi ja, ko kema baki lafiya ?
 Ni lafiyata qalou, damuce ta hana ni yin bacci... bata ?are maganar ba batul ta kuma cewa
 Ina danish dinmu ?
 Inaso zanyi maku bayanin komai amma sai mun koma Waki, Yanzu ki fada min ya akai mura ta kama ki? Ina kuma aunty ummi ?
Murya ?asa ?asa Batul tace nima bansan ya akai ta kamani ba, aunty ummi kuma tana a toilet, itace ma ta kira awaya don akawo min magani, kuma kinga ta bani kaya na sanya tayi maganar tana nuna mata kayan sanyin jikinta.
Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke mun haWu da boss man shine ya bani maganin mura in kawo, ni nama yi tsammanin aunty ummice ba lafiya kamar yadda ya fadamin ashe kece
Jinjina mata kai batul tayi Allah ya baki lafiya sisterna, kayan jikinki sunyi maki kyau, a ina aunty ummi ta samu kayan nan dai dai size dinki kamar donke aka dinka su ?

 Nima bansani ba, Mu tafi daki atakure tayi maganar, tare da ruko hannun Angel, tajata suka nufi down stairs.




*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*








Adai dai lokacin Su parveen suna a zazzaune tsakiyar gadonsu Batul, sun kewaye juna, sai faman zazzare idanuwansu suke yi don har yanzu basu daina jin fargabar macijin nan ba.

Motsin buWe ?ofa ne Yaja hankalinsu ga kallonta, Atare suka shigo hannun su ru?e cikin na juna, wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da gudun gaske Jemimah da Azeeza suka diro daga saman gadon suka nufi unaisah, tunkafin su ?araso ta ware masu hannayenta fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, zubewa tayi saman gwiwowinta yadda tsawonta zaiyi dai dai da nasu, gaba Wayansu ta haWasu ta rungume a ?irjinta, tare da zagaya hannayenta saman bayansu, jemimah tuni ta fashe mata da kuka hada bubbuga bayan Unaisah alamar ranta ya 6aci.

Batul dake a tsaye tana kallonsu sam bata ji takun tafiyar Parveen ba, Sai dai taji muryarta Batul tun Wazu muna ta jiran ki shiru baki zo ba, Ina fata babu wani abu daya same ki ?

Kallonta Batul tayi da ido tayi mata alamar tayi shiru bata son Unaisah taji komai daya faru, jinjina kai parveen tayi don ta fahimci me take nufi.

 A ina kika sami kayan jikin ki masu kyau ? Ta fada tana duban Kayan sanyin jikin batul
Murmushi batool tasaki kafin tace Aunty ummi ce ta Bani su
Parveen tace ko a ina ta same su, ban ta6a ganin kayan da suka yi maki kyau ba kalar waWannan kafin batool tayi magana muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta, A lokacin sun Wago da kansu daga rungumar da Unaisah tayi masu, fuskokinsu sharkaf da hawaye kamar waWanda suka yi shekara basu ganta ba.

 Meyasa jiya kika tafi kika barmu? Inata kiran sunanki baki amsa ba, tsoron wannan abun ya kamamu

Shafa fuskarta Unaisah tayi Am sorry nasan ban kyauta ba, amma kuyi ha?uri, bawani wuri na tafi ba, Ina atare da Wan uwanmu Danish bashi da lafiya......

Tunkan ta ?are maganar, hankalinsu yai mugun tashi jin cewa danish dinsu baida lafiya, damuwace ?arara akan fuskokinsu

 Unaisah meke damun shi? Meyasa jiya ba kizo kin kaimu mun ganshi ba ? Acewar parveen
Batul tace ni da ma saida naji araina Wan uwanmu baida lafiya, Allah sarki danish din mu, Yanzu yana a ina? Ina son ganin shi ta fada idonta akan unaisa dake ?o?arin mi?ewa tsaye tana dubansu.

Ru?o hannunta Azeeza tayi acikin nata dan Allah ki kaimu wurin shi, muna son ganin shi idanuwanta sun ciko tab da ?walla tayi maganar.

Numfasawa Unaisah tayi kafin ta soma yin magana na yanke shawara ?wara na faWa maku halin da danish yake aciki, saboda bana son ku guje shi ko ku dinga jin tsoron zuwa wurinshi....... shiru ta Wanyi na wani lokaci duk sun ?ura mata ido cike da zumuWin son jin ?arashen zancen.

 Amma kafin nan inason ganin sauran ?an uwanmu, naga babu Hannah! Ina taje ne ? Atare suka hada baki wurin bata amsar cewa suma basu sani ba, tun daren jiya basu ganta ba.

AruWe Unaisah take dubansu, Kafin ta furta magana, sallamar Big Guy taja hankalinsu ga duban ?ofar, shigowa cikin Wakin yai hannun shi ru?e dana Hannah, daga bayansu ?an uwansu ne maza tun daga kan Sajeed, Haris, Javed and Naufal, ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Hannah sai faman zare ido take yi kamar wadda aka faWa ma sa?on mutuwarta, sakin hannunta big guy yai jiki na rawa ta nufi Unaisah ta rungumeta, sunyi farin cikin ganin ?an uwansu, Sajeed ya nufi azeeza fuskarshi dauke da murmushi yai hugging dinta, Naufal yajanyo parveen ya rungumeta Yana bubbuga bayanta da hannu Waya,
Batool da Haris suka rungume junansu, Ran jemimah ya 6aci ganin babu wanda ya rungumeta, harta fara tatta6e la66anta za ta yi masu kuka, javed yai saurin Waukarta saman jikin shi, Fashewa tayi da dariya saboda an dauketa.
Big guy dake a tsaye yana kallonsu ya goya hannayensa saman broad chest dinsa, Yaran sun yi matu?ar burgeshi.

Tsawon mintuna suna a manne da juna, kafin daga bisani kowan nan su ya rabu da jikin Wan uwanshi, gyaran muryar da Big guy yai masu ne yasa suka mayar da hankalinsu gare shi a tsanake Ya soma yin magana.

 Inaso ku natsu ku saurareni, dalilin dayasa na tara ku a Wakin nan, saboda na fahimci haryanzu baku daina jin fargaban abunda ya faru jiya ba, Ga ?ar uwarku nan Unaisah zatayi maku bayanin komai yadda zaku fahimta, sannan please bama bu?atar ganin gifcin kowan nan ku a falo! Ku tsaya a Waki, mai bu?atar shiga toilet ya shiga, wanda zai yi bacci ga gado nan ya kwanta,........ kafin Ya ?are maganar Parveen tayi ?asa ?asa da murya tana fadin breakfast din mu fa? ni ina jin yunwa, Jiya da dare bamu ?arasa cinye abincinmu ba murmushi big guy ya saki ta cikin face mask dinshi
Da zolaya yace ki kwantar da hankalinki foodie, Indai abincine har sai kin gaji da shi, kamar kina a gidan manomi ne, Yanzu zansa a kawo maku lafiyayyan breakfast ya faWa tare da nufar kofar fita yana fadin Unaisah Ki kula da su amsa mashi tayi da toh, kamar jira su ke yi ya fita, Har suna haWa baki wurin tambayarta meke faruwa da Danish.

 Zanyi maku bayani, amma kafin nan ku jira waWanda basu yi salla ba su yi tukunna, batool tace min ba ta yi sallah ba
Badan sunso ba suka amince mata

 Kunyi sallah ? Ta jefa masu tambayar
Sajeed yace munyi a Waki
 Kufa ta faWa tana nuna su Azeeza
Girgiza mata kai su kayi alamar a a, Hannah ma tace nima banyi ba, saboda babu hijabi.

 Okey, yanzu abun da za ai ku shiga toilet ku yi alwala, kafin ku fito zan dauko maku hijabin amsa mata sukayi toh.

?aya bayan Waya suka shiga toilet, bayan sunyi alwala kowaccensu ta sanya hijabi, asaman carpet din da ta shimfiWa masu su ka yi sallar, bayan sun kammmala suka cire hijaban suka bata ta ninke ta maida su a wardrobe.

Zama sukayi kan carpet din gefen gado, mazan suna fuskantar matan, sun ?urama Unaisah ido suna jiran jin me zatace masu.

 Kin yi shiru ba ki ce komai ba sister, ke muke sauraro meke faruwa da Wan uwan mu ? Acewar Haris
Sajeed yace tun jiya da abun nan Ya faru mun ganki kina kuka kina fadin danish ya rikiWa ya koma maciji, abun ya tsaya min araina da damuwa a fuskarsa yai maganar.

 Akwai abun da na 6oye maku tun muna a prison ban samu damar faWa maku ba....... a tsanake Unaisah ta labarta masu dukkan abun da ya faru tun daga kan tattaunawarsu da Salsabeel farkon haWuwarsu a gidan kurkukun ?addara da kuma gwagwarmayar da suka yi wajen shawo kan Danish da ruwan zam zam, Har izuwa kan abunda ya faru jiya daya rikiWa ya zama maciji, tunda tafara basu labari hankalinsu ya tashi matu?a, sun girgiza da jin cewa Danish dinsu GIANT ne, Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu, idanuwansu a zazzare, Jikin ta ?aura yai la asar, wato an gudu ba atsira ba.

La66an Sajeed na kerma ya furta kina nufin Danish Giant ne ? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, dafe kai haris yai da hannu Waya da wata irin karyayyar murya ya furta inna lillahi wa inna ilaihirraji un! Mun shiga uku! Wai su waWannan azzulaman mutanan wani zunubi muka aikata masu ne? Da suke azabtar da rayuwarmu? Meyasa suka cutar da rayuwar Danish? Me bawan Allahn nan yayi masu ? Idanuwanshi tuni sun kaWa sunyi jawur da su
 Ni dama nasani bazasu ta6a ?yale mu ba, zasuyi amfani da danish ne donsu maida mu kurkukun ?addara !
Cikin sanyin murya Batool tace bawan Allah danish, shine abun tausayi, wallahi ina jin ba?in ciki da takaicin azabtar mana da rayuwar Wan uwanmu da suke Yi, danish tun yana ?arami suke juya shi, sun hana rayuwarshi sakat, narasa gane dalilin dayasa suke yi mashi haka, Ya Allah ga bawanka nan kai kadai kasan a wani hali yake aciki, Ya Allah Ka fitar dashi, ka kawo mashi Wauki acikin rayuwarshi , tuni hawaye sun wanke fuskar Batool.

Cikin shesshekar kuka Azeeza tace Allah ya isa ba zamu ta6a yafe masu ba, Mugaye azzalumai ?an wuta, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara danasanin cin zalunmu da su ka yi da kuma ?untata rayuwar Wan uwanmu da suke Yi

Azeeza na rufe baki, Naufal da takaici ya ishe shi, cikin jin ?unar rai Ya soma magana wannan wace irin rayuwace? ya zamuyi da ranmu? Ni yanzu na fahimci KURKUKUN ?ADDARA RAYUWARMU CE!! mune kurkukun ?addara saboda duk inda zamu kasance gidan kurkukun ?addara yana atare damu, Meyasa!!! ? Ya jefa tambayar idanuwanshi akan fuskar Unaisah, wadda tayi shiru tana sauraronsu, tabbas maganar Naufal abun dubawace, Yanzu ta fara zargin wani abu.

 Naufal, kamar yadda ka faWi nima haka nake tunani, rayuwarmu itace gidan kurkukun ?addara, amma meyasa zai kasance haka? Su wanene suka sadaukar da mu?.... ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta.

Sajeed yace yakamata mu fallasa asirin komai ke faruwa agidan kurkukun ?addara ga mutanan da suka taimaki rayuwarmu ina da tabbacin zasu taimaka mana don ganin an gano su wanene munafukan dake sadaukar damu ta hakanne zamu tabbatar da zarginmu

Javed yace nima ina goyan bayanka Sajeed! Mu tona masu asiri kawai, idan da rabon mu rayu zamu rayune duk runtsi duk wuya, kai koda ace zamu mutu ne bayan mun tona masu asiri wallahi munci galaba akansu, tunda har muka yi nasarar guduwa daga cikin kurkukun ?addara, wanda ko a tarihi ba a ta6a samun prisoners da suka gudu suka tsira ba sai akanmu !

A hankali unaisah take binsu da kallo, ta fahimci ransu yakai ma?ura wurin 6aci, Jininsu akan akaifarsu yake, kowannansu atsorace yake da abunda ke faruwa da danish.

Fashewa da kuka jemimah tayi haWi da Waura hannayenta biyu saman kanta tana fadin Wayyo Allahn mu mun shiga uku, Yanzu shikenan danish din mu ya zama dodon kurkuku zai Wauke mu ya maida mu can mu cigaba da cin ganye fuskarta sharkaf da hawaye, ruko hannunta Unaisah tayi acikin nata Ya isa haka, Ki daina kuka, kanki zai Iya yin ciwo, girgiza kai ta dinga yi tana fadin genie ba zaki gane ba, wallahi banason komawa kurkukun nan, haushinsu nake ji, Allah zuciyata zata Iya bugawa in mutu kowa ya huta
Gaba Waya idanuwansu na akan fuskar jemimah, ta ha?i?ance tana yin magana shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruWu ruWu saman fatarta.
 Sun kashe mun majnoon dina, sun kashe mana Unaizah, Yanzu kuma mu suke son kashewa fa ta ?are maganar tana faman jan majina
Kwanto da kanta Angel tayi saman cinyoyinta, ta Waura hannunta kan sumarta cikin sigar lallashi take yi mata magana in sha Allah bazamu ta6a komawa gidan kurkukun ?addara ba, Har bada, munbarshi kenan bi iznillahi mune zamu kawo karshen kurkukun da fasi?an Shuwagabannin su, zamu tarwatsa ba?in tarihin da suka kafa, zamu shafe babinsu a doron duniyar nan, zasu WanWanin kuWarsu har sai sunji inama ace ba a halitto su a duniyar nan ba, wannan Al?awarine! da ?warin gwiwa unaisah ta ?are maganar.

Shiru jemimah tayi tuni ta haWiye kukanta, Jikin kowannansu yai sanyi, maganganun da suke yi yai silar fama masu tabon dake acikin zuciyoyinsu.
Da?yar Hanna ta Iya buWe baki tace ni yanzu damuwata a wani hali danish yake aciki ? Tayi tambayar idanuwanta cike tab da ?walla

Angel ce ta bata amsa da cewa har yanzu bai dawo mutun ba, amma Wazu boss man ya fada min cewa malamin da zai duba jikinshi ya ?araso Ina da tabbacin Yana acikin gidan nan, shiyasa Big guy Yace mu zauna a Waki bayason ganin gifcinmu, yakamata mu tayashi da addu a, ita yake bu?ata daga gare mu tunkan ta rufe baki, sukayi saurin daga hannayensu sama, Itama ta Waga nata,
 Jemimah ki tashi muyi ma Wan uwanmu addu a Unaisa ce tayi mata magana, da?yar ta Wago da kanta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login