Showing 63001 words to 66000 words out of 260999 words

Chapter 22 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

muka haWu anan, Ubangiji Allah Ya haWamu A gidan aljanna alfarmar Annabi muhammad SAW, kusan atare suka haWu wurin furta kalmar SAW

 Yakamata mu fara yiwa annabi Salati Abie ne yai maganar, tare suka Waga hannuwansu bayan sunyi salati ya ci gaba da jero masu addu o i Suna amsawa da ameen ameen Bayan ya kammala, Uncle Wan Iya ya wurga idon shi kan Aneelerh da ke ta faman sakin murmushi tana no?e kai
Jin Muryarshi tasa ta Wago da ido tana kallon shi
Da?uwa ya sakar mata Ungo nan, jira ki ke sai mun ce ki je ki gaishe da surukan naki? yarinya sai ka ce jinin fulani Tsuntsirewa su ka yi da dariya gaba Wayansu, Yadda yai magana yai matu?ar basu dariya hada Aneelerh, Da sauri ta mi?e daga saman sofa ta nufi Hajiya adama daga ?asa saman carpet ta zauna gefen ?afar Hajiya adama, muryarta ?asa ?asa ta furta Sannunku da zuwa, Ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can Waura hannu hajiya adama tayi saman kafaWar Aneelerh

 Lafiyalou daughter in-law Fatan na same ki Lafiya
Aneelerh ta amsa da lafiyalou, kafin ta matsa gefen uncle abdallah Ta gaishe da shi, da fara a ya amsa mata

Bayan sun gama gaisawa da aneelerh, Zahra ta gaishe dasu, suka amsa mata
Kafin daga bisani, Mami tace bismilla mu shiga ciki, Ku huta kada mu Cika ku da surutu,  ta faWi hakan ne don tasan yanayi na matafiya yafi bu?atar hutu, Mi?ewa su ka yi Mami da Abie na agaba Hajiya adama da uncle abdallah suna abiye dasu, wuce abie yai da uncle abdallah zuwa Wakinsa, Itama mami ta wuce nata Wakin tare da hajiya adama bayan tafiyar su.

Fira ta 6arke tsakanin Zahra da Ummi, a lokacin Uncle Wan Iya ya fita waje domin amsa kiran da akayi mashi a waya

 Wlh ummi takalman ?afarta kalar na saratu obinna ne, kinsan ko kuWinsu yakai dubu talatin ?an zaro ido Ummi ta yi Tab Aneelerh ashe surukan ki Attajiran masu kuWi ne, ai naga sar?ar wuyanta da awarwaron hannunta duk na zanari ne, gaskiya kin taki sa a, Yarinya mai ?ashin arzi?i,

kwa6a fuska Zahra ta yi ni kuma mai ?ashin tsiya ko ? ummi na dariya tace Ni dai bance ba, kema ina maki fatan miji na gari da surukai na gari yatsina fuska ta yi ?asa ?asa da murya ta furta Suruki na gari kamar Owais, surukai na gari hamsha?an masu kuWi irin hajiya sarauta Aneelerh dake zaune saman carpet ta mi?e ta koma saman sofa ta zauna
Ummi ta kalleta nasan zasu bu?aci ganin jikansu, gashi ya tafi school till 6 na marece za a tado su saboda lesson na Islamiya da ake Yi masu,  zahra tace Zan kira mahboob A waya ya je ya Wauko shi, Ni fa dama can banso aka sanya shi hada islamiyyar ba, ace kullum sai ?arfe shidda zai dawo gida, in banda weekend,

Harara ummi ta Wan watsa mata Sannu Uwarsa, islamiyarce ke ba ki so ya yi kenan sai dai na bokon Girgiza kai zahra tayi Ba haka nake nufi ba ummi, Yaron ya yi ?aranta brain Winsa ma ?arama ce ta ya ya ki ke tunanin zai Iya Wauke duk abunda aka koya masa

Tun da suka fara magana aneelerh ta yi shiru tana kallonsu, acan ?asan zuciyarta kewar baby junaid ce ta addabeta, maganar zahra tasa duk ta ji ba daWi ita kanta ba ta son Yana kaiwa har ?arfe shidda sai dai ba yadda za ta yi ita kanta tana so yaronta ya saba da karatun boko dana addini.

Tsawon lokaci suna fira a tsakanin su jefi jefi har aka fara kiran sallah, Abie da Uncle abdallah suka fito da haramar zuwa masallaci, a harabar gidan suka yi arba da uncle Wan Iya zaune saman Kujera Yana danna waya, Abie ya ce da shi Ya tashi su je masallaci, A nan suka jira shi ya shiga gidan ya Wauro alwala kafin ya dawo suka Wunguma zuwa masallacin dake a kusa da gidansu

Acan Cikin Gidan kowa ya koma Waki domin yin sallar magrib, hankalin Aneelerh Ya?i kwanciya, Jin shiru mahboob bai dawo mata da yaronta ba, Gashi har an kira sallah. A zaune ta ke saman darduma hannayenta Biyu sama tana jera addu o i tasha dogon hijabinta.

Ba zato ba tsammani ta ji saukar mutun saman Bayanta, Ya ?an?ameta Yana ti?ar dariya babyn mommy is back Gabanta harya faWi sai da taji muryarshi tukunna ta sauke ajiyar zuciya, haWi da Wan sakin murmushi jin ya kirata da sunan da malamansu suke kiranshi wato babyn mommy, bayan ta shafa addu ar, ta zagayo da hannunta ta ru?o damtsen shi ta zagayo da shi tare da zaunar da shi saman laps Winta, Kamar kullum fuskarshi duk jirwayen hawaye, uniform Win jikin shi riga ce fara sai wando red colour, daga saman rigar akwai ?ar coat launin Ja, kafin ya ta fi school saida ta gyara mashi sumar kanshi amma yanzu da ta kalli sumar kan nashi A hargitse ta ke.
Idanuwanshi luhu luhu ya furta Mommy, kin ga banyi kuka ba yau ko? Ai kince in daina smiling softly tace jirwayen menene akan fuskarka tai maganar tana nuna hawayen da indext finger dinta, kwa6e mata fuska yai mommy ai ni bake nayi ma kuka ba, uncle mahboob ne da safe da zamu school, Ya cinye min chocolate Wina da kika saka min a basket

idanuwanshi cike tab da ?walla yai mata maganar, ranshi ya 6aci.

?aure fuska aneelerh tayi Na rasa gane me ke damun mahboob, shi bai siya maka ba sai dai ya cinye maka? Tir wlh andai ji kunya

 Mommy don t worry, Ni ma ai na rama
 Dame ka rama da mamaki ta yi mashi tambayar, hannu taga ya zura cikin aljihun wandonsa, ya zaro Wan ?aramin box mai kyan gaske Ya nuna mata
 Menene wannan ? Shu umin murmushi babyn mommy ya saki pls mommy kada ki yi min faWa, inaso yadda ya sani zubar da hawayena shima ya yi kuka, A motar shi na samu wannan, buWe ki gani abun da ke a ciki yai maganar yana mi?a mata box din, bayan ta kar6a ta buWe akwatin, haWaWWen zoben azurfa ne, na mata mai kyan gaske stone Win jikin shi har ?yal?yali Ya ke yi,
Jinjina kai aneelerh tayi Lallai Mahboob Ya iya kashe na ?an mata kuWi amma bai Iya kashe ma ?an uwan shi ba, dama irinsu babu mai cin moriyarsu sai mata, kowace mai sa ar ce wannan Ya siyama zobe kuma daga gani mai tsada ne
 Mommy daga ni sai ke, kada ki faWa mashi ni na Wauka, Mubar shi yai ta wahalar nema shima Ya ji idan akwai daWi Cikin 6acin rai ya ke yin maganar.
 Babyn mommy, ai ni farin cikinka shine nawa, don haka kar6i box Win nan ka 6oye mana shi cikin rigar pillow, kar6ar zoben junaid yai da gudu ya nufi gado ya haye tare da ru?o pillow ya zuge zip Winshi Ya tura box Win, abun mugunta ya samu sai faman sakin murmushi yake yi kamar gonar auduga

Mi?ewa ta yi daga saman sallayar, bayan ta cire hijab din jikinta ta tura a wardrobe, Baby junaid ta Wauka ta nufi toilet dashi, Wanka tayi mashi bayan sun fito ta Wauko mashi riga da wando na shadda, ta zura mashi kayan ajikin shi, ta feshe ko ina na jikin shi da turare bayan ta kammala gyara mashi sumar kansa ta Wauke sa suka nufi Palour, kafin su ?arasa sai da ta yi mashi huWuba akan ya natsu ya gaishe da kakanninsa kada ya bata kunya, ya amsa mata da toh, Lokacin da suka ?arasa palourn babu kowa duk suna a dining area sun hallara domin Cin abincin da aka shirya masu, dukkansu Ne a zazzaune saman dining chairs, zahra da Ana ke yin aikin zuba masu abinci.

Farin Ciki a wurin Hajiya adama baya misaltuwa, shima Uncle abdallah sai murmushi yake saki ganin jikan nashi, Yayi matu?ar tafiya da hankulansu, tun daga kan yadda ya zu?unna kamar wani babban mutun ya gaishe da su, Hajiya adama ta Wauke shi Tana shafa sumar kanshi tace Masha Allah, Yaro kamar rainon turai, Jawur dashi atare suka ci abinci, tana ci tana bashi abaki, Junaid an samu jikin Granny, Ya ?an?ameta yana zuba mata shagwa6a shi ala dole ga jikallen Hajiya adama da uncle abdallah.

Bayan sun kammala Cin abincin, aka fara kirayen kirayen sallar isha i, Mazan suka tashi domin zuwa masallaci.

Shigowa cikin kitchen Mahboob yai fuskarshi a Waure babu annuri, Ana dake a tsaye bakin sink tana wanke kwanukan da aka 6ata, Jin motsin mutun yasa ta waiwayo don ganin wanene, ganin mahboob ne atsaye sai ta saki fuska tana faWin mahboob sannu da dawowa ashe kaine banji motsin shigowarka ba Yamutsa fuska yai muryarsa agajiye ya furta kin ban mamaki Ana, Yanzu hada ke aka haWa baki wurin yin almubazzaranci? Sai ka ce gidan Obinna abinci har kala Biyar? Ina laifin ko shinkafa da wake ne adafa masu In yaso sai a yayyanka masu kayan lambu asama ranshi a matu?ar 6ace yake yin maganar, Fuskar Ana da alamun ruWu take kallon shi
 Mahboob me kake nufi ? Hura mata hanci yai magana nake akan almubazzarancin girka abinci da ku ka yi saboda surukan Aneelerh dafe kai tai da hannu Waya

 Pls mahboob ka daina magana kada wani daga Cikin su Ya faWo kitchen Win ba tare da sanin mu ba, bansan meke damunka ba, menene damuwarka idan an girka masu abinci kala Biyar? Ko sisin ka babu acikin kuWin girkin harara ya wurga mata tamkar ?wayar idon zata faWo kasa, rai a6ace ya ce Abar zancen, Zuba min abinci yunwa nake ji

girgiza kai Ana ta yi kafin ta nufi dish rack ta Wauko plate ta zubo mashi dambun shimkafa, Ta mi?a mashi, Matsiyacan kallo yabita da shi

 Shi kaWai aka girka? da mamaki akan fuskarta tace yanzu ka gama zazzaga min masifar almubazzaranci na girka abinci Kala Biyar, yanzu kuma ka ke tambayata shi kaWai aka girka? Dalla ni kar6i plate if not shima zaka rasa ne

fuskarta a Waure ta yi mashi maganar, hakan ba ?aramin kayar mashi da gaba yayi ba, sassauta muryarshi yai nifa wasa nake yi maki, dan Allah ki zuba min komai da aka girka yunwa nake ji, idan na gama cin abincin akwai wata kyauta da zanyi maki magiya ya dinga yi mata da?yar ya samu Ana ta zuba mashi abinci kala Biyar ta Waura masa saman dinner table na kitchen Yana ci yana santi, Musamman da ya zo kan Farfesun ganda, duk ya bi ya susuce hada siWar hannu kamar Wan maro?i.

Bayan kammala sallar isha i tun akan hanyar dawowa daga masallaci Uncle abdallah yace da abie Yana so zasu wuce idan sun koma, abie yace ba zai yiwu ba, dama ba kwana zasuyi ba? uncle Wan Iya da ke atare da su Yace Yaya ka ?yale shi, sai mu ga ta ?ofar da zai fita, Dama Hajiyar shi na cikin gidan dole shima Ya shiga, Haba Abdallah yanzu ku kwaso uwargajiya sannan ka ce zaku tafi? A wani masauki zaku sauka ne da yafi namu? Uncle abdallah yace A hotel ne zamu sauka ya 6oye masu cewa sunyi gida a abuja, Uncle Wan Iya na jin haka yace ai da kuWin hotel Win da zaka bayar ?wara ka dun?ule su ka bani sai ku kwana a gidanmu dan na fahimci kuWin ne su ka yi maka yawa dariya suka saki gaba Wayansu suna tafiya suna Yin fira gwanin ban sha awa, Bayan komawarsu gidan uncle adallah da abie suka nufi Waki atare.

Hajiya adama na akwance saman gadonta, Har ta canza kayan jikinta daga Lace zuwa Rigar bacci, da har ta yi shirin tafiya tana jiran uncle abdallah ya dawo su tafi, sai ga mami ta shigo Wakin, ganin tana shirye shiryen tafiya yasa ta ce da ita ina zuwa tace ae zasu sauka a hotel ne, girgiza kai mami ta yi ki ma daina faWin hakan don ba zai yiwu ba, ga gida kuma sai ku ce zaku kwana a hotel? Hajiya adama tace bamu son mu Waura maku nauyi ne, mami tace babu wani nauyi wlh, idan ma kina tunanin ko dan saboda gidan ?aninsa ne, to ki kwantar da hankalin ki, gidansu ne su biyu, kusan ma rabi da kwata na abunda aka kashe a ginin da kuWin abie ne, Allah ne bai nufa zamu dawo nan Win ba, sai daga Baya da ya samu ?arin matsayi awurin aiki kin ji yadda akai muke zaune agidan, na faWa maki ne don ki kwantar da hankalin ki, idan da kara ae gidan surukai gidan ?an uwana ne tun da anzama Waya, Ga Wan jikanmu junaid ya ?ara mana dan?on zumunci

maganar Mami ce tasa hajiya adama fasa shirin tafiyar, mami bata jima da fita daga Wakin ba Kiran uncle abdallah Ya shigo wayarta, ko da ta Waga kiran sanar da ita yai game da fasa tafiyar su sai zuwa gobe, hankalin ta ya ?ara kwanciya, ba tare da 6ata lokaci ba ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, tana shirin kwanciya, muryar Aneelerh daga waje ta katse ta, sallama tayi mata, hajiya adama ta amsa mata da wa alaikum salam, Suruka ta gari shigo ciki mana

cikin Jin kunya Aneelerh ta turo ?ofar Wakin hannunta Wauke da baby junaid, saukowa yai daga jikinta da gudu ya nufi hajiya adama tana dariya ta Wauke shi kafin ta zauna gefen gadon tana shafa sumar kanshi, ganin Aneelerh na ?o?arin zama daga ?asa yasa ta katse ta da cewa ki Zaune gefe na, Muyi fira komawa gefen gadon aneelerh tayi
 Mommy barka da dare, Ya gajiyar tafiya ?

Hajiya adama tace ai Gajiya tabi jiki tun da na ga jikana shiru suka Wanyi kafin Hajiya adama ta ce Ya ha?urin rashin da mu ka yi ? Du?ar da kai Aneelerh ta Wanyi, a duk lokacin da aka yi mata maganar 6acewar su tajudden tamkar an fama mata mikin dake acikin zuciyarta ne, nan take hawaye suka cika idonta, Muryarta na Wan uwa ta furta Ha?uri an gode Allah, muna ta binsu da addu a,
 Ko akwai wani abu da ku ke shiryawa ne game da 6acewarsu ? Jinjina kai Aneelerh tayi Eh mommy, dama na jira ne sai kun huta mu yi magana..... gaba Waya Aneelerh ta kwashe komai dangane da tada zancen 6acewar su Uzair ta labarta mata, annurin da ta gani akan fuskar Hajiya adama ne Ya tabbatar mata da zata samu goyon bayanta,
 Kunyi tunani mai kyau surukata, Naji daWin shawarar da zahra ta baki, Yarinyar tana da hankali, duk cikinmu babu wanda yai tunanin tada zancen, idan har akaci nasara silar shawarar da ta bada, Na yi mata al?awarin kyauta ta musamman Ba ?aramin daWi Aneelerh ta ji ba, Mommy adama ta Waura da cewa In sha Allah zamuyi magana dashi abdallahn dangane da tada zancen, sannan zamu bada tamu gudummuwar, fatana Allah ya dafa mana, Ya dube mu da idon Rahma, Ya bayyanar mana da su idan suna a raye, ko da basa a raye da bu?atar muji meya faru da su ! Cikin girmamawa aneeleeh tace In sha Allah zamuyi nasara mommy, saboda bana son in rasa surukai na gari irin ku Sam batasan Ta furta hakan ba, Dariya Hajiya adama ta yi Nima ai bana so na rasa suruka ta gari irin ki Aneelerh, domin kuwa zai yi wuya asamu tamkar ki, cikin jin kunya aneelerh ta mi?e tana faWin Bari na kawo maki abun sha bata jira amsarta ba, ta yi saurin Juyawa ta fuce daga Wakin, Bayan fitarta Hajiya adama ta dubi Baby junaid dake kwance saman ?irjinta, Ya tsareta da ido, tun da suka fara magana bai tanka masu ba, ya kasa kunne yana sauraronsu, sai yanzu ya samu damar yi mata magana

 Granny kinsan Angel jinjina mashi kai tayi nasanta mana, Inason Angel sosai marairaice mata fuska yai tamkar zaiyi kuka baiwar Allah Angela Wina, Mommy ta faWa min da ita da daddynta da daddyna sun 6ace, ni tsorona ma kada ace 6era ne ya cinye su ba.... Zaro ido Hajiya adama tayi can kuma sai ta tuntsire da dariya
 Granny, mommyna kusan kullum sai ta yi kuka saboda su angel, ?ar baiwar Allah, mami ta hanata Yin kuka amma bata Jin maganarta, sai da nayi mata faWa, na nuna mata raina ya 6aci tukunna ta daina sosai hajiya adama ke yin dariya, Sambatu iri iri junaid ke yi mata ba ?aramin nishaWi ya ke sanyata ba,
 Gobe akwai school junaid, mu kwanta mu yi bacci ma?e mata kafaWa yai Ina tsaraba na ?
 Nayi maka amma sai gobe zan baka, nafi so ka huta yanzu muyi bacci amsa mata yai da toh mu jira mommy ta kawo mana abun sha ko? in mun sha sai mu kwanta,
Turo ?ofar Wakin Aneelerh tayi hannunta Wauke da cup of coffee asaman table ta ajiye mata shi, Godiya hajiya adama tayi mata, daga nan su ka yi sallama da junansu Aneelerh ta fuce,
Atare da junaid suka sha coffee Win Bayan sun kammala, Hajiya adama Ta kwantar dashi ta tottofe shi da addu a, sauka tai daga saman gadon ta nufi switch ta kashe hasken Wakin, kafin ta dawo ta hau gadon ta rungume jikallanta a?irji, ahaka bacci ya Wauke su

****JOS CITY MUN WAYI GARI LAFIYA AGIDAN ALHAJI UBAID*******

zazzaune suke a saman dining suna Yin breakfast A tsanake shiru baka jin sautin komai saina cokulansu, kwas


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login