Showing 189001 words to 192000 words out of 260999 words

Chapter 64 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

sparkling chandeliers, ga Banquet chairs da aka tanada domin baki su zauna, kowani table saman shi an Waura bouquet of flowers, tare da Crystal glasses and silverware, da sauransu, floor din hall din kuwa an shimfiWe shi da ?ayataccen red carpet, daga can gaban hall din Gingirimeman Cake stand ne an ?awata shi sosai, Mawa?a da makaWa hada maro?a sun hallara, domin suma su kwashi rabonsu, an shirya kayan abinci saman zungureran table kala daban daban, sai mutun Ya za6a ya darje, duk haWuwar taron nan mutun Wayane bai hallaraba, Hakan ba ?aramin ta6a zuciyar obie yai na, Yaci buri akan zuwanshi amma shiru babu shi babu alamarshi, mutane sai tambayar shi suke Yi, ya akai basu ganshi ba? Iyayenshi sun rasa amsar dazasu basu, sai dai suka dinga cewa bai kaiga zuwa ?asar ba, farin jini gare shi shiyasa duk wanda yazo sai ya tambayi ina owais Yake, Taro Yayi albarka, Anci ansha anyi kullu wash rabu hani an, Anyi harka ta arzi?i ta kece raini, daruruwan mutanan dasuka kawo mashi kyauta taban mamaki basu ?irgiwa, baba obie Ya mori lokacin shi, Yayi farin cikin dabazai Iya misalta shi ba, ?an uwa da abokanan arzi?i sun faranta mashi rai, sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, Sun taka rawar girma, sai dai muce Alhamdulillah taro Ya tashi Lafiya, gab da magrib ba?i suka ragu waWanda suka rage ?an uwane na jini, da kuma mutanan Hateem.



*WAIWAYE ADON TAFIYA=ث?*



(Abunda ya faru bayan zahra ta faWa ma Aneelerh halin da take aciki, Na kuWi da hajiya falmata take binta bashi, bayan ta koma Waki damuwa ta isheta, tayi ?arfin haline kawai wurin bata shawara akan ta amince da bu?atar hajiya falmata saboda tana son ta jaraba zahra ne don taga idan tana da hankali, tunani ta soma yi ta wace hanya zata Iya taimakonta? Nan take zuciyarta ta bata shawarar tayi amfani da sauran kuWin nan da jami an sirri suka bata, har yau bata ?arar dasu ba, tamkar tana jin tsoron ta6a su, tun dai data siya ma baby junaid kayan wasa bata ?ara cirar ko naira biyar ba.

Ba tare da sanin kowa ba Aneelerh ta tuntu6i mahboob, a Wakin shi ta same shi, ta tambaye shi koya san gidan hajiya falmata mahaifiyar ?awar zahra? Yace mata eh yasan gidan, sun ta6a zuwa tare da zahran ma, tace toh so nake ka rakani gidan, da mamaki akan fuskarshi yace amma me zakiyi acan din kinsan ta ne? girgiza mashi kai tay alamar a a, kawai inaso ka rakani muje, idan mun fita zan faWa maka komai, amma kafin muje gidan zaka fara rakani banki, akwai wasu kuWi da nakeson in cira, Jin ta ambaci kuWi yasa mahboob saurin amincewa zai kaita gidan, a cikin motarshi ya dauki aneeleeh saida suka fara biyawa banki ta ciri kuWin kafin suka nufi gidan hajiya falmata.

Lokacin da suka karasa gidan, A parking space mahboob Ya tsayar da motar, Aneelerh tace dashi ya jirata anan, ya amsa mata da toh, da sallama abakinta ta shiga palourn gidan, adai dai lokacin mai aikin gidan ta fito daga kitchen ta yi arba da aneelerh, fuskarta da fara a suka gaisa tace mata wurin hajiya falmata tazo, Allah yasa tana nan, Mai aikin tace bata jima da dawowa daga office ba, ki zauna bari naje in sanar da ita, da sauri mai aikin taje ta fado mata, jim kadan ta dawo ta sanar da aneelerh sakon hajiya tace ta jirata gata nan zuwa, aneelerh ta amsa mata da toh, kusan mintuna biyar Aneelerh tana a tsaye ta ru?e qugu tana jiran fitowarta, cikin jin fargabar ganin matar, sai faman bin palourn take yi da kallo.

Sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin Aneeleerh ga kallonta, A hankali take saukowa down stair, ta Wauki wankan tsadaddan leshi, kanta yasha Waurin Wan kwali, ta manna farin glass a idonta, Babbar macace tana da jiki, tana tafiya tsokokin jikinta na motsawa, Fatar jikinta tasha hutu har ta gaji, daga ganin fuskarta masifaffiyace, idanuwanta mitsi mitsi da su kamar na mutanan Yankin china, hancinta kuwa abaje yake, ga big mouth dinta yasha man baki.

Ta6e baki Aneeleerh tayi aranta ta furta jibarta dan Allah, ?atuwar banza da ita kamar buhun masara, a haka take lalata rayuwar matasan ?an mata, Allah dai ya shirya, wasu mutanan sunyi asarar rayuwarsu.

Lokacin da hajiya falmata ta ?arasa saukowa daga saman benan, idanuwanta suka Yi mata tozali da kyakkyawar fuskar Aneelerh nan take taji ta burgeta, tayi mamakin ganin ba?uwar fuska agidanta, bakomai yafi tafiya da imaninta ba face Kyawun surar Aneelerh.

Ganin Yadda Ta tsareta da idone Yasa Aneelerh tayi saurin gyara mayafinta ta rurrufe jikinta, Aranta ta furta A uzubillahi minasshaidanirrajin, Aniyarki ta biki ba?ar mayya
Saman sofa din dake fuskantar Aneelerh Hajiya ta zauna, tana dubanta da wani irin mayataccen kallo.

Yamutsa fuska Aneelerh tayi fuskarta ba wasa tace barka da Yamma
Hajiya falmata ta amsa mata da barka dai, bismillah ki zauna mana

?aure fuska Aneela tayi bana zama agidan da ake aikata sa6on Allah, saboda ni tsarkakakkiya ce, bai kamata in goga ma jikina najasa ba !! Mamakine Ya kama hajiya falmata, a hankali ta sauke glass din dake saman fuskarta don ta samu damar ?arewa Aneelerh kallo.

 Bansan wacece ke ba, sai dai na fahimci haukan talauci ne ke damunki shiyasa kika kwaso ?afa kika zo gidana don in taimaka maki

Dariyar rainin wayau Aneelarh Tayi kafin tace ki kalleni daga ?asa har sama, kema kinsan nafi ?arfin ki kira ni da talauci, Ni banzo don nayi cece kuce dake ba saboda bani da lokacinki, Maganar kudin zahra da kike bin ta bashi ne
Shu umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar Hajiya falmata da sha?iyanci ta furta oh, kinzo ne ki fanshe ta, shiyasa kika kawo min kanki? Donni banga alamun zaki Iya biyan kuWin ba
Girgiza kai Aneelerh tayi ranta a6ace tace wato shi dai jaki duk yadda akai dashi sai yaci kara, idan kina tunanin na kawo maki kaina ne don in fanshi zarah to ki daina, domin kuwa nafi ?arfin ?as?antacciyar mace ballagaza jahila kuma da?i?iya irinki, Mace mara tsoron Allah, me yin amfani da dukiyarta don lalata rayuwar matasan ?an mata masu neman nakansu, Wlh kinji haushin rayuwar...... gigitacciyar tsawa Hajiya falmata ta daka ma Aneelerh, tamkar damusa ta yun?ura ta mi?e tsaye tana duban Aneelerh da mummunar fuskarta babu annuri ko mis?ala zarratin ta nuna mata Hanyar fita da yatsan hannunta Ke Fuce kibar min gidana, tunkafin ranki Ya 6aci, matsiyaciyar banza masu ?ashin tsiya

Aneelerh da ?arfin Hali tace idan kinga na fita gidan nan to nagama faWin ta cikina ne, Kuma wallahi koda gigin wasa kika ce zaki ta6a lafiyar jikina saina na?asa ki bakisan wacece Ni ba ta faWa tana jefa mata harara, lamarin Ya Waurewa Hajiya falmata kai, ganin karfin hali na Yarinyar nan data zo gidanta tana Yi mata rashin Kunya.
Goya hannayenta tayi saman ?irjinta ina sauraronki, Me ya kawo ki gidana!
GyaWa Kai Aneelerh Tayi zuwa nayi don Inyi maki nasiha, don na fahimci Wadda iyayenki suka yi maki tuni shaiWan Ya hure maki kunne, dan Allah Jibarki cikin shiga ta mutunci kamar wata mutuniyar arzi?i, al halin nan kuwa fuska biyuce ke, A fili musa a zuciya fir auna, Haba baiwar Allah, Da hankalinki da tunaninki da shekarunki kika za6i ki sa6awa Allah don kawai ki ji daWin duniya? Kin manta da Allah yana ganinki kuma zaki mutu ki koma gareshi, a ko wani yanayi mutuwa tana iya riskarki, idan ta?amarki kuWine ki tuna Allah ne Ya baki Arzi?in bake kikayi ma kanki ba, Idan yaso zai Iya ?wace wa, kuWi da kike gani wallahi masifane Idan baka tafiyar dasu ta hanyar da ta dace ba, Ita kuma rayuwar duniya jin daWinta ?alilan nan bata da tabbas, bakisan yaushe zaki mutu ba, kin sanya mugunta aranki saboda Allah Ya azurtaki, Kina cutar matasan ?an mata, waWanda Iyayen su suka sha wahalar basu tarbiya ke kuma kina gur6ata masu rayuwarsu, Allah kaWai yasan adadin ?an matan da kika 6ata, kin goga masu jarabar da bazasu Iya gogeta ba, Kin cutar da rayuwarsu mutane suna kuka da su saboda sun addabi rayuwar al umma kuma ire-iren ku ne ku ka yi silar lalacewarsu, wallahi kiji tsoron Allah kamar yarda ba zaki so ayi da ?ar ki ba to kema kada Kiyi da Wan wani, duk da naji irinku Harda ?a ?an naku kuke Yi, saboda shafewar basira da neman duniya kun makance bakwaji bakwa gani ku ala dole saikun siyama kanku tikitin shiga wuta ? Tun da Aneelerh ta soma Yi mata magana da faWa haWi da tsiwa take ta faman zare ido tana binta da kallo, tun da take arayuwarta wani Wan adam bai ta6a gigin tunkararta Ya faWa mata magana game da abunda Take aikatawa ba sai Yau da Allah Ya haWa ta da Auntyn Zahra mai dimple, Ayoyin kur ani aneelerh ta soma karanto mata tana fassara mata, kamar an rufe mata baki takasa dakatar da ita duk irin masifar da take da ita yau an kashe mata bakinta??
 Allah Yana son bayinshi waWanda suka aikata 6arna suka tu6a saboda tsoronshi suka koma gareshi, dan Haka ina baki shawarar tunkafin lokaci Ya qure maki Hajiya falmata ki Gyara Halayanki, Ni bance zan sanyaki ki shiryu ba don nasan irinku taurin kaine daku kamar kwakwa, ko malamai sunyi maku nasiha bakwaji bakwa gani sai ranar da Allah Ya dam?e ku tukunna zaku gane kurenku, Ni in banda ma shafewar basira, wai ku bakwa tuna mutuwa da kwanciyar ?abari ne? Baku tuna duk abunda kuka mallaka zai ?are, daga kai sai halinka za a binne ka a ?abarin ka fa? Ke yanzu kin za6i ki mutu kina aikata mummunan zunubi na bin ?an uwanki mata? Ga hakkin Iyayen da kika sanyasu zubar da hawayensu ta silar lalata masu rayuwar ?a ?a da ki ka yi ga kuma Matasan ?an matan da kika gur6ata ma rayuwa, wannan fa zunubine mai cigaba da yaWuwa ko bayan kin mutu zaki cigaba da samun kamasho acikin shi, saboda kinbar tarin ?an matan da kika gur6ata agari suna aikata fasadi, wallahi kiji tsoron Allah tunkafin lokaci Ya qure maki, Ina ?ara jan hankalinki ki tuba ki koma ga Allah tunkan mutuwa ta ris?e ki don ita bata kwankwasama mutun ?ofa balle Yace zai shirya mata

Wata irin zuface ta soma wanke goshin Hajiya falmata, Ha?i?a kalaman Aneelerh sun fara karya mata zuciya, sai faman zare ido take Yi, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin maganar Aneeleerh ba, Yarinyar tayi matu?ar burgeta kuma ta bata mamaki da har ta iya yi mata nasiha batare da jin shakkarta ba, saboda mutane dayawa basa Iya yin magana agabanta, amma Ita wannan ido cikin ido take furta mata magana .

 hajiya falmata, duk runtsi duk wuya kada ki Karya zuciyar wanda Ya aminta dake! Ina magana akan zahra da ta dauke ki tamkar mahaifiyarta saboda ?aunar dake a tsakaninta da ?arki fatima, Kin karya mata zuciya, naji daci lokacin da na sameta ta kulle kanta acikin toilet tana Yin kuka babu ci babu sha ita kaWai batare da kowa ya sani ba, Kin hanata runtsawa saboda ta?i baki haWin kai ku aikata sa6on Allah, haba baiwar Allah, idan kece akayima yarki haka zakiji daWi! Don kawai mutun Na bu?atar agazawarka sai kayi anfani da dukiyarka donka cutar dashi? Babu wanda yafi ?arfin ya nemi taimako a duniyar nan, koda ba a wurin mutun Wan uwansa ba, zai nema awurin Allah Idan har baka agazama bawansa ba tayaya kake tunanin zai agaza maka?

Jinjina kai Aneelerh tayi, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskarta cikin muryar kuka taci gaba da cewa Kin ?ona mata rai, zahra ta yarda dake fiye da tsammaninki, tana kuka tana fadamin yadda ta aminta dake amma kika karya mata zuciya, Zahra da kike gani tafi ki Hankali, Yarinyar tana da tawakkali, tana jin tsoron Allah, Na jarabata don inga ko tana da wayon jure ?addara idan ta sameta, Ni dakaina nabata shawarar ta baki haWin kai, da buWar bakinta sai ce mun tayi ita ko duniya za a mallaka mata bazata ta6a amincewa ta sa6ama Allah ba, saboda tana jin tsoron shi kuma tana jin tsoron ranar da zata koma gare shi, Hajiya falmata kin ta6a tunanin hakan? A matsayinki na babbar mace wadda ta haura shekara arba in da Wuriya a duniya? Shekaru sunja amma baki tsoron mahaliccin ki? Kina amfani da dukiyarki wurin Gur6ata duniyarki da lahirarki, maimakon kiyi amfani da su wurin taimakon bayin Allah marasa ?arfi wadanda zasuyi alfahari dake ko bayan ba ranki kuma ki samu lada awurin Allah, Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar da kika daukarwa kanki !?

?afafuwanta ne suka gaza ru?eta, Jiri Ta soma gani a cikin idanuwanta, adaddafe ta nufi sofa ta zauna tana faman fitar da numfashi.

HankaWe KafaWa Aneeleerh Tayi Alhamdulillah nagama faWar ta cikina, duk wanda yayi da kyau don kanshi, akwai mutuwa akwai hisabi, maganar kuWi Kuma nazo maki da su miliyan Uku Cuf, Idan ma kina son ?ari zan ?ara maki, saboda inaso kisan muba jinin fa?irai bane idan arzi?ine muma mun gaje shi gaba da Baya

?aga murya Aneelerh Tayi da ?arfi ta furta sunan Mahboob, shigowa Wakin Yayi hannun shi ru?e da jaka ba?a, tunkan ya ?arasa yake bin ko ina da kallo, ganin haWuwar falon gidan aranshi Ya ayyana Lallai hajiyar nan ta tara shiyasa take tsula tsiyarta son ranta saboda tana da arzi?i.

 Zoka ajiye mata tsiyarta, Aneelerh ta faWa tana nuna mashi gaban Hajiya falmata, Ta zabga uban tagumi da hannu biyu, da alamun nadama atattare da ita.

Koda mahboob Yayi arba da fuskarta saida yasha jinin jikin shi ganin yadda ta haWe rai, ga gumi na fita a goshinta.

Kamar mai jin tsoronta Haka Ya ajiye mata jakar agabanta.

Aneelerh ta ru?o hannun shi acikin nata, har sun Waga ?afa zasu bar falon muryar Hajiya falmata ta dakatar da su
 Dan Allah Ku tsaya !! Kusan atare zuciyarsu ta buga, a sukwane suka waiwayo suna dubanta, Gabansu ba ?aramin faWuwa yayi ba ganin ta fashe da kuka, mi?ewa tayi daga saman sofa din ta nufe su tana fadin wallahi nayi nadama, dan Allah kuyi ha?uri da abun kunyar dana aikata, Nima ba halina bane ?awayene suka tunzurani har na faWa harkar zubewa tayi saman gwiwowinta agaban aneelerh tana kuka tace Tun da nake a rayuwata wani Wan adam bai ta6a yi mini nasihar data ratsa zuciyata ba sai akanki, bansan wacece ke ba, amma nayi sha awar In yi koyi da kyawawan halayanki, duk naji na tsani kaina, na zubda mutuncina da girmana a idon zahra, wallahi naji kunyar da ban ta6a jin taba, Naji ?uncin Halin dana jefa zahra, saboda ni tagaza runtsawa Na hana baiwar Allah yin bacci na hanata cin abinci, na jefa rayuwarta cikin ?unci batare da nayi tunanin raWaWin da zataji acikin Zuciyarta ba, wallahi nayi nadama koda ace bazaku yarda dani ba, Na tuba kuma in sha Allah bazan ?ara aikata zunubin nan ba, angama bi iznilillahi, saboda inaso Inyi kyakkyawan ?arshe kuma inaso in tsira ranar gobe ?iyama, In sha Allah daga yanzu nagama yin amfani da dukiyata don in sa6awa Allah, da kuma gur6ata tarbiyar ya yan mutane..... da?yar ta ?are maganar tana faman jan magina.

Ba Aneelerh ba hatta Mahboob Yayi mamakin wannan Ikon Allahn, sun yi sototo suna kallonta kamar sakarkaru duk ta zama abun tausayi tsoron Allah ya shigeta, wata ?il dama itace silar shiriyarta shiyasa Allah Ya haWasu da ita.

Muryar Hajiya falmata na rawa tace Ku taimaka mun dan Allah, inason in wanke kaina awurin zahra, saboda inason taci gaba da kallona kamar yarda tasanni ada, Nayi al?awarin zan taimakamata, kuWin da ku ka zo dasu na yafe mata ku Wauka ku maida mata su, Sannan inaso taci gaba da yin aiki a company dina, Kayan da suke son ayi masu order A dubai gobe in sha Allah zasu iso Nigeria

Kallon juna mahboob da Aneelerh suka ?ara Yi, Atare suka furta Alhamdulillah, Aneelerh tace nagode ma Allah daya bani baiwar Iya tsara kalamin da har suka ja hankalinki, Naji daWi dana zama silar shiriyarki, Ina fata zaki canza rayuwarki daga Yau ki koma ta gari, wadda kowa zaiyi alfahari da ita

Jinjina kai Hajiya falmata tayi Cikin sanyin murya tace in sha Allah, ru?o hannayenta aneelerh tayi acikin nata, mi?ewa tayi tsaye suna fuskantar juna
 Ki godema Allah, saboda Yana son ki da shiriya shiyasa Ya baki damar gyara rayuwarki tun da sauran numfashinki,

Jinina Kai Hajiya falmata tayi.
Aneeleerh ta ?ara da cewa sai dai kiyi ha?uri, ba zamu maida kuWinba, nariga dana kawo maki dasu, Ki ru?e su a hannunki, zahra kuma bazata ?ara Yin aiki a companynku ba, zan nema mata aiki awani wurin !!

Magiya hajiya falmata tadinga yi mata akan tayi ha?uri su koma da kuWin, ta yafe masu, amma Aneelerh ta?i yarda, mahboob ne yace ta jira zasu yanke shawara a tsakaninsu, ru?o hannun Aneelerh yai acikin nashi yajata zuwa gefe Waya akwai tazara tsakaninsu da hajiya falmata, tayi kasake tana kallonsu
 Aunty aneelerh tunda tace ta yafe kuWin mu koma dasu kawai, ai ba ro?onta mukayi ba
Girgiza kai aneelerh tayi nidai hankalina bai kwanta da matar ba, wallahi irinsu shaiWanune Mahboob, inajin tsoron ace wani tuggun zata kitsa mana shiyasa tace ta yafe kuWin, ?wara mu maida mata aniyarta
Yamutsa fuska mahboob yai aunty aneelerh just ki gane, ni dai na yarda da ita, sau dayawa zaki ga mutun yana aikata ba daidai ba idan Allah yaso shi da rahama saiki ga ya shiryu cikin sau?i batare da ansha wahala ba, Yanzu ki duba matar can, hada fa kukanta kuma har zu?unnawa tayi saman gwiwowinta tana ro?onmu, why bazamu yafe mata ba? Komai ya wuce, ita kanta zahran


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login