Showing 204001 words to 207000 words out of 260999 words

Chapter 69 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

a a baiyi min komai ba, dan Allah ka taimaka mashi, nasan kai kaWaine zaka Iya fahimtana,

Jinjina kanshi yaWanyi okey, Ki kwantar da hankalin ki, kidaina kuka bana son ganinki cikin damuwa
Fuska amarairaice tace dole in damu boss man, rayuwar Wan uwana abun tausayice, bazasu ta6a ?yale shi ba, tun yana jariri suke cutar dashi har izuwa girmanshi sun?i su ?yale bawan Allahn nan, mugaye in sha Allah bazasu ta6a yin nasara akanshi ba
Idanuwanshi tuni sun cicciko tab da ?walla
 Dan Allah ka taimaka mashi, akwai ruwan zamzam da ake bashi na addu a ina da tabbacin idan yasha zai dawo dai dai
Cikin sanyin murya yace A ina za a same shi ?
 ?an uwanmune Ya bani address din gidan da zamu Wauko, namanta takardar acikin aljihun uniform dina, ai kace min kayan suna a hannunku, idan ka duba zaka ga wandona launin ba?i, mu uku keda kalar kayan dani da batul saina danish, pls ka bincika ka dauko ta, Allah yasa bata faWi ba, nasan ma zaiyi wuya asamu zam zam din koda an samu takardar adreshin
 In sha Allah za a nemo zam zam din, ki koma ki zauna amma pls kada ki bari ya cutar min dake amsa mashi tayi da toh ajiyar zuciya ya sauke, tamkar karya tafi yabarta haka yake ji, duk da Ya yarda Yaron bazai Iya cutar da ita ba, tunda gashi ya same su asaman gado Waya batare daya sare ta ba, shi tausayin yaron ma yake Ji.

Juyawa yai da sauri Ya nufi down stair.
Komawa tayi saman gadon ta haye, ta kwanta daga gefenshi taci gaba da yi mashi karatun qur ani.

Da matsakaicin gudu motar chief ta ?araso bakin entry hall na shiga babban falon gidan baba Obie, dasauri jami en Ya fito daga motar Ya zagaya other side Ya buWe mashi murfin car din, Ya zuro kafarshi Ya nufi Cikin gidan da sauri, Kamar yadda yabarsu haka ya same su a tsaitsaye cirko cirko , damuwace ?arara akan fuskokinsu, hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba idan har ba gawar macijin suka gani ba.

 Owais ! Obie ne ya ambaci sunan shi da mamaki akan fuskarshi.
Dagowa yai da kyawawan idanuwanshi ya daurasu akan faces dinsu, kamar yadda yake kallonsu haka suma suke binshi da kallo, Kamar yaune rana ta farko da suka fara ganin juna
 Owais Ina macijin ? hateem ne ya jefa mashi tambayar.
Calmly ya furta mun fitar dashi daga gidan ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Senate lateef Yace Wacece yarinyar dake atare dashi? Munji tana kuka tana fadin Wan uwanta ba maciji bane shin dagaske ne !
Jinjina kanshi yai alamar eh, ya ?ara da cewa ?ar uwarshi ce, ba maciji bane mutunne kamar kowa, ?addara ce ta afka mashi
 Wai kana nufin Wan mutunne ya rikiWa ya koma maciji ? His excellency deen ne Ya jefa mashi tambayar, gaba dayansu sun ruWe da jin maganar,
Abdul razak Yace bazai yiwu ba, owais kodai ka fara shaye shaye ne? In bahaka ba ta ina mutun zai Iya komawa dabba kamar maciji? Ai sai dai idan ya kasance ba mutun bane shi
Obie duk Yafi su firgita jikinshi ya?i daina yin kerma
 Owais bana son ganin macijin nan, ku tabbatar kun fitar dashi daga gidan nan, Idan ba haka ba zai Iya cutar da rayuwar ahalina
 Baba ka kwantar da hankalinka, zuwa gobe in sha Allah zan shigo muyi magana, nasan yanzu ko nayi maku bayani ba lallaibane ku fahimceni ba, ni kaina hankalina ba a kwance yake ba
Girgiza kai obie yai owais idan kaga na kwantar da hankalina to macijin nan baya acikin gidan nan, Ni ban ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, wai yaushema ka dawo kasar? Ita yarinyar dake tare da macijin ?ar wacece? A ina take zaune ?
Shiru yai yana duban face dinshi, sam bayason yawan surutu, abu kadan ke hasala shi, baisan amsar da zai basu ba, don ya fahimci hankulansu ba akwance suke ba.
Gyaran murya mai girma sharafudden Yai, hankalin owais ya dawo kan mahaifinshi kada ka damu, ka koma bakin aikin ka My son, Ni na fahimce ka, kaje kawai zuwa gobe zamu nemaka donka zo ka warware mana rudanin da muke aciki lumshe ido owais yai ha?ika yaji dadin maganar mahaifinshi, dama yasan shi kadaine zai Iya fahimtar halin da yake aciki
Kafin Ya juya saida ya fara kallon Obie, wanda tuni idanuwanshi sun kaWa jawur, tausayin tsohon ne Ya kama shi, yayi matu?ar yin kewar kakanshi.
Matsawa yai kusa dashi Ya rungume shi saman faffadan ?irjinshi, baba Obie Ya kankame owais tamkar zasu koma mutun Waya.
Cikin sigar lallashi yake yi mashi magana nayi kewarka baba, kana araina, nasan ban kyauta maka ba, amma in sha Allah idan komai Ya lafa zuwa gobe zan shigo gidan cikin sanyin murya obie Ya amsa mashi da toh, ji yake tamkar karya tafi yabarshi, yana matu?ar ?aunar jikannan nashi.
Iyayenshi dake kallonsu, murmushi ne saman fuskokinsu.
Raba jikinshi yai daga na baba obie, yakai hannu Ya shafi dogon gemun shi, da zolaya ya furta kakana nakaina, nifa da jarumta nasanka, kai Win Namijin duniya ne, dan Allah kada ka bani kunya, kada ganin macijin nan ya hanaka rintsawa adaren yau, kayi bacci ka huta gobe jikanka zaizo gareka, sabon cake zamu yanka atare
Farin ciki Ya cika obinna, yayin da yake duban owais, yana dariya yace ka wahalar dani, bakasan irin kewarka da nayi ba, Na ?wallafa raina akan son ganinka, ka manta dani owais, gobe idan kazo har tsallan kwaWi zan sanyaka dariya Iyayenshi suka sanya, Owais yace kowani horo zakayi min bazan musa ba, Na cancanci fiye da hakan, Ni zan tafi, ku kulamin da kakana, Make sure he sleeps peacefully tonight. ya faWa yana duban iyayenshi, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, owais ba ?aramin burgesu yake Yi ba, saboda yana son mahaifinsu.
Juyawa yai da sauri ya nufi ?ofar fita daga falon, idanuwan kowan nansu akan bayanshi, Harya Waga kafa zai fuce, muryar prime minister ta dakatar dashi
 Owais! ina son yin magana dakai a hankali Ya juya yana dubanshi, da sauri Hateem Ya nife shi, babu mai Iya jin abunda suke cewa saboda sunyi nesa da sauran mutanan.
Dafa kafadarshi yai da hannu Waya, tunkafin hateem yai magana owais ya riga shi furta uncle sai kunyi hakuri dani, ka zo kasar bansamu lokaci nazo gaishe ka ba murmushin gefen fuska yasakar mashi ni wannan ba damuwata bace, nayi maka uziri saboda nasan yanayin aikin ku, ya faWa yana dubanshi kafin yaci gaba da magana.
 Inaso ka faWamin dagaskene macijin nan mutunne ?

Jinjina kai owais yai dagaske ne mutunne ya rikida, matashin saurayi
Shiru hateem yaWanyi kafin ya kuma cewa Ya sunanshi ?

 Danish ata?aice ya bashi amsa.

 Duk da bansan abunda ke damunshi ba, amma idan har mutunne ya rikida hakan na nufin aljanune atare dashi ko ?
?aga mashi kai owais Yai haka muke tsammani
Hateem Ya numfasa kafin Yace Inason ganinshi idan yadawo suffarshi ta ainahi, sannan Yakamata a kira sheikh imam ya duba shi, ina da tabbacin zai Iya taimaka mashi
Amsa mashi yai da toh, daga haka sukayi sallama owais ya fuce daga falon.
Bayan tafiyar owais, su Hateem suka raka baba obie bedroom dinshi, babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwanta ya runtsa amma Ya?iya gani yake tamkar macijin zai faWo Wakinshi, duk yabi ya firgice, adole mutun biyu suka tayashi kwana, Sharafudden da senate lateef, sauran kowa Ya nufi masaukin shi.
Hankalin Hateem Ya?i kwanciya, Macijin Ya tsaya mashi aranshi, ya ?walla fa rai akan son ganin yaron, ko bayan daya koma Gidanshi dake a estate din, a Waki ya tarar da gimbiya mujeedat, tana faman yin zarya, ta kasa kwanciya saboda rashin dawowarshi, babu wanda yasan abunda ya faru a gidan baba obie sai wadanda ke zaune agidan.
Bai sanar da ita komai ba, Saman gadonsu Ya haye ya kwanta yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, tayi mamakin ganin damuwa atattare da mijin nata, har tambayarshi tayi meke damunshi amma sai yace mata babu komai, bacci yake ji, ?o?arin faranta mashi tayi har saida ta tabbatar ya fara yin bacci tukunna hankalinta ya kwanta.


*SIR MUBARAK
'*

Babu wanda ya motsa acikinsu, tun da suka ji muryar mutumin daya kira layin jazz, Jikin kowannansu yai sanyi la?was tamkar an zare masu laka, har sun fara danasanin jahilin bugun da sir mubarak yaiwa jazz domin kuwa sun tabbatar sune sukayi kuskuren yanke hukunci batare da sun fara bincikarshi ba.
Yarinyar dake a zaune dirshan idanuwanta sun kaWa jawur yayin da hannuwanta ke asaman fuskar jazz.

kafin Sir mubarak Yai ?wa??waran motsi, Muryoyin yaran dake tunkaro Wakin Ya karaWe kunnuwan sojojin
Kusan atare suka Wago suna kallon ba?in ?ofar shigowa Wakin.

Matasan ?an mata ne kowaccensu sanye cikin rigunan bacci, babu huluna akansu sai zallar sumar kansu mai tsayi har gadon bayansu, namiji Wayane acikinsu shima kayan baccin ne ajikinshi, fuskokinsu a yamutse sai hamma suke Yi, ga dukkan alamu kukan ?ar uwarsu ne Ya farkar dasu daga bacci.

 Meya faru da yaya jazz dinmu? Su wanene ku ? Har suna haWa baki wurin tambayar sojojin.

Cikin shesshe?ar kuka Yarinyar dake ru?e da dr. Jazz ta kware murya tana kallon ?an uwan nata tace Sun kashe mana shi, bansan su wanene su ba, kawai sun shigo mana gida sun kama bugunshi
Fashewa sukayi da kuka kamar gidan mutuwa, da gudu suka nufi inda yarinyar take a zaune, a kewaye da dr jazz suka zu?unna Suna ambaton sunanshi tamkar ransu zai fita.
Ba zato ba tsammani, sojojin suka jiyo muryar babban mutun Yana fadin meke faruwane? Su wanene suka shigo gidan ?
Fadowa cikin Wakin Yayi, daga shi sai short a jikinshi babu riga, yana da faffaWan kirji ga ?irar ?arfi kamar Wan dambe, kallon Waya zaka yi mashi ka shaida farar fatane, fatarshi jawur take daga gani bature ne.
Lokacin da yai arba da su sir mubarak a Wakin Ras yaji gabanshi yai mugun faWuwa, adabarbace ya furta su wanene ku? Meya kawo ku cikin gidan nan ? Kafin wani ya furta kalma, Mutumin ya wurga idanuwanshi akan yaran dake kuka.
Zaro idonshi waje yai ganin yadda suka raunata jazz, da ?arfi yace don ubanku ku faWamin su wanene ku? Uban me yayi maku da kukayi mashi wannan bugun? Waye ya turo ku? Babu alamun tsoro akan idanuwanshi, sai ma dun?ule hannayenshi da yai da niyar yakai masu hari,
An rasa me magana tsakanin Sir mubarak da su tiger.
Gigitacciyar tsawa ya daka masu Yana fadin bakuji ina magana ba? Idan har baku faWamin ba, daya bayan Waya zan salwantar da rayuwarku
A harzu?e tiger da Major suka zaro bindigunsu tare da saita shi, maimakon yaji tsoron bindigar hannunsu sai gani sukayi Ya sanya hannu ya daki ?irjinshi da ?arfi Yana fadin Kunyi kuskuren shigowa gidan nan, abun hannunku bai isa yasa inji tsoronku ba, tunda kuka ta6a jazz sai kunyi danasanin haihuwarku da uwarku tayi acikin duniyarnan, kawai saboda zalunci saiku faWo gidan mutane kukama bugun mutun baiyi maku laifin komai ba ? Tamkar mayunwacin zaki haka yake yi masu magana yana fitar da huci mai Wumi
Da?yar sir mubarak Ya iya sarrafa kanshi, muryarshi a haushine ya furta dan Allah ka faWamin wanene kai, Ni da kake gani mahaifin jazz ne, mun shigo gidan nan batare da sanin shi ba, saboda mu atunaninmu wani mugun abun yake aikatawa..... a tsanake sir mubarak Ya kwashe duk abunda Ya faru dangane da zargin da yake yima jazz ya sanar da matashin saurayi
Lokaci Waya sukaga ya sassauta fushin fuskarshi, ga dukkan alamu ya fahimce su.
 Amma baku kyauta mashi ba, shiyasa akace zato zunubi koda ya kasance gaskiya, jazz dai ba mugu bane, mutumin kirkine fiye da tunaninka, waWanda yaran kuma dakuka gani marayune basu da gata aduniyar nan daya wuce Allah sai kuma waWannan bayin Allahn da suka taimaki rayuwarsu yai maganar yana nuna jazz da hannunshi, Yaran dake sauraron su idanuwansu sunyi luhu luhu sunsha kuka kamar ransu zai fita don ba ?aramin ?aunar jazz suke Yi ba
Cikin karyayyar murya sir mubarak yace kana nufin Chief owais shine ke kula daku? ya tambayeshi saboda yaji muryar owais a wayar jazz yana da tabbacin shine Ya kira layinshi

Jinjina kai mutumin yai ?warai kuwa, a ?ar?ashin kulawarshi muke gaba Wayanmu, shi kuma jazz shine likatan daya dauki nauyinshi don kula da marasa lafiyan cikinsu, Yarinyar nan kuma daka ganshi atare da ita saman gado, bata da koshin lafiya, tana da ta6in hankali, ga magungunanta can saman drawer da alluran da yake yi mata, abunda yasa kuka same shi asaman kanta, ni nasan saboda babu mai iya rike mashi itane, idan dare yayi bayason tashina daga bacci, ni ne nake taimaka mashi wurin ru?eta ayi mata allura saboda buge bugen da take Yi, idan har ba a ru?eta ba baza a iya yi mata allura ba, tana da ?arfine, kunyi zargin jazz yana aikata fasi?anci da ita bahaka bane abunda na faWa maku shine gaskiyar zance
Dafe kai Sir mubarak yai da hannu Waya, Wani irin matsanancin ciwon kaine ya farmashi, su tiger sunyi danasanin zargin jazz da sukayi jikin ta?aura yayi la asar
 Dan Allah ku taimaka mashi kada ya mutu, har yanzu baidaina bleeding ba Waya daga cikin matasan yaran ce tayi maganar, fashewa sir mubarak yai da kuka tamkar ?aramin yaro, cikin rauni na murya yake fadin Inna lillahi wa inna ilaihirraji u! Jazz baka kyautamin ba, meyasa baka sanar dani ba, kabar ni inata zarginka gashi har nayi maka illah! Yanzu ya zanyi? Me zan faWama mahaifiyarshi? Matar da ko bacci bata iyayi idan har bai dawo gidaba saboda ?aunar da take yi mashi!
Juyawa yai da sauri ya nufi inda yaran suke, bai bi takansu ba, ya sanya hannayenshi biyu ya cuccu6i Jazz Ya Waura shi saman kafadarshi, ya dubi su Tiger da rinanun idanuwanshi yace major muje mu kaishi asibiti, kai kuma Tiger ka tsaya atare da army ku lallashi yaran dan Allah ya ?are maganar da sauri ya nufi ?ofar fita, Major yabi bayanshi bayan ya kar6i key din motar a hannun tiger.

Har sun kusa futa daga dakin, matashiyar nan mai fama da ta6in hankali ta fasa ?ara hadi da yunkurawa ta mike aguje tabisu tana fadin mugaye ku dawo mana da Wan uwanmu kada ku kashe shi, wayyo Allahna Yaya kana gani zasu gudu dashi  har takusa fucewa daga Wakin, Mutumin Ya dam?o damtsen hannunta, Ya rungumeta a chest dinshi yaci gaba da lallashinta.
Tiger ne ya soma lallashin ?an uwanta dake kuka
 Kuyi ha?uri, kuskure mukayi wurin bugunshi, mu ba mugaye bane kamar yadda kukayi tsammani, mutumin daya dauki jazz mahaifinshine ba wani ba, kuma asibiti zasu kaishi inda za a duba lafiyarshi, da zarar yaji sau?i za a dawo maku dashi cikin shesshe?ar kuka suka amsa mashi da toh, banda mahaukaciyar yarinyar daketa Wura masu ashar, kamar zata bugesu, mutumin ya ?ankameta ya hana ta kubce mashi.

Kusan rabin awa da tafiyar Sir mubarak, motar Big guy ta shararo da gudu cikin unguwar, tunkafin ya ?arasa bakin gate din gabanshi ya fara faWuwa ganin ?ofar gate din abude kusan ?arfe goma sha Waya na dare, nan take ranshi ya bashi cewar wani mummunan abunne ya faru watakil shiyasa lokacin da chief Ya kira wayar jazz yace mashi ya Waga baiyi mashi magana ba!!!!=?3?=?3?=?3?





*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'
'?=؋?>?
?*





A tsiyace yai parking din motar, tsabar sauri a buWe yabarta, da gudun gaske ya nufi cikin gidan batare da jin shakkar komai ba, Shigar shi keda wuya cikin falon ya soma jiyo sautin kukan yarinyar nan mai fama da ta6in hankali, ta dage sai zazzaga masifa take yi tana fadin wallahi saina tona maku asiri ranar lahira, dukanku sai kun shiga wuta tun da ku ka ta6a min yaya jazz Wina . Zuciyarshi ce ta soma dukan uku uku, zaro bindigarshi dake soke a ?ugunshi yai, cikin sanWa yake tafiya yana tunkarar Upstairs, Ya haura second floor, daga ?ofar Wakin Ya la6e Yana sauraronsu.

 Ki daina magana mana, bakiji suna bada hakuri ba? Kuskure suka yi wurin bugunshi, bada son ransu ba

Jin muryar mutuminsu yasa shi yin wuff Ya afka cikin Wakin, Jin takun tafiyarshi ne Ya janyo hankulansu ga dubanshi, kusan atare suka Wago suna kallon shi.

Nauyayyar ajiyar zuciya big guy ya sauke haWi da furta Ya Allah kafin Ya daura eyes dinshi akan face din mutumin yace meke faruwa ne ? Waya ta6a khadeeja take kuka? ya akai naga yaran duk sun farka daga bacci ?

A ruWe yake jefa mashi tambayoyin, sam bai lura da Sojojin ba, waWanda tun da ya shigo suke dubanshi da mamaki.

da ido mutumin Yai mashi nuni da sojojin gasu nan, mahaifin Jazz ne yazo tare dasu, wani abune ya faru na rashin fahimta da yajawo har suka bugi jazz shine take ta kuka

A hanzarce ya mayar da dubanshi ga Sojojin, Kusan atare suka buga ?afa tare da Sara mashi.

Jinjina kanshi yaWanyi da mamaki ya furta Tiger ! Army Boy! Ya akai kukazo gidan nan?

 Tsautsayi da ?addara acewar Tiger, Army ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar da Big guy, sai lokacin ya lura da jinin dr jazz daya daskare saman floor, ga kuma Dressing mirror da daya fashe ta silar buga kan jazz jikinshi, cikin matsanancin tashin hankali ya furta Inna lillahi wa inna ilaihirraji!

Cikin sanyin murya Army Boy yace sai ha?uri yalla6ai, rashin sanine, tabbas


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login