Showing 30001 words to 33000 words out of 260999 words

Chapter 11 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

dogon tsoki taja tare da zuwa gaban dardumar ta shi ta kai hannu ta rufe qur anin da ya ke karantawa, a tsiyace ta ?wace cazbagar dake nannaWe a hannun shi ta Waura ta saman qur anin, don ta fahinci da gayya ya ke yin karatun duk don kada ya saurari maganarta.

Tana huci ta Wago tana kallon shi still bai buWe idanuwanshi ba, kuma bai dakata da yin karatun ?ur anin ba domin kuwa haddace akanshi

 Ka da ka bari raina ya 6aci wlh zan yi maka abunda baka tsammani, na rasa uban me na yi ma ka daka Waura mun karan tsana sai ka ce ba uwarka ba! Ko kana da wadda tafi ni ne a duniyar nan ? Ta jefa mashi tambayar, Shiru bai ce uffan ba, gyaWa kai tayi ilmin addinin na ka ya tashi abanza tunda ba ka san ka girmama iyayen ka ba, tsawon shekara da shekaru kana nuna wariya tsakanina da mahaifinka laifin me namaka Shureim ? Cikin jin ?unar rai ta yi maganar, A hankali ya buWe idanuwanshi farare ?yal da su ya Waura su akan fuskar Mahaifiyar tashi, ba kowa ba ce fa ce Layla mahaifiyar Benazir, Doctor shureim shine babban Wansu, Ya ya ne awurin Benazir mahaifiyar Angel.

DaddaWar muryar shi ce ta ratsa kunnuwanta ba ki min laifin komai ba, har yanzu kina nan a matsayinki na mahaifiyata, kawai bana bu?atar kusancin ki da ni Zagayawa ta yi zuwa gefen gadon shi ta zauna suna fuskantar Juna Nasan dalilin dayasa ka ke yin fushi dani, haba shureim tsawon shekaru nawa why za ka ru?e abu aranka yai ta damun ka? Yakamata mu manta da abunda ya wuce, kuskure ne an riga da an ta6ka, kuma in sha Allahu hakan bazata ?ara faru wa ba fuskarshi a Waure ta ke babu walwala tayi tsammanin zai tanka mata sai ji ta yi ya yi shiru bai ?ara magana ba.

?ululun ba?in ciki ne ya tokare mata ma?oshinta, zuciyarta na ?una tace na lura sam faWuwar mahaifinka bata dame ka ba, An ya kuwa shureim kana ?aunar mu a matsayin mu na iyayenka? Cos na fahimci baka son cigaban mu murmushin takaici dr shureim ya saki, da ido tabi shi da kallo ganin yana dariya har fararen ha?oran sa su ka bayyana masu kyau da tsari.

 Mahaukaciya ka mai da ni? ina magana kana dariya fuskarta a Waure tayi maganar, Yun?urawa yai tare da mikewa Ya fuskance ta kafin ya soma magana Saboda ku ba iyaye bane daya kamata a nuna damuwa akan ku! Daga ke har shi bakusan ciwon kan ku ba, Gaba Waya hankalin ku na akan son abun duniya damuwar ku akan cigaban ku ne ba akan mu ba! Ta ya ya zan damu don mahaifina ya faWi a za6e? Aini abun farin cikine agare ni, don na fahimci siyasarshi tafi komai mahimmanci awurinku! Saboda rashin sanin ciwon ?a ?a Yau tsawon shekara goma sha shidda Benazir bata a tare da ku, hankalin ku a kwance ba ku iya ta6u ka komai ba, duniya kawai kuka sa agaba, Wlh na jima ina danasanin kasancewar ku Iyayen mu! Na yi fatan ace mutun yana iya canza iyaye da tuni na yi hakan, Nifa ba ku da amfani acikin rayuwata! Kun riga da kun yi min abunda har abada zuciyata bazata ta6a mantawa da shi ba, kune silar duk wata masifa dana tsinci kaina aciki....... da?yar ya ?arasa maganar cikin jin ?unar rai, a bun ka ga farin mutun tuni fuskarshi ta canza launi zuwa ja, numfashi yaja muryarshi adisashe yace kun manta cewa ?a ?a amana ne agare ku? Ranar gobe ?iyama Allah zai tambaye ku game da amanar da ya ba ku, Rashin nasara yanzu ku ka fara gani, in sha Allah ba zaku ta6a samun abunda ku ke so ba, har tsayuwar dare zanyi maku akan kada Allah ya cika maku burinku na mallakar kujerar..... bai ?arasa maganar ba sakamakon zazzafan marin da Layla ta sakar mashi, da sauri ya dafe kuncinsa da tafin hannun shi na dama, Idanuwanshi sun rune zuwa ja.

Tana hu ci ta nuna shi da yatsa don uban ka ka tattara kayan ka kabar gidan nan tunkafin ranka ya 6aci, shashasha kawai wanda baisan ciwon kanshi ba, Cikin sanyin murya yace zan tafi koda ace baki kore ni ba Mommy, dama ita gaskiya Waci gare ta, kuma in sha Allah zanje na nemo ?ar uwata benazir aduk inda take, idan ku bakusan ciwon kanta ba ni na sani.... tunkan ya kai ?arshen maganar layla ta nufi ?ofar fita Waki kamar zata tashi sama tsabar 6acin rai.

Zu?unnawa yai saman gwiwowinsa idanuwansa jawur hawaye na cigaba da gangarowa saman kuncinsa, ha?i?a mahaifiyarshi ta fama mashi mikin dake acikin zuciyarshi, matsawa yai gaban gadon shi ya mi?a hannu ya Wauki wayarshi yana duban hoton da ke a kan wallpaper na wayarshi, lumshe idanuwanshi ya Wanyi kafin ya ware su sosai akan hoton da yake kallo, baya gajiya da kallon fuskarta A hankali ya furta

_ke ce silar tarwatsewar farin cikina kuma kece silar shiriyata! Ki yafe min nayi kuskuren da bazan ta6a gyara shi ba, ina son ki sosai ina jin ki har cikin raina, nasan ha??in ki ne ya ke bibiyar rayuwata_

kifa kansa yai saman mattress sosai ya fashe da matsanancin kuka kamar ?aramin yaro.

Bayan fitar Layla kaitsaye ta nufi falon gidan, ranta ya 6aci sosai, kalaman Dr shureim sun sosa mata zuciyarta, yau kusan shekara uku da dawowarsu Nigeria tun bayan barin su Dubai, Layla taji takaicin faWuwar Alhaji ubaid saboda tafi kowa ?wallafa rai akan hawan shi mulkin shugaban ?asa don ta ji daWin yin sharholiyarta a matsayin first lady, sai dai Allah bai basu nasara ba, bugu Waya aka ?undumo shi ?asa, tun farko sai da ya ji fargabar tsayawa takarar jin wanda za su kara da shi, don kuwa yasan muddin Sharafudden Ya nemi takarar shugaban ?asa zaiyi wuya ya iya kada shi, sanin farin jinin da Allah ya yi mashi, Mutun ne na jama a mai kyautatawa al umma.

 Hajiya.. muryar mai aikin gidan su ce a dabarbarce ta ambaci sunanta ganin yadda ta bi ta da matsiyacin kallo lafiya ?

Cikin harshen larabci ta ce  Mun yi ba?i ko da ya ke sun wuce ba?i

 Saboda ?annan uwata ne ? Ta jefa mata tambayar, Sunnar da kai ?asa zainab ta Wan yi Hajiya Aisha ce matar governor tare da.... bata kai ga ?arasa maganar ba, layla ta dakatar da ita ta hanyar Waga mata hannu ni ban gayyaci uban kowa ba a gidana, Matsiyatan banza gulmace ta kawo su wato an zo aga yadda na ?are to ta Allah ba ta su ba ?an kutmar uba, jajen ne har yanzu bai ?ara ba abu an kusa rabin shekara da faruwarshi saboda ba?in hali sun?i su manta.. tun da ta fara sambatu zainab ta yi kasa?e tana kallon fuskarta ba ki asake, ta fahimci zallar ba?in ciki ne Azuciyar uwar gidan ta ta, rashin nasarar su ya tsaya mata a zuciya nema ta ke ta zauce, dama ya lafiyar gwiwa mutun mai ?arancin imani.

Tsawa layla ta daka mata, firgigit! zainab ta Wan zabura Ki je ki sanar da su cewa bana nan muryarta na Wan rawa tace Ae an riga an faWa masu cewa kina a cikin gidan, yanzu haka anyi masu iso suna acikin main palour... da?yar zainab ta ?arasa maganar tana mai haWiyar yawu ganin irin kallon da layla ta ke jefa mata tamkar ?wayar idonta zata faWo ?asa, guntun tsoki taja masu aikin gidana sun fara raina ni saboda rashin nasarar mu dole na yi wani abu akai, su kuma waWancan taron magulmatan zanje gare su, bari na fara zuwa Waki in zuba gwalagwalai na don kar su raina ni acikin zuciyarta ta yi maganar tare da juyawa ta nufi sashen da Wakinta Ya ke.

Binta da ido zainab ta yi haWi da Wan girgiza kanta Allah ya shirye ki layla har zata Juya idon ta ya sauka akan Dr shureim da ke shirin fitowa daga Wakin shi hannun shi ru?e da key Win motarshi, tsananin tausayin shi ne ya kamata ganin yadda ya canza, ta lura da damuwar da ke akan fuskarshi, a hankali yake tafiya yana tunkaro inda take ga dukkan alamu bai lura da ita ba har sai da Wan yi mashi gyaran murya, tukunna ya Waura fararen idanuwanshi akanta, Sam babu walwala akan fuskarshi, darajar da ta ke da shi a idon shi yasa shi nufarta, ya Wauki zainab taimkar auntynsa, Babbar macace mai hankali da natsuwa.

Yana ?arasa gabanta ya du?ar da idon shi ?asa ba tare da ya gaishe da ita ba

 Ko ba ka faWamin ba dr shureim naga damuwa akan fuskarka, na Wauke ka tamkar Wan ciki na, dan Allah shureim ka da ka bari damuwa ta canza ka, inaso ka sani komai ya faru mu?addari ne daga Allah, rubutacciyar ?addara ce wadda ba wanda ya isa ya canza ta cikin kwantar da murya ta ke lallashinsa, sai faman karkaWa car key Win hannunsa yake yi, tun da ta fara yi mashi nasiha bai tanka mata ba sai da ta kai aya tukunna ya soma magana a tsanake  Aunty zainab na aikata babban zunubin da har abada ni nasan Allah ba zai ta6a yafe min ba, Ni kaina nayi danasin mara amfani.... duk yadda yaso ya jure ya kasa kamar ?aramin yaro cikin muryar kuka yaci gaba da cewa Ina sonta aunty zainab sune silar komai, bazan ta6a yafe masu ba na tsane su, Mu kuma tamu jarabtar ta iyaye ce, basu damu da mu ba, bu?atar su itace agabansu, Yan zu haka da nake maki magana Mommy ce ta kore ni saboda na faWa mata gaskiya, ki yi ha?uri Aunty zainab kada ki ce za ki dakatar dani ?wara na tafi, zama atare dasu bai da amfani, zanje na nemo ?ar uwata Benazir In ru?e ta a hannuna waWannan mutanan ina zargin sune silar tarwatsewar rayuwarta kamar yadda su ka yi silar tarwatsewar tawa rayuwar...... yana magana hawaye na cigaba da wanke fuskarsa, ita kanta zainab Win tuni idanuwanta sun cicciko tab da ?walla, ru?o hannunshi tai a cikin nata, da sauri ya Waura kanshi saman kafaWarta Shureim Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wanda ya cuci wani Allah zai saka mashi, ko a tsakanin ?a ?a da iyayen su akwai hisabi, Na yi maka al?awarin zan taimaka maka akan komai, ashirye ni ke dana zama uwa agareka, Ae Wa na kowa ne idan su basu so to ni inaso, dama ban ta6a haihuwa ba jin abinda tace ne yasa shi Wago da fuskarshi yana kallon ta, murmushi ya ?a?aro akan fuskarshi, ha?i?a kalamanta sun sanyaya masa zuciyar shi.

 Aunty zaina are u serious zaki taimaka min ? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, farin cikine ya bayyana akan fuskarshi Aunty zainab akwai wani aiki da nake so mu yi atare bana so kowa Ya sani.... bai kai ?arshen maganar ba, Takun tafiyar Mahaifiyarshi Ya dakatar dashi, muryar zainab na rawa tace mashi

 Ka tafi kawai zan kira ka awaya anjima sai mu yi magana amsa mata yai da toh, Da sauri Ya fuce ita kuma ta nufi hanyar kitchen.

Cikin takun izza ta ke tafiya, har ta canza kayan jikinta zuwa tsadadden leshi wuyanta da hannyenta Zinari ne, ta buga uban Waurin kallabin nan ture kaga tsiya, Takalman ?afarta high hills ne, ta wanke jikinta da turare, tana tafiya tana hura hanci

Tana dab da zata shiga palourn gidan muryoyin manyan matan da suka kawo mata ziyara ta karaWe kunnuwanta, da sauri ta la6e tana sauraron abunda su ke tattaunawa

 Ae ban ta6a ganin mutum mai haWamar tsiya irin Alhaji ubaid ba, nifa tun lokacin da ya sauka mulki yana fama da ciwon ?afa raina ya bani cewar wani munafuncin suka ?ulla ashe kujerar shugaban ?asa yake so, yanzu gashi ba wan ba ?anin duka sun rasa 6a66akewa su ka yi da dariya

 Ni dama tun da naji Sharafudeen Ya tsaya takarar shugaban ?asa raina ya bani cewar shi zaiyi nasara, sai gashi ta tabbata, wa zai Iya ja dasu? Ganganci ne ya kai Alhaji ubaid, Ko da ya ke matar shi ce mai haWamar a yadda na fahimta hajiyar da ta yi maganar ta ?arasa tana dariya, wata ta Waura da cewa ai ko sharafudeen bai tsaya takara ba kinsan Allah ba wanda zai za6i ubaid, Mutanan da basu son darajar ?a ?an su ba taya zasu Iya ru?e ?asa irin nigeria mai cike da taron Talakawa? ?ar ta fa benazir tana ?asar ture, ayadda naji labari karuwanci take yi kuma ana zargin uwarce ta turata, Allah na tuba zato zunubi, duk da ni dai daga majiya mai ?arfi naji ... Hankalin layla idan yai duba toh ya tashi, tseguminta da suke yi yayi matu?ar gigitata, bata ta6a tunanin mutane zasu sanya masu ido game da rayuwarsu ba, ha?i?a ranta ya 6aci, Ta yi niyar ta shiga tayi masu korar kare amma saita lallashi zuciyarta, Ta daidaita natsuwarta tare da yi masu sallama ta kutsa kai cikin katafaren palourn jin motsin shigowar ta ne yasa su ka yi saurin dakatawa da yin firar, Waya bayan Waya ta ke binsu da kallo, mata kenan abin a Jininsu ya ke.......

*UNCLE ABDALLAH*

A ?alla yau wata Waya da dawowarsu Nigeria, sun fara sauka a adamawa state wurin dangin hajiya adama kafin dawowarsu gidansu da ke anan Jihar jos, zaune ta ke saman sofa mai mazaunin mutun uku, Jikinta na sanye da riga bubu ta material ta yafa mayafi akanta, Yayin da idonta ke asanye da farin glass, hutu yazauna mata ta ?ara ?iba abunta.

Ta natsu tana kallon portrait artist Win dake zu?unne agaban Drawing board Yana gudanar da aikinsa, daga ?asa gefenshi Kayan zananshi ne, Hada hoton Angel da hajiya adama ta mi?a mashi don Ya zana mata Ita, tana son ganin yadda zata koma a shekarunta na yanzu don su samu sau?in gane ta

 Ranki shi daWe, Yarinyar zata kai shekara nawa Ayanzu ? Me zanan ne yai mata tambayar.

 I think 15 to 16 years, amsa mata yai da okey, Kafin yaci gaba da aikin zanan shi,

 Mijina ya faWa min cewa kai ?wararre ne a 6angaren zana mutane, so please don t disappoint me murmushi mutumin ya saki ba tare daya juyo ya kalle ta ba ya furta mata In sha Allah

 Assalamu Alaikum ! Muryar Uncle abdallace ta janyo hankulansu ga dubanshi, Shigowarshi kenan Jikinshi na a sanye da shadda launin maroon, idan ka kalli fuskarshi Sak Uzair hatta duhun fatarsu iri Wayane.

Cikin girmama mai zanan ya gaishe da uncle abdallah, Bayan ya amsa mashi da fara a ya Wago ya kalli Hajiya adama mu shiga ciki ina son magana da ke amsa mashi tai da toh, Yai gaba ta mi?e tabi bayanshi, A cikin bedroom Winsu su ka tsaya suna fuskantar Juna

 Tun Wazu nake jiran shigowarka, Inataso muyi maganar zuwan mu abuja, almost one month da dawowarmu Nigeria banje naga jikana ba duk irin yadda na ?wallafa raina akan son ganinshi, 

 Duk yadda kika kaiga ?agara da son ganinshi ba ki kaini ba,

 Ni banga alamun hakan ba, pls idan munje mu tafo dashi, tunda ka ga bamu da wani Wa da zamu dinga kallo muna jin daWi fuskarta amarairaice tayi mashi maganar, girgiza mata kai Uncle Abdallah yai idan mukayi hakan bamuyiwa Mahaifiyarshi adalci ba, ta rasa mijinta yanzu kuma sai mu tada zancen zamu kar6i yaro daga gurinta ? ?aure fuska Hajiya adama tayi, ranta ya 6aci Abdallah baka son farin cikina, Ni zan koma palour wurin mai zanan can Ta ambaci hakan tare da juyawa a fusace zata tafi, Har takusa kaiwa bakin ?ofa muryarshi ta katse mata hanzarinta ba zan ta6a manta irin wahalar da nasha kafin na mallake ki a matsayin matata, ta ya ya kike tunanin bana son farin cikin ki ? shiru bata Juyo ta kalle shi ba, idonshi na akan bayanta

 A yanzu haka da ni ke yi ma ki magana, na yi mana cuku cukun komawa can da zama, na samu aiki a babban companyn sharafudeen saboda ba zan Iya raba uwa da Wanta ba, haka zalika bazan Iya raba kaka da jikanta ba, shiyasa na yanke shawarar komawarmu can, Nasan hankalin ki zaifi kwanciya idan kina ganin shi akai akai idanuwanta ne suka cuko tab da ?wallar farin ciki.

Fasa fita ta yi daga Cikin Wakin, Jiki asanyaye ta nufe shi tare kwantar da kanta saman ?irjinshi, Hannun shi Ya Waura saman bayanta yana cigaba da gayamata daWaWan kalamai masu kwantar mata da hankali, tsawon mintuna biyar kafin ta Wago dakai Tana kallon shi

 Inaso zanyiwa Aneelerh kyautar zanan fuskar Angel da akayi min a south korea, Nasan za ta yi farin ciki saboda tana matu?ar ?aunarta, kuma zatayi mamakin ganinta a shekarunta na yanzu don inada tabbacin idan har Allah yasa ta bayyana zamu iya ganinta da suffar da mai zanan ya zanata, kasan sun ?ware a iya zane tana magana Hannunta ru?e da gaban rigarshi kamar tana gyara mashi ma6allinta

 Idan ki ka bata zanan ke fa? Almost dala dubu Wari akayi maki shi fa

murmushi ta Wan saki saboda haka yasa nace ka kiramin wani mai zanan ni sai na Wauke shi, yace mai zai hana ki bata sabon zanan da za ayi ke sai ki ru?e na koriyan? Girgiza kai ta yi alamar  a a, Nafison nayi kyauta da abunda yafi kyau da tsada, Farin cikinta kawai nakeso, yanayin fuskarshi ya nuna tamkar bayason taba Aneelerh zanan fuskar Angel da akayi mata a?asar korea, ba ta kawo komai aranta ba saboda ta fahinci Son zanan ya ke yi ba don saboda tsadarshi ba.

 Hajiya an kammala daga Cikin palour su ka jiyo sautin muryar me zanan, da sauri Hajiya adama ta nufi falon uncle abdallah yabi bayanta, tunkan su ?arasa shiga Ciki idanuwansu suka soma hango masu Kyakkyawar fuskar Angel


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login