Showing 243001 words to 246000 words out of 260999 words

Chapter 82 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

soma janye sumar kanshi daga kan fuskarshi,
Tunkafin Ya ?arasa kau da sumar, Hankalin prime minsiter yai matu?ar tashi hai?am, zuciyarshi ta soma harbawa da matsanancin speed, Yayin da idanuwanshi suka zazzaro waje, tamkar eye balls dinsa zasu fado ?asa, ha?i?a yayi matu?ar girgiza da ganin abunda idanuwanshi suke nuna mashi, kowa dake a Wakin saida ya lura da yanayin da prime minister ya shiga na tsantsar mamaki da Al ajabi, bashi ba hatta sheikh imam da Chief owais al ajabine akan fuskokinsu.
Muryar prime minister na rawa ya furta Sheikh...! Owais Kuna ganin abunda nake gani kuwa? a ruWe ya furta maganar yana ?arema fuskar Danish kallo.
Sheikh Imam da al ajabi Ya gama kamashi, Baisan sa dda ya furta amma dai wannan yaron Jininka ne ko? don wannan yafi ?arfin ace kamanceceniyace ta halitta sai dai ta jini, saboda kamanninshi sun 6aci dakai da kuma yarinyar wurinka Nazli, Tamkar kayi kakinsa, komai nashi kalar naka ne, tun da Allah Ya halicceni ban ta6a ganin kama irin wannan ba, gaskiya nayi mamaki.....
Boss man yace ai ba tun yau ba, nasha faWama chief owais cewa Yaron Yana kama dashi, bani ba hatta abokanan aikin mu sun shaida hakan, sai dai wani abu daya ?ara Waure mun kai ayau, Yaron yafi kama da prime minister hateem, bai baro komai nashi ba, tun daga kan shape din bakinsu, dogon hancinsu da idanuwansu, Yalla6ai da zaka ga launin idonshi zaka sha ruwan mamaki, domin kuwa kalar nakune
Dafe kai prime minister yayi da hannun shi Waya, Hankalinshi Ya?i kwanciya da kamanninsu da yaron.
Gyaran murya salsabeel Yayi kafin ya soma yin magana yana duban su
 Ni kaina na jima ina mamakin kamannin dake a tsakanin Chief owais da Danish, komai nasu kala Waya ne banbancinsu launin fata ne da kuma tsayin sumar kai, wani iko na Allah sai gashi Yalla6ai Hateem Yafi kama da Danish
Runtse ido prime minister yayi, baisan ya akai yake jin wani irin yanayin atattare dashi ba.

Muryarshi araunace ya furta ban haWa komai dashi ba, bani da ala?a da shi, Yauce rana tafarko dana fara yin tozali da fuskarshi, amma meyasa nake jin wani abu agame dashi? Dan Allah ku fahimtar dani na shiga ruWani, ya akai komai nashi kalar nawa ? Yana magana la66ansa na kerma.

 Owais ka faWamin wanene Yaron nan? Su wanene Iyayenshi? Meyasa yake kama dani da ?ata Nazli ? Da kakkausar murya ya furta maganar saboda aruWe yake da lamarin.
Shi kanshi chief owais din Ya kasa furta komai, Lamarin Ya ruWar dashi ya rikirkitar mashi da tunaninshi, bai ta6a tsammanin kamanninshi da yaron sun 6aci har haka ba.

A hankali Ya soma yin taku Izuwa gaban Prime minister hateem dake dubanshi fuskarshi a yamutse.

Cikin kwantar da murya ya furta Uncle, bamu da masaniya akan su wanene Iyayen shi, saboda bai dasu a halin Yanzu, da shi da ?an uwanshi dake ahannunmu bamusan komai nasu ba, tamkar marayu suke a hannunmu, Yarinya Wayace mukasan Mahaifinta tajuddeen ya faWa yana nuna Boss man da hannun shi.
Girgiza kai yaWanyi numfashinshi na fita da huci yace Owais kada ku maidani mahaukaci, nafasan me nake yi, taya za ace babu danginshi? Kyakkyawan yaro kamar wannan?ni kawai so nake ku faWamin meyasa muke Kama !!! Ga dukkan alamu prime minister ya fara zaucewa, wata irin zuface take tsastsafo mashi saman goshin shi.
Hankalin kowan nan su Yana akanshi, owais baisan taya zai fahimtar da uncle din nashi ba, Mi?ewa Sheikh Imam yai tare da nufar prime minister Ya tsaya agabanshi, tare da kai hannu Waya ya dafa kafaWarshi, a tsanake Ya soma yi mashi magana
 Ka kwantar da hankalinka, yakamata ka fahimci abun da Awaisu Yake ?o?arin faWa maka, su kansu basu da masaniya akan yaron, kaWan daga cikin ikon Allah kenan, kowani Wan adam yana da masu kama da shi A duniya..... tunkan sheikh Imam Ya ?are maganar, prime minister yace baba, wannan yafi ?arfin ace kamace kawai, ka dubi fuskarshi dakyau, tamkar anyi photocopy dina, kamar dai nina haife shi, Ina jinshi tamkar jini na, ?aunar da nake yi mashi kaWai abun dubawace, ta zarce misali, saboda shifa na kasa runtsawa adaren Jiya, na damu da shi fiye da tunaninku......... gaba Waya sun rasa taya zasu shawo kan prime minister, a iya sanin su da shi bai ta6a haihuwar Wa Namiji ba, balle ace yarom shine daya 6ata.

 Yanzu abun da za ai, tun da kana ?aunarsa kuma yaron baida iyaye, mai zai hana ka Wauki ragamar kula dashi kafin komawarka canada? Wata ?il hankalinka zaifi kwanciya acewar sheikh Imam, ya fadi hakanne donya kwantar masa da hankalinsa ganin irin ruWun daya shiga.

 hakan yayi shiekh, Uncle ka ?addara cewa jininka ne shi, kana da damar da zaka Iya bashi kyakkyawar kulawa Chief owais na ya furta hakan.

Kalamansu sun tausasa mashi zuciyarshi, har cikin ranshi Yaji dadin jin hakan.

 Inaso na taimaka mashi yayi wankan ya sanya sutura a jikinshi, zan kira Wan uwana awaya don yazo ya ganshi, nasan shi kadaine zai ?ara tabbatar min da abunda nake gani a idona, sannan Idan yaron yaji sau?i kafin in koma canada, zan je dashi gidana don in nuna ma gimbiyata shi da ?a ?ana nasan zasuyi mamakin kamanninsa dani musamman Nazli, hatta hasken fatarshi kalar nata ne murmushi ne akan fuskokinsu, sunji daWin sakewar da prime minister yayi, hankalinsu ba ?aramin kwanciya yayi ba.

NaWe hannun rigarshi yayi, tare da cire agogon azurfarshi, da zoben hannun shi, Ya mi?a ma owais su, da sauri owais ya sanya hannu ya kar6a, gaba Waya kallon shi suke da mamaki akan fuskokinsu.

Murmushin gefen fuska yasaki har dimple dinsa ya lotsa kada kuga ina zumuWi akanshi ?aunarsa nake Yi da zolaya ya furta maganar kafin yace wazai taimaka min mu shiga da shi bathroom room ? da sauri Salsabeel Yace ni Yalla6ai
 Yawwa, ru?o min shi mu shiga ciki, ko da ya ke naga yana da girman jiki zaiyi nauyi, bari na kama maka a hanzarce Ya zagaya ta 6angaren da salsabeel Yake, a lokacin sabeel Yayi ko?arin janyo danish da ?yar ya kawo shi bakin gadon.
KafaWunshi suka rurru?e shi da prime minsiter suka mi?ar dashi tsaye, wanda badan ?arfin giant da sabeel yake dashi ba da kuwa babu mai iya Waga shi, jikin shi ya saki tamkar wanda baida ?ashi, kanshi ya kalli kasa sumar kanshi ta lullu6e fuskarshi, idanuwanshi suna arufe gam, zufa ta ko ina take tsasstsafo mashi, a hankali suke tafiya dashi suna nufar toilet, har suka yi nasarar shigar da shi ciki
Bayan shigarsu, sheikh imam ya dubi boss man da owais
 Inason ganin sauran Yaran da kuke ruko a hannunku
Da sauri Boss Man Ya amsa mashi da toh, Ya mi?a ma sheikh imam rawanin shi daya ru?e a hannunshi tare da hularshi, godiya yayi mashi, har ya juya zai fuce muryar chief owais ta dakatar dashi
 Boss, Ka tara yaran a main falo, Yanzu zamu sauko down
Amsa mashi yai da toh, kafin yasa kai ya fuce daga dakin Ya sauka down.

A hanzarce yake tattaka staircases din benan, har ya kusa saukowa down yai tozali da big guy dake tafiya cikin takun sauri, ganin boss yasa shi fadin Ya ake ciki mutumina?
Boss yace Alhamdulillah Danish ya dawo ainihin suffarshi, Sai dai babu kuzari ajikinshi, Ko yatsanshi bai iya Wagawa, ga tabonnin harbin bindigar da akayi mashi ta ko ina saman fatar shi
Cike da jin alhini Big guy yace bawan Allah, banji dadin jin hakan ba, wallahi yaron tausayi yake bani, ashe munyi mashi illa da harbin bindigar amma ina fata baiji mugun rauni ba ko ?

?aga mashi kai boss yayi alamar eh, fuskarshi da damuwa yace ubangiji Allah yaba shi lafiya, Allah kuma ya kawo mashi ?arshen wahalar shi Boss ya amsa mashi da ameen kafin yace yanzu haka Prime minister da Wan uwanshi, sun shiga dashi bathroom zasuyi mashi wanka, sheikh imam ne ya bada shawarar yin hakan
Zaro ido big guy yai da zolaya yace Yanzu wannan ?aton balagaggen zasuyi ma wanka? Yaron fa yakai chief dinmu girman jiki,
Harara Boss man ya jefa mashi laifina ne dana tsaya yin magana da Wan ?waya, sai kace ba ka ji nace maka bai iya Waga koda yatsansa ba, lalura ce ko kai kanka akwai ciwon da sai dai adinga yi maka wanka, ba fata nake yi maka ba, ina dai kwatanta maka ne babu wanda yafi ?arfin ?addara
Dariya big guy yasaki Haba mutumina, nima fa wasa nake yi, nadai jinjina lamarin ne, amma baka fadamin ba prime minister baiyi mamakin ganin fuskar yaron ba ?
Dariya boss yayi kafin yace daWina da kai shegen son gulma uwa mace
Cike da zumuWi big guy yace ni dai ka amsa min tambayata na ?osa naji
Boss man yace kallo yabarka, hankalin prime minister ba ?aramin tashi yayi ba, kusan fa hauka yayi mana gaba Waya ya rikice tunda yayi tozali da fuskar yaron, da?yar fa muka shawo kanshi, duk yabi ya ruWe...... a tsanake Man ya labarta mashi komai.
Dariyar sha?iyanci Big guy yasaki hada tafa hannayensa yana fadin ni dama nasan za a rina wallahi, nifa tuntuni nake mamakin kamanninsu da yaron, koda ake maganar yana kama da chief namu saida na raya arainacewa duk ranar da hateem yayi arba da yaron sai ya sha mamaki, donni nafi ganin kamanninshi da nashi, sai gashi maganata ta tabbata da ?warin gwiwa ya ?are maganar, boss da zolaya yace sannu malamin duba, aikinka na kyau, ka tsareni da surutu kamar kanyar da bata da daWi, ka hanani ?arasawa inda zanje
 Ina zakaje ne ? Big guy ya jefa mashi tambayar.
 Sheikh imam ne Ya bu?aci atara mashi sauran yaran yana son ganinsu
Big guy yace ai ?wara yagansu domin kuwa suna bu?atarshi kodan saboda wannan jarin taka, ni ina da tabbacin ba a rasa almatsutsai akanta..... dariyace ta kubce mashi da?yar ya ?are maganar, ganin yadda boss man ya haWe fuskarshi.
Harara ya jefa mashi Idan ka isa ka maimaita maganarnan agaban chief
Big guy yace ai ko giyar wake nasha bazanyi wannan gangancin ba,
Fuskar boss Wauke da fara a Yabi ta gefen big guy Ya yi gaba abunshi
?aga murya big guy yai tare da cewa Yaran suna a Wakin Jarinka gaba Wayansu na tarasu anan
Murmushi taj yasaki, haWi da girgiza kanshi, bakomai yasa shi yin hakan ba face sunan da big guy yake kiran Babynsa angel, wato JARI, saboda yace mashi chief zaiba auranta yafi son inda zata huta shine fa ya ru?e abun azuciyarshi har yake tsokanarshi da sunanta.

Idan muka koma 6angaren su unaisah, tuni sun kammala yin breakfast dinsu, kowa yaci ya ?oshi yayi hani an, sai dai damuwa ta hanasu sakat, Hankalinsu ba akwance Yake ba, sunyi zugudum saman carpet, kowa ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, jefi jefi sukan buWe baki suce Allah sarki danish dinmu, ko awani hali yake a yanzu, a lokacin ummin america ta shiga toilet din dakin nasu.

Batool ta kwantar da kanta kan kafaWar unaisah, Azeeza ta Waura nata kan a shoulder din Sajeed, hannayensu ru?e cikin na juna, Jemimah ta haye bisa laps din haris idanuwanta alumshe sai faman firgita take Yi tana jan numfashi kamar baccine ke ?o?arin yin awon gaba da ita, parveen da naufal sun jingina bayansu jikin gado fuskokinsu babu walwala, hannah kuwa ta Waura kanta saman laps din javed, sunyi shiru babu mai magana, daga tsakiyar carpet din tray din kayan abincin da suka kammala ci ne ba akaiga kawar da su ba, wasu daga cikinsu sai faman lumshe idanuwansu sukeyi alamun bacci suke ji.

Jin motsin buWe ?ofar toilet yasa Batool yin saurin runtse idanuwanta ta ?an?ame unaisah, gudun kada ta haWa ido da aunty ummi, fitowa tayi daga cikin toilet din, sautin takalman ?afartane ya fargar da masu gyangyadin cikinsu, gaba daya suka ware idanuwansu akan ummi dake tunkarosu.

Ta fahimci tsantsar damuwace atattare dasu, tun Wazu da suna cin abinci ta lura da kyar suke cusa abinci abakunansu, tasan bai wuci damuwar halin da Wan uwansu yake aciki bane
 Aunty ummi, Inaso zanje dakin danish in duba jikinshi unaisah ce tayi maganar
Ummi tace a a, ba a bada iznin wani daga cikin ku Ya fita ba
Ya mutsa fuska unaisah tayi tamkar zata fashe da kuka ta kuma cewa aunty ummi batool ta manta doguwar rigarta a Wakinki jiya da su ka je kwana, zanje na Wauko mata
Girgiza kai ummi tayi basai kinje ba, zuwa anjima da kaina zan dauko mata rigarta zumbura mata baki Unaisah tayi duk yadda taso tayi ma ummi wayau ta?i barinta ta fita.
A ?ule unaisah tace  To waimu haka zamuyi ta zama a Waki kamar an kulle kaji a keji
Dariya ummi tasaki har fararen ha?oranta suka bayyana tar dasu kamar gonar auduga
 Kin gaji ne ? ?aga mata gira unaisah tayi alamar eh.
GyaWa kai ummi tayi okey, bari na taimaka maku ku girgije jikinku, basu fahimci me take nufi ba.
Zura hannu tayi cikin aljihun doguwar rigar jikinta ta zaro iphone dinta, duk sun ?ura mata ido suna jiran ganin me zatayi da wayar.
Zira ziran yatsun hannunta ta Waura kan screen din wayar ta soma yin pressing dinta, jim kaWan daddaWan sautin kiWa ya soma karaWe bedroom din nasu, taken wa?ar ed shareen mai suna Shape of you.

Fuskarta Wauke da shu umin murmushi take kallonsu, sun ?ura mata ido suna kallonta, ganin ta fara jujjuya qugunta tana taka rawa.

 Idan kuna ra ayi ku taso muyi rawa Waure fuska Unaisah tayi ranta a6ace take dubanta har ta buWe baki zatace mata bazasuyi rawarba, Sajeed Ya mi?e Yana taka rawa ya nufi tsakiyar Wakin, mi?ewa Azeeza tayi da sauri tabi shi Ya ru?o hannunta Yana jujjuyata, tuntsirewa Ummi tayi da dariya tana kallon su, abu kamar wasa sautin kiWan yafara kai masu karo, Naufal ya mi?e ya ru?o hannun Parveen suka nufi tsakiyar Wakin suma suka fara yin rawa, AruWe unaisah take kallonsu kamar waWanda akayima asiri, lallai ummi ba ?aramar shaidaniya bace hakanan taja hankalinsu da sautin kiWa, ru?o hannun Hanna javed yai suka mi?a suma suka nufi tsakiyar dakin, Haris Ya mi?e Jemimah ta like mashi tana fadin itama zatayi rawar, ya ruko hannunta suka bi sahu, Ya rage saura Unaisah da Batool su kadai ne suka ki tashi.

 Sanya damuwa aranku bazai ta6a yi maku maganin matsalarku ba, Ni taimakon ku nake sonyi don na fahimci baku san me ake nufi dajin dadin rayuwa ba, kunfi so kuyita ?untata kanku bayan kowani Wan adam yana da damar da zai sanya kanshi farin ciki, If you let me do my job, you ll see the positive results soon. ...... muryarta da kwarkwasa take yin magana tana kallon Batool da Unaisah.

 Idan kunaso mu zauna lafiya daku, to ku bani haWin kai, Ni kuma zan wayar maku da kanku, zan sanyaku farin cikin da zai kawar maku da damuwarku da sha?iyanci take yi masu magana tana Wage girarta.

Sunyi shiru babu alamun zasu tanka mata, shu umar dariya tasaki tare da cewa Na fahimci unaisah kece mai taurin kai, Saboda ke Batool ta?i tashi ta taka rawa ko ? MurguWa mata baki unaisah tayi.
 Idan kika bani hadin kai mukayi rawa zan barki ki fita daga Wakin nan kije wurin Wan uwanki danish.... tunkan ummi ta rufe baki unaisah tayi saurin furta a a sai dai ki bari in fara zuwa dakin shi, Idan na dawo sai muyi rawar
 Zaki rasa damar da kike da ita acewar ummi, Ta furta maganar tare da mi?a ma batool hannunta alamar ta taso suyi yawa, cike da jin shakkarta Batool take kallonta, fuskar ummi a Waure tace da ita Come to me sai da batool tafara kallon unaisah jikinta sukuku kafin ta yun?ura ta mi?e tare da Waura hannunta na dama saman hannun ummin america, gam ta ru?e hannun tajata zuwa tsakiyar Wakin rawa suka soma takawa kamar mace da namiji haka take juya batool tana rungumeta idonta akan unaisah data haWe fuska tana satar kallonsu.

Canza masu wa?a tayi ta sanya masu wa?ar rema mai taken baby come down, tunda sautin kiWan Ya fara ratsa mata zuciya takasa jurewa ji tayi kamar ana janta a hankali ta mi?e tsaye tana kallon ?an uwanta dake ta ti?ar rawa suna dariya, itama sai taji tana bu?atar yin nishaWin kota Webe kewar danish dake damunta.
Ganin ta mi?e tsaye sototo tana kallonsu yasa ummi mi?a mata hannu Waya alamar tazo gareta.
Ma?e mata kafaWa tayi alamar bazata zo ba, batool tace please sister kizo muyi yawa atare dan Allah harara ta watsa ma batool, muryar sajeed ce ta janyo hankalinta ga dubanshi.
 Sister zo mu taka mana, muna bu?atarki afilin nan murguWa mashi baki tayi.
 Genie dan Allah kizo muyi rawa, kinga ni banda abokin yi haris baiyi dani da shagwa6a jemimah tayi mata maganar, hada marairaice mata fuska.
Magiya suka dinga mata akan tashigo suyi rawar, tun tana ma?e masu kafaWa, har dai jemimah tazo taja hannunta suka shiga filin, ai tunda tafara taka rawa kamar Wiyar roba, daWi ya kamasu ganin unaisah ta saki jiki tana ti?ar rawa, nan fa kowa ya bada


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login