Showing 255001 words to 258000 words out of 260999 words

Chapter 86 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

Hajiya saratu tayi min kyautar tsadadden leshi guda biyu, da hand bag, hada set na agogo da zobe, da turarurruka...... jinjina kai Aneelerh ta yi tana fadin masha Allah, zahra najiye maki daWi, kin samu na sallah

 Bangama fada maki ba, bayan kuWin aikin decoration da hajiya saratu ta biyamu, prime minsiter yayi mana kyautar kuWi duk mutun Waya 1.5 million waro ido waje Aneelerh tayi mahboob dake la6e jin an ambaci kuWi sai gashi ya dawo gefen zahra Yana raira wa?a.

 In rabo ya tsago dakai kuma abun ya tabbatar saida kai to rabbine yace sai da kai in sai da kai kawai sai da kai, don haka nima Allah ne ya tsaga da rabona ashe arzi?ine ke kirana...... gaba Waya suka sanya dariya, Aneelerh tace mahboob yaushe ka shigo kitchen din nan

Da murmushi akan fuskarshi yace tun Wazu ina la6e bakin ?ofa na kasa kunne ina sauraron aku sarkin Wumi, yau surutun zahra yayi min rana wannan arzi?i haka, wato saboda ba?in ciki zahra ?iri ?iri kika hana in rakaki obie estate da yanzu hadani za ayi rabon kuWin nan....

Dariya zara tayi tana fadin ai baka ji komai ba, bayan kuWin da prime minister yabamu, president Ya ?ara mana, duk mutun Waya dubu Wari takwas dafe ?irji mahboob yayi kamar wanda yaji wani mugun abun
 Sannan Abokin Baba Obie, Jan kunne ya raba mana dubu Wari biyar biyar da dollar ya bamu su
Kallon juna mahboob da Aneelerh su kayi.
 Anya zahra dagaske kike kuwa? Wannan kuWi haka kamar akan bishiya ake tsunkosu

Hararar shi zahra tayi an gaya maka kowa mai ma?one irinka, ai su a wurinsu kuWin da suka bamu bakomai bane

Jinjina kai mahboob yayi Allahumma arzu?ni, Sister Yanzu ina kuWin suke? inaso zan tayaki ?irgawa

Dariyar sha?iyanci zahra tayi kafin tace suna kwance cikin account bank dina suna bacci, dollar din da aka ba mu ne kaWai suke a dakina kuma na 6oye su saboda nasan halinka sarai, tsaf zaka Iya zuwa Waki yi min halin 6era

Dariya Aneelerh tasaki, a lokacin ta kammala yin wanke wanken, ta mayar da hankali akan fuskar zahra
Mahboob Yace kar dai kice zakiyi min rashin mutunci wallahi sai inyi zuciya inje in nemi auran Waya daga cikin jikokin baba obie

Dariya suka saki gaba dayansu bayan sun tsagaita Aneelerh ta dubi mahboob Ya ake ciki? Kunyi magana da Ana ?
?aga mata kai yai alamar eh, zahra tace me ya faru ne ko bata da lafiya

Nan mahboob Ya kwashe komai Ya sanar dasu dangane da halin da Ana take aciki.

Shiru sukayi jikin kowa yayi sanyi, musamman Aneelerh, ranta Ya dan 6aci bata ji dadin ?in gaya matan da tayi ba.

 Idan kuwa hakana Ana bata kyauta min ba,Yanzu har akwai abunda zata 6oye min duk irin sha?uwar dake atsakanin mu?

 Aunty Aneelerh please kada ranki ya 6aci, na riga da nayi mata faWa, abun da ya dace ku harhaWa mata kudin da zata turama ?an uwan nata

Zahra sarkin tausayi tace nida da halima wallahi da sun dawo gidan nan da zama..... wata uwar harara Mahboob Ya watsa mata saboda ke zaki ciyar dasu ko ? Fashewa sukayi da dariya.
Aneelerh tace baka da dama mahboob, yanzu fa ka gama fadin a harhada mata kudi aturawa ?an uwanta shine kuma don tace su dawo nan da zama kake tada jijiyoyin wuya daga maganar taimako

Yamutsa fuska mahboob yayi abun da nake nufi Aunty Aneelerh, Wan adam ba abun yarda bane, muna iya mu taimake su su kuma su butulce mana shine abunda nake jiye mana, kawai dai ?wara in taimakon zamuyi masu mu tura masu can su ?arata

 Ka faWi gaskiya mahboob, nima nayi wannan tunanin, Yanzu me yakamata muyi ? Acewar Aneelerh.

Zahra tayi karaf ta kar6e dacewa kowa ya kawo abunda yake dashi hada kai mahboob nakama sai yafi yawa tunda kaine jagaba atafiyar

Harararta yayi zahra ki daina wannan maganar, ni bawai bazan bada ba, idan na bada ai ba faduwa nayi ba, duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai ji ?ansa, ga lada da mutun zai samu, kawai dai ni bani da kuWinne Yanzu..... ya fada yana soso keyarshi.
da zolaya zahra tace hmmm, Ana fa ba musulma bace, ta ina zamu samu lada idan muka taimake ta ?
Banza yayi da ita baice komai ba, Aneelerh tace babu ruwanmu da wannan, don Allah zamuyi da kyakkyawar niya, kidaina wannan tunanin gyaWa kai zahra tayi shikenan naji, zan bata wani abu cikin kuWin dana samu, Mahboob Idan kana da acct number dinta ka tura min Aneelerh tace Ina da ita, Idan muka koma Waki zan tura maki, Nima zan sanya nawa kudin
Farin ciki ne tsantsa akan fuskar mahboob, Yaji daWi zasu taimaki Ana batare da ko sisin shi ba.
 Allah yabarmun ku sisters dina, zahra Allah ya baki miji nagari mai sonki mai ?aunarki, and aunty Aneelerh ubangiji Allah ya bayyanar mana da mijinki da ?an uwansa , Allah ya raya mana baby junaid dinmu.... addu o i yadinga yi masu suna amsa mashi da ameen, kafin Ya juya zai fuce daga kitchen din
 Mahboob kiran sunanshi da Aneelerh tayine ya dakatar da shi daga yin tafiyar ya waiwayo yana kallonta
 Please idan ka fita ka faWama su mami, zuwa anjima Hajiya adama zata zo kawo mana baby junaid nasan bata sanar da ita ba

 Aunty Aneelerh ashe yau muna da babban ba?o agidan namu, mutumina zai dawo, zamu dasa daga inda muka tsaya

Murmushi Aneelerh tasaki, zahra tace wallahi har na kosa in ganshi,Yau zaisha da?una duk saina sale mashi fatarshi Aneelerh na murmushi tace inaso zamu shirya masu abincin da zasu ci, tun da Ana bata jin dadin zuciyarta mubarta ta huta sai muyi aikin atare

Zahra tace Lafiyalou, dama na kwana biyu banyi girki ba, har cake zan haWama baby junaid dina

Sun jima suna yin fira a kitchen kafin daga bisani suka fuce zuwa Wakin domin yin sallar azhar da aka fara kira.


*OBIE ESTATE


Idan muka koma 6angaren dattijon arzi?i, tunda garin Allah ya waye Hankalinshi ba akwance Yake ba, gaba Waya yabi ya furgice masu sun rasa gane kanshi, ko jiya da dare bai runtsa ba, sambatu yadinga yi masu yana firgita yana fadin ga macijij nan zai sare shi, Ina owais dinshi Yana gani za a cutar da shi bazai kashe macijin ba, mutun biyu da suka taya shi kwana a Waki his excellency Deen ne tare da His excellency abdul razak, su kansu basu yi bacciba jiya saboda halin da baban nasu yake aciki, hatta sallar asuba agida sukayi ta ya?i fita daga Waki, kuma ya hana su tafi subarshi, bawan Allah ba ?aramin jiki yaji ba, hada ruWun tsufa ke damun shi, da?yar suka samu nasarar sanya shi yin baccin dole.??

A yanzu haka Yana daga kwance saman gadonshi Ya Waura kanshi kan pillow, deen da Abdul razak suna a zaune saman arm chairs din dakin idanuwansu akan fuskar baba obie.
Jin motsin buWe kofane Yaja hankalinsu ga kallon mai shigowa
Senate lateef ne, fuskarshi babu walwala.
Daren jiya da damuwar abunda ya faru ya kwana
Mi?a masu hannu yai suka gaisa da ?an uwan nashi
Kafin ya dubi baban nasu dake kwance kan gado yace Bacci yake yi ko idon shi biyu ?
His excellency Deen ne yace bacci yake yi, da?yar muka samu Ya runtsa ajiyar zuciya senate lateef ya sauke kafin yace banji dadin abunda ya faru jiya ba, gashi har yana neman zautar mana da mahaifinmu, wai taya ma akai har maciji ya shigo part din nan ? Rai amatu?ar 6ace yayi maganar
His excellency Abdul razak Yace abun da yafi Waura min kai shi Owais din Yace ba maciji bane mutunne ya rikiWa.... tunkan Ya ?are maganar Senate lateef yace inko dagaske ne wannan maganar to kuwa ba mutun bane dama, Aljani ne sannan ita wannan ifritun yarinyar mai kasada dana gani atare da shi wacece ita! ? Kafin wani ya bashi amsa sallamar Pravin ta katse masu hanzarinsu,
Shigowa yai cikin shiga ta black suit.

Cikin girmamawa pravin ya gaishe da su, bayan sun amsa masu fuskokinsu babu walwala, pravin ya soma yin magana
 Baba bashi da lafiya ne? naga da asuba bai halarcin masallaci ba
 Baka ga abun da ya faru jiya bane ? Acewar senate lateef.

 Nagani, kar dai ace shi ne ya hana shi sukuni ? Cikin nuna kulawa yayi maganar.

His excellency abdul razak Yace ai kuwa dai shine, don jiya ko bacci baiyi ba tsabar firgici, yanzu haka ma da kake ganin shi a kwance da?yar muka samu yayi bacci
 Abu baiyi daWi ba pravin ya faWa yana Wan girgiza kanshi ubangiji Allah ya bashi lafiya atare suka amsa mashi da Ameen.
Senate lateef ya Waura da cewa ni yanzu so nake naji daga bakin shi Owais, ya faWa min wanene macijin menene ala?ar shi dashi
 Bari na kira shi awaya, ai jiya yace zai shigo yai mana bayani amma shiru kake ji wai malam yaci shiru Deen ne yai maganar tare da curo wayarshi daga aljihu ya danna ma Chif Owais Kira, kusan sau uku tana yin ringing bai yi picking ba.

 Bai Waga ba, may be baya akusane da wayar ya fada yana kokarin maida wayar cikin aljihun, kwatsam kiran owais ya shigo wayar tafara ruri, ajiyar zuciya ya sauke tare da duban su yace shi ne ke kira, ya fada tare da yin picking din kiran Ya kara wayar a kunnanshi, bayan sun gaisa deen yace muna ta tsammanin zuwanka gida shiru baka shigo ba, ga babanku nan kwance ba lafiya saboda abun da ya faru jiya ko runtsawa baiyi ba sai firgita yake yi .

On the other hand chief Owais ya furta I will come later, insha Allah,

 Okay, we ll be waiting for you, sannan inason sanin Ina macijin nan yake? Naji kace mutunne
Muryar chief owais tamkar bai son furta maganar yace please uncle can i text you deen yace okey ba damuwa , rejecting call din yayi, kafin wani ya furta magana ?arar shigowar sa?o Ya dakatar da su.

Karanta sakon Deen ya soma yi duk sun ?ura mashi ido suna jiran jin me zaice masu, musamman pravin har wani zo?a kai yake yi yana le?en wayar Deen.

?agowa yai da alamun mamaki akan fuskarshi yace tabWijancan, wallahi dagaske macijin mutunne wai shaidanun aljanune a jikinshi, yanzu haka ya rikiWa ya koma mutun acan gidanshi yake zaune,........ aruWe suke kallon shi.

 Wai ko kunsan Prime minister namu shine ya tura da jet din da zai Wauko sheikh imam daga sudan saboda kawai ya taimaka ma macijin ya dawo halittarsa ?
Jin wannan maganar ba ?aramin firgita senate lateef yayi ba ranshi a6ace ya furta what? Bangane me kake nufi ba! Yaushe akayi hakan?batare da sanin mu ba! a kausashe ya furta maganar,, a sukwane his excellency abdul Razak Ya mi?e Yana fadin Anya ka karanta sa?on nan dai dai, bani wayar na duba, ya furta hakan tare da kar6ar wayar Deen Yana duba sakon, bayan ya gama yace ba shakka, kuwa owais dinne ya rubuta da kanshi, magana ta tabbata prime minister namu shi ya tura da jet din daya dauko sheikh imam daga sudan don kawai a duba yaron, muna nan zaune muna jinyar ubanmu shi yana can wajen taimakon yaron da bamusan wanene shi ba, bamu haWa ala?ar komai da shiba, bansan meke damun prime minister ba, daga shi har owais din shegen son taimakonsu shi zaija su jefa family dinmu cikin matsala ...... kafin Deen Ya ?are magana senate lateef daya gama fusata yana huci yace Wallahi basu isa ba, ni bani bu?atarma jin wani ?arin bayani daga garesu, Yaron nan bazai zauna a estate dinmu ba, tunkafin aje ko ina harya fara mallake zuciyar Wan uwanmu hakan na nufin da wata manufa ya shigo family dinmu, zai iya yiyuwa wasu mugayen ne daga ma?iyan jam iyarmu sukayi amfani da shi don su tarwatsa family dinmu, ku duba kuga fa duk gidajen dake a estate dinmu bai shiga kowanne ba, Ya tsallake nasu Ya faWo gidan babanmu saboda shine target dinsa..... a harzu?e senate lateef Ya ?are maganar.
Kanwa uban ?an Zigi Pravin Ya haWe girar ?asa da sama yace Ni dama tun Jiya hankalina bai kwanta da shigowar macijin nan ba, Ai daga jin yadda abun ya faru zaka shaida makircine aka shiryama baba, so suke kawai su kashe shi, in ba haka ba taya za ai ace wai mutun ya koma maciji ai sai dai idan sihirine da shi, munafuki kawai wallahi bazamu yarda ba, Yaron nan bazai zauna mana a estate dinmu ba, dole ne owais Ya kore shi daga estate dinmu, sannan A yanke ala?arshi da kowa na family dinmu idan ba haka ba zaija mana masifar da bazamu Iya shawo kanta ba Rai a6ace pravin yayi maganar Yana kallon fuskokinsu.

Jinjina kai kowan nan su yayi alamar gamsuwa da bayanin pravin,
His excellency abdul razak Yace Ai bazamu ta6a yin gangancin nan ba, mu jira owais din ya shigo anjima, shima hateem din Zanyi waya da shi
Pravin yace  yamakata atara kowa har shi kanshi yaya sharafuddeen din yazo yaji abun da owais ke shirin janyo mana a family, wallahi jiya Saratu batayi bacci ba, saboda fargabar macijin nan, sambatu ta dinga yi min tana kuka tana fadin gashi nan zai sareta, duk tabi ta haukace ta rikice min aWaki, da?yar nashawo kanta da ayar Allah
AruWe Senate lateef yace kunji ko? Tun yanzu ana kokarin ganin bayan ahlinmu
Damuwa ?arara akan fuskar Deen yace Pravin kana nufin saratu batayi bacci ba jiya saboda macijin ? Batare da War ba yace bata yi ba yaya, yadda taga rana haka taga dare, ni na zauna ina yi mata fifita saboda zufar dake tsastsafo mata gafa ac a daki amma haka ta dinga zubda gumi
Hankalinsu ba ?aramin tashi yai ba, gaba Waya sunyi amanna da maganar pravin
Murya na rawa his excellency abdul razak Yace Yanzu awani hali take ciki? Tayi bacci da safe?
Girgiza kai pravin yai fuskarshi da alamun jimami yace batayi ba idonta biyu ko abinci takasa ci,
 Inason ganinta pravin acewar abdul razak
Pravin yace toh, bari naje nazo da ita ya juya jiki na 6ari ya fuce daga Wakin.

Yana fitowa daga dakin su ka yi kici6us da Hajjaty, ta Wauki wankan bubu gown ta lace a jikinta, ta ca6a uban ado, ?amshin turarenta ya buWe ko ina, mayafin rigar asaman kafaWa ta daurashi, doguwar suman kanta ta zubo har gadon bayanta, Hannayenta biyu ru?e da faffaWan tray daga saman shi an Waura jerin kayan abinci.
Wani mugun kallo da pravin ya watsa mata saida gabanta Ya faWi, duk tabi tasha jinin jikinta, sarai tasan ya hanata yin kwalliya idan har bashi zatayi mawa ba amma ta?i jin maganarshi.
Sai faman ?yaf?yafta idanuwanta take yi, tayi mashi kyau sai dai yaji haushin adon data ca6a.
 Kin manta gargaWin da nayi maki? Baki jin maganata ko ? muryarta na rawa ta furta am sorry dear, na saba ne guntun tsoki Yaja  yanzu ahaka zaki shiga dakin obie, bayan kinsan bashi kaWai bane aWakin, Balagaggun ?a ?ansa duk suna aciki, duk kamun kansu bazasu iya jure sha?ar ?amshin turaren jikinki ba batare da kin jefa su yanayi ba, ko kallon ki su ka yi sai sun ayyana wani abun aransu.... shiru tayi mashi ba tare da tace komai ba, numfasawa yayi kafin ya Waura da cewa bazan bari ki shiga Wakin ahaka ba, sai dai ki ha?ura da kai masu abincin ki koma Waki ni sai in kai masu

muryarta tamkar zata fashe da kuka tace dan Allah dear ka barni in kai masu, Jiya fa bansamu damar gaishe dasu ba da shagwa6a tayi mashi maganar, nan take kasala tafara kama shi, matsawa yayi dab da ita, ya ru?o mayafinta data Waura kan kafaWarta, ya janyoshi zuwa saman kanta ya lullu6e mata sumar kanta da kirjinta saboda yana jin kishin agane mashi majiyar dadin shi, ?o?arin manna mata kiss yayi saman red lips dinta, kamar daga sama yaji ance Daddy! A firgice pravin ya Wago yana faman zazzare idanuwanshi Jin muryar zayn, su biyune hannayensu ru?e cikin na juna shida Zaid, fuskokinsu da alamun ruWani, kafin ?arasowarsu pravin yayi saurin Waukar juice dake acikin jerin drinks din tray din hannun hajjaty ya buWe murfin ya watsa mata ruwan lemun gefen galenta, baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, mugun tsoron Zayn take yi, tasan muddin ya gane abun da pravin ke ?o?arin yi mata sai ta yaba ma aya za?inta, ajiya juice din pravin yayi, ya dai daita natsuwarshi, ya nufesu fuskarshi dauke da murmushi ya ware masu hannayensu da niyar yayi hugginsu dinsu,
Sai dai sun?i bashi haWin kai, wani irin matsiyacin kallon zayn yake watsama hajjaty data juya masu baya.

Adabarbace pravin yace kun ganmu atsaye ko? na fito daga Wakin baba ne na bankaWeta batare dana ankara ba kallon tuhuma Zayn yayi mashi kafin yace daddy mayafinta fa naga ka ru?e a hannunka akan wani dalili
 Baka ji mena ce ba, bugeta nayi har tray din hannunta ya girgiza lemu ya 6arar mata jikin gyalenta shine fa na ruko gyalen ina ?o?arin goge mata yayi maganar tare da juyawa ya ru?o bakin gyalen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login