Showing 48001 words to 51000 words out of 260999 words

Chapter 17 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

suka Waure masu kai, Komai suka gani sai sun tambayi Angel menene shi? Lokacin da rana ta ?walo Kowannansu Ya zazzare idanuwanshi suna kallon Sararin samaniya inda rana ta hudo, Angel sai ?o?arin hanasu takeyi akan su daina kallonta, gudun kada hasken ranar ya kashe masu idanuwan su.

Bakomai yasa su yin hakan ba face tsantsar mamaki da al ajabi, su fa duk Waukarsu Fitila ce aka ajiye sama, kamar dai yadda ceiling Win Wakin su na kurkuku Yake, Parveen sarki kwa6a magana da ta gaza jurewa tace da Angel ta faWa mata tayaya akai har aka Waura fitilar sama? Ita bata ta6a ganin fitila mai hasken ta ba, Dariya Angel tasaki tare da cewa Kai parveen Nafa ta6a faWa maku saboda gudun haka, Rana ce wannan da kuke Gani, Babu wanda ya Waurata Yana daga cikin halittar ubangijin mu Allah, bayan ita akwai Wata da taurari suma duk Allah ne ya halicce su, Idan Dare yayi zan nuna maku su, taci wahala wurin wayar masu da kai da?yar ta samu suka fahimce ta, kusan saida ta maimaita masu karatun data koya masu tukunna suka Iya tunawa, A ?alla sun shafe awanni suna kutsawa cikin Dajin babu alamun zasu shigo cikin Garin, Wani irin kurman Dajine ta ko ina acunkushe yake da tsirrai.
Gaba Waya sun gaji da tafiya, Dama jikinsu bai saba da wahala ba, Ga6o6in jikinsu duk sun raunata, Mutun Biyune basu jikata ba, Jemimah da Azeezah, hankalinsu kwance Har bacci ya Wauke su a goye sai daga bisani suka farka,
 Wlh mun gaji Angel, Wai haka zamu dinga tafiya ba tsayawa? ?afafuwana duk sun rurru?e, Ga yunwa inaji Parveen ce tayi maganar,
 Ya ki ke so muyi parveen dole muyi tafiya da da halima hada gudu, in ba haka ba zamu ?are acikin Dajin nan ne, fuskar Angel ayamutse ta yi maganar,
Danish duk yana sauraronsu, hankalin shi na akan Haris daya ru?e.
Parveen ta hanasu sakat, don dole Naufal Ya goyata abayanshi, Jemimah hada tsokanarta ?atuwa dake dole sai an maki goya irin namu Harara parveen ta watsa mata. Ba tare da tace komai ba.
Zogin da ?afafuwansu suka fara yi masu ne yasa suka yada zango agaban wata ?atuwar bishiya suka zazzauna suna faman yin haki, Gorar ruwa parveen ta curo masu, Bayan tasha ta mi?a ma Naufal yasha ya mi?a ma Hannah, sai dakowa yasha ruwan, Sun natsu suna faman lumshe idanuwansu,
 karfa kuyi mana bacci anan, bamu gama tafiya ba, naga kuna rufe ido, Angel ce tayi masu magana, Fuskar Parveen atur6une tace kaWan zamuyi,  batul Ta natsu tana kallon Bishiyoyin dake a kewaye dasu,

 Angel Su waWannan basu gajiya da tsayuwa ne !? Fuskar ta aWaure tayi maganar babu alamun wasa
 Su wa kike nufi Angel ta tambaya tana kallon fuskar Batul, Da hannu ta nuna mata Bishiyoyin dake fuskantarsu, ?an zaro ido Angel tayi tare da kallon Danish dake kallon fuskarta, kiris ya rage ya saki murmushi jin wautar Batul. hankalinta a kwance taci gaba da cewa tun da muka taho suke ta tsayuwa babu motsawa, Itama rana sai binmu takeyi da gudu duk inda mukayi sai na ganta, to wai su basu gajiya ne ? Kalamanta sun rufe ma Angel baki ta kasa bata amsa, da?yar ta iya cewa Haka Allah ya Halicce su Batul

Gabriel da ya ?umshe dariya abakin shi yace da ita ke yanzu idan waWannan bishiyoyin suka motsa zaki tsaya? Har kina da bakin cewa Basu gajiya da tsayuwa ? Sai lokacin ta Wan saki murmushi ba tare data kalle shi, shiru su ka Wanyi na wani lokaci, Har bacci ya fara ?o?arin Waukar su Jemimah ta fara ambaton fitsari take ji, ?aukarta Angel tayi tare da mi?ewa ta kalli Danish Zanje nakaita tayi fitsari, lumshe mata ido yai tare da cewa No, basai kunje nesa ba, Zata iya yi ko abayan bishiya ne Amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi bayan bishiyar da ita, bayan sun dawone tace dasu su tashi suci gaba da tafiya kada dare yayi masu anan, Mi?ewa su kayi jiki duk ba ?wari, Ta maida goyan Jemimah gabriel ma ya goya azeezarshi suka dasa da tafiya.

Allah ya tsare su tunda suke tafiya babu wata muguwar dabbar da suka ci karo da ita, Sai dai sautin koke kokensu da suke ji acan wani sashe na Dajin, Sunyi nisa da tafiya kwatsam Ba zato ba tsammani Akuya ta faWo wurinsu kamar an jehota, a matu?ar figirce suka watsa da gudu cikin dajin duk su ka tarwatse saboda tsabar firgitar da su ka yi.

Hankalinsu Danish ba ?aramin tashi yai ba, babban abunda suke jima tsoro kada wata dabbar ta handamesu, Mutun biyar ne suka watse waWanda suka rage Danish ne sai haris shima saboda Ya ru?e shi ne ya kasa guduwa, Gabriel dake goye da azeeza sai Jemimah da Angel, Basu ta6a ganin akuya ba sai yau, shiyasa Suka watse, mun shigo uku Danish! Ya zamuyi? Angel ce ta ambaci hakan, Bai amsa mata ba ya kwantar da Haris jikin bishiya da gudun gaske ya faWa Cikin Dajin don Ya tattarosu.
Jemimah ta ?an?ame angel sai satar kallon akuyar take Yi, ta yi tsaye tana Lasar baki, Ciyawar dake awurin take Ci,
Ran Angel ya 6aci, Duwatsu ta tsinta a kasa ta dinga jifar akuyar, Da gudu Ta watsa tana kuka, Sautin dariyar Jemimah ne ya karaWe kunnuwansu
 Genie ashe ma matsorayaci ce, wai wannan abun su Batul suke ma gudu, ni sun bani dariya, Ko kunya ma bata ji tana yawo zindir babu kaya a jikinta, ?an nonuwanta azube kamar na tsohuwa, Genie itama mutunce kamar mu ko ? shiru Angel bata tanka mata, Damuwace ?arara akan fuskarta, Hankalinta ba zai ta6a kwanciya ba idan har ba adawo dasu Batul ba.
Azeeza tana a la6e saman bayan Gabriel, Muguwar matsoraciya tun da akuyar nan ta faWo wurinsu Ko yatsanta tagaza motsawa, Numfashinta ma a dabarbarce yake fita, Jikinta sai kakarwa yake yi, ba dan Allah yasa tana a goye a bayan Gabriel ba kuma ya Waureta da mayafi da kuwa Silar 6acewar azeeza kenan acikin Daji, Allah kaWai yasan inda zata kutsa kanta saboda tsoro.
 Shiru basu dawo ba Angel, Ni inaga zan bi bayan Danish ne Gabriel yai maganar, da sauri tace A a, Kada kaje ko ina, Inaji araina zasu dawo atare, nasan duk inda suka shiga Danish zai nemo su

Haris dai Yana a langwa6e jikin bishiya, suna cikin jimamin rashin ?an uwansu, suka soma Jin takun tafiyarsu da sauri suka Juya baya suna kallon su, a jere su ke tafiya suna tunkaro su, abun da zai baka mamaki Hada naufal da javed su da suke maza, Batul na aru?e da hannun Hannah, dana Parveen Sai haki sukeyi sun hada uban gumi, Danish na abiye da bayansu, Tunkan su ?araso Angel ta fashe da dariya hada dafe cikinta, Hatta Gabriel dariyar yake yi masu, hakan ba ?aramin ?ona ransu yai ba.

Ko da su ka ?araso zazzaga masu masifa Naufal ya shiga yi yana fadin meyasa basuyi masu bayanin cewe akuyace ba, ae su basu son suffarta ba, iya namanta da suke ci ne suka sani, Sai da yayi mai isarshi parveen ma ta Waura da nata faWan akan dariyar da suke yi masu, sauran dai basu ce komai ba, Ru?o haris danish yai tare da taimaka mashi ya mi?e tsaye. Zuciyarsu Naufal a jagule suka ci gaba da tafiya, Rayuwarsu ta daji gwanin ban sha awa, Ga cin dariyar kwa6ar su batul komai basu sani ba sai Angel tayi masu bayani, idan dare ya tsala gefen bishiya Danish Yake yi masu shimfiWa, bayan sun kwanta Yabi su da barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji Ya samo itace ya haWa masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan Danish bai runtsa ba, Su kaWai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima, basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan Watansu Waya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya Waga hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare ya nutsa bacci ya Wauke su Waya bayan Waya ya ke Waukar su Ya nutsa dasu Cikin dajin ya yi tazarar tafiyar awanni dasu, basu ta6a lura da hakan ba, duk don ya sau?a?a masu wahalar tafiyar, shiyasa ya ke yi masu hakan, don kuma su yi gaggawar barin Dajin, Don ya fara Jin alamun wani ba?on Yanayin a jikin shi, fargabarshi kada Giant s heart Winshi ta motsa batare daya Nisantu daga dajin ba.

*PRISONERS=ؔ?*


Dare Ya nutsa sosai suna akwakkwance suna bacci, Hasken Wutar Dake Ci Ya haskaka zagayen wurin da suke, yana a Zaune gaban wutar idanuwanshi akan shimfiWarsu, Sai faman lumshe idanuwanshi Yake yi, ga dukkan alamu baccine yake ?o?arin fuskarshi.

Angel da ke a kudundune cikin bargo ta?i runtsawa duk don saboda shi, ta kasa samun natsuwa, Yaye bargon tayi tare da fitowa daga Ciki Ta mi?e tana mi?a ta nufi inda yake zaune, Tunkan ta ?arasa taga yana gyangyaWi ?iris Ya rage ya kifa kanshi Cikin wutar dake agabanshi da gudun gaske Ta ?arasa tare da zubewa gefen shi saman gwiwowinta, da hannyenta biyu ta tallabo fuskarshi tana bin shi da kallo, Sam ya gaza buWe idanuwanshi sunyi mashi nauyi, rungume kanshi tayi saman kirjinta, idanuwanta suka ciko tab da ?walla, tsananin tausayinshi take ji.
 Danish muje mu kwanta, muryarshi ?asa ?asa ya furta mata bazan iya bacci ba Angel idan har ba barin Dajin nan mukayi ba, Ina jin fargabar wani abu ya same ku ta silar rauni na ?ara ?an?ame shi tayi a jikinta In sha Allah ba abunda zai same mu Danish, Allah Yana atare damu, Kuma Inayi mana addu a, Kada kaji komai kazo mu kwanta, rashin yin baccin zai Iya ja maka wata matsalar da bana fata A hankali ya zagayo da hannayenshi saman waist Winta, kafin ya lumshe idanuwanshi. Jin shiru bai ?ara motsi ba yasa tayi tunanin ko baccin ya Wauke shi ne, Kiran sunanshi tayi Danish amsa mata yai Na am cikin kulawa tace dashi nayi tsammanin ka fara baccin ne, pls kayi bacci Danish, inaso ka huta, bana so kana wahala daWin murya yake ji acikin kunnuwanshi, har baison intana magana tadaina, Yafi son taita yi mashi surutu.
 Danish naji ka yi shiru baka ce komai ba ? Har saida ta fidda rai da zaiyi mata magana tukunna taji yace Angel ni wannan ba damuwata bace, i ave told u duk wahalar da zanyi indai akan ku ne bana gajiya, ke ce ?warin gwiwar da nike da shi Angel  murmushi tasaki idanuwanta akan Kitson zanan dake akanshi,
 FaWamin me ka ke ji akaina? sannan Meyasa kake ?aunata? Ta yi maganar tare da ?aura yatsun hannunta saman kanshi, tuntuni ta ke son ta kwance mashi kitson da akayi mashi a prison don bata son ganin shi da kitso kamar mace tafi son ta ganshi a Namijin shi.


 Nikaina bansani ba amsar daya bata kenan,
?agowa yai da kanshi tsinin hancinsu Ya haWe jikin na juna, Hasken wutar dake cine ya haskaka fuskokinsu
Hakanan Taji gabanta na faWuwa, ganin launin idonshi na canza mata, duk tabi tasha jinin jikinta, ?warjini yayi mata da sauri ta kawar da idonta gefe Waya
 Abu Waya nake fargaba a duniyar nan! Shi ne ace za a raba ni da ke! Dawo da dubanta tayi akan fuskarshi, jaddada mata maganar shi yai Zan iya komai a wannan lokacin,
 Maganar raba ni da kai ma bata taso ba Danish, dani da kai tamkar anta da jini ne, mutuwace kaWai zata Iya raba ?aunar dake a tsakanina dakai, Amma agidan duniya bani da madadinka kalamanta sun Wan sanyaya zuciyarshi,
 Ina tsoron ranar da zaki Canza min, duk da bana kawo hakan araina, Angel wani zai Iya ?wace min ke, kinga ni bani da komai da zan iya faranta maki da ya wuce kaina Muryarshi araunace yai maganar.

?aure mashi fuska ta yi  Danish zaka Iya bari wani ya ?wace maka ni ? Girgiza mata kai yai alamar a a, ya ?ara da cewa Sai inda ?arfi na Ya ?are, 

Lumshe ido ta Wan yi calmly ta furta  Yadda muka sha wahala atare Danish, Haka nake so Mu ji daWi atare, Bani da abokin rayuwar daya wuce kai a faWin duniyar nan, Kaine mallakina, masoyi na har abada, ta ya ya kake tunanin zan iya canza ma ka? Ai kaine nake tsoron Ka canza min idan mun shiga Cikin gari, saboda nasan mutane da yawa zasu dinga rububinka saboda kyawun Da Allah yayi maka, Sannan bansan su wanene Iyayenka ba, amma inaji araina ba ?ananun mutane bane yadda kake da kyan nan da izza Wabi unka sak Irin na ?a ?an Hamsha?an masu kuWi ne, Ni ko ka ga ba ?ar kowa bace, Mahaifina Wan Jarida ne kuma ya rasu ma,  Idanuwanta acike tab da ?walla tayi maganar, ?wallar na gangarowa saman kuncinta yai saurin sanya tongue dinshi Ya lasheta, nan ta ke ta ji yanayin jikinta ya fara canzawa.


 Ni bani da iyaye Angel, Ki daina yi min maganarsu bana son ji, ke ce uwata kuma kece ubana, Kece gatan da nake dashi, Idan ina dake bani bu?atar kowa, muryarshi a kausashe yake yi mata magana, Ta fahimci bayason zancen Iyayen shi da take yi mashi.

 Meyasa bakason Inayi maka maganar iyayenka? Danish Salsabeel ya faWamin tun kana jariri aka sadaukar dakai, Naji raWaWi jin hakan acikin zuciyata, sai dai Ni bazan Iya yankewa iyayenka hukunci ba, Kada ka manta sadaukarwar kurkukun ?addara ba dole sai iyayenka ba, zai iya yiwuwa ba sune suka sadaukar dakai ba, wata ?il ma basu da masaniyar kana araye.... bai bari ta ta?arasa maganar ba yai saurin toshe mata bakinta da tafin hannun shi Is ok, Kije ki kwanta dare Yana ?ara yi, ma?e mashi kafaWa tayi Idan Kaga na kwanta toh muna atare da juna ne, kafiya ta sanya mashi ya rasa ya zaiyi da ita, A ?arshe dole Ya ha?ura Ya ?yaleta, kwantar dakanshi yai saman ?irjinta, Taci gaba da kwance mashi kitson kanshi, Kafin bacci Ya Wauke su saida ta warware kitson duka, A manne da juna suke ta sharar baccin su, Karo na farko da ya fara runtsawa Acikin DajinW'W'W'


*Boss Bature
'? Mu haWu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*KURKUKUN ?ADDARA*_



_The Prisoners E10=?%?=ث?_


*Daga al?alamin Boss Bature*


~Middle step~



_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty=ؔ?._





A Kwance ya ke saman shimfiWeWan gadonsa, Kamar kullum cikin shigar larabawa, hannun shi a ru?e da wayarshi, Ya ?urawa Hoton wallpaper Win shi ido, ko ?yaftawa bai yi sam baya gajiya da kallon hotonta, Yanayin fuskarshi Ya nuna tsantsar damuwa, a hankali ya Waura yatsun shi saman hoton kan wayar yana shafa fuskarta, lumshe idanuwanshi Ya Wanyi kafin a hankali ya ware su kan hoton, wa?ar larabci ya soma rairawa da daddaWar muryarsa duk akan hoton wadda ya ke kallo, ya dage yana yi mata wa?a mai nuni da ?aunarta da yake yi, Tunawa da bata a raye yasa shi dakatawa da raira wa?ar, Ya jefar da wayarshi gefe Waya saman mattress Win, haWi da kifa kanshi saman pillow, kamar ?aramin yaro ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, abun ne yana damunshi ya hana rayuwarshi sakat.


 Shureim, Ka yi ha?uri Ka daina sanya damuwa aranka, I know it hurts you, but worrying won t make anything better, it ll only make things worse kuma ka tuna Allah yanasan bayinsa masu tuba, Kana fa da ilmin ka ba sai na tunasar da kai ba,

bai tsammaci jin muryarta ba, A hankali Ya Wago da idanuwanshi WaWanda su ka kaWa jawur da su, ya Waura su kan fuskar Zainab.

Tana a tsaye cikin shiga ta riga da skirt, kanta sanye da hula, ga dukkan alamu daga kitchen ta fito.

 Babu wanda yasan nashigo shureim, Satar hanya nayi don nasan idan hajiya layla ta sani ba za ta bar ni in zo wurin ka ba....... numfasawa ta Wanyi kafin ta Waura da cewa Tuntuni na so mu samu lokaci muyi magana sai dai ban samu damar yin hakan ba saboda baka nan, till today har cikin zuciyarshi ba ?aramin sanyi yaji ba, yun?urawa yai tare da mi?ewa ya zauna ya jingina bayansa jikin headboard din gadon Yana kallonta, Still hawaye basu daina wanke fuskarshi ba, Zainab ta damu dashi sosai, har mamaki ta ke yi yadda wasu iyayen Allah ya basu damar haihuwar ?a ?a nagartattu amma suke watsi da su, basu damu da damuwar su ba, yayin da wasu neman ?a ?an su ke yi ruwa Ajallo, tana matu?ar jin takaicin haka.

 Aunt Zainab, Kin tabbata ba wanda yasan kin shigo? Ina mommy da daddy ne
 Layla tana a palour, mahaifin ka kuma Yana a garden shi da kawunka Musa Jin hakan Yasa shi saukowa daga saman gadon shi Ya nufe ta, tsayawa yai suna fuskantar Juna.

 Ka faWa min wani taimako ka ke so In yi maka? in sha Allahu babu abunda zai gagara, a shirye nake da in share maka hawayen ka

Hannayen ta biyu ya ru?o a cikin nashi gabanta sai faWuwa ya ke yi, tsoronta kada wani daga cikin Iyayenshi ya faWo Wakin, muddin hakan ya faru zata WanWani kuWarta ne.

 Aunt Zainab I feel in


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login