Showing 177001 words to 180000 words out of 260999 words

Chapter 60 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ya fadi ?asa, da sauri ya Waga ido sama don ganin wanene ya wurgo mashi pillow saman bayanshi, karaf idanuwan shi suka sauka akan Danish dake tsaye can second floor, hannun shi ru?e da wani pillown Yana niyar ?ara jeho mashi, fitowar shi kenan daga Waki idanuwanshi suka hango mashi Angel Winsa rungume da wani ?ato, shine fa yaje Waki ya Wauko fululluka har biyu Ya jeho mashi Waya.

Ya haWe fuska babu annuri, kayan bacci ne ajikinshi riga da wando launin pink sunyi bala en yi mashi kyau.

Harara ya watsa ma boss man, ganin Angel taki barin ?irjin mutumin yasa shi ?ara daddagewa ya wurgo mata pillow, da sauri boss man Ya tarbe pillown a hannun shi, Lamarin ya Waure mashi kai, sai yanzu ya gane dalilin dayasa yaron ya?i sakar mashi fuska tun jiya yake daure mashi fuska, ashe kishi ne ke damun shi.

 Unaisah ! Jin boss man ya ambaci sunanta yasa ta Wago da kanta tana kallon shi, mamaki ne ya kamata ganin pillow a hannun shi, da ido yai mata nuna da bayanta, da sauri ta juya don ganin wanene, a tsaye ta hango shi ya ru?e qugu yana aiko masu da harara.

Batasan sa adda ta tuntsire da dariya hada dafe ciki,
da zolaya boss man yace kishine ya addabe shi shiyasa yake jifar mu da pillow, faWa min meke a tsakaninki dashi.

Tana dariya tace babu komai, sha?uwace a tsakaninmu, baya son yaganni tare da wani idan ba ?an uwanmu ba, haushi yake ji

 Kice ?wara in lalla6a in gudu, tunkan ya sauko don wannan har buguna zai Iyayi,  ya fada tare da dam?a mata pillow din hannun shi, Ya juya da sauri ya nufi ?ofar fita Yana faman sakin murmushi, bai ta6a ganin namiji mai kishi ba irin Danish.

Zukunnawa tayi ?asa ta Wauki Wayan pillow, ta haWa dana hannunta, ta nufi upstairs, Har tsoron tunkarar shi take Ji, saboda yadda ya kumbura fuska, soft red lips dinsa sunyi suntum da su
Koda ta haye up din, taga Ya dun?ule hannu kamar zai nausheta, wurga mashi pillows din tayi saman faffadan kirjinshi, da gudu ta sauko down tana ti?ar dariya, akan idonta ya tattara pillows din ya nufi dakinshi ya shige.

Yau da wuri suka yi breakfast dinsu, saboda gyaran jikin da ummi zatayi masu.

A Katafaren Home beauty station Win dake a cikin part dinsu, saboda su aka tadani komai na cikinsa, Wakin Ya haWu, bangon dakin beauty shelf ne An jera Kayan gyaran jiki kala kala, dana gyaran gashi acikin kowani shelf, hada foot care product and skin care product, Ga wani faskeken mirror a jikin bango, daga gabanshi wasu hadaddun kujerune kusan guda takwas, A saman kujerun kowa Ya samu wuri Ya zauna su shidda ne matan dake acikinsu, banda mazan tun bayan da suka kammala yin breakfast suka tafi Waukar karatu a inda suke Yin sallah. Suma matan acan za a dinga yi masu karatu.

Kowaccensu tana sanye da bathrobe a jikinta, Ummi ce ta basu rigunan, saboda da taji daWin gyara masu sumar kansu.

Kujerar farko Unaisah ce zaune asamanta, ta biyu batul ce akusa da ita, sai Parveen itama ta hakimce saman tata kujerar, daga gefenta Jemimah da Azeeza ne saman nasu kujerun bayan su sai Hannah.

sun natsu suna kallon faces dinsu ta cikin madubi sai faman sakar ma juna murmushi suke yi kamar wasu zautattu, daWi suke ji za a gyara masu sumar kansu, har sun fara imaginning din kyawun da zasuyi

babu mai magana acikin su, saboda ummi tana acikin dakin ta hanasu surutu

tana a sanye da dogon wando ?ar rigar data sanya da?yar ta rufe cibinta, babu mayafi akanta.

 Dawa zamu fara ta faWa tana dubansu, har suna haWa baki wurin furta Ni,
 bari in za6a da kaina ta fada tana binsu da kallo Waya bayan Waya, a ?arshe ta tsayar da idonta Kan Unaisah da Batul, daku zan fara, saboda yawan sumar kanku saukowa su ka yi daga saman kujerun, ta juya ta nufi Corner din da Sink Yake, gefen shi beauty cabinet ne mai Wauke da jerin shampoo da conditioner da suran mayukan gyaran gashi.

Taci ba?ar wahala wurin gyara masu gashi, musamman mutun biyun nan Unaisah da Batul, saboda yawan gashinsu ga tsawo, da ruwan zafi ta jika sumar bayan ta ji?u ta shafa shampoo ta cuccuWa ko ina na gashin, bayan ta wanke shampoo din ta sanya conditioner na tsawon mintuna kafin ta wanketa, tayi masu amfani da Hair dryer ta busar masu da sumar kansu, ta fara shafa masu smoothing serum ta Wauki comb taci gaba da sharce gashin, tunkafin ta kammala take santin kyawun sumar kansu, bayan ta gama sharce gashin ta kwarara masu hair oils kala daban daban saman sumar taci gaba da cuWasu da hannuwanta, tuni gashin ya ciza launin shi dark brown sai ?yalli yake yi da Waukar ido, ?amshin hair oils din data shafa masu Ya cika hancinansu.

Lokacin da suka kalli sumar kansu ta cikin madubi, Ihun farin ciki suka saki suna faman yi mata godiya tace su koma zu zauna, bata gama gyara masu ba, su Azeeza sunyi zuru suna jiran suma ayi masu, sai faman santin su Unaisah da Batul suke Yi har suna fadin suma kalar nasu za ayi masu.

Ummi tayi ?o?ari wurin gyara su, Yara kamar ?a ?an wani shege maiji da raina, saida tayi amfani da almakashi ta datse sumar kansu ta rage tsayinta ta dawo dai dai tsakiyar bayansu, hair style din da tayima Batul da Unaisah Triple twist half up ne, Bayan ta gama dasu ta bi sauran Waya bayan Waya ta wanke masu sumar kansu kamar yadda tayi masu Unaisah haka suma tayi masu banbancin wurin hair style ne, saida ta mi?ar masu da gashinsu ta hanyar yin amfani da Straightener, kafin ta Waure ma Azeeza da Jemimah gashinsu da ribbom guda biyu gefe da gefe wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaWunsu.

Duk wannan gayun da akayi masu, Jemimah bata gode ba, ta sanya rigima akan sai an maida launin gashinta kalar nasu Batul, Ummi taci dariya, bata ta6a tsammanin zata ji ?aunar yaran ba sai yau, su kansu sunyi mamakin yadda ta dage damtse wurin Yi masu hidima, Abu kamar wasa Jemimah ta fashe masu da kuka, ita damuwarta launin gashinsu Yafi nasu kyau, da ita da azeeza sumar kansu blonde ne kalar na turawa, ita Azeeza bata damu ba sai murna take yi an gyara mata gashi, jemimah daice ta matsa lamba, ummi harta fara tunanin ta canza mata launin gashin da yake suna da Hair dye cikin jerin Kayan gyaran gashin su, Unaisah ce tace abar mata launin gashin kanta, saboda yana dakyau ba lallaima idan aka maida mata kalar nasu yayi kyau ba, da?yar suka lallashi Jamimah tadaina yi masu kuka.

Tsawon lokaci kafin Ummi ta kammala Gyara su, hatta skin dinsu da akaifunsu da tafukan ?afafuwansu duk saida ta gyara masu, ko ina ka kalla na jikinsu saiya burgeka, kamar basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, tun bayan da aka gama kowannansu Ya koma bedroom dinshi, bacci mai nauyi ya dauke su, duk don saboda gyaran gashin da akayi masu kada Ya 6ace yasa suka kwanta ta rubda ciki.

*OBIE ESTATE*

Dan?ara dan?ara motocine masu numfashi suke ta kurWaWowa ta cikin babban gate din Obie Estate a ?alla sunkai goma sha wani abu gaba da bayansu motocin fusatattun sojoji ne sun mimmi?e tsaitsaye hannayensu ru?e da manyan bindigu, jiniyar motocin jami an ta karaWe ko ina na yankin, da matsakaicin gudu suka haura saman titin da zai sada da su da Airport, Motar farko zungureriya tana Wauke da dattijon arzi?i tare da Dr.Jaz, mota ta biyu sanate president lateef ne zaune a mazaunin baya shi da Iyalansa Hajiya madina da ya yan ta biyu Ziyad da zuhra, Mota ta uku Hajiya saratu ce a cikinta tare da twins zayn da zaid, da shi kanshi pravin din, Motar bayansu Sir mubarak ne tare da Hajiya Turai, daga motarsu sai ta sauran ?an uwa da abokanan arziki da suka hallara domin zuwa tarban babban ba?onsu, kowan nan su yayi shiga ta alfarma, mazan cikinsu shaddojine ajikinsu, matan kuma wankan abaya suka Wauka, har sun kusa isa Airport din ba zato ba tsammani suka soma hango wasu hamsha?an motocin daban sun biyo ta titin da zai jagorance ka zuwa Aso Villa, ?arshen HaWuwa ta glass din motocinsu suke hangen su, tunkafin suga su wanene acikin motocin ransu ya basu Mr.president ne tare da mu?arrabansa shima yazo tarban Wan uwan nashi, abun yayi matu?ar ?ayatar dasu, basu yi tsammani zai halacci zuwa Airport din ba, zuwan bazata yai masu, Motocin shugaban ?asa na ?arasowa suka haWe da nasu motocin Yawan adadin motocin suka ?aru, hankalin kowannansu akwance yake sun ci burin haWuwa da babban ba?on nasu, duk sun ?agara su ?arasa Airport din.

 Ziyad Ina fata baka faWa ma ?an uwanka ?an jarida ba ko ? Sanate lateef ne yai maganar a yayin da yake zaune gefen Hajiya madina a back seat na motarsu.

Ziyad na murmushi yace ai daddy tuni na sanar dasu ku jura zuwansu kawai
BuWe baki sanate yai amma dai wasa kake min ko? Kadai san Kawun naka bai san taron ?an jarida,

Ziyad na sakin murmushin sha?iyanci ya zuge mashi glass din motarsu, har sai da gaban Senate yadan buga ganin motocin ?an jarida birjik sai faman sharara gudu suke yi har sunfi nasu motocin sauri duk dan su ?arasa su dauki rahoto.
Dafe kai Senate yai ziyad kana da matsala, yanzu menene na gayyatar waWannan mutanan ina amfanin yin hakan ?

Sai lokacin Hajiya madina ta sanya masu baki a maganarsu ai indai ziyad ne dama ka daina damun kanka, ka riga da kasan halinshi, jikin shi har 6ari yake yi idan ya samu abun daukar rahoto

Dariya ziyad yai jin abunda mommyn shi tace, shi dai senate lamarin ya Waure mashi kai.

Kusan atare motocin suka yi parking a wurin da aka tadana domin ajiye motoci, jami an suka diddiro daga saman motocinsu suka soma bubbuWe masu murfin motocin, Waya bayan Waya suke fitowa, ?an jaridan ma suka fito Hannayensu ru?e da Cameras, wasu a wuya suka rataya cameran su, wasu kuma sun ru?e welcome sign a hannun su duk da akwai tazara a tsakanin su saboda mugun tsaron dake wurin dan ma yan jarida ne masu naci da ba wanda ya isa ya tsaya a wurin.

Lokacin da Sharafudden Ya fito daga cikin Motarshi gaba Waya ido Ya dawo kanshi, mutumin babu wasa a fuskarshi, kamanninshi sak da mahaifinshi Obinna, launin fatarsu ne ba Wayaba, Yana da hasken fata sai dai bai kai na Obie ba, nashi yadan yi duhu, fatarshi taji hutu, babban mutunne mai cikar kamala, ya iya dattako ga wadatar arzi?i, kusan duka halayan Owais shiya Wauko babu abunda ya bari mashi, hatta kyawun fuskarshi na mahaifinshi ne, Yana da tsawo da fadin ?irji, wankan suit ne a jikinshi, ya manna farin glass a idonshi, security detail din dake take mashi baya sunyi mashi rumfa, Cikin takun ?asaita Ya nufi mahaifinshi dake ta faman aiko mashi da sakon murmushi, rungume juna sukayi, ?an jarida kamar jira suke yi nan fa suka fara daukarsu hotuna, bubbuga bayanshi obie yai da hannun shi yana fadin Nayi kewarka son, tsawon lokaci ka hanani ganinka sai yau, da yake Wan uwanka zaizo yanzu zan dinga ganinka akai akai dagowa yai da kanshi da?yar yake murmushi kamar yana yi mashi wahala ya motsa baki ya furta aymin afwa baba, kana araina koba dan shi ba, nayi niyar shigowa gidan yau saboda nayi kewarka obie yaji dadin kalamanshi, da hannu ya nuna mashi sauran ?an uwanshi, Jiki na rawa dr jazz da twins suka ?araso suna gaishe shi cikin girmamawa, Waya bayan Waya yake amsa masu, bayan sun kammala ?an gaishe gaishen nasu, suka Wunguma gaba Wayansu suka shiga Arrival area din, duk Inda suka gifta ma aikatan airport din sara masu suke yi, sau da ?afa suke Yi masu biyayya, a katafaren waiting area kowannansu Ya samu wuri Ya zauna sun natsu suna jiran ?arasowar jirgin ba?on nasu.

Jami an suna a kewaye da su, ?an jaridan ma suna a tsaitsaye acen baya suna jiran Ya ?araso don su fara Waukar rahoto.

Vip Area din Ya cika ma?il da Waruruwan mutane wasu ma daga baya suka zo, Ko ina ka kalla kawunan Bil adama ne, kowanene wannan Babban ba?on daya tara dubban jama a dake cike da Waukin ganinshi? lallai ba ?aramin mai farin jini bane, shi Win na musamman ne.

Agogon bangon Nigeria Yana bugawa ?arfe goma shabiyu adai dai wannan lokacin sautin katafaren jirgin shugaban ?asar dake shawagi bisa sararin samaniya Ya karaWe Kunnuwan mutane, gaba Waya ransu ya basu cewar jirginshi ne Hakan yasa su ka fara sakin murmushin farin ciki,

A katafaren Filin tashi da safkar jirage masu zaman kansu, Jet din ya sauka a hankali Yake bin runway har Ya ?araso dai dai Inda zai dakata, tsawon mintuna kafin ?ofar Jirgin ta buWe matattakalar shi ta sauko ?asa, hadadden red carpet, ma aikatan airport din suka shimfiWa mashi tun daga bakin stair din har izuwa entry din Vip area, mutanan dake aciki tuni sun mimmi?e suna atsaitsaye curko curko suna jiran ?arasowarshi.

Musamman ?ungiyar masu daukar hoto da  yan jarida sun Harzu?a Jira suke kawai Ya duro da ?afarshi waje don su fara haska shi da kyamarorinsu kowa burinshi ya kasance mutun na farko da zai fara ?yalla mashi camera,

Jami an sun kewaye Jirgin saboda su bashi tsaro, Maimakon mutumin da suke tsammani Ya fara saukowa sai suka ga Security detail dinshi Royal Canadian Mounted Polices suna fitowa daga cikin jirgin, zaratan Maza ?arfafa Masu ?ira Irinta zakuna, Sanye Cikin kakinsu, Qugunansu a soke da bindigu Pistols, A bakin stairs Win Suka Tsaya sun haWe da sojojin Nigeria dake a bakin jirgin.

Lokacin da Ya zuro ?afarshi dake sanye cikin wasu hadaddun leather shoe Hankalin kowa ya dawo kanshi, tabarakallahu ahsanul khalikin, ?an jarida har goga kafada suke Yi garin yin saurin haska shi da camera, A hankali Ya ?arasa fitowa, Babban mutunne ya fito sanye Cikin tailored suit, sun zauna mashi, Sunbi shape Win Jikinshi, Fari ne Ba irin sosai Winnan ba, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi, kanshi babu hula, Sai ka rantse da Allah matashin saurayi ne, saboda haWuwarshi da iya Waukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara, tsakiyar gashin kan nashi akwai siraran hurhurar gado, da akayi gayu da ita, ba ?aramin kyau tayi mashi ba,Yana da tsayin fuska, Manyan idanuwa, ga dogon hanci, bakowa bane wannan face PRIME MINISTER HATEEM OBINNA! namijin zaki uban dawa, Waya tamkar da dubu, gwarzon Namiji mai Wauke da suffofin jagwaranci, mutun mai daraja da ?ima a idon al umma. yana da farin jini ba Iya kasarshi ba a ?asashe da dama rububin shi suke Yi saboda kyawawan Wabi unshi da halayanshi, mutumin ma?urane a 6angaren Kyau, ilmin addini dana zamani, uwa uba Ya fito daga babban Gida, kallo Waya zakayi mashi ka shaida ruwa biyune, gashi Hamsha?in Mai kuWi Ya shahara Aduniya.

Cikin dattako Yake taka matakalar benan, All eyes on him mutanen dake can nesa suna hangenshi kamar zasu ?etare Iyakarsu su faWo gabanshi donsu Tarbe shi, Fitowarshi Keda Wuya Uwar Gidan shi Gimbiya Mujeedat ta sauko daga cikin jirgin, nan fa kallo Ya koma Kanta, Hankalin maza ya tashi, Ko mace ta kalleta saita girgiza balle Namiji, ahaka ma ta sanya Arab gown launin fara ajikinta, Ta rufe fuskarta da Niqab, dirin Jikinta Yafi komai jan hankali, da kuma kyawawan idanuwanta da suka bayyana sun sha uban ado farare ?yal, price din takalman ?afarta kaWai sun ishi wani talakan jari, hatta hannayanta Safa ce ta sanya, Mijinta yana matu?ar jin kishinta shiyasa duk inda zasuje da ni?ab a fuskarta, bayan ta fito, matasan ?a ?ansu biyu suka fito tare da Faryat ?ar gidan saratu, sunyi shiga kala Waya data mahaifiyarsu dukansu matane, dogaye masu kyan sura, atare dasu akwai advisors dinsa, manyan mutane masu bashi shawara, sun hada da chief of staff, national security advisor, Fararen turawa sun Wauki wankan black suit, kowan nan su ya manna sunglases a idanuwanshi, ajere suke taka shimfiWaWWan red carpet din da zai jagorance su zuwa Vip arrival area, lokacin da suka karasa jama a kamar zasu haWiyesu tsabar murnan ganinsu, Bawan Allah bai nufi kowa ba sai Mahaifinshi Obinna, Hannu bibbiyu ya rungume shi ajikinshi, tsawon shekara basu ganaba sai yau da Allah Ya nufa zai samu damar zuwa Nigeria, Wata irin runguma yayi ma Obinna, gaba daya mutane suka sanya ihu suna tafa masu, ?an jarida Sun dage sai daukarsu hoto suke Yi, sautin ?arar kyamarorinsu ya cika airport din ji kake kyat kyat, Gimbiya Mujeedat, da fara a akan fuskarta ta rungume Hajiya saratu, kamar ?an uwan juna, Faryat kuwa da gudu ta faWa jikin Zayn tana dariya, bayan ta rungume shi ta kuma rungume Zaid, sai daWi take ji taga ?an uwanta, Nazli da Yazrin kuwa kamar basu son ganin mutane, dama suna da wuyar sha ani har ?wara Yazrin tafi sakin fuska akan ?ar uwarta nazli, da?yar suke rungumar ?an uwan mahaifinsu, izzace ta bala e suke fama da ita, su ala dole ga jinin sarautar daular larabawa, Bayan prime minister Ya saki mahaifinshi, Ya rungume ya yanshi sharafudden kamar zasu koma mutun Waya tsabar yadda suka hade jikinsu. Tuni ?walla ta cicciko tab a idanuwansu, da?yar suke yima juna magana, Waya bayan daya saida yabi ?an uwanshi ya rungumesu, kafin ya soma gaisawa da sauran manyan mutanan da suka zo tarbarshi, yaji dadin ganin daruruwan al ummar da suka taru domin shi, wannan abun farin ciki ne, Obie ne yai mashi magana akan Yan jaridan da ke son yin magana da shi, A hankali yake bin welcome sign din dake a ru?e a hannunsu.

Rubutun dake ajiki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login