Showing 201001 words to 204000 words out of 260999 words

Chapter 68 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

mahimmanci da nakeson Yi dakai, tunda yanzu duk mun haWu agaban ka, Inaga Yakamata muyi anan idan ka bani dama !

Mayar da hankali obie Yai akan abdul razak ina sauraronka

 Dangane da matasan family dinmu, bai kamata mu zuba masu ido muna kallonsu ba, yakamata kowan nan su ya fidda matar da zai aura

His excellency Deen Yace Ni kaina abun yana damuna, wani abin Waure kanma Yaran tamkar basu da ra ayin ajiye Iyali, kaga Justice namu da dr nawaz sam basu son Inyi masu zancen aure

Murmushi obie Yasaki yana binsu da kallo Waya bayan Waya.

Senate yace har ?wara Ziyad, idan nayi mashi maganar aure sai kaji yace inada wannan burin baba in sha Allah nan bada jimawa ba zan fidda matar da zan aura ka tayani da addu a Allah ya bani mace ta gari

Mai girma sharafuddeen dake sauraron yayyan nashi, hannun shi ru?e da mug na tea da yake kur6a, da alama yana jin dadin tattaunawarsu.

Deen yace su kuwa waWannan ba a maganar ?a ?ansu, dama ance magaji mafiyi, akansu na fara shaidar hakan yai maganar Yana nuna Sharafuddeen da Hateem.
Gyaran murya sharafudden yai kafin ya soma magana atsanake lamarin Owais namu sai addu a, Ni bana gane kanshi, mace bata agabanshi, na ta6a yi mashi zancen aure sau Waya sai ce min yai baya son ya Waurawa kanshi nauyin da bazai Iya sauke shi ba

Murmushi kowan nan su ya saki, Obie yace kada ku takura kanku akansu, lokacin yin auran nasu ne baiyi ba, da zarar time yayi babu wanda zan saurara acikinsu sai dai kawai suji sanarwar Waurin auransu a masallaci

Jinjina kai sanate Yai baba ka kawo shawara mai kyau, mu haWa kowan nan su da abokiyar rayuwarshi, tunda muna da ?an mata a family namu
His Excellency abdul razak Yace wai Ina Wan uwa mubarak Yaje ne ?
Senate lateef Ya bashi amsa da cewa Wazu dai muna zaune naji wayar shi na ruri har nace mashi ya dubata ana kiranshi, tun da ya fita har yanzu shiru bai dawo ba, wata?il ya wuce gidanshi
 Mu ma yakamata muje mu kwanta, mu huta acewar deen.
Daura ido obie yai akan fuskar Hateem babu alamun Yana sauraronsu.
Gyaran murya yai mashi haWi da zungurin kafaWarshi da hannu, firgigit Ya ware idanuwanshi Yana faman yamutsa fuska Idan bacci kake Ji yakamata kaje ka kwanta girgiza kai yai a a ba bacci nake ji ba, Ina sauraronku

da zolaya senate lateef yace Oh, mu ka maida shashashu mun saki baki munata surutu ka kasa kunne kana sauraronmu, Wato kafi ?arfin ka tanka mana

Mai girma sharafudeen Yace bacci yake ji fa, ba sauraronmu yake yi ba, tun Wazu na lura dashi, baba ne Ya farkar da shi, ya faWa yana duban hateem malam ka tashi kaje wurin Iyalinka ka kwanta ka huta
Yamutsa fuska Hateem yai Na faWa maka ba bacci nake ji ba, idona biyu ya faWa yana zare mashi manyan idanuwanshi, dariya suka saki gaba Wayansu.

Kafin wani Ya kuma furta kalma, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka Jiyo masu sautin fashewar glass, Baba obie Yace kuna jin abunda nake ji kuwa? Ko dai kunnuwana ne suka jiyo mun badai dai ba

Senate yace kamar fashewar glass, bari in duba ya faWa yana mikewa tsaye, karaf idanuwanshi suka sauka akan Giant snake din dake ?o?arin faWowa ta ?ofar glass din wani Waki dake acan upstair hawa na Uku, ras yaji gabanshi Yai mugun faWuwa, Muryarshi na rawa ya furta inna lillahi wa inna ilaihirraji in! Jin ya zabga salati yasa Sauran ?an uwan nashi sukayi saurin mi?ewa, tare da daura idanuwansu saitin inda senate Yake kallo, tashin hankalin da ba a sanya mashi date, sunyi matu?ar firgita da ganin dan?areran macijin dake bin jikin bene Yana ?o?arin saukowa down, jikin baba obie Ya hau yin kerma abunka ga tsoho, Ido Ya raina fata, lamarin ya Waure masu kai, Deen yace maciji kuma? Tayaya akai ya shigo gidan nan? ina jami an dake tsaronshi? Wannan wani irin ganganci ne ?

Kafin wani ya bashi amsa, kwatsam suka jiyo takun tafiyar jami an isod, da gudun gaske suke shigowa cikin falon, hannayensu ru?e da bindigu, atare suka hada baki wurin furta yalla6ai ku kwantar da hankalinku, zamu kawar maku dashi, A matu?ar ruWe baba obie yace baku da hankali, taya akai kuka bari maciji Ya shigo gidana? A haka kuke fadin mu kwantar da hankalinmu? Kun makance ne baku ganin girman shi? tayaya zaku Iya kamashi ! Da sauri Senate ya tari nunfashinshi baba kayi ha?uri, zasu fitar dashi, mubarsu suyi aikinsu

Daya daga cikin jami an yace kayi hakuri yalla6ai ba laifinmu bane, mu kanmu bamusan tayaya akai Ya faWo cikin estate din nan ba, babu wanda yasan daga ina Yake

da hannu deen Ya nuna masu hanya ku shiga kuyi aikinku da sauri suka nufi benan.

Adaidai lokacin Unaisah dake ta faman gudu ta shigo cikin falon tana haki, duk ta fita hayyacinta, kusan atare suka Waura idanuwansu akanta, da mamaki akan fuskokinsu suke dubanta, kafin wani yai yunkurin yi mata magana, Chief owais Ya faWo falon tare da big guy, sunyi mamakin ganinshi babu wanda yasan yana a ?asar, tsabar firgici da tsoro Ya hana Obie furta sunanshi sai faman binshi Yake Yi da kallo.

Umarni yaba big guy akan ya dauki Unaisah ya maidata gida, jin ya furta hakan yasa ta watsa da gudu cikin falon bata nufi ko ina ba sai saman benan da zai sadata da macijin, da gudu big guy yabi bayanta, cikin shesshe?ar kuka take fadin dan Allah kada ku kashe shi, wallahi ba maciji bane, Wan uwanane danish

dam?o hannunta big guy yai, tadinga kiciniyar ?wace kanta ranta amtu?ar 6ace ta soma zazzaga masu masifa tana fadin wallahi babu inda zanje, nace maku dan uwanane, ku ?yale shi ku daina harbinshi tunda bai cutar da kowaba, wayyo Allah na danish Wina

Sautin koke kokenta Ya cika gidan, hatta sauran mazauna gidan baba obie saida suka jiyota, Waya bayan Waya masu aikin gidan suke fitowa daga makwancinsu, Pravin bai jima da shiga Wakin hajjaty ba ya jiyo sautin Kukan mutun agidan, sai gashi ya fito hajjaty na abiye dashi, Hajiya saratu kuwa jin sautin kukan Yasa ta fito daga Waki ta shigo falon, koda tayi arba da unaisa ga jami ae da kuma shirgegen macijin dake bin bango, hannayenta biyu ta Waura akai tana ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji un! Maciji acikin gidan nan? Wacece wancan Yarinyar? Ya akai ya shigo? AruWe ta furta hakan
Kowa Ya shiga ruWani, Jami an sun dage sai antaya mashi Harsashi suke Yi, Ganin suna ?o?arin yi mashi illa yasa Unaisa tayi wani irin kukan kura, ta bangaje big guy da iya ?arfinta na ?arshe, ta haura sama da gudun gaske, duk yadda suka so su kawar da ita sun gaza yin hakan har saida tayi nasarar ?arasawa inda yake, tsawa suka dinga dakata mata suna korarta daga gabanshi amma ta?i matsawa, macijin yabi ya nannaWe kanshi Ya dun?ule waje guda saman floor, lullu6e shi tayi da bazar rigarta, tana kuka tana fadin danish dan Allah ka saurareni, ka taimaki rayuwata, bana so na rasa ka, ka canza halittarka ka tabbatar masu da cewa kai mutunne ba maciji ba, idan ba haka ba zasu Iya kashe mun kai cikin jin ?unar rai take Furta maganar, ta ?an?ameshi kamar zata maida shi jikinta, jami an sun natsu suna kallon ikon Allah, Hajiya saratu sarkin tsoro sai faman baza idanuwanta take Yi, baba obie Yana la6e bayan Mai girma sharafuddeen, Senate Ya ru?o hannunshi dake tayin kerma, A hankali Hateem Ya zare farin glass din dake asaman fuskarshi Ya ru?e ahannunshi, komai ke faruwa akan idanuwanshi, tamkar amafarki suke kallon lamarin, an rasa wanda zai janyeta daga jikinshi. Abunda ya Waure masu kai babu alamun macijin zai cutar da ita.

Duk da baya iya furta mata magana, ranta yana bata cewar yana son ya rikiWa ya koma mutun sai dai ya kasa yin hakan, jikinshi ya Wau zafi sosai, cikin sanyin murya ta soma yin magana, hawaye naci gaba da wanke fuskarta
 ?an uwana rabin raina, dan Allah ka canza halittarka, idan ba haka ba babu wanda zai yarda cewa kai mutunne zasu ci gaba da cutar min dakai ta faWa tana ?ara kankameshi a Jikinta.
umarni Owais Ya ba jami an akan su daina yun?urin harbinshi, amsa mashi sukayi datoh, ya fadi hakanne saboda ya fara kokwanton mutunne kamar yarda ta faWi, a faWace hajiya saratu tace akan me zaka basu umarnin su daina harbinshi? idan ya cutar da wani fa ? Ko kallo bata ishe shi ba, muryar baba obie Na rawa ya furta Ku kashe macijin nan, bana son ganinshi, ku kawar mana da shi

 Baba ka kwantar da hankalinka, Ni na yarda da maganar yarinyar ba maciji bane mutunne mai girma sharafudden ne yai maganar.

A harzu?e Obie Yace tayaya mutun zai zama maciji? hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Ni bazan ta6a yarda ba, ku kawar mana dashi kawai, idan baso kuke zuciyata ta buga ba, Ita kuma waccan Yarintar mai kasada ?ar wacece? Ku Wauke ta mana daga Jikinshi kada ya sare ta yai maganar yana nuna Unaisah da sandar hannunshi.

Duk yabi ya furgice masu, big guy ne ya kutsa ta cikin jami an Ya nufeta, muryarshi ?asa ?asa tamkar tame Yin raWa ya furta Unaisah, ki tashi mu tafi gida, za a dawo maki dashi ma?e mashi kafaWa tayi, la66anta duk sun bushe sun faffashe.

 Babu inda zanje, Ina atare dashi, Idan nayi nesa dashi, ba zaku Iya sarrafashi ba, zai Iya guduwa ya nufi wani wajen magiya ya dinga yi mata akan ta mi?e amma ta?i tashi, hakan Yasa Chief owais motsawa ya haura saman benan Ya nufe su, Darewa jami an suka dinga yi suna bashi hanya har ya kaiga ?arasawa inda suke, faffaWan tafukan hannaye shi ya Waura saman unaisa ya WaWWagota tare da Waurata saman broad shoulder dinshi, juyawar da zaiyi da niyar ya tafi da ita, giant snake din Yai wata irin girgiza da gudun gaske yabi bayan owais daya Wauketa.

Jami an suka saita shi da bindiga owais Ya hana su harbeshi yace masu su barshi akwai dalilin dayasa yayi hakan, Yana tafiya macijin Yana bin bayanshi, kasancewar ya Waurata saman kafadarshi tana Iya kallon giant snake din daketa ta faman jan ciki Yana nufosu, hawayenta tamkar zasu ?are muryarta sha?e take ambaton sunan Danish.

Ganin macijin zai sauko down yasa Hajiya saratu ta watsa da gudu zaninta har yana kwancewa ta ru?o shi ta nufi hanyar part dinsu aguje ta shiga Waki ta datse kofa, tabi tagogi duk ta rufesu, a karshe cikin toilet ta shige tayi locking kanta.

Hankalin baba obie yai matu?ar tashi sai ?ara ?ankame jallabiyar mai girma sharafuddeen yake yi, Hateem kuwa ko kadan baiji tsoron macijin ba, tsabar mamakine Ya hana su furta magana, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah, duk inda owais yai da ita sai macijin yabisu, fucewa yai daga falon Ya nufi motarsu da su ka yi parking dinta abakin entry hall, Ya buWeta Ya shigar da unaisah aback seat na motar, ya buWe front seat a mazaunin driver Ya zauna yai mata key, da gudun gaske Ya fusgi motar, ta cikin glass din motar take kallon macijin daketa binsu da ?arfi Ya daka uban tsalle Ya haura saman motar Yai kwanciyarshi.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin yana atare dasu, bai nufi ko ina ba sai sashen da gidansu yake, ta gate din Baya ya shigar dasu a bakin entry hall chief Yai parking din motar, Ya fito Ya buWe back seat din Ya cuccu6i unaisah Ya Waurata saman kafaWarshi Ya nufi Babban falo da ita, hankalin shi kwance tamkar baisan da zaman macijin ba, saukowa yai daga saman motar yabi bayansu da gudun gaske yake jan jiki.

Cikin takun sauri Owais Ya haura upstairs da ita, kafin Ya ?arasa second floor, macijin Ya riga shi isa, wani wawan tsalle ya daka Yabi ta jikin bene Ya faWo tagabansu, ?o?ari yake ya nannaWe ?afafuwan owais sai dai yakasa yin hakan saboda owais bai bashi damar ru?e mashi ?afa ba, sai kakkauce mashi yake Yi, a haka ya ?arasa bedroom din Danish Ya shiga daga ciki, Ya kwantar da ita saman gado, Shigowa Wakin macijin Yai yana faman huci kamar zai kai mashi hari, saman gadon Ya haye Yana faman bin mattress din. Owais dake a tsaye ya goya hannayenshi saman wide chest dinsa, Ya natsu yana kallonsu.

Giant snake din Ya nannaWe jikinshi agaban unaisah ya Wago da kanshi Yana kallon owais, duk a tunaninshi wani abu zaiyima unaisah shiyasa Yabiyosu, shi kuma owais daya fahinci Baya iya cutar da ita shiyasa yai dabarar daukota sai gashi yaci nasara akanshi

Fitowa yai daga Wakin Yaja ?ofar Yai locking dinta, Yabarsu su biyu adakin Ya nufi down.

Hankalinta ba ?aramin tashi yai ba, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi, tsananin tsorone Ya kamata, amma saboda ?aunar da take yi mashi takasa motsawa, duk tasha jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta sunan shi danish Wina juyowa macijin yai da kanshi Yana dubanta, jikinta na kerma saboda ?arfin hali ahaka ta mi?a mashi hannunta, jan jiki ya somayi yana nufarta, saman kirjinta ya nannaWe kanshi, wani irin sanyi taji ya ratsata, lokaci Waya tadaina jin bugun da ?irjinta keyi mata, asaman fatar shi ta Waura hannunta, a hankali take shafashi duk don ta kwantar mashi da hankalinshi, ita kaWaice zata Iya fahimtarshi a halin da yake ciki.

Walking quickly chief Ya nufi ?ofar fita daga part din, Kafin Ya ?arasa Muryar Boss man ta katse mashi hanzarinshi yalla6ai cak Ya tsaya da tafiya ya waiwayo yana dubansu, su biyune suka fara shigowa shida big guy, daga bayansu sauran jami an isod ne da suka Biyosu, hankalinsu duk ba a kwance yake ba, musamman Boss man da yaji labarin abakin big guy shigowar shi kenan gidan duk wannan budurin da akeyi baida masaniya yana a part dinsa.

Fuskar chief owais ta canza zuwa yanayi na damuwa.
 Yalla6ai Ina macijin yake ? Big guy ne ya jefa mashi tambayar.
Da?yar Ya iya buWe baki Ya furta yana adakin shi, tare da yarinyar na kullesu waro ido waje sukayi suna kallon shi
Muryar boss man na rawa ya furta kana nufin tare da Angel ka rufe su aWaki? Idan ya cutar da ita fa ? Gaba Waya yabi ya ruWe.

Big guy yace ka kwantar da hankalinka, Ni na fahimci hikimar yin hakan, da ace bai daukota ba macijin bazai dawo gidan ba, bamusan inda zai shiga ba, amma yanzu kaga mun kulleshi aWaki ta dalilinta

Cikin rashin fahimtar kalaman big guy Boss man yace bazai yiwu ba, ?ata fa aka kulle aWaki Waya da maciji, Idan ya kashe min itafa dafa kafaWarshi Owais Yai da hannu Waya kadaina kiranshi maciji, mutunne, bazan iya yin abunda zai cutar maka da ?arka ba, Kamar yarda kake jinta nima haka nake jinta, fatan ka fahimce ni gyada kai Yai still hankalinshi bai kwanta ba.
 A wani daki ka kulle su ?
Atakaice owais Ya furta A dakin shi jiki na rawa boss man Ya watsa da gudu ya nufi upstair.
Chief owais Ya maida dubanshi ga Big guy,  Things are starting to get out of control, and I don t know what to do now. But I want to see his brother, maybe he can control him. kaje ka zo dashi ya faWa in a cool voice, amsa mashi yai da toh, da sauri Ya juya ya fuce daga Wakin, Kallon sauran jami an yai ku koma bakin aikin ku, ku tabbatar kun kula sosai Cikin girmamawa suka amsa mashi da toh, juyawa sukayi da sauri kowa Ya nufi hanyar komawa bakin aikinsa.
Shafa sumar kanshi yai da tafin hannun shi nadama, yanke shawarar komawa gidan obie yayi, yasan suna can hankali duk Ya tashi, ba lallai su iya runtsawa ba.
Cikin takun sauri Ya fita daga part din, Ya nufi Waya daga cikin motocinsu, wani jami i ne Ya nufeshi da sauri Ya buWe mashi motar ya shiga a mazaunin baya, shi kuma ya zauna a driver s seat, yai ma motar key ya tashe ta, suka nufi cikin Obie estate......

Unaisa tana akwance idanuwanta sun kumbura suntum, kumatuntu sunyi jawur saboda kukan da tasha, busassun hawayene saman fuskarta, ta lumshe idanuwanta akan giant snake din daya Waura kanshi saman kirjinta, karatun qur ani take raira mashi cikin disasshiyar muryarta da?yar sautin ke fita, macijin Yayi lamo sai ?ara narke mata yake Yi, ga dukkan alamu yana sauraronta.
Da karfi tajiyo muryar boss man Yana kwaWa mata kira daga waje Unaisah, Unaisah!!.
A hankali tasoma ?okarin raba jikinta daga na macijin, ta lalla6a ta sauko daga saman gadon tana cigaba da yin ?ira ar al qur anin, agogon bangon Wakin ta kalla almost 10 na dare.
A jikin glass door din Boss man Ya jingina yana le?ensu.
?arasowa tayi gaban ?ofa suna fuskantar juna, batasan sa adda ta fashe mashi da kuka ba, Cikin shesshe?ar murya take fadin kaga irin ?addarar da ta sami Wan uwana ko? Nayi ?o?arin na fahintar dasu cewa mutunne amma sun?i su gane, sai harbinshi suke Yi da bindiga

Tsananin tausayine ya kamashi ganin yadda ta canza saboda damuwa.
Cikin kwantar da murya yace Yana ina  ?
Matsawa tayi daga bakin ?ofar, karaf idanuwanshi suka sauka akan giant snake din dake nannaWe saman gadon kamar bacci yake yi.
 Unaisa bai cutar dake ba ? Tambayar daya jefa mata kenan, Girgiza mashi kai tayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login