Showing 192001 words to 195000 words out of 260999 words

Chapter 65 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

ba ?aramin daWi zataji ba saboda tana son fatima ?arta aminnan junane tun tuni, sannan taci burin zuwa obie estate, bayan haka aikin nan da take Yi a companyn su ba ?aramin ?aruwa take Yi ba, ita kanta tana faWi da bakinta irin alheran da take samu ta silar aikin da suke Yima mutane, idan ma da wata manufa tace hakan to mu barta da Allah, In sha Allah babu abunda zata Iya yi mata, gyaWa kai Aneelerh tayi shikenan na amince da bu?atarta, mu koma mu faWa mata komawa sukayi cikin falon, bayan sun sanar da ita shawarar da suka Yanke ta dinga yi masu godiya farin ciki duk Ya cikata, kafin tafiyarsu saida ta ro?e su alfarma akan su taimaka mata, tana so zahra taci gaba da ganinta a matsayin mahafiyarta, tasan ayanzu bata da sauran mutunci a idonta.
Aneelerh ce tabata shawarar yadda zata tsara ma zahra, duk don ta amince da cewa ba halinta bane, sun jima agidan kafin daga bisani sukayi mata sallama, sunyi rabuwar mutunci da hajiya falmata, har musayar number sukayi da Aneelerh saboda acigaba da zumunci.

( kunji abun da Ya faru, kafin washe garin ranar da zahra taje kaima Hajiya falmata kuWinta)

Wuraren ?arfe takwas na dare, motar drivern da yaje dauko su Alhaji ubaid daga airport ta kunno kai gate din gidan, tunkafin ?arasowarsu, Dr Shureim da zeenatu suna atsaye bakin Entry hall din falo, hannunsu ruke cikin na juna, daga ita har shi jallabiyace ajikinsu, ta yafa mayafi akanta, tsantsar farin cikine akan fuskokinsu, sunyi matu?ar ?agara da son ganinsu.
Zeenatu sai faman washe baki take Yi, tunda tayi tozali da motar dake shigowa tana tunkaro bakin entry hall din
Da zamudi tace ya shureim kana ganin aunty benazir zata Iya gane ni kuwa? Saboda mommy ta fadamin tun ina jaririya ta 6ace ba a ganta ba
Fuskarshi dauke da murmushi yace idan ma bata gane ki ba, da zarar anyi mata bayani zata shaidaki, zan faWa mata cewa zeenatu ce Wiyar uncle musa, and my wife to be tuntsirewa tayi da dariya taji daWin maganarshi, muryarta da shagwa6a tace amma ya shureim ai ni banaso ka faWa mata, wallahi kunya nake ji, ko mommy layla ma kada ka fada mata please da daddyn ku ta faWa tana duban face dinshi.
 Ai ni nafiso suji My zeenatu, saboda a fara shirye shiryen shafa fatihar auranmu zaro mashi blue eyes dinta tai kafin tai saurin sanya tafukan hannayenta biyu ta rufe fuskarta cikin jin kunyar maganarshi ta furta dan Allah yaya shureim dina kada ka fada masu yanzu, nidai kunya nake ji

 Kunya kamar bafullatana, kin manta mommynki baturiya ce, daddy musa kuma Hausa fulanine, kakarmu bafullatana ce kakan mu namiji kuma bahaushe ne, Ni bansan inda kika gado Kunyar nan taki ba, a haka zamuyi aure kina jin kunyata ?

Kafin ta bashi amsa, motarsu Alhaji ubaid ta ?araso gab dasu, bayan drivern yai parking, da sauri Dr shureim Yaja hannun zeenatu suka ?arasa bakin motar, yakai hannu ya buWe masu murfin back seat, a hankali ta zuro da ?afarta dake sanye cikin takalma, ?arasa fitowa tayi tun daga ?asa dr shureim yake binta da kallo, wankan atamfa ne a jikinta riga da skirt, ta kashe daurin dankwalinta, yalwatacciyar sumar kanta ta sauka gadon bayanta, gyalen asaman kafaWa ta yafa shi, idan kaganta ahaka bazaka ta6a ce wa ta ta6a yin aure ba, kamar budurwa saboda babu abunda ya canza a jikinta, dama bata ta6a shayarwa ba.

Wani irin kallon so da ?aunar ?an uwantaka suke jefa ma juna tsakanin ta da shureim, idanuwan kowannansu ya ciko tab da ?walla, La66anshi na kerma ya furta sunan ta be.. Nazir! Yar uwata rabin raina, Jinin jikina Dagaske ke ce idanuwana suke nuna min? Fashewa tayi da matsanancin kuka, gaba Waya ta faWa saman chest dinshi, ya zagayo da hannayenshi biyu ya rungumeta tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi, Zeenatu dake tsaye tana kallonsu hawaye tuni sun wanke fuskarta, tsananin tausayin benazir ne Ya kamata, Fitowa Alhaji ubaid yai daga cikin motar shida Hajiya layla, ya dauki wankan shadda, itama layla Atamfar ce ta sanya sunyi anko da benazir hatta daurin dan kwalinsu da mayafin da ta daura a kafaWa iri dayane dana benazir, idanuwansu na akan dr shureim da benazir, sun ?an?ame juna sai kuka sukeyi kamar waWanda suka rasa mafaWi a duniya, zagayawa zeeenatu tayi ta 6angaren da su hajiya layla suke koda sukayi arba da ita, Hajiya layla ta buWe mata hannu da fara a akan fuskarta take fadin Zonan My daughter zeenatu kamar jira take yi da sauri ta ?arasa ta faWa jikin Layla, rungumeta tayi sosai, tana dan bubbuga bayanta ta furta kin ?ara girma daughter, tsawon lokaci bamu haWu ba, Daddynki Ya hanaki zumunci da ?an uwanki, baison kina taka wajen mu, gashi mu kuma muna ?aunarki ta faWa tana raba jikinta da na zeenatu, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, kallon Alhaji ubaid tai sannunku da zuwa daddy mi?a mata hannu yai da sauri ta ?arasa gare shi, Yai hugging dinta yana fadin fatan mun same ku lafiya, Wagowa tai da kanta tana fadin Lafiya lou daddy mu shiga daga ciki
Drivern daya daukosu Yana daga tsaye ya jingina bayanshi jikin motar, Yace yalla6ai ku ?arasa shiga gidan, za a shigo maku da kayan naku amsa mashi sukayi da toh, layla tace da su shureim ayi ha?uri adaina kukan ya isa haka mu shiga cikin gidan inyaso kun ?are kukan naku acan Alhaji ubaid na murmushi yace ke ko kibarsu mana, An daWe ba a haWu ba, Jini Waya ba wasa ba, mundai godema Allah daya bayyana mana ita da ranta da lafiyarta ubangiji Allah Ya ?ara tsare mana ita, layla da zeenatu suka amsa mashi da ameen,
Gaba suka fara Yi, Ya rage saura zeenatu data ?ura ma benazir da shureim ido.

Ta kwantar da kanta saman kafadarshi, yayin da hawaye masu Wumi suke cigaba da wanke fuskarta, cikin muryar kuka take fadin yaya shureim nayi danasanin duk wani abu daya faru arayuwata, wallahi nayi danasani mara amfani, bansan meke damunaba, hakanan na tafi nabar dangina nabar mijina, babban takaicina ?ar jinjirar dana bari cikin jini, na haura ?afa na tafi nabarta saboda rashin hankali irin nawa, bansan meyasa na aikata hakan ba cikin jin ?unar rai ta ?are maganar.
?aura hannunshi yai saman bayanta cikin rauni na murya ya soma magana kiyi ha?uri benazir, wallahi ba laifinki bane, ni nasan duk rashin jin maganarki bazaki ta6a iya aikata hakan ba, Ina yi maki kyakkyawar zato, ki kwantar da hankalinki My sister cikin kwantar da murya yake lallashinta
Shesshe?ar kukan zeenatu ne Ya janyo hankalinsu ga kallonta, idanuwanta sunyi luhu luhu, da mamaki akan fuskar benazir ta furta yaya shureim a ina muka samu kyakkyawar matashiyar baturiya ?
Fuskarshi dauke da murmushi yace zeenatu ce, nasan ba lallai kisanta ba, saboda ba ajima da haihuwarta ba ki ka tafi, Wiyar uncle dinmu ce, ki kalli fuskarta dakyau

Farin cikine Ya lullu6e benazir, Yarinyar ta burgeta, Gata ?ar kyakkyawa da ita, mi?a mata hannu tai zonan ?ar uwata, Ina fata an fada maki wacece ni, idan ma ba a sanar dake ba toh nidai sunana benazir, ?anwar dr.shureim fashewa Zeenatu tayi da dariyar farin ciki, Hawaye nabin fuskarta.
 zonan In rungumeki ajikina, Nima yau inji Wumin ?ar uwata jiki Na rawa zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna kamar zasu koma mutun Waya
Cikin shesshe?ar kuka Zeenatu take fadin Aunty benazir munyi kewarki sosai, Mommyna tana bani labarinki, najima ina son ganinki arayuwata, duk da bamu ta6a haWuwa ba amma kullum idan nayi sallah sai nayi maki addu a Akan Allah Ya bayyanar mana dake idan kina araye, Idan bakya araye Allah Yaji?anki yakai rahama agareki, ashe da rabon zamu haWu.... dakyar ta ?are maganar saboda kukan daya cimmata, daga ita har benazir din kukan sukeyi, Kalaman zeenatu sunyi matu?ar ta6a mata zuciyata, tayi mamakin irin ?aunar da take Yi mata, ita da bata ta6a ganinta ba, labarinta kaWai aka bata, ha?ika taji dadi mara misaltuwa, kaunar zeenatu ta shigeta, tayi fatan Ace itama ?arta data bari tana yi mata addu a.

 Aunty benazir dan Allah kada ki ?ara tafiya kibarmu, wallahi muna kaunarki nida mommyna sosai benazir ta fashe da kuka tana fadin in sha Allah bazan ?ara tafiyaba, nadawo kenan zeenatu, naji dadin kalamanki agareni, ?ar uwata rabin raina
Dr.shureim Ya natsu yana kallonsu, idanuwanshi sun kaWa jawur, hawayen dake gangarowa saman kuncinshi sai ?ara ninkuwa sukeyi.
Cikin sanyin murya yace dasu Mu shiga cikin gidan amsa mashi sukayi da toh, hannun benazir acikin na zeenatu suka dunguma zuwa babban falon gidan.
Lokacin da suka ?arasa ciki, Alhaji ubaid da Hajiya layla suna a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, a yayin da Hajiya sarah ta zauna saman 3 sita, Alhaji musa yana daga zaune gefenta, kamar kullum fuskarshi babu annuri, kamar wanda akayiwa albishir da ranar mutuwarshi, shaddar jikinshi ta zauna mashi launin blue sky, daddadan kamshin turarenshi Ya karade hancin kowa, Hajiya sarah Lace ne ta sanya kalar shaddarshi, head dinta kalar takalman ?afarta, sunyi kyau abunsu kamar sabbin ma aurata

Jin takun tafiyarsu yasa hajiya sarah ta Wago tana dubansu, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin benazir, Jiki na rawa ta mi?e tana faman sakin fara a fararen hakoranta tarr dasu ta nufi benazir tana fadin ashe rai kanga rai? Benazir dagaske kece idanuwana suke nuna min? Wayyo Allahna, Idan ma mafarki nake Yi toh kada atadani abarni in tayi dan Allah Rungume juna sukayi, Benazir ta fashe da wani sabon kukan bata ta6a tsammanin zata samu kyakkyawar tarba a wurin ahalinta ba, Tabbas sun bata mamaki tayi tunanin kamar yadda ta gudu babu wanda zai saurareta donta dawo gare su.
Hajiya layla sai faman sakin murmushi take Yi ita da Alhaji ubaid hankalinsu na akan Hajiya sarah data rungume benazir, Shi kuwa Alhaji musa ko kallo bata ishe shi ba, tamkar baisan sun shigo falon ba.

 Allah sarki benazir, Ashe da rabon zamu sake ganawa a duniyar nan! Tsawon shekaru sai yau Allah Ya nufa zan ?ara Yin tozali dake ta fada tana duban benazir da hawaye suka gama wanke fuskarta
Cikin shesshe?ar kuka tace Aunty Sarah nayi danasani, naji haushin kaina, naji na tsani kaina saboda komai ya faru arayuwana laifina ne, tunda nida kaina na gudu na tafi batare da nayi shawara da kowa ba, Dan Allah ku yafe min, nasan na 6ata maku rai
Idanuwan hajiya sarah tuni sun cicciko tab da ?walla, kasancewarta mace mai tausayi.
Cikin karyayyar murya ta furta dan Allah ki daina fadin hakan, Komai ya riga daya faru kuma ya wuce

Kafin benazir ta kuma yin magana muryar Alhaji musa ta katse masu hanzarinsu
 Idan kun gama jimamin, ku ?araso ku zauna cikin isa Ya furta hakan, sai lokacin Benazir ta Wago da ido tana dubanshi, Ya haWe rai babu annuri sam a fuskarshi, gani take kamar baiyi farin ciki da dawowarta ba.
Ru?o hannunta Hajiya sara tayi acikin nata, suka ?arasa tare da samun wuri kowannansu ya zauna, zeenatu da dr shureim suna zaune saman lallausan carpet, Benazir kuma tana agefen hajiya sarah, ta ?ankame hannunta.
A tsanake Alhaji musa Yasoma yin magana batare daya Wago da ido ba
 Da farko, Inayi maku barka da zuwa, yayana da kuma hajiya layla, kwa6e fuska layla tayi aranta tace dallah jibarshi Wan rainin wayau
Numfasawa yai tamkar bayason buWe baki Ya furta benazir, amsa mashi tayi da na am.
Dawo nan ki zauna yai maganar yana Nuna saman carpet daga gefen hannun sofa din da yake zaune, jiki asanyaye ta mi?e ta dawo inda ya bata umarni ta zauna.
Kowa ya natsu yana jiran jin me Alhaji musa zaice da ita.
 Meyasa kika gudu daga gidan auranki har na tsawon shekaru baki nemi kowa ba ? Kafin benazir ta bashi amsa hajiya layla tayi saurin cewa Bai kamata kayi mata wannan tambayar ba, kodai mu da muke Iyayenta bamu tambayeta komai ba, duba da halin da tadawo gidan
Ranshi a matu?ar 6ace ya dago da ido Yana binta da matsiyacin kallo batare daya furta komai ba
Sai Alhaji ubaid ne yace wannan maganar bata shafeki ba, tsakaninshi da Wiyarshine don haka ki daina sanya masu baki harara ta wurga ma Alhaji ubaid kaima ka sani bazan ta6a rufe baki na ba, akan me zai tambayeta meyasa ta tafi? Lokacin da ta gudun ya nuna damuwane akanta? Ko kuwa ya bada gudummuwar da za a nemota ne eye? Daga zuwanmu gidanshi zai tsareta da tambaya? Dama ya kira mune don Ya tuhumi ?ar mu badan Ya tayamu murnar ganinta ba tunda tafara zazzaga masifa hankalin hajiya sarah dana zeenatu ya tashi hai?am, shi kanshi shureim jikinshi yai sanyi la?was, benazir dai ta saddar da kanta ?asa hawaye na cigaba da wanke fuskarta.

Lallashinta Alhaji ubaid Ya soma Yi, Alhaji musa kuwa sai faman jinjina kanshi yake Yi, Yama rasa bakin magana

Hajiya sarah na faman yarfa hannu tace dan Allah kiyi ha?uri aunty, idan ranki ya 6aci, nasan ba a kyauta ba, Ni tun farko banso yace kuzo nan ba, har magana nayi mashi akan mu yakamata mu taka muje tayaku murna amma ya hanamu zuwa.... da?yar ta ?are maganar ganin irin kallon da Alhaji musa ke binta dashi, ba arzi?i taja baki tayi shiru

Jinjina kai yaWanyi kafin ya Waura da cewa Allah Ya huci zuciyarki Hajiya layla, Naji bazan ?ara tambayarta ba, tayi mamakin jin abunda yace, har saida ta kalli cikin idonshi, murmushin gefen fuska yasakar mata afakaice, kafin Ya maida dubanshi ga benazir ina yi maki barka da zuwa My daughter, naji daWi da kika yi tunanin dawowa gida, ki kwantar da hankalinki, kuma ki share hawayenki, abunda ya faru ya riga daya wuce
Ajiyar zuciya benazir tadan sauke, cikin sanyin murya ta soma magana nagode uncle, sannan idan na 6ata maka rai, kayi hakuri, nasan komai ya faru laifinane, dana kama hanya na tafi
Lumshe idanuwanshi yadanyi kafin ya waresu akan fuskarta kada ki damu ni ban ru?e ki araina ba, kawai dai banji dadin guduwar da kikayi bane na tsawon shekaru batare da kin tuntu6emu ba, amma yanzu tunda kin dawo da ranki da lafiyarki falillahil hamdu, sai dai fatan Allah ya kyauta gaba, In sha Allah zanyi ?o?ari dan ganin na inganta maki rayuwarki, duk wani abu da kike bu?ata ki sanar dani zanyi maki shi, kada ki ?ara yun?urin guduwa saboda muna bu?atarki, zaifi ki sanar damu idan ma wani abune ya 6ata maki rai a tsakaninmu zamu Iya sama maki solution, Ina fata kina jina
?aga mashi kai tayi alamar eh, lamarin Alhaji musa ya Waurewa hajiya layla kai, bata ta6a tsammanin ya iya tsara kalami irin haka ba, hatta Alhaji ubaid yai mamakin yadda ya sakar ma benazir fuska yana yi mata magana cikin lallami, aranshi ya ayyana wata ?il tsananin tausayinta ne Ya kamashi, yaji dadin hakan, hankalin hajiya sarah ya kwanta dana zeenatu, sai faman sakin murmushi suke Yi, haka zalika dr.shureim shima murmushi ne akan fuskarshi.
 In sha Allah uncle bazan ?ara yunkurin guduwa ba, duk runtsi duk wuya zan zauna atare daku, nima nayi danasanin abunda na aikata,
GyaWa kanshi yai,
Hajiya sara tace tun Wazu fa na sanya masu aiki sun shirya maku lafiyayyan abinci, yakamata muje muci kada ya huce da fara a akan face dinta ta furta hakan,
Mi?ewa sukayi atare suka dunguma zuwa dining room, benazir ta girgiza da ganin daular uncle musa, Gidan Ya tafi da imaninta.
Saman dining chairs suka zazzauna, ga kayan abinci an jera masu saman table,
Tani da lami ne suka zo domin yin serving dinsu, Bayan sun gaishe da alhaji ubaid da hajiya layla, suka soma zuzzuba ma kowannansu abunda yake ra ayin ci, hankalinsu kwance suke ci baka jin sautin komai saina ?arar cokulansu.
Jefi jefi zeenatu take satar kallon benazir da zarar sun haWa ido sai ta sakar mata murmushi, Ta fahimci yarinyar ba ?aramin so take Yi mata ba, Dr shureim na kallonsu, shima murmushine akan fuskarshi, Hajiya layla dai ta?i sakewa, itafa har yau har gobe bazata ta6a yadda da alhaji musa ba, gani take yi kamar akwai wata manufa atare dashi, abincin ma da?yar take cin shi

Bayan sun kammala cin abinci, Hajiya sarah ta rakasu zuwa masaukinsu da zasu zauna, Hadaddun bedrooms aka ware masu, Zeenatu ta hana benazir sakat, tsabar Iyayi hada Wauko bargonta da pillow ta dawo down stair dakin benazir donsu dinga kwana atare, Hakan ba ?aramin daWi yayi mata ba,

*SIR MUBARAK
'*

Yana acikin dangi suna ta yin firar yaushe rabo tare da ?an uwanshi, Wayarshi dake acikin aljihunshi ta soma Yin ruri, kusan sau uku kiran na shigowa yana yin rejecting batare daya ankare ba, saboda hayaniyar ?an uwan shi da suke Yin fira a tsakaninsu, a babban katafaren falon gidan, a kira na huWune, Senate lateef dake zaune gefenshi ya ankarar dashi ta hanyar yi mashi magana ka duba wayarka tun dazu nake jin sautin ringing Winta, amsa mashi yai da toh, sai da ya fara curo wayar ya duba sunan mai kiran nashi tukunna ya mike yai masu sallama Ya nufi ?ofar fita daga babban falon, bayan ya fitone Ya dakata da yin tafiya, Yabi kiran da aka yi mashi, bugu Waya aka Waga kiran
 Major, ince dai lafiya? Naga miss call dinkane
On the other hand major yace yalla6ai yaron nan na wurinka jazz Ya fita daga gida Yanzu haka da nakeyi maka magana munbiyo bayanshine muna asaman titi,
Cikin saurin murya sir mubarak yace gani nan zuwa, kubi a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login