Showing 33001 words to 36000 words out of 260999 words

Chapter 12 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

jikin allon zanan nashi, Tsabar mamakin yadda suffarta ya fito ne yasa su sakin baki, Kamanninta sak dana tajudden Hasken fatarne kaWai na mahaifiyarta da kuma sumar kanta.

 Wow! Zanan sak kalar na south korewa nayi mamaki! Banbancin kawai tsadar kayan aikin da akayi amfani wurin yin wancan zanan amma wlh yayi kyau over hajiya adamace take ta sambatun ganin zanan, Shi kanshi uncle abdallah Ya yi mamakin ganin zanan, Suffar Angel sak sai dai an ?ara mata girmanta, takai dai dai age Winta na yanzu 15 to 16 years,

Mai zanan yana atsaye yana kallonsu, sai sakin murmushi yake yi jin yadda suke yabon aikinsa

 Ina fata Angel ta bayyana kamar yadda muka ganta a zananta, in har hakan ta faru nayi maka al?awarin zan ninka maka kuWinka fuskarta Wauke da murmushi tayi maganar tana kallon mai zanan, washe baki yai yana faWin In sha Allah ranki ya daWe ?ar ki zata bayyana kamar yadda na zana ta a hoton nan, kuma ina ro?on Allah yasa zanene ya zama silar ganinta atare suka amsa mashi da ameen, Kafin tafiyar mai zanan saida suka haWa mashi sha tara na arzi?i.

*EVIL FOREST*

*the Prisoners=ؔ?*

Kamar matattu haka su ka sha baccin su cikin kogon dutse, Allah kaWai yasan awanni da su ka kwashe suna sharar bacci, Bawan Allah Danish A zaune ya ke bacci, Wutar da ya kunna masu tuni ta jima da mutuwa, Hasken rana ya kwalo daga sararin samaniya duhun dajin ya Wan washe, A hankali ta soma mutsun mutsun buWe idanuwanta a yayin da ta ke ambaton Sunan Allah, tsabar kumburan da idon nata yai da?yar ta ke iya buWe shi, ga uwar kwamtsa cunkushe da idon, kaWan ta ke iya buWe shi tana kallon Saman kogon dutsen, cikin rashin fahimtar ina ne? sam ta manta cewa sunbar kurkukun ?addara, wani irin tsorone ya kamata muryarta sam babu wadataccen sauti ahaka take ?o?arin ?walawa ?an uwanta kira Waya bayan Waya, duk tabi ta furgice.

 Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai ji na ne ? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi da ?arfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta, slowly ya Wan ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a iya ?irjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin sanyin murya ya furta sunanta My Angel jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin sambatun nata, ?o?ari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin fuskarta yai mata rumfa da faffaWan ?irjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana juna, kaWan ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, muryarta na Wan rawa ta furta sunanshi Da..Nish fatanta Allah yasa ba mafarki bane.

Dogayen yatsun hannun shi ya Waura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta Waura nata hannun saman nashi dake akan face Winta, Sai yanzu ta samu damar motsa jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, ?ago da ita yai zuwa saman ?irjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta, sosai ya ?an?ameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu dake harbawa da sauri da sauri,

 I can t explain how much I miss you. I m sorry for what happened, it s all my fault. I m sorry, Angel.

Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shesshe?ar kuka ta soma yi mashi magana ba laifinka bane Danish, ka daina faWin hakan, ni abunda yafi damuna rashin ?an uwan mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu al?awarin da na Waukar masu ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran ?an uwan mu da mu ka rasa da?yar ta ?arasa maganar, zafin jikin su duk ya Wumamasu, Yanayin weather Win dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun dawa.

?aura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi kaWai yasan raWaWin da ya ke ji acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta Wago da kanta daga saman ?irjinshi ta Waura eye balls Winta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke ?arewa juna kallo tsawon mintuna goma sha biyar, 

 Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun zai ?ara ta6a zuciyarsu, ka taimaka min Danish mu binne su kafin farkawarsu, shiru bai tanka mata ba sai kallon ta ya ke yi kamar yau ya fara ganinta

 Danish! Am talking to u, bana jin daWin jikina, maganar ma da?yar nake iya furtata Still bai motsa la66ansa ba ta rasa meyasa ya ke kallonta yana lumshe ido Ya ?i tanka mata, GyaWa kai tai shikenan tun da bazaka taimaka min ba, Ni zan je na rufe su tana ?o?arin mi?ewa sexy voice Win shi ta ratsa kunnuwanta Kin ta6a ganin an binne mutun da ranshi !! ras taji gabanta ya faWi a matu?ar ruWe ta zazzaro idanuwanta waje tana kallon shi........



*Boss Bature
'? Mu haWu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ?addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuWin*



First bank



3196407426,



*Bature Hafsat Muhammad, za a tura evidence of payment ta phone number Wina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_


_*KURKUKUN ?ADDARA*_



_The Prisoners E7=?%?=ث?_


*Daga al?alamin Boss Bature*


~Middle step~



_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty=ؔ?._



 ka na nufin ba su mutu ba suna a raye ? A ?agare ta jefa mashi tambayar, jinjina mata kai yai ba tare da ya furta mata kalma ba, bugun zuciyarta ne ya qaru a sukwane ta juya baya don ta samu damar ?are masu kallo, bargunan da ya lullu6e su da shi ya hana ta gan su da kyau, jikinta na 6ari ta ?ara sa gaban su ta zu?unna tare da kai hannu ta Wage saman bargon, duk wani motsin ta akan idon Danish.

Wani irin farin ciki ne Ya lullu6eta ha?i?a ta yi al ajabin wannan iko na Allah, kamar zautacciya haka ta dinga Waura kanta saman ?irjinsu haWi da jogana kunnanta saitin zuciyar su don ta ji idan tana bugawa, daga kan Jamimah ta fara tana Wosa kunnanta bugun zuciyar jemimah ya daki dodon kunnan, nan ta ke ta fahimci cewa bacci su ke yi, Tambayoyi ta shiga jefawa kanta, Ta ya ya akai haka ta faru? Dama wanda ya mutu yana tashi? don ita dai a iya saninta idan an mutun ba adawowa, Waura kunnanta ta yi saman ?irjin Azeeza lumshe idanuwanta ta yi wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, jin bugun zuciyar azeeza na har6awa, matsawa ta yi gaban Parveen tunkan ta Waura kanta saman ?irjinta idanuwanta su ka sauka akan ?aramin bakinta ganin yana motsi yasa ta fahimci tana araye, Lamarin yai matu?ar Waure mata kai, ta ya akai su ka rayu! Kuma Danish da kanshi ya tabbatar masu cewa Heart attack ne yai silar mutuwarsu, duk da bata da ?oshin lafiya hakan bai hana smart brain Winta aiki ba, Zurfin tunani ta shiga idan har su Jemaimah su ka iya jure abunda ya faru dasu ya kenan ta 6angaren Sauran ?an uwansu da su ka baro? Waro idanuwanta waje ta yi yayin da zuciyarta ka harbawa da sauri da sauri, a fujajen ta zabura ta mi?e kamar an zungure ta, ta juya ta nufi Danish dake a zaune Ya Wan lumshe idanuwanshi, ?o?ari ya ke ya hana kanshi yin bacci gudun kada yaja masu matsala, zu?unnawa tai agabanshi

 Danish taya akai su Jamima su ka rayu? Bayan kai da kanka ne ka faWa mana cewa zuciyarsu ce ta buga ware idanuwanshi yai akan fuskarta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, damuwarta akan ?an uwanta, bata damu da kanta ba, ?arantar shekarunta yafi komai Waure mashi kai, yadda harta iya jure waWannan wahalhalun rayuwar wanda yayi imanin ko wani babban ba zai Iya jurarsu ba.

 Danish bana so ina magana kana share ni, ka faWa min ta ya ya akai su ka rayu? A iya sanina idan mutun ya mutu baya tashi, Sai gashi su Azeeza sun tashi, ko dai ka yi amfani da sihirinka ne wurin dawo masu da rayuwarsu... ? A ruWe tai maganar babu kwanciyar hankali atattare da ita, a hankali ya Wan motsa la66ansa.

 My Angel, u should stop talking about them, ba ki da lafiya u need a rest, dam?ar wuyar best Win jikin tai sosai ta fashe mashi da kuka tana faWin Danish ka faWa min dama kasan suna araye shi ne ba ka bari mun goyo su Deeja mun taho da su ba? Me yasa ka yi mana ?aryar cewa zuciyarsu ce ta buga ? Tana magana tana ku ka, raunin gefen bakin ta tuni ya fara tsastsafo da jini.

Ranta yai mugun 6aci zuciyarta ta harzu?a, A haukace ta mi?e tana faWin Zan koma na taho da su Deeeja, ban damu da in rasa raina ba, a hanzarce ya mi?e jin abunda tace, ido cikin ido su ke kallon juna Am sorry Angel i don t mean to hurt u, kinsan bana ?arya, sannan bani da amsar da zan baki that s why nayi shiru, hatta su Azeeza ban san suna araye ba, a daren jiya na yi ?o?arin binne su cos bana son ku farka ku taras da gawawwakinsu, hakan zai fama ma ku ciwon da ke a cikin zuciyarku, nayi amfani da sihirina wurin tsaga ?asa har na fara sanyasu a ciki idona ya sauka akan yatsun ?afafuwansu dake motsi, i was shocked cos ban yi expecting din zasu rayu ba, kin ji yadda akai nasan suna a raye

kamar ta so ta fahimce shi sai dai wani sashe na zuciyarta ya?i aminta dashi, girgiza mashi kai tai Ni dai zan koma kurkuku in Wauko su Deeja, Saboda ina ji araina cewa Suna araye

Ya fahimci damuwace ke ?o?arin zautar da ita, Zaiyi wuya ta fahince shi, yasan halin kayansa da rigima ga kafiya da taurin kai, juyawa ta yi tare da nufar ?ofar fita daga kogon dutsen, da sauri Ya bi bayanta tare da ru?o arm Winta ya janyota zuwa jikinshi, sosai ya matseta.

 Angel daji ne fa, ba mu a kusa da kurkukun ?addara, ta zarar awanni ce, A daren Jiya bayan mun fita ni ne na Wauko ku na dawo da ku nan duk don na sau?a?a maku wahala da?yar ya ke magana, damuwace ?arara akan fuskarsa, ?o?arin raba Jikinta tayi daga nashi.

Zuciyarta ce ke azalzalarta sam bata fahimtar kalamansa, idanuwanta sun makance

 Ka sake ni Danish, nasan ko nace kaje ka Wauko min su Deeja ba za ka je ba, don haka ni zanje, saboda ina ji araina ?an uwana suna araye basu mutu ba gashi mun baro su a hannun Azzaluman mutanancan..... cikin shesshe?ar kuka ta ?arasa maganar, duk yadda yaso ya hanata tafiya ta?iya, har kwatanta mata haWarin da dajin gare shi amma ta kafe akan sai taje, sakinta yai idon shi akan bayanta, sam babu kuzari a jikinta ahaka ta fuce daga cikin kogon dutsen, Hasken ranane ya galle mata idonta da sauri ta lumshe su na Wan sakanni kafin ta ware su tana ?arewa ?urmin Dajin kallo, DaddaWar iskar dajin ce ta ratsa sassan jikinta ni imtacciyar gaske, hatta sumar kanta sai kaWawa take yi saboda ?arfin iskar, saboda taurin kai irin na Angel da kasada, Ahaka ta soma tafiya tana nufar cikin dajin ita ala dole saita gano inda kurkukun ?addara ya ke, tun kan aje ko ina ta fara tsorata da ganin ?ananun halittun da ke yawo Saman bishiyoyi, duk da haka bata sare ba taci gaba da tafiya hada Wan saurinta da gudunta, ko takalma babu a ?afarta.

Tun bayan fitarta Danish Ya fito daga cikin kogon dutsen, ya goya hannayenshi saman faffaWan ?irjinshi Yana kallon bayanta, Ta yi matu?ar bashi mamaki, duk da ya fahimci babu hankali atattare da ita, in ba haka ba ta ya ya wanda ya tsira yake ?o?arin komawa ga halaka. Yarinta ce ke damunta da kuma son ?an uwanta.

Tana cikin yin tafiyar nan, kukan namun dawa Ya dakatar da ita cak ta tsaya tana ?arewa wurin da take atsaye kallo, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Snake Win dake bin jikin bishiya yana ?o?arin saukowa ?asa, zaro ido waje tai a gigice ta fasa ?ara tare da juyawa da gudun gaske tamkar zata tashi sama, majicin na ?arasa saukowa yabi bayanta, tashin hankali duk ta bi ta rikice don ta fahimci ita yake bi, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a yin tozali da maciji ido da ido ba sai yau da Allah ya haWosu, Tarasa gane ta wace hanya zata bi ta koma cikin kogon dutsen.

Danish ta dinga ?walawa kira kamar ma?oshinta zai 6allo, sai da ta gama galabaita cikin rashin sa a tai tuntu6e da dutse gaba Waya ta tafi zata kife ?asa, ?iris ya rage ta kife ?asa a lokacin da ba ta yi tsammani ba taji Ya dam?o ta tare da kwantar da ita saman chest Winsa.

?an?ameshi tayi sosai ta fashe mashi da kuka tana zazzaga mashi masifa akan me zai barta ita kaWai acikin daji? Idan ma don saboda ta yi mashi kafiya ne, bai ga ita yarinya bace, tun da fara mashi faWa bai tanka mata ba, hannayen shi biyu suna tallabe da ita, sai da ta yi mai isarta, tukunna ta buWe kumburarrun idanuwanta akan fuskarshi, tun daga kan tausasan red lips Winsa ta soma bi da kallo har izuwa ga dogon hancin sa kafin ta Wauke idon nata ta Waura su kan sexy eyes Winshi masu matu?ar jan hankali.

?o?arin shagala su ke yi da kallon Juna, tunawa da ?an uwansu da su ka baro a kogon dutse ne yasa tayi saurin katse masu kallon ?urullan da suke bin juna dashi Danish mu koma kada wani abu ya same su girgiza mata kai yai in a smoky voice ya furta mata ba abunda zai same su, ina sane dasu, na rufe kogon dutsen babu wani abun cutarwa da zai Iya tunkarar su Sam hankalin bai kwanta da kalaman shi ba

 Danish ni dai mu koma, ashagwa6e tayi mashi maganar, ita kanta batasan ta sanya shagwa6a ba


 Zamu koma, but before that, Inaso ki raka ni cikin Dajin in nemo mana abunda zamu ci, ko kina so su farka suna Jin yunwa ne ?

Girgiza mashi kai tayi a a amma ni ba zan bi ka ba, Ka maida ni cikin kogon dutsen in ya so kai sai ka je nema mana abunda zamuci kafe ta da ido yai, hakan yasa ta jefa mashi harara haWi da murguWa mashi baki, munin fuskarta bai hana shi ganin kyanta ba, musamman da ta yi mashi abunda ke jan hankalin shi gareta, Harara da murguWe abun A jinin ta ya ke.

 Idan ba za ki bi ni ba, Ga hanya nan ki koma kogon dutsen ni kin ga tafiyana yai maganar tare da nufar Cikin dajin, da ido tabi bayanshi da kallo, ranta a 6ace yasan ba zata iya kai kanta ba shiyasa yace ta koma, Tunawa da macijin da ya biyota ne yasa ta zabura da gudu tabi bayanshi, Yana cikin tafiya yaji ta zura hannunta cikin nashi, ?ayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi.

Ta yi tsammanin Iya abincin da zasu ci ne zasu nemo, ba ta san plan Ya shirya mata ba, Yanayin Iskar dajin ba ?aramin ni ima ta saukar masu ba, Suna tafiya suna kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta Wan kalli fuskarshi Na gaji Danish ?afata ciwo ta ke yi min ba tare da ya amsa mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan Ya mi?e Wauke da ita, ba ?aramin daWi taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar kurkuku, ta ?an?ameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman sha?ar mashi fatar wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari ?al dashi.

 Mun ?araso, Jin abunda yace ne yasa ta Wago da kanta, tana ?arewa wurin kallo, nan ta ke ta ji tana sha awar shan ruwan, Zu?unnawa yai ta sauko daga saman bayan nashi, a jere suka tsaya suna bin ruwan da kallo, ga dukkan alamu ya burgesu .

 Danish ?ishi na ke ji, nasan kaima kana ji, mu sha sai mu Webi wani mu kai ma su Parveen ko ? Ba tare da ya juyo ya kalli fuskarta ba ya soma magana Wanka nake so nayi maki, saboda kinyi muni, jikin ki yayi datti

Har saida gabanta ya faWi jin abunda yace, juyowa yai da fuskarshi ya kalleta tare da kashe mata ido Waya

 za ki iya cire kayan ko in taimaka maki ne ? gabanta ne ya dinga faWuwa sai ta ga kamar ya canza mata, babu alamun wasa akan fuskar shi yai maganar.

Ganin yana matsowa kusa da ita, yasa ta juya da niyar ta gudu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login