Showing 39001 words to 42000 words out of 260999 words

Chapter 14 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

twin stairs da U-shaped stairs, Idan ma mutun baida ra ayin Hawa Benan Kowane Villa yana Wauke da residential elevator wadda aka fi sani da lifter, tun daga Hawa na farko zata Wauki mutun har izuwa hawa na Uku, dai dai da cokalin amfani na gidan babu wanda aka ?era a ?asa Nigeria, kaf kayansu daga ?asar waje ake shigo dasu, mai karfin imani ne KaWai zai iya rayuwa acikin estate dinsu ba tare daya shagala daga yin ibadarshi ba, sai dai ta inda masu rayuwa cikin gidajen zasu burge ka Allah ya hore masu baiwar Ilmin duka na addini dana zamani, wayayyun mutanene masu daraja da ?ima a idon duniya, Sun Iya takun su ba zaka ta6a Iya aibatasu ba, saboda kyawawan Wabi unsu da halayansu, komai nasu is Extraordinary.

Tun da garin Allah ya waye masu aikin gidan su ke ta kai komo, kowaccensu ta yi dressing cikin chef s uniform launin farare, ?wararru ne a 6angaren girke girke da gyaran gida, basu wasa da aikin su, Suna ba lokacin mahimmancin sa, kuma suna takatsantsan wurin kula da bu?atun mutanan gidan.

A tsastsaye su ke a Cikin Katafaren Kitchen Win gidan mai girman gaske, A sha?e ya ke da kayan Amfani, ko ina a tsaftacensa ya ke tamkar ba amfani su ke yi da shi ba, aiki su ke yi tu?uri babu kama hannun yaro, Matasan ?an mata da manyan su, wasu suna aikin wanke nama wasu suna yanke yanken kayan lambu agaban cutting board, yayin da wasu su ke agaban manyan gass cooker suna kula da girkin da suka Waura, akwai waWanda ke a tsaye in front of kitchen microwave suna aiki.


?amshin girkinsu ya karaWe ko ina tun daga cikin kitchen Win har izuwa Babban falon gidan.

Babbar macace ta shigo kitchen Win domin duba masu aikin don ganin yadda komai ke gudana, A ?alla za ta kai shekara 40 a duniya, Ta kasance Waya daga cikin Masu yi masu hidima a gidan, ita ce head maids shugaban ma aikatan Cikin gidan, Macace mai yawan fara a ga son mutane, ma abociya son Shigar fararen Kaya, A yanzu haka pakistan ne a jikinta riga da wando farare ?al anyi masu adon duwatsu launi daban daban, ?afarta na sanye cikin flat shoes, bakowa bace wannan face *DIVYA* ba indiyace amma sunfi kiranta da *HAJJATY* tun da ta shigo kitchen Win masu aikin suka fahimci itace tazo dubasu nan fa suka ?ara dage damtse suna aiki duk don su ku6uta daga faWanta.

A hankali ta ke zagaye Kitchen Win, Hannayenta a goye saman ?irjinta, Waya bayan Waya take binsu da kallo, na Wan wani lokaci kafin tayi masu gyaran murya, kusan atare su ka Wago suna kallonta, Hannu ta tafa masu

 Aikin ku yana kyau, You ladies Are doing a fantastic job, everything smells delious, i m sure WanWanon girkin zaiyi daWi kamar yadda ?amshinsa ya ke da daWin sha?a, Ina ?ara jinjina ma ku, ta ?arasa yi masu maganar tare da Waga masu babban yatsan hannunta na dama alamar Jinjina.

Murmushi ne Ya bayyana akan fuskokin su, ba ?aramin daWi suke ji ba, Idan hajjati ta yabe su, suna matu?ar sonta kuma suna girmamata saboda kyawun halayanta da Wabi unta.

 Dame dame aka kammala ne ? ta yi tambayar tana kallon faces Winsu, Abla ce ta soma Yi mata jawabi

 Kebab with chips, Beef shawarma, burger and pancakes,... kusan abu goma ta lissafa mata, Jinjina kai Hajjaty ta Wanyi kafin ta Waura da cewa Kada na katse maku aikin ku, lokaci Yana ?urewa, Ku hanzata ku kammala, 

 An aikawa Hajiya saratu Breakfast Winta! ? da sauri Safa tace yanzu nake shirin zuwa in kai mata, Nice nike duty part Winta GyaWa kai Hajjaty ta yi.

 Okey, shirya min fresh fruit ki haWa min da kakkauran tea, Wadda aka kira da Sarah ta amsa mata da toh, ba tare da 6ara lokaci ba ta shirya mata kayan marmari a cikin ?ayataccen wooden tray, tare da cup of tea, ta mi?a mata hannu biyu tasa ta kar6i tray din tare da juyawa ta fuce.

Bayan fitarta, Fira ta 6arke a tsakaninsu

 Safa ashe ke ce kike duty a part Win Aunty jarabatu zaki sha Masifa,  Abla ce tai mata maganar, murmushi suka saki, sophia tace Ai hajiya saratu ba daga baya ba, In dai wurin Iya masifane, Last time fa da naje kai mata abinci cewa ta yi wai na gutsiri ?afar kaza, hada cewa ita bata yarda damu ba, wama ya sani ko mun saka mata guba acikin abinci donta ci ta mutu, dariya suka saka


 Tana da wuyar sha ani bata yarda da kowa ba, In ba wannan Mijin nata ba, Uban son banza suruki da zaman gidan surukai Ko kunya babu sophia ce tai maganar, Safa tace Ai koni na samu wurin zama agidan nan abunda zanyi kenan, waman taraka bati siddan, shiyasa a kullum nake ro?on Allah ya bani bugun zuciyar family Win, Wlh idan na Aure shi nadaina sakin baki ina bacci, nafilfili zanta yi akan Allah ya dawwamar da auran mu don nasan ma?iya da mahassada ba zasu bar mu mu zauna lafiya ba, Musamman Mahaifiyarshi uwar Ji da izza, kinga matar nan bata Waukar raini batason Mu amala da bare.... tun da ta fara zuba suke binta da kallon rainin wayau saida takai aya tukunna Abla tace you don t ave sense, Dama najima da zargin kwakwalwarki ba dai dai take aiki ba, Ko Jazz da muka raina wlh yafi ?arfinki, Ni kaina ba zance bana son Owais ba, amma ance abunda yafi ?arfinka ka haWa shi da baka so kwa6e fuska Safa tai kiyi min fatan alkhairi kawai, Nima a hausa novels ni ke jin irin hakan na faruwa, mafi yawanci zaki ga ?ar aiki ta auri Wan masu gida, wani sa in ma mai gidan ta ke aurewa.... sautin dariyarsu ne Ya hana ta ?arasa maganar, suna fira suna aiki,

 Safa kina atare da wahala, in dai ko zaki cigaba da tunanin zaki samu abunda ki ke so kamar yarda ki ke karantawa ahausa novels, Ni Bance baya faruwa ba amma Allah a zamanin da mu ke ciki zaiyi wuya, mai kuWi sai ?ar mai kuWi, talaka sai Wan talaka, Ina jiye maki tsoron heart attack ya kama ki silar son wanda bai son Kina yi ba, a ?arshe ki ?are a emergency room

Dariya suka saki gaba Wayan su, kwata kwata firar da suke yi bata Wauke masu hankali daga yin aikin su ba, manyan cikin su ne kadai basa magana sai dai idan sun faWi abunda ya basu dariya su Wan murmusa.

 Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa, duk irin tarin dukiyar nan ace Iya mutun goma sha biyar ne ke da gadonsu Abla ce tai maganar.

Abla tace Nikaina abun na damu na, Yana yi mun ciwo a zuciya, na rasa gane meyasa basa son haihuwa, daga mai ?a ?a biyu sai mai ?a ?a uku, Allah ya hore masu wadatar arzi?i sai ?a ?a ne zasu gagare su? Abun na ?ona mun rai, komai nasu na rayuwar turai, Mu da zasu taimaka su Aure mu, duk bayan ?an watanni zamu dinga sakar masu ?a ?a tuni zamu cika famiy Win

Maganar Abla ba ?aramin dariya ta basu ba, Sofiya tace Sannu kaza suma ai suna son ?a ?an, sannan bada son ransu bane ba su haihuwa, ?addarar su ce ta zo masu ahaka, naji labari a bakin Hajjaty saboda tafi mu daWewa a gidan, Suna haihuwa amma ?a ?an basu zuwa da rai, A mace ake haihuwarsu yawanci da zarar sun yi haihuwar fari da ta biyu zaiyi wuya kiga sauran sun rayu a matattu su ke haihuwarsu, Allah ni tausayi suke bani, Musamman prime minister Hateem shifa Bai ta6a haihuwar Wa Namiji ba, shi da matarshi Gimbiya mujeedat, ?a ?a biyu duka mata, rashin haihuwarsu ba ?aramin gi6i yai masu ba arayuwarsu, Ki duba fa hateem shine yafi kowa arzi?i a family Winsu daga shi sai sharafudeen, mamakine akan fuskar Wasu daga cikinsu waWanda basu daWe da fara aiki ba

 Abun da Waure kai, Kuma an duba lafiyarsu? Ko dai wata lalurar ce da suka gada tun kaka da kakanni ?

 Ko Waya, Tun daga ?asa Nigeria har zuwa ?asashen waje an bincika lafiyar kowan nan su, Ba su da wata matsala da ta shafi ?wayoyin haihuwarsu, lafiyar su ?alau, har manyan malaman addini saida kakansu ya sanya don su bincika mashi meke faruwa a zuri arshi, Sakamakon Waya ne dana asibiti, basu da wata lalura,

Jikin su duk yai sanyi, Basu ta6a sanin zancen haihuwar da matansu keyi yara suna zuwa ba rai ba sai yau da sophia ta sanar da su.

 Allah mun tuba ka yafe mana, shiyasa akace zato zunibi koda ya kasance gaskiya, Gulma ba ta yi rana ba, Mune kullum tsegumin mu akan suna yin irin rayuwar turai ba su son haihuwa ashe ba laifin su bane, jarabtace daga Allah murya asanyaye Safa Tayi maganar.

Abla tace  Na tausaya masu, kuma In sha Allah zamu ta ya su da addu a, akan Allah ya yaye masu lalurar da ke damun su shiru suka Wanyi Na wani lokaci, daga bisani Safa ta shirya Kayan breakfast Win Hajiya saratu A Babban tray ta jera mata su, Bayan fitarta daga Cikin kitchen Win su ka Waura da wata firar, sam basa gajiya da firar Familyn Obinna.


 Muna fa da gagarumin bikin ranar zagayowar Haihuwar Obie, Nasan za ae shagali na kece raini, za a yi 6arin Dollar da pounds, Aranar zamu ga Zaratan ?a ?an Obinna da Jikokinshi waWanda basa a ?asar, Ina da tabbacin Owais ma zai halarta

Fuskar Sophia Wauke da farin Ciki tayi maganar, Abla tace Anya ko Owais zai zo? Kinsan fa halinshi, samun lokacin shi abune mai wuya

 ai ko baiyi niya ba sai obinna Ya matsa mashi akan ya zo, Kinsan fa kaf cikin jikokinsa yafi ?aunar Owais, kowa yasan da wannan zancen, Kinga ko ba zai so ayi shagalin nan ba tare da Owais Ya halatta ba, acewar Abla

Murmushi Sopy tayi  Can t wait to see Allah Ya nuna mana Lokacin, Dole naje ayi min wankin ido, don na samu damar ?are Mashi kallo

 Da rabon kisha mari, Owais baya son Kallo Idan Yana magana mutun bai isa Ya Waga ido ya kalle shi ba, Sannan ba a katse shi, Sau?in shi Waya Idan har kika karanci halayanshi da Wabi unsa tsaf zaku zauna lafiya, mutunne mai sau?in kai baida girman kai, Yana da tausayi ga taimakon na ?asa dashi..... tun da ta fara jera masu Kyawawan halayanshi bata tsagaita ba har saida Landline Win dake a bakin ?ofar fita kitchen Win ta yi ringing tukunna ta dakata da yin magana, da sauri Sophia ta fuce ta je ta Wauki landline Win Ta Waga kiran daya shigo, Cikin girmamawa tayi sallama, Jikinta sai 6ari yake yi.

 Cofee.... Iya abunda Taji an furta mata acikin wayar, jin yayi rejecting yasa ta zame ta daga saman kunnanta ta ajiyeta saman table, Dawowa Cikin kitchren Win Tayi Hankalinsu gaba Waya ya dawo kanta.

Har suna haWa baki wurin tambayar ta  Wanene Ya kira kwa6e fuska tayi tare da cewa Nakasa gane muryar wanene acikinsu, Zaid ne ko Zayn, Coffee su ke bu?ata, wa zai kai masu ? Ta yi tambayar tana kallon sauran. Shiru babu wanda yace zai kai, saboda Mugun tsoron shiga part Winsu suke Yi, saboda masifarsu,

 Kinga tun da ke kika Waga Kiran nan Ki lalla6a ki je kawai ki kai masu awuce wajen Acewar Abla, Yamutsa fuska marwa ta yi, Ba yadda ta Iya don dole ta haWa masu coffee acikin mugs guda biyu ta Waura saman Plate ta fuce daga cikin kitchen Win.

Tun lokacin da Able ta fita hannunta Wauke da tray Na breakfast Win Hajiya Saratu, Kai tsaye ta nufi Part Winsu, Tun kan ta ?ara sa gaban ?ofar Wakin ta daddaWan ?amshin turarenta Ya daki hancinta, macace mai son ?amshi ga iya Waukar Wanka, A bakin door Win Ta tsaya tare da Yi mata sallama, daga cikin Wakin tajiyo muryar Hajiya saratu

 U can come in A hankali ta tura ?ofar ta shiga, Hajiya saratu tana azaune tsakiyar Katafaren gadonta, jikinta na asanye da jallabiya, Kanta babu Kallabi Kitson zanene all back Wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaWarta, fararen idanuwanta suna a manne da farin glass medicated, tana da duhun fata mai kyan gaske, Hutu ya zauna mata, Hankalinta gaba Waya yana akan tsadaddar Apple Laptop Win da ta ke yin operating, ga dukkan alamu aiki ta ke yi.

 Once you re done looking at me, please put the food on the table and leave my room. Muryarta ce ta fargar da Safa daga kallon ?urullan da ta ke bin ta da shi, Adabarbace ta gaishe da ita Ina kwana Hajiya, Guntun tsoki taja ba tare da ta amsa mata ba, ko kallo ba ta ishe ta ba, asaman front table din bakin gadon, Safa ta Waura mata tray din

 ko akwai wani abu da ki ke bu?ata  ? cikin Jin shakkarta Safa ta yi mata tambayar don tasan halinta, in har bata ba mutun iznin tafiya ba, yai yun?urin Juyawa zai tafi atsawace zata ce mashi da Iznin wa!

Safa har ta gaji da tsayuwa shiru bata tanka mata ba, tamkar bata san da mutun awurin ba, Halinta ne share mutane, sai da ta mula ta sha iska tukunna ta ba ta zinin tafiya, bayan fitar Safa daga Wakin, Ta dakata da yin aikin laptop Win, Yun?urawa tayi tare da kai hannu ta dam?o Burger Ta soma turata abakinta tana ci, Bata wasa da Cikinta, Cikin ?an?anin lokaci ta handameta, ta kuma janyo Chicken wings tana ci, baya tagama ta Wauki bowl Win dake sha?e da plaintain chips hannu baka hannu ?urya kamar mai fama da cutar yunwa, Saida ta lamushe komai, a ?arshe ta kora da ruwan lemu mai sanyi.

 DaWina dake bakya wasa da Cikin ki, Jin muryar Mijin nata yasa ta Wago da eye balls Winta akan fuskar shi, Daga cikin toilet ya fito waist Winshi Waure da towel, ?irarshi tamkar Wan wrestling, Kakkarfan mutunne Jibgegen ?ato, Kyakkyawan ba indiye Sumar kanshi akwance luf saman kanshi, Ga wani kwantaccen saje gefe da gefen doguwar fuskarshi,  ta6e mashi baki Tayi meye haka? Bana hanaka yawo da towel a qugunka ba? Yanzu da ace mai aikin nan tana acikin Waki ka fito fa? Fuskarta aWaure tayi mashi maganar, Matsawa yai kusa da ita yaWan ran?wafa saitin fuskarta yaushe zaki daina kishina? Murga mashi baki tayi Bansani ba, Ni dai na faWa maka, Karka kuskura ka ?ara fitowa Waure da guntun abu a qugunka bana son ta6ara Ido cikin ido suke kallon Juna.

 ?a ?an mu Uku, kowan nan su Ya mallaki hankalin shi, Na yi tsammanin zaki rage kishi na da kike Yi harara ta watsa mashi pls Ka wuce ka je ka sanya suturarka, bana son ganin ka ahaka Hannu ya kai yana ?o?arin warware towel Win gabanshi da sauri ta dam?i hannayenshi aWan fadace tace Pravin meye haka? Yarinta ce fa wannan ? Kashe mata ido Waya yayi fuskarshi Wauke da murmushi yace indai ina atare dake bazan ta6a girma ba, saboda tsantsar ?aunar da kike nuna min ta6e baki Saratu Tayi naji yanzu kaje ka sanya suturarka, Sannan me kake son Ci insa akawo maka Murmushin fuskarshi bai washe ba yace abunda kika ci shi nake sonci abar ?aunata, naga ma har kin kammala naki breakfast Win why ba ki bari na fito munci atare ba? ?aure mashi fuska tayi  Pravin mu fa ba ?ananun yara bane da zaka tsaya kana gayamin kalaman Soyayya, ko da ya ke nafa tuna kufa indiyawan nan bautawa soyayya kuke yi har ku tsufa kuna abu Waya cikin Zolaya ta ?arasa maganar, gyaWa kanshi yai komi zaki ce bazanji haushin kalamanki ba, Amaryata kuma uwargidana, sannan uwar ?a ?ana abun alfaharina, lumshe ido ta Wanyi idan zata biyewa pravin ba zai barta taci gaba da yin aikinta ba, gwanine a fagen Iya soyayya da daWin baki, Ya ?ware wurin Iya jan hankalin mace.

 Romeo, now your Juliet is at work, I m almost done, zansa a kawo maka breakfast Win ka, Ni da kaina ma zan baka abincin abaki Amsa mata yai da Okey, Da?yar ta lalla6a shi Ya mi?e ya nufi Cikin Wakin Yana tafiya tana satar kallon Bayanshi, a gaban closet Win kayanshi Ya tsaya tare da kai hannu ya buWe

 My Juliet ba ki faWa min kayan da ki ke so In sanya ma ! Murmushi ta saki Yau babu aiki, ka samu hutu don haka Nafi sha awar ganinka Cikin shigarku ta al ada, Ya gane me take nufi, riga da wando Ya curo kalar na mazan Indiya ya sanya su ajikinshi, sun bi shape din jikinshi yadda kasan matashin saurayi saboda haWuwarshi.

Bayan ya kammala Shirya kanshi, Hajiya saratu tasa aka kawo mashi breakfast, Da kanta take bashi abaki Yana ci, mugun son shi ta ke yi, ta mutu akan pravin, kamar yadda shima yake ?aunarta, Allah Ya hada jininsu. Babu mai cin moriyarta irin Mijinta, komai nata mallakin shi ne.

Lokacin Da Sophia ta ?arasa Bedroom Win twins dake acan Upstairs Second floor, Jikinta na kakarwa ta yi knocking ?ofar, almost 3 times kafin tajiyo muryar Waya daga Cikinsu  you can come in Numfashi taja kafin ta tura ?ofar HaWaWWen bedroom Winsu, Sanyin A.c da ?amshin Turarensu ne Ya daki hancinta har sai da ta lumshe idanuwanta saboda tsabar yadda ?amshin Ya kurWaWa ta ?ofofin Hancinta, tunkan ta shiga ciki Ta hango ?aya daga Cikinsu A tsaye Gaban tan?ameman dressing mirror Daga shi Sai short a jikinsa launin ja, Yayin da twin brother Win shi yake a kwance saman gado rabin jikin shi lullu6e


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login