Showing 207001 words to 210000 words out of 260999 words

Chapter 70 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

munyi kuskure, amma shima jazz din hada laifinshi, Yakamata ace komai zai yi ya sanar da Sir mubarak a matsayin shi na mahaifinshi bawai yayi gamon kanshi ba, kuma a yanayin yadda Sir mubarak yake riskarshi Yana yin waya ta sirri, kalaman da yake furtawa sun yi kamanceceniya dana masu safarar mutane

Tiger ya Waura da cewa yanzu haka sun tafi asibiti dashi, Muna jira muji daga gare su, In sha Allah zaiji sau?i
Numfasawa big guy yai, jikinshi duk yai sanyi kamar wanda aka zarewa laka, babban tashin hankalin shi halin da suka jefa jazz basu ta6a tsammanin abun zai jaza mashi matsala ba.

Tuni idanuwan big guy sun kaWa jawur tamkar zai fashe da kuka Ya soma yin magana ba laifin shi bane, laifinmu ne da muka hanashi yasanar ma kowa dangane da aikin da muka sanya shi, saboda bama son kowa ya sani

komawa yai daga gefen gadon dakin Ya zauna, Yana duban Yaran dake raku6e jikin bango, idanuwansu sunyi luhu luhu.

Mai ta6in hankalin tuni tayi shiru, sai faman zazzare idanuwanta take Yi tana dubansu.

Tiger yace shi kanshi Chief Owais bazai ji dadi ba, ranshi zai Iya 6aci amma nasan zai fahince mu
Ganin yadda yaran suketa Yin hammar bacci, yasa Big guy yi masu magana Kuje ku kwanta, Zuwa gobe idan Jazz Yaji sau?i zamu dawo maku dashi

Mi?ewa su ka yi a jere suka nufi hanyar fita daga Wakin jikinsu babu ?wari, hankalinsu ba kwance yake ba saboda Jazz dinsu da babu lafiya.

Har sun kusa fita daga Wakin, Big guy ya kwaWawa Waya daga cikinsu Kira  Hawwa! zonan, matashiyar daya kira da hawwa ta juyo tana dubanshi, Ki ru?e hannun khadeeja ku tafi da ita daki ta kwanta ya fadi hakanne don yasan su kadaine zasu Iya control dinta har asamu tayi bacci.

Muryarta asha?e take fadin ni bazan bisu ba, kuma bazan Yi baccin ba, wallahi sai kun dawo mun da jazz dina

Lallashinta mutumin dake ru?e da ita ya somayi kinsan dai bazanyi maki ?arya ba khadeejata, da kaina zan dawo maki dashi, Yanzu dai kije ki kwanta gobe zaki ganshi, amma idan har bakiyi bacci ba, toh bazan dawo maki dashi ba
Kwa6e mashi fuska tayi kayi al?awari ?
Jinjina mata kai yai in sha Allah ta amsa mashi da toh, sakarni inje in kwanta sakinta yai, tafiyarta sam babu natsuwa da sauri ta nufi su hawwa ta ru?e hannunta acikin nata suka fuce daga Wakin.

Bayan fitarsu, Big guy ya mi?e ya dubi mutumin Muna bu?atarka da gaggawa, ka koma Waki ka sanya sutura a jikinka, idan kuma zamu Iya tafiya haka toh, ya fada yana nuna gajeran wandon jikin shi da hannu.

Mutumin yace bari naje na sanya jallabiya, ?wara aganni da mutuncina da zolaya ya faWa, murmushi sojojin suka saki, fice wa yai daga dakin.

 Yalla6ai wani abu na faruwane ? Tiger ne ya jefa ma Big guy tambaya kusan haka sai dai kasan yanayin aikin mu jinjina kai big guy yai don ya fahimce me yake nufi
Shigowa Wakin matashin saurayin yai, Jikinshi sanye da jallabiya fara tayi mashi kyau.
Mi?ewa big guy yai tare da kallon su tiger zamu tafi gidan chief, babu tabbacin zamu dawo yau, wani muhimmin aikine me girma agaban mu, dan Allah ku kula da yaran, babu wadataccen tsaro agidan amsa mashi sukayi da toh, army boy yace Amma yalla6ai zaku sanarma chief abunda ya faru tsakanin Jazz da sir mubarak ?
Big guy yace ya zama dole mu sanar dashi, sai dai ba yanzu ba tunda shi kanshi hankalin shi ba akwance yake ba, amma idan komai ya lafa zamu fada mashi gyaWa kai army yai okey, Allah ya tsare hanya
Amsa mashi yai da ameen, kafin Yaja hannun mutumin suka fito daga gidan, jin ?arar tashin motarsu, Yasa Army da tiger suka sauko down, zuwa sukayi bakin gate din gidan suka datse shi, kafin suka koma palour suka zauna saman sofa suna fuskantar juna

Army boy yace tiger ya kaga yaran? Nayi mamakin kyawunsu, Allah yasa oga ya amince min in samu matar aure acikinsu tunkan ya ?are maganar tiger ya wurga mashi kallon harara amma baka da hankali, kai waWannan yaran sunyi maka kama da matan yaku bayi? Ka manta matsayinka ne? Karfa ka cika za?ewa, wallahi yazu kaji ka a saman kujerar lantarki kana kar6ar punishment, ni kaina ?an matan sun burgeni, gaskiya Oga ya iya kiwo, fatarsu har ?yalli take Yi sunji hutu abunsu, yara kamar matan aljanna gashi har gadon baya, gaskiya dakyar idan iyayensu ?an nigeria ne

Ya fada yana yin hamma ni yanwa ma nake ji, Allah yasa suna da abinci agidan, nasan ba za a rasa farfesu ba tunda Chief owais ne ke kula da cinsu nasan za ayi harka ta arzi?i, duba mana kitchen dinsu yai maganar Yana duban Army boy, mi?ewa yai da sauri ya nufi hanyar kitchen, har zai wuce yaci karo da freezer, buWewa yai ya le?a ciki, Kayan marmarine nunannu, da drinks

washe baki yai yana faman shafa ciki yace mutumin yaufa kakarmu ta yanke sa?a
Tiger yace ba kallo zaka tsaya yi ba, ka shiga kitchen ka dauko tray ka kwaso mana sauran abincin da suka rage amsa mashi yai da toh, da sauri ya shiga kitchen.
Jim kaWan sai gashi ya fito hannunshi ru?e da katon tray, daga saman tray din plate biyu ne, Waya na fried rice daya kuma na chicken wings, saida ya fara tsayawa agaban freezer ya buWe ya dauko masu kayan marmari ya jera gefen plates din ya ?ara da robobin juice masu sanyi, tiger sai faman haWiye yawu yake yi,.

Zama su ka yi saman lallausar carpet din falon, kamar masu fama da ciwon yunwa haka suka dumbuza hannu, sunaci suna fira.

Kamar daga saman suka jiyo muryar matashiyar nan mai fama da ta6in hankali tana fadin wayyo Allah, mayu zasu cinye mana abincinmu! afirgice suka Wago suna kallonta, daga can saman bene take zazzaga masu masifa, gashin kanta duk ya rufe gefe da gefen fuskarta, da gudu ?ar uwarta hawwa ta fito daga Waki, Taja hannunta suka koma ciki, ta rufe kofar ta yadda bazata sake fita ba.

Tiger yace jarababba, wallahi hartasa gabana ya fadi ya fada yana dariya
Army yace ai daga ganinta anyi rashin ji a ?uruciyarta, kunnuwanta tsaitsaye suke irin na zomo, gata kyakkyawa da ita cigaba da cin abincinsu sukayi hankalinsu kwance, bayan sun kammala army boy ya tattara kayan abincin ya maidasu kitchen, a saman sofa suka kwanta ga sanyin A.c, sufa ashar kakarsu ta yanke sa?a.

*Daular Alhaji Musa*

*BENAZIR=ؔ?*


Tayi nisa acikin baccinta, ba zato ba tsammani taji an sha?e mata wuyanta, sha?a bata wasaba, nan take numfashinta ya soma kiciniyar Wauke wa, mutsu mutsu ta somayi yi tana harba ?afafuwanta, hannayenta biyu ta daura saman wuyanta a ?o?arinta nata kwace kanta daga hannun mutumin dake yunkurin kasheta, wata irin zuface ta soma tsastsafo mata saman goshinta, zuciyarta tashiga harbawa da ?arfi da ?arfi, ta zazzare idanuwanta cikin duhu bata Iya ganin komai saboda sun kashe ?wan dakin, duk yadda taso ta ?waci kanta ta kasa, an toshe mata baki babu halin ta ?wala kira don azo ataimaketa, hannunta tadinga lalubawa saman mattress cikin sa a ta cafko hannun zeenatu dake akwance gefenta, cikin fitar hayyaci take tsunkulinta har saida zeenatu ta farka tana shesshe?ar kuka ta furta wai.. wanene ke cunkulina tunda zeenatu tayi magana, Benazir taji an sakar mata wuyanta, fashewa tayi da matsanancin kuka, sakamakon raWaWin azabar da taji wuyanta nayi mata, a matu?ar ruWe zeenatu takai hannu saman bedside drawer ta kunna fitila haskenta ya haskaka saman gadon, muryarta adabarbarce take fadin Auntyna meya faru kike kuka? Baki da lafiya ne ? da rarrafe ta ?arasa gaban benazir tana duban fuskarta, a lokacin ta zabura a furgice ta mike zaune tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta biyu ru?e da wuyanta, fuskarta tayi sharkaf da zuba, ma?oshinta ya bushe ?amas, tsananin rudanine ya kamata, kokwanto ta somayi akan abunda ya faru da ita shin dagaske ne wani ya sha?e mata wuyanta ko kuwa mafarkine take yi ?

 Aunty Benazir dina, dan Allah kiyi min magana, meyasa ki yin kuka? Ko kinyi mafarki ne? Sam takasa buWe baki tayi ma zeenatu magana sai faman zazzare manyan idanuwanta take Yi tamkar kwayar zasu faWo kasa, ha?ika ta sha?i ?amshin mutuwa.
Dafa kafaWarta zeenatu tayi mafarki kikayi aunty? ko wuyanki yana yi maki ciwo ne ta fada cikin kulawa da nuna damuwa take duban fuskar benazir.

Dogon numfashi benazir taja yayin da zuciyarta ke harbawa da sauti mai ?arfi, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta, gaba Waya ta dabarbace tarasa gane meke shirin faruwa da ita! Idan mafarki ne tayi an sha?e mata wuya meyasa take jin raWaWin bayan tafarka daga bacci?

Shesshe?ar kukan zeenatu ne Ya fargar da ita, tana faman haWiyar yawu idanuwanta da fargaba take duban zeenatu
Da?yar ta iya buWe baki ta yi mata magana zeenatu ruwa! Ruwan zan sha
Tsagaitawa zeenatu tayi da yin kukan jiki na rawa ta sauko daga saman gadon, ta nufi ?aramin frigde din Wakin, ta buWe ta Wauko mata bottle water me sanyi ta dawo ta haura saman gadon ta mi?e ma benazir, yatsun hannunta na kerma ta kar6i roba ruwan tacire nurfin ta kafa abaki tana sha, ma?oshinta har sauti yake badawa kwat !kwat!. zeenatu ta natsu tana kallonta, gaba Wayansu sleeping dress ne ajikinsu.
Bayan ta gama shanye ruwan ta daura bottle din saman drawern gefen gadon,
Ajiyar zuciya tadan sauke, kafin ta dubi zeenatu data kwa6e fuska idanuwanta sunyi luhu luhu bacci bai isheta ba an tashe ta daga bacci
 Aunty ki faWamin meke damunki
Lumshe ido benazir tadanyi kafin ta waresu akan fuskar Zeenatu
 Babu komai ?anwata, mummunan mafarkine nayi
Ajiyar zuciya zeenatu tasauke amma aunty kin tada min hankalina, nayi tsammanin wani abunne ke damunki ko baki da lafiya, kuma naji kina cunkulina ta fada tana nuna mata damtsen hannunta, fatar wurin tayi jawur saboda tsunkulin da benazir tayi mata kiris ya rage ta fashe.
Jikin benazir ba ?aramin sanyi yayi ba, ganin irin illar da tayi mata
 Kiyi ha?uri ?anwata, bansan nayi ba, cikin magagin baccine na cunkule ki
Murmushi zeenatu tasakar mata kada ki damu auntyna, na fahimce ki, ?a?alo murmushi benazir tayi yarinyar ba ?aramin burgeta take Yi ba, ta damu da ita sosai,
 Ki koma baccinki, kada ki makara a school gobe
Muryar zeenatu da shagwa6a tace ae bana zuwa makaranta tunda na kammala secondry school daddy ya hanani cigaba da karatu, yace wai sai idan nayi aure mijin da zan aura ya amince min in cigaba da karatu tukunna zani barni

Jinjina kai benazir tayi har yanzu bata warware daga fargabar abunda ya faru da ita ba, dauriyace kawai take Yi don kawar mata da damuwar dake atare da ita.

 Idan kina son karatun, meyasa ba zaki fidda miji ba? Duk da ni aganina kinyi ?aranta da aure, gaskiya uncle bai kyauta maki ba
Sunnar dakai ?asa tayi cikin jin kunyar benazir tace to ai nima inason nayi auran kuma ma ina da mijin da zan aura da zolaya Benazir ta zaro idanuwanta masu dauke da bacci, da sauri zeenatu ta daura kanta saman pillow tana dariya
Kallon bayanta benazir tayi fuskarta dauke da murmushi,
 FaWamin sunan saurayin naki inji idan yayi mani
Muryarta ?asa ?asa tace ki tambayi yaya shureim, yasan shi zai fada maki sunanshi benazir bata kawo komai aranta ba, tace to zan tambayeshi idan Allah yakaimu gobe, yanzu dai mu kwanta muyi bacci amsa mata tayi da toh, atare suka kwanta, hankalin benazir ya?i kwanciya gani take tamkar abunda ya faru a mafarkinta zai faru gaske, hakan yasa ta rungume Zeenatu ajikinta, gudun kada a?ara sha?eta, addu o i ta karanto ta tottofa masu kafin ta lumshe idanuwanta.

Bakomai take tariyowa ba face fuskar tajuddeen, da fuskar baby din data bari acikin kwamin wanka, tuni hawaye sun wanke fuskarta, ta?osa su dawo ?asar, fatanta Allah Yasa taj dinta baiyi aure ba, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.

*Ex-prisoners=ؔ?*

Tsoro da fargaba ya hanasu runtsawa, sunyi zazzaune saman dining chairs, ummin america bata ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, sam takasa samun natsuwa, jefi jefi takan dago da ido ta dubi su Batul, Har yanzu hanna bata fito daga ?ar?ashin table ba.

Jemimah tana azaune saman laps din Haris Ta ?ankameshi tuni bacci yajima da yin awon gaba da ita, abun duniya ya ishi Parveen, Jikinta sai rawar Wari yake yi saboda ruwan data watsa ma rigarta, ta ji?e sharkaf, ga sanyin a.c abu goma da ashirin, azeeza data suma ta farfado tun bayan da sajeed Ya yayyafa mata ruwa, sai faman firgita take Yi, macijin tamkar Yana yi masu gizau, ga bacci a idanuwansu sai dai sun kasa runtsawa, kowa da abunda ke damunshi basu san meke wakana acikin gidan ba.

 Dan Allah Ku bani mayafinku In lullu6e jikina sanyi nake ji parveen ce tayi maganar, babu musu Batul Ta curo mayafinta ta mi?a mata ta sanya hannu ta kar6a ta lullu6a shi ajikinta.

 Ni nakasa gane meke faruwa! ya akai maciji Ya shigo gidan nan? Ummi ce ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta.

Shiru sukayi babu wanda ya tanka mata, babban abunda suke jima fargaba kada ace mutanan prison ne suka kawo masu hari, shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.

 Ni abunda ke damuna, Danish dinmu da unaisah, bansan awani hali suke aciki ba, Allah yasa babu abunda ya same su In a cool voice Batul ta furta maganar.

Tamkar ta tsokano Jemimah, cikin bacci ta fashe da kuka tana sambatun wayyo Allah genie dina, dodo zai cinyeta, kuje ku dauko mun ita da sauri Haris Ya toshe mata bakinta da tafun hannunshi kiyi mana shiru, ko so kike dodon Ya jiyo kukanki yazo wurinmu ?

Ba tare data buWe idanuwanta ba tace a a amma genie fa? Tana can ita da Danish dodo zai cutar dasu, Ni dai ku ?yaleni inje wurinsu ta faWa tare da buWe kumburarrun idanuwanta, da ?arfin hali tasoma kiciniyar saukowa daga saman laps din haris don ta fita daga dakin
Ummi tace kada ka bari ta sauko ka ru?eta, idan ba haka ba zata iya janyo mana macijin nan
Amsa mata yai da toh, ya rurru?e jemimah ajikinshi.
 Ki kwantar da hankalinki, babu abunda zai samu Unaisah, ai naga mutanan nan masu ba?a?en kaya, wata ?il ma harsun kashe shi

Javed ne yayi maganar, jemimah dai ta?i ha?ura, tacika masu kunnuwa da shesshe?ar kuka.

?wan?wasa glass din ?ofar da akayine ya firgitar dasu, arazane suka dago duka a tunaninsu macijin ne Ya daki glass Win, ganin Boss Man yasa suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa Ummi ta mi?e ta nufi ?ofar, ta bude mashi bai shigo ba daga waje Ya tsaya.

 Ina macijin ? Tambayar data fara jefa mashi kenan
Yayi mamakin ganin yadda jikinta ke rawa, har saida yadan saki murmushi ta cikin face mask dinshi
 Haba ummi tsoronshi kike ji kema ?
Ta6e baki tadanyi kafin tace bazaka gane bane, wallahi na firgita macijin yayi girma dayawa
 Ki kwantar da hankalinki, ba maciji bane mutunne nasan ko nayi maki bayani ba lallai ki fahimce ni ba

Zaro ido waje tayi what! Kana nufin mutunne? Tayaya haka zata yiwu ? A rude ta jefa mashi tambayar

 Kodai kana nufin abunda naji unaisa tana faWi gaskiyane? Na cewa Danish ne ya zama maciji !

Jinjina mata kai yai hakane, gaskiya ta faWi

Cikin jin faWuwar gaba ummi tace ni dama najima ina zargin yaron nan ba mutun bane, saboda kyanshi yayi yawa ashe aljanine

Boss yace ba aljani bane, mutunne shi kamar kowa, yanzu bani da isasshen lokaci, zuwa gobe da safe zanyi maki bayani, tsantsar mamakine Ya kamata.

Muryar Jemimah ce tajanyo hankalinshi ga kallonsu Boss man ina genie Wita? Dodon nan ya cinye min ita ko
Shiga cikin Wakin yai, sam sun kasa motsawa suna jin muryarshi sai dai tsoro Ya hana su je gare shi
?aya bayan Waya yake dubansu,
 Dan Allah ku kashe abunnan bamu son ganinshi duk ya firgitar damu parveen ce tayi maganar tana dubanshi
Batul tace boss ina ?an uwanmu suke ne? Bamusan awani hali suke ciki ba
Goya hannayensa yai saman ?irjinshi Yana dubansu
 Basai nayi maku bayani ba, unaisah ce zata faWa maku komai, abunda nakeso daku Yanzu ku kwantar da hankulanku, Ku tashi muje na raka ku Waki ku kwanta kuyi bacci, dare yayi sosai kusan ?arfe goma sha daya da rabi

 Nidai bazan kwanta bacci ba, sai naga genie dita acewar jemimah
Azeeza sarkin tsoro tace bazan Iya kwana aWaki ba, wannan abun zai Iya faWowa Wakin Ya cutar damu
Dama yasan da wuya su iya kwantar da hankalinsu.
Kallon Ummi yai please ki tafi da dasu Wakinki su kwana kafin zuwa gobe idan komai ya lafa, sai su koma nasu Wakin
 Badamuwa, ku tashi mu tafi acewar ummi.

Mi?ewa sukayi daga saman kujerun, matan dake acikinsu, Batul azeeza da jamimah, Boss Yace Ina ?ar uwarku Hannah ?
 Gatanan ?ar?ashin table, sajeed ne ya faWa tare da du?awa ya janyota da ?yar, ta ?udundune kanta kamar kifin gwangwani,.
 Hanna ki tashi ku tafi da?yar ta mi?e tsaye zufa duk ta wanke fuskarta,
 Sannu da jiki boss ne yai mata maganar, sai faman zazzare idanuwanta take Yi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login