Showing 90001 words to 93000 words out of 260999 words

Chapter 31 - KURKUKUN ‘KADDARA BOOK 2 BY BOSS BATURE.doc

muguwar sangartacciyace ta saba tun tana ?ar ?arama duk In za ta yi make up ko zata sanya sutura masu aikin gidansu ne ke taimaka mata, saboda ba ta Iya komai na aikin wahala ba, hatta sanya Wan kunne bata Iyaba wahala take sha, Yau saboda zumuWin zuwan ya ya shureim bata bari wani ya taimaka mata wurin sanya sutura ba, tun tana agaban mirror mai aiki ta ?wan?wasa ?ofar Wakinta ta nemi zinin shigowa, ta tambayeta Ko tana Bu?atar wani abu, tace mata a a taje kawai za ta yi komai da kanta, ashe da rabon tasha wahala.

Gaba Waya saida ta faffasa kayan kwalliyar gaban mirror, bata da natsuwa ko mis?ila zarratin tana da rawar kai da zumuWi, tun daga kan Hoda da ta Wauko zata shafa, Ta sil6e daga hannunta gaba Waya ta tarwatse a saman tiles, garin hodar ya zube, Ta kuma janyo janbaki a tsiyace take murza ma la66anta nan take ya gutsire guntulan Ya faWi ?asa ta jefar da shi, duk kwalbar turaren data Wauka sai ya sil6e ?asa Ya daki tiles kwalbar ta fashe ruwan Ciki Ya tsiyaye, hakan bai dame ta ba, don ta yi asararsu.

Bayan Ta kammala ?an shafe shafenta, bata bi takan kayan da ta faffasa ba, tsallake su ta yi ta nufi tafkekiyar glass wardrobe Winta, daga wajen glass Win kana Iya ganin jerin suturar sanyawarta asha?e tamkar a company, Abayas, shadda atampa leshi, material, english wears, Pakistans, ga jerin Kayan baccinta, komai fa anzuba mata su, shalelen daddy musa

Da hannu ta zuge glass wardrobe Win, Ta ?ura ido tana tunanin suturar da zata sanya don ta burge Yayanta shureim, idanuwanta ne su ka sauka akan haWaWWiyar atampa, yatsun hannunta na kerma ta cafko ta, tana kiciniyar ciro atamfar ai ko gaba Wayan jerin Kayan da ke a gidan tsakiya suka zazzago saman tiles, ko ajikinta, saida ta 6arar da kayan wardrobe Win wurin neman sutura Waya kacal da zata sanya a jikinta, Ga abu a fili ta Wauka tasa shine bazata Iya ba, tafi so saita haukata komai na Wakin tukunna a ?arshe tabar masu aiki da wahalar gyara mata su.

Tamkar zata fashe da kuka, ruwan ido Ya hanata Waukar Kayan da zata sanya don ta burge Yayanta.

 Assalamu alaikum Muryar Waya daga Cikin masu aikin gidan ce babbar mace wadda suke Kira da Tani.

Da sauri Zeenat ta juyo tana kallonta,
 Yawwa Tani, shigo ciki ki taimaka min narasa wasu Kaya zasu dace dani, Inaso ne na burge yaya shureim

Baki asake Tani take bin Wakin da kallo, Sam ba ta yi mamakin ganin yadda Zeenatu ta faffasa Kayan Kwalliyarta da turarurrukanta ba, Halinta ne yin 6arna kamar 6era.

 Haba zeenat, Dubi yadda kika zazzago da ninkakkun Kayan Cikin wardrobe Winki ?asa, sannan kinbi kayan kwalliyarki da kwalaban turare duk kin faffasa su why pls? Harfa larai na turo donta taimaka maki ki shirya a tsanake amma sai ki ka ce mata ta tafi za ki yi da kanki, yanzu kin kyauta abun da ki ka yi ? Cikin kwantar da murya take Yi mata magana.

Zumbura mata Baki Zeenat tayi Nifa bana son faWa, Idan ma na faffasa su ai daddy zai canza min wasu, kuma ai bada gangan nayi ba ko

Girgiza kai Lami tayi haWi da sakin murmushin takaici  Oh, Saboda kinsan daddynki zai siya maki wasu shiyasa kika faffasa su? Ke Baki damu da asarar dukiyar da za ayi ba kenan ?

Bubbuga ?afafuwa Zeenatu tayi fuskarta a tur6une tace Ni ki daina Yi min faWa, Nace maki ba laifina bane kuma in sha Allah zan gyara, pls ki taimaka min In gyara komai kada mommy tazo taga ban shirya ba

GyaWa kai Tani tayi ai dole kam in tayaki gyarawa, idan ba haka ba hada ni zata shafa

?arasa shiga Wakin Tani tayi, cikin ?an?anin Lokaci ta Wauko Parker ta tattara Kayan kwalliyar da zeenatu ta faffasa ta zubar a trash can na Wakin, Ta koma bakin wadrobe din ta soma ninke mata kayan da ta zubar a kasa ta jera mata su a cikin wardrobe, duk tana a tsaye ta ru?e qugu tana kallon tani.

Wani haWaWWan Cord lace ta Wauko mata Red colour anyi mashi adon flower yellow.

 Zeenat wannan zaiyi maki kyau sosai, Red and yellow, kalar farare ce sannan kuma kyawawa irinki

Washe fararen Ha?oranta tayi Jiki na rawa ta sanya hannu ta kar6i kayan da Tani ta mi?o mata, Sai da Tani ta taimaka mata wurin Waura zani da Waura Wan kwali don ba ta iya ba, masha Allah Lace Win Yayi bala en Yi mata kyau.

 Bari na Wauko maki Takalman da zaki sanya Tani ta yi maganar tare da nufar Shoe rack din Wakin, Inda jerin takalman Zeenatu suke na gayu masu tsini da flat, ta Wauko mata yellow kalar head Winta.

Ta dawo ta ajiye mata su agabanta, ta koma ta Wauko Jewelry box dinta, ta Wauko mata sar?ar diamond da earrings, Bayan ta kammala sanya mata su, sai da ta gyara mata make up Win fuskarta.

Ita kanta Tani Kyawun Zeenatu ya tafi da imaninta, Inaga wanda Akayi adon domin shi.

 Kinyi kyau sosai shalelen daddy musa, Muje kitchen Win in shirya maki dinner dinsa ki kai mashi

Ta amsa mata da  Toh

Da?yar take yin tafiya da high hills din ?afarta, Bawai don bata saba sanya takalmi mai tsini ba, sai don rashin natsuwarta.

Bedroom Winta a second floor Yake, ?a ida ne idan zata sauko down stairs sai dai Ta hau elevator saboda a wurinta wahala ne taka bene.
Atare da Tani suka Hau elevator Win ta sauko dasu down, da kwarkwasa take yin tafiya tana taka tiles sautin na bada kwas kwas kwakwas.

Kaitsaye kitchen suka nufa, tun daga Cikin Katafaren palourn gidan kana Iya hangen Masu aikin dake safa da marwa acikin kitchen, a tsakiyar falon ta dakata da yin tafiya.

Tani tace  Bari na Wauko maki Kayan abincin ta ?arasa maganar tare da juyawa ta nufi kitchen, badajimawa ta fito hannun ta ru?e da wooden tray faffaWan gaske, daga saman shi wasu haWaWWun Warmers ne da flatware da sauran kayan abinci

 Anya kuwa zeenatu zaki Iya ru?e tray din nan? Naji da nauyi, ko dai In raka ?i Wakin nashi ?

Girgiza mata Kai tayi a a Zan Iya ki bani kawai mi?a mata tray din tani tayi,
Ta rurru?e shi da hannu Biyu, tana tafiya tana rangwaWa, Tani dake a tsaye ta ?urawa bayanta ido, ita tasan da?yar zata Iya kai shi Wakin ba tare da ta 6arar dashi ba.


?akin da aka warema Dr shureim a gidan baida banbanci dana sarki saboda luxury furniture dake a cikinsa, sam ta manta ba ta tambayi Tani a wani room ya sauka ba, sai faman wurwurga eye balls Winta take yi a ?o?arinta nata gano masaukinsa, Cikin sa a ta hango Waya daga cikin Wakunan dake a rufe ?ofar shi ta buWe hakan na nufin anan aka saukar da shi.

A lokacin Yana a kwance saman katafaren gadon Wakin, Ya cire Jallabiyar jikinsa, Iya short ne fari, ya zame arab turban din kansa, Kwantacciyar sumar kanshi ba?a wulik, ya sanya singlet tabi shape Win ?irjinsa.

Bacci ne ya Wauke shi gefen shi wayarshi ce ajiye yana cikin kallon hotunan abar ?aunarsa bacci yai awon gaba da shi.

 Yaya shureim Wina Muryar Zeenatu ce ke ?wala mashi kira, tun kafin ta ?arasa bedroom Win.

 Ya ya shureim am coming kasancewar tana da za?in murya mai tsiwa har cikin kunnanshi yake jin muryarta.

 Yaya shureim firgigit! ya farka daga baccin haWi da mi?ewa zaune la66ansa na ambaton sunan Allah, idanuwanshi har sun canza launi saboda bacci.

Wakin Yabi da kallo a ?o?arin shi na ya gano ta inda zata 6ullo, sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin shi ga kallon ?ofar Wakin.

Da?yar ta ke tafiya, sai faman zabga murmushi take yi akan fuskarta, tun da ta shigo Waki ta tsayar da blue eyes Winta akan fuskarshi, da ?arfi ta furta hubby na kamar a mafarki shureim ke kallon zeenatu, kamar yau ya fara ganinta sam ya kasa motsawa daga zaunan da yake saman gadon.

Ganin yadda take yin tafiya babu natsuwa yasa shi yin saurin furta bari nazo na taimaka maki maimakon ta dakata da yin tafiyar tun da yace zai taimaka mata, sai ma ta ?ara saurin tafiyar da take yi, a hanzarce dr shureim ya haura ?afafuwanshi ya sauko daga saman gadon sai dai kafin yai saurin zuwa gareta, Cikin rashin sa a takalmin ?afarta ya karkace ai ko Gaba Waya Ta saki tray Win hannunta Ya kife saman tiles kayan abincin ciki duk suka tarwatse, Nan take zanin da aka Waura mata Ya warware Ya zame ?asa, Daga Ita sai Wan pant Winta.

Runtse ido dr shureim yai, ba arzi?i ya dakata da yin tafiyar.

Jikinta sai kerma yake yi, Kunya duk ta isheta muryarta na rawa ta soma magana wayyo Allah na, Am sorry yaya shureim wlh duk zumuWin ganinka ne bansan ya akai zanin ya warware ba, gashi na zubda maka kayan abincin ta yi maganar tana faman yarfa hannayenta, Kunyar duniya ta ishe shi

 Yaya shureim bari na koma Tani ta gyara min Waurin zanin, yanzu zan dawo maka da wani abincin tun da wannan Ya 6are saboda tsabar ruWu Anan tabar mashi zanin da kallabinta da ya warware, da takalmanta, da gudu ta juya ta fuce daga Wakin

A hankali dr shurem ya buWe idanuwanshi Yana kallon 6arnar da Zeenatu tayi mashi, rashin natsuwar yarinyar ba ?aramin burge shi yake yi ba, Saboda yana samun nishaWi sosai, tsabar shiririta ita da tace za taje a gyara mata zani ta tafi tabar zanan a ?asa.

Yaushe rabon da ya yi dariya irinta yau harya manta, Hada dafe cikinsa tun da zeenatu tabar Wakin bata ?ara dawowa ba saboda Kunya gare ta, kamar ba jinsin turai ba, Tani ce tazo Wakin ta bashi hakuri game da 6arnar da zeenatu tayi mashi yace mata bakomai ai yarinyace yana yi mata uziri, Bayan tani ta kwashe kayan da ta 6arar mashi, Ta koma kitchen ta canzo mashi wani abincin ta dawo ta kawo mashi, kafin Tani tabar Wakin sai da ta tattara kayan zeenatu da ta bar masa zaninta da Wan kwalinta da takalman duka ta kwashe ta fuce da su, dr shureim yaso ta dawo suyi fira sai dai yasan abune mai wuya ta bari su ?ara haWuwa yau sai dai zuwa gobe idan kunyar ta sake ta.

*PRISONERS MIDDLE STEP=؋?d'*

?arfe 7 na safe agogan San antonio ta buga, adai dai lokacin Sojojin sun zo duba marasa lafiyansu daga headquater, mutun uku ne Commender, Major, tare da Captain sun zo cikin shigarsu ta kaki, A office Win dr. Laura davis suka fara zama domin tattaunawa.

A6angare Angel tana ?udundune cikin bargo tasha baccinta, sai mutsu mutsu take yi duk ta yamutsa bedsheet Win ga dukkan alamu mafarki take Yi, A firgice tafarka HaWi da yakice bargon ta wurgar da shi gefe Waya, hannayenta biyu saman fuskarta, cikin sha?a??ar murya take ambaton sunan Danish, Mummuna mafarki tayi akanshi Ya farka Ya rikiWa ya zama dodo Yana shan Jinin mutane, Hankalinta duk yabi ya tashi hai?am gani take kamar mafarkinta zai iya zama gaskiya.

Ta yi zurfi acikin tunaninta muryar Nurse ta Fargar da ita
 Barka da safiya Masoyiya Angel, fatan kin wuni Lafiya da sauri ta Waura idonta kan fuskar nurse Win

In a cool voice ta amsa mata Lafiyalou

 How are you feeling today? Are you experiencing any pain? girgiza kai Angel tayi A a
 Okey, nasan zaki bu?aci shiga toilet, ki gyara fuskarki, akwai sojoji da suka zo suna son ganawa dake, Amma kafin nan Zan kawo maki breakfast Winki ko kina da za6i na abunda kike son ci ?

Girgiza kai Angel tayi a a
Okey daga haka Nurse Win ta juya ta fuce, Saukowa tayi daga saman gadon abakin ?ofar shiga toilet ta zura slippers dake ajiye saman carpet, kafin ta tura door din ta shige ciki.

A hankali take tafiya tana bin ko ina na toilet Win da kallo A tsaftace yake fari ?yal Kamar ba a ta6a amfani da kayan Cikinsa ba.

Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples Winta biyu suka lotsa, yatsun Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba ?aramin kyau za su yi ba, fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha awar son Yin alwala, nan take ta canza ra ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet Win tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? BuWe ?ofar da akayine yasa ta Wago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ru?e da tray na kayan breakfast Win Angel asaman table ta Waura mata shi.

?agowa tayi suka hada ido da juna Is there anything you need?

Da sauri tace Hijabi da abun sallah inaso zanyi
Da murmushi akan fuskar nurse Win tace are u muslim ? ?aga mata kai Angel ta yi alamar eh, nurse Win tace Okey, ki jira ni yanzu zan dawo

Fuce wa tayi daga Wakin, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tana ?are ma Wakin kallo, shigowa nurse Win tayi hannunta ru?e da hijab da Prayer mat ta mi?a mata, Farin Ciki a wurin Allah bakinta ya?i rufuwa.
 Thank u so much nurse Win na murmushi tace da ita never mind ita kanta batasan Ina ne al?ibla ba, sai da ta tambayi nurse Win tayi amfani da wayar hannunta wurin yi mata bincike ta gano mata Al?iblar da zata fuskanta tukunna ta shimfiWa carpet Win, a tsanake ta kabbara sallah, saman chair nurse din ta zauna tana jiranta, Raka a Biyu Angel tayi kafin ta sallame sallar, wani irin daWi take ji yau tayi sallah, bakinta ya?i rufuwa, tafin hannayenta biyu ta Waga sama tana karanto addu o kirari tafara yi ma Allah kafin tayi ma ?an uwanta da suka rasu addu a, da su kansu a ?arshe ta ro?i Allah akan Ya haWa ta da ?an uwanta ba tare da ta sha wahala ba, Allah yasa daddynta Yana araye, da auntynta Aneelerh. bayan ta kammala Yin addu ar, Ta shafa a fuska, ta yun?ura ta mike, ta nannaWe prayer mat Win da hijabin ta dubi nurse Win

 Kin gama Waga mata kai Angel tayi alamar eh, Mi?ewa tayi tare da zuwa gaban angel ta kar6i carpet din da hijabin juyawa tayi ta nufi closet Win Wakin ta buWe ta sanyasu aciki.

 Aduk lokacin da kika bu?aci yin ibadarki zaki iya Wauka ki yi godiya Angel tayi mata, daga bisani ta zauna zaman Cin breakfast, lafiyayyan kalaci aka haWa mata, tana ci tana tunane tunane sam tamanta da sojojin dake jiranta.

Sai da ta kamalla cin abincin ta ?oshi, Nurse Win ta tattara komai ta fuce dashi, Zama tayi gefen gadon idonta akan ceilling ta ?urawa haWaWWen kwan Wakin ido, Yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru.

Ba zato ba tsammani ta tsinkayi muryoyinsu a yayin da suke shigowa Wakin, A hanzarce ta mi?e tana faman zazzare gray eyes Winta akansu, sojojinne tare da likitocin, saman doguwar sofa Win Wakin suka zauna a jere suna fuskarta, Dr Laura davis ta zauna gefenta, Kamar wata mara gaskiya duk ta kama kanta, Hankalinta ba ?aramin tashi yai ba.

 Masoyiya Allah fatan Kin wayi gari lafiya? Ya jikin naki muryarta adabarbarce tace da sau?i sosai cikin kulawa suke Yi mata magana da harshen turanci

Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana mun nemi jin bayani daga bakin Wan uwanki Gabriel sai dai bai bamu haWin kai ba, Yace duk abunda muke son sani ke ce zaki amsa mana.

Jin wannan maganar yasa hankalinta ?ara Wugunzuma.

Fahimtar yanayin ta ne yasa dr mark cewa Ki kwantar da hankalin ki, Bamu zo da niyar mu takura maki ba, ?an tambayoyi ne zamuyi maki da zarar kin amsa mana zamu tafi, munfiso ki natsu kiyi nazari kafin ki amsa mana

 Kin shirya ? ?aga mashi kai tayi alamar eh, duk tabi tasha jinin jikinta.
 Da farko zamu so ki fada mana Ya akai kuka tsinci kanku A daji? Waye ya kai ku can? Sojojin kasar mu suna hasashen Wan Ta addan daya gudu zuwa canne Yai garkuwa daku don ya kare kanshi daga farmaki da suka kai mashi, shin dagaske ne ko kuwa? ?ura masu ido ta yi Waya bayan Waya take kallon fuskokinsu, tsabar fargaba ?an hanjin cikinta sai kaWawa suke Yi, Tarasa Tayaya zata fara basu amsar tambayarsu? sam ba ta jin zata Iya faWa masu ainihin Abunda Ya faru da rayuwarsu, ita aganinta kamar idan suka ji zasu guje su ne, musamman idan Danish Ya farka a matsayin giant ba ?aramar masifa zaija masu ba, Zaiyi wuya su yarda da abunda zata faWa masu, saboda Labarin ba?ar izayar da suka sha a prison ba kowane zai gasgata kalamanta ba, zama su Iya tunanin ?arya take yi masu, bayan haka tana tsoron ta fada masu, su kuma su tara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login